Free chapter · Read without an account
3-4
by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · kyautar koda
🍇🍇KYAUTAR KODA🍓🍓
(Its all about love, sacrifice, hatred and destiny)
_by Noor Eemaan_📚✍️
Wattpad
@NoorEemaan
***
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
Page 3-4
A nutse suke tafiya kan shimfud'ad'iyyar kwalta reras gwanin sha'awa, yayinda wasu mutanen ki bin had'add'u kuma tsad'add'un motocin da kallo.... yayinda budurwar nan take kallon titi ta cikin glass din motar, amma a zahiri ba kallon motocin dake ta wucewa a kan titi take ba, tunani mai zurfi take, tana tunanin waye wanna daya iya zana fusk'ar ta haka tsaf, abin ya kasa barin zuciyar ta da ma k'wak'walwar ta....
★ Unguwar *ikoyi* suka nufa, unguwa ne masu hannu da shuni domin babu gidan marasa hali a unguwar, domin talaka bazai iya siyan ko hayan muhalli a unguwar ba.
Babban estate din motoci ke ta shiga, duk yanda baki zai kwantata estate din abin zai faskara, sai dai wanda ya ganewa idanun sa kawai. Domin girman estate din zai iya yin girman wani karamin unguwa, Had'add'en gine ne tamk'ar a turai, domin a turan ma ba ko ina bane za'a samu irin wanna estate din...
Bayan sun gama d'aidaita parking motocin kana dukkanin su suka fito, daya daga ciki ya buɗe mata mota cikin girmamawa,... har kofar da zai sada ta da bangaren mahaifiyar ta suka rakota kana suka juya cikin girmamawa suka koma.
Shigar ta cikin had'add'en falon, yayi d'aidai da tahowar wata K'yak'yyawar mata da zata yi shekaru arba'in da biyar a duniya, wanda idan ka ganta zaka dauka cewa bata fi shekaru talatin da biyar ba saboda kyawun jikinta, tana matsakaicin jiki, yayinda take da tsayi babu laifi, kallo daya zaka yiwa matar ka hango jindadi, Hutu, hadi da kwanciyar hankali a tare da ita.
Murmushi matar ta sakar mata kana tace "welcome back sweetheart, ya gajiya?"
Martani murmushi ta mayar wa matar kana tace "Thank you Mommah na" hadi da bata kisses a kumatun ta biyun.
Riko ta matar ta yi tamk'ar wata yarinya karama ta zaunar da ita kan daya daga Cikin had'add'un royal chair kana tace "bari na zuba miki juice ki sha" murmushi kawai tayi tana bin Mommah'n ta da kallo, bayan Mommah ta dawo ta zauna ta sanya mata juice din a baki bata wani sha da yawa ba ta janye bak'inta, "sweetheart!" Mummy ta kira ta, dago kanta tayi ta kafe su kan Mommah ba tare da ta amsa ba.
Cikin serious tune tace "fadeelah meye damuwar ki, you re not looking okay?"
Budurwar nan mai suna fadeelah tace "ba komai Mommah, ina son hutawa ne kawai" ta fad'a tana sakar wa Mommah murmushin k'arfin hali.
Ita ma Mommah murmushin tayi ta riko hannunta, har part dinta ta rakata sai da ta tabbatar ta kwanta kana ta fito, tana ganin fitar Mommah ta sake bud'e cardboard paper'n nan, take zanen ya bayyana, kurawa zanen hoton ido tayi, tunani masu yawa na zuwar mata, ta gyara kwanciyar yafi sau ba adadi, domin babban burinta a yanzu ta ga waye wanna daya iya zane fusk'ar ta tar tar babu ko mistake, ta duba ta ga ko akwai sunan sa ko number'n sa a kasan zanen kamar yadda masu zanen kan saka, amma babu...
*** *** *** ***
Kwance matashin nan mai zane yake kan cinyar wata mata mai kimanin shekaru hamsin a duniya, sosai take da k'yau domin bazaka yi tunanin ita ce mahaifiyar wanna saurayin ba, saboda bambamcin kalar fatar su, domin baki ne shi irin black beauty din nan yayinda matar ta k'asance fara sosai duk da cewa kalar fatar ta ta dan dishashe sak'amak'on halin babu da suke fama dashi, domin kallo daya zaka yiwa gidan ka tabbatar da hak'an...
"Fadeel my son, lafiyar ka kuwa tun jiya na kasa gane kanka, na kuma tambayeka kace babu komai, shin kana da kowa a duniyar nan da zaka iya raba damuwar ka da shi baya ga ni ummin ka?"
Ta tambayeshi cikin tsananin kulawa yayind'a hannun ke kan gashin sa tana shafawa har yanzu.
Cikin son mahaifiyar sa yace "Mahmah... na fada soyaayyar wata yarinyar" ya karasa yana sauk'e numfashin idanu sa a lumshe yana tuno kyakyyawar fusk'ar ta, murmushin ta, tsarin jikinta da ma dukkanin wani abu daya dangance ta.
"Oohh ya rabb! Fadeel da gaske kake? Yau da kanka kace kana son wata? Gaya min ka sanar da ita? A wani unguwa take?" Mahmah ta yi masa tambayar cikin zallan farinciki da zumudi.
"Ooh Mahmah relax, shiyasa bana son baki labari sometimes fa" ya karasa yana murmushi.
"Bazaka gane ba son, tun yaushe nake cewa ka samo budurwar ka ki, yau kuma ka sanar dani kace bazan yi farinciki ba?" sai k'uma yanayin ta ya sauya a take
Cikin damuwa yace
"lafiya Mahmah?"
Hawaye ne suka ciko idanun ta tace "ina son ganin kayi aure ka tara zuri'a, inason ganin jikokina daga tsatson ka, kai kadai na haifa, kuma ina alfahari da kai, domin daya kake tamkar da dubu, damuwa ta shine idan ma auren ya taso ina muka ga kudin da za a yi hidimomin biki? Ni da kai mun sani cewa kullum cikin babu muke sai godiyar Allah"
Jikinsa ne yayi sanyi d'omin baya kaunar ganin Mahmah cikin damuwa sam, da yana da iko daya cire wanna damuwar, sai dai babu yanda zai yi, ƙaddarar su ce hakan, cikin sanyin muryar sa yace "Mahmah wanna dalilin ne yasa na kasa kowa miki suruka d'omin bazan iya tukarar kowacce mace a haka ta saurare ni ba, d'omin yawancin yanmmatan yanzu are after Money not Love, sannan ita wanna yarinyar ban ma san sunan ta ba, balle gidan"....
SHARE✔
VOTE✔
COMMENT✔
EDIT❌
shhhh!🤫 Ƙarku ce update yayi kadan🤒 just manage 😘
NoorEemaan
***
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851