Free chapter ยท Read without an account

61-62

by ๐™ฝ๐š˜๐š˜๐š›๐™ธ๐š–๐šŠ๐š— ยท Rayuwar Faheemah

๐Ÿ‡๐Ÿ‡RAYUWAR FAHEEMAH๐Ÿ“๐Ÿ“



_by NoorEemaan_ ๐Ÿ“šโœ๏ธ



Wanna littafin kyautane( free novel)



***


Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




when you truly care for someone, their mistakes never change your feelings because it's the heart that get angry but the heart still cares. โœŒ๐Ÿ˜




61-62


(Not edited)



Gaba daya yan falon cikin mamaki suke, suka shiga bin su da kallo, amma sam wandan da suka san dangantakar dake tsakanin Faheemah da abbuh basu yi wani mamaki ba, yayinda Mami da jameela suka shiga wani hali wanda kai tsaye ba zaka fassara su ba, musamman Ganin yanda faheemah tayi mugun kyau ta murje abunta, mahaifin umaimah mai suna Yakub kuwa tambayar kansa yake a ransa cewa yaushe Fu'ad Yayi aure bai sani ba? domin iya tunanin sa Fu'ad na tareda Lalurar paralyze yaushe ya warke be sani ba?



"Abbuh kada ka kuma barina, kada ka kuma juya min baya, ka yafe min idan na bata maka rai, kada ka kuma kin amsa gaisuwata, kada ka ki bani kulawar ka please abbuh na" ta fada tana sake k'ank'ame shi sosai yayinda hawaye ke zuba a idanunta tamkar an balle famfo.



Hawaye ne masu zafi suka sauka a idanu abbuh, sai ma yanzu yake komai ke dawowa masa dangane da shariya, hantara, kyara, daya aikata ga faheemah suka shigo dawowa kwakwalwarsa a yau... Shima Kara rungume ta Yayi sosai hadi da cewa


"kiyi hakuri diyar abbuh'n ta, ki yafewa abbuhnki kinji, hakika ban rike amanar umminki haleema ba, amma ina mai tabattar miki bansan dalilin yin hakan ba, ban ma san nayi ba"



"nina sani kuma nice sila" suka ji saukar muryan Mami ya daki dodon kunnen su.


Gaba-daya yan falon da suke sharar kwalla tausayin Faheemah dama abbuhnta suka yiwa Mami kallon mamaki banda hajja hindu dama jameela da ta san wasu Daga cikin mugun tan da mami tayi.


Ahankali Faheemah ta kalli mami hakama abbuh fuskar ko Wanne da neman karin bayani zama Abbuh yayi domin tsayuwar ta fara gagarar sa, Faheemah kusa da abbuhnta ta zauna hadi da dora kanta a kafadar sa, Fu'ad da tun shigowar su bai zauna ba ya nemi gefen ummu ya zauna tausayi heemahnsa fal ransa yayin da wani mugun tsanar mamin ya sake darsuwa a ransa.



"Na sani ni din muguwa ce, mai raba soyaayar ya da uba, a yau banda mafita daya fi in tona asirin kaina, amma wallahi nayi nadam...."


Wata tsawa mummyn zaynab ta daka wa mamin kasancewar ta mai sauri fushi kuma bata daukan raini musamman da maganganun mami ya soma karyan ta maganar Faheemah na cewar tabi saurayi sun gudu..



" ki fito ki fada mana Kawai ki daina jan magana" hannun mummy zaynab mijinta ya kamo alamun rarrashi domin yasan halin matarsa sarai tana da hot temper.



Mik'ewa Ummu tayi, hadi da yiwa fu'ad da fareesa ido akan su tashi, cikin kamilalliyar muryar ta tace "am... bari mu baku waje idan kun gama zamu dawo domin wanna maganar family issue ne"



"A'a a'a hajiya ku dawo Ku zauna dan Allah, domin wanna maganar har daku za'a yi mun zama daya, tun da kuka rike mana diyar mu bisa amana ai babu wata boye-boye atsakanin" mu cewar kawu anas.


Ummu bata ce komai ba ta koma ta zauna haka ma su fu'ad.



Wani yawun tsoro mami ta hadiya kana cikin cracking voice ta soma cewa "ni ce naje wurin boka ya raba soyaayar faheemah da abbuh'n su tare da taimakon hajja hindu"


Zaro ido sukayi dukkansu cikin kad'uwa da mamaki!



Nan ta shiga basu Labarin komai tiryan tiryan ko tsallake bata yi, daga muguntar data gana wa mahaifiyar faheemah, zuwa duk wahalar data bawa Faheemah, har ma zuwan ummu gidan, da zuwan mummy zaynab da irin karyar da ta yi cewa tabi saurayi sun gudu, da raba tsakanin Faheemah da Fu'ad da suka so yi ita da Hindu domin ko waccen su so take yarta ta auri fu'ad din har zuwa gidan boka da mutuwar wulakancin da Yayi har izuwa hatsarin dasuka yi....





Gaba dayan dakin ya kaure da Kuka hadi da mamaki irin mugunta, son zuciya, ko suke son duniya irin na mami... cikin kuka mai taba zuciya faheemah tace "mami why! Why!! Why!!!! Mami? Meyasa baki cigaba da dukana ba? Meyasa baki cigaba da bani aiki ba? Meyasa baki cigaba da gana min azaban ba? Domin zan jure hakan akan raba ni da abbuh na da kika yi tsawon shekaru, daman abunda kike nufi da ALHAJI YA MANTA WACECE NI kenan" ta karasa tana fashewa da kuka mai taba zuciya, gaba-daya tayi mugun fita a hayyacin ta.


A karon farko a rayuwa da Mami da taji tausayin faheemah, lallai a yau an kai faheemah bango tunda har da iya bude baki tayi wa mami wadannan tambayoyin, domin bata taba yiwa wa mami magana irin wanna ba, saboda tsananin hakurin ta.


Tabbas ta cutar da ita da yawa ita kanta ta san da hakan, sai dai son kai, da son zuciya hadi da tsantsar mugunta ya rufe mata ido. " ki yafe min faheemah, nasan ni mai laifi ce babbba a gareki, na cutar da ke na cutar da umminki a zamanmu, gashi bata duniyar bare in nemi yafiyar ta, kaico nah da son duniya irin nawa, gashi bai amfane ni da komai ba, ku yafe min dan Allah, kalli Allah ya yi miki sakayya tun a duniya Faheemah, nayi hatsari na rasa hannu daya da kafa daya, hajja Hindu ta rasa hannu, a dallilin son duniya irin nawa yar'uwarki Jameela tayi ciki kuma saurayin ya gudu, har da alhakinki ne yake bibiyar mu"


Sai yanzu faheemah da ma sauran wandanda basu sani ba suka lura da hannu da kafar mami hakama hannu hajja Hindu, ihu hadi da salati Faheemah tayi tana boye fuskarta a jikin abbuh domin yanayin hannu da kafar mamin yayi muni, ita ma faheemah Kuka take sosai, lallai mami tayi nadama ita ta kira anty Jameela da yar'uwarta ayau, ita ke mata magana cikin sanyi murya ba kyara, ba hantara, ba zagi? duk ta ayyana hakan a ranta tana shirin bude baki tayi magana taji muryan abbuh...



"Nagode miki kwarai da irin sakayyar da kika min hajara, banda abun da xan ce miki, domin tun avduniya kin fara girban abunda kika shuka, waya sani ko ke kikayi sanadiyyar mutuwan matata?" Abbuh ya fada wani daci ya cika bakin sa.



Ai kuka mami tafara tace "alhaji wallahi tallahi ban taba kisa ba, ka yafemin, duk da bana da imani amma bazan iya kashe rai ba, duk da bana shiri da haleema a zaman da mukayi, amma bazan iya kashe ta ba, hajja Hindu ke gaya masa wallahi ban kashe ta ba".


*(Illar mugunta ko wani hali Mara kyau kenan domin koda Baka yi Abu ba za'a ce kayi, domin mugun halin zai iya sawa mutane suyi tunanin kai ka aikata )*


cikin kuka itama ta fara tonon asirin kanta, ciki har da asirin data yiwa baban umaimah ( yakub) saboda irin kulawar da ta ga yana bawa ya'yan Wansa a lokacin da mahaifin su fu'ad ya mutu, saboda daman tana matukar jin haushin ganin su Ummu sun fisu arziki, kana ta sanar dasu cewa ita ta bawa umaimah karfin guiwan xuwan gidan akan ta raba su faheemah da Ummu, domin ita umaimah tasamu ya aureta sai ta kare da cewa "alhaji kuyi hakuri har da laifi na da gudunmawata a wahalar RAYUWAR FAHEEMAH kuma wallahi ba ita ta kashe mahaifiyar faheemah ba domin har shawaran hakan na bata ta ki, nice nan na nuna mata gidan boka, Ku yafemin dan Allah. Baban umaimah na tuba na yi nadama"


sallallami da koke -koke ke tashi a dakin...


*(duniya ina zaki damu ne? Mutuwa ake a kullum amma mutane basa tunanin komawa ga Allah, wasu mutane sun dauko xasu dauwamma ne a gidan duniya! Ga dai mami da hajja Hindu ce ta nuna mata hanyar bata, amma sai ya zamana ita mami tana neman fin Hindu yin mugun tan. Ya Allah! Kasa mufi karfin zuciyar mu ka tsare imaninmu ameen)*.



"Bazan iya zama dake ba hajara, domin ban san wani muguntar kike shirya mana nan gaba ba Dan haka na...."




"Dakata abubakar! idan hankali ya bata, hankali ke nemo shi, yanzu idan ka rabu da da ita me aka yi kenan? Ta tuba tunda ta tono asirin kanta da kanta, matukar na isa da kai, ka kuma daukeni uba toh kada ka rabu da ita".


Shiru abbuh yayi domin kawun ya masa komai a rayuwa baya jin zai iya yin butulci ga kawun"



Shima Baban umaimah dage wa yayi zai rabu da da Hindu domin cewa yayi ita din masifa ce ga ahalin sa, ita din mai bata zumunci ce, kawu da Malam iliyasu ne ke basu baki hadi da yi musu nasiha musamman akan hakuri da yafiya.




Ganin hakan yasa mahaifin mami bai ce komai ba, domin yayi tunanin cire ta a sahun y'ay'an sa domin ta aikata abun Allah wadai, sai dai tunda wandanda tayi wa sun hakura yasa shi yin shiru, amma tabass yaji haushin halayenta kwarai kuma zai mata hukunci personal a matsayin shi na uba....








Share and comment




Thanks for reading

# rayuwar FAHEEMAH


Noor Eemaan๐Ÿฅ€๐ŸŒธ





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.