Free chapter · Read without an account

67-68

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · kyautar koda

🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓

(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)




*WATTPAD*

@NoorEemaan










*** amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWED❌




No editing🤒





Page 67-68


........Wani mugun ƙara mai hade da Salati fadeelah ta saki, kana ta shiga kuka mai sautin gaske gwanin tausayi, fadi take "fadeelah don't do this to me, Ka dawo, ka dawo please kada ka min haka, ka dawo mu rayu tare ko da baza mu haihu ba, bazan iya juran rasa ka ba, wanna aikin na da matuƙar hadari, ka dawo please Fadeeeeeeeeeeel" ta kara sa tana zubewa kan gadon ta shiga rera kuka gwanin tausayi, ta jima sosai tana kukan domin ta fi awa d'aya, har idanun ta ya fara yaji sosai ko bud'e su bata iya wa, sosai zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta.






Haka ta kasance har karfe hudun yamma, sallar azahar da la'asar ma a zaune tayi ta, domin ko k'arfin tsayuwa bata da shi, tun safe bata sa komai a cikinta ba, minti d'aya biyu sai kaga hawaye ya balle mata gwanin tausayi...





bayan sallar ishaq ta ga yunwa na kokarin yi mata illa sannan ta rarrafa bakin hada'dd'en medium size fridge ta dauko yogurt mai mixed fruit, bakin ta na rawa haka ta kafa baki ta sha sosai fiye da rabi, kana ta dire robar a gefe tana sauke numfashi tamkar wacce tayi tseren gudu....




Ta kai mintuna goma a zaune cikin mayuwancin hali kana ta Mike da kyar ta koma kan gado...




Sosai wani mugun sanyi ke shiga jikin ta, gashi dama bata saka kaya ba, domin tun towel din safe shine har yanzu a jikinta, haka ta yi ta zumbula yalwataccen hijab take sallar da shi...




Da kyar ta ja duvet bedsheet ta rufe jikinta da shi tana sauke huci da numfashi irin na masu zazzabi....




Ta bangaren masu aiki kuwa sosai sukayi mamakin ganin su Fadeelah basu taba abinci safe, rana, bare na dare ba, domin basu da matsaniƴa kan Fadeel baya kasar, gashi Fadeel bai bawa ma'aikatan sa damar shiga part part din gidan a akodayaushe ba, musamman bedrooms din.


rashin taɓa abincin ya dan basu tsoro amma sai suka dauka ko basa gidan ne, domin sun san waye Fadeel ya kan fita wani zubin bai sanar da su ba, musamman idan ba lokacin aikin su bane, domin a Cewar sa baya son shiga hakkin ma'aikatan sa ...







*WASHEGARI*


Har yanzu fadeelah bata bar kukan ba, sai ma abinda ya karu, domin fadeel ya sabar mata kwanciya a jikin sa musamman d'addare, hakan yasa ta ga daren jiya yayi mata nisan gaske...





Wanka tayi da kyar, tayi brush kana ta sanya wani palazzo trouser da wata riga daya zo mata guiwa, wanda bai kamata ba, sai tayi rolling da black Veil, wani flat palm sandals ta sanya a kafarta, komai a sanyaye take yin sa, amma hakan bai boye kyan ta ba, wani babban sunscreen (glass or tabarao) ta saka a fuskar ta domin ya boye kumburin fusk'ar ta....





Waje ta fita, sosai tayi kokarin danne hawayen ta, nan ta tarar da tarin ma'aikata, security, hadi da escort din sa, wasu a tsaye wasu a zaune, wasu na zaga gidan domin tabbatar da tsaro....






Cikin girmamawa suka shiga gaisheta, amsawa tayi tana kokarin k'ak'aro murmurshi, tun kafin ta isa wajen har sun bud'e mata kofar wata had'add'iyar *Mercedes Benz* ash color domin ta shiga...




Kallon wanda ya bud'e motar tayi, tace "ku barshi zan fita ni kadai karku damu"




Kansa a kasa cikin girmamawa yace "sorry madam, bazai yu ki yi tuki ke kadai ba babu tsaro, domin yallabai ya ja mana kunnen kan hakan tun washegarin ranar da kika tare, please ki yi hakuri ki barmu muyi aikin mu kamar yadda boss din mu ya bamu umarni" Ya karasa cikin tsantsar ladabi.





"ok fine" fadeelah tace tana zama cikin motar a sanyaye, yayinda sauran suka fada sauran motocin domin bata tsaro, a jere reras suka bar gidan, "estate dinmu muka nufa" abinda tace wa driver kenan ta lumshe idanun ta Yayinda hawaye masu zafi suka ciko Idanunta ta, tsananin kewa da tsoron rasa shi ne suka yiwa zuciyar ta kawanya....






Jin tsayuwar motocin ya tabbatar mata da sun iso estate dinsu, cikin hikima ta share hawayen ta, kana ta daidaici muryarta tace wa driver'n daya tuko ta su tafi idan zata dawo bodyguards din estate dinsu zasu dawo da ita, cikin girmamawa ya amsa, already an riga an bud'e mata kofa, hakan yasa ta sanya kai ta fita....





Sosai ma'aikatan gidan suka gaishe ta, kowa fusk'ar sa dauke da murmushi da farincikin ganin ma'am dinsu da ta san darajan mutane, sosai ta dinga sakar musu murmushin yake domin bata son kowa ya fahimci halin damuwar da take ciki...






Part din Mommah ta nufa, tana daf da shiga Parlon mommah ta ga kukun Grandma to zo fita, hakan yasa ta tsaya suka gaisa kana matar ta dora da fadin "ya muka ji da asaran da mai gida yayi, toh Allah ya tsare gaba ya kiyaye"





Sosai zallan mamaki ya kama fadeelah, wani asara kenan Daddy yayi? Ta aiyana a ranta, amma sai bata nuna ba tace "Alhamdulillah"




Cikin sauri ta nufi part din Mommah, cikin wani sabon tashin hankali, ta kuwa tarar da Mommah zaune, tare da Daddy...




Cikin sauri ta fada jikin Daddy tana saukin wani kuka mai dauke da abubuwa da dama... Cikin tashin hankali mommah da Daddy suka hada baki wurin fadin




"Subhanallahi! Sweetheart, princess, meya faru?"







Wani kuka mai sautin gaske ta kara saki tace "Mommah! Daddy! Fadeel ya...ta...fi...ya barni"





"Innalillahi! ya tafi ya bar ki, zuwa ina?" Mommah ta fada hankali a tashe, gabanta na fadu'wa, sak'amak'on bata san amsar da Fadeelah zata basu ba...




Sai da Fadeelah ta saki wata sheshek'ar kuka kana tace "y...ya...ta..fi....a Sanja masa jinin sa zuwa wani blood group din, domin shima blood group din sa SS ne"





"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" suka fada hankali a tashe, domin sun san had'arin dake cikin aikin, duk da sun san cewa fadeelah SS ce, amma basu taba tunanin shima Fadeel din SIKILA bane sak'amak'on yana da ginanan jiki, ga kuma yanda bikin yazo, hakan yasa babu wanda hankalin shi ya kawo kan suyi blood group test irin wanda ma'aurata masu son mallakar junansu ke yi yanzu...






Daddy kasa magana ma yayi, domin sabon nadama, da kaunar Fadeel din ne ya rufe shi, tabbas Fadeel na matuk'ar son gudan jinin sa, tunda har zai iya zuwa a cire masa jinin sa kaf a sanya masa wani, duk da yasan hadarin dake cikin aikin, ya kuma godewa Allah da Fadeel ya kasance cikin ahalin sa, domin samun kamar sa a wanna al'ummar tamu da wuya, haka kuma rasa shi a Al'ummah babban rashi ne.






Mommah kuwa sosai ta dinga taya fadeelah kuka, domin wanna maganar da Fadeelah ta zo musu da shi ya shige ta matuk'a.






Duk jikin su a sanyaye yake, ga kukan fadeelah yaki karewa sannan suka hau lallashin ta hadi da kalamai masu kwantar da hank'ali, Shiru tayi lamo jikin Daddy tana sauke numfashi, sosai suka tausaya mata, Daddy ya kuma ji dadi da Fadeelah ta samu muradin ranta (fadeel) da bai san halin da zata shiga ba, domin rashin ganin sa kadai ya sa ta shiga wanna halin, ina ga bata mallaki shi ba?...





"Daddy wani asara kayi naji kukun Grandma na mun jaje?" fadeelah ta katse masa tunani da muryar kukan ta...




Daddy bai so ta sani ba, domin kada hankalin ta ya tashi, amma yanzu dole zai sanar da ita, saboda zancen duniya bata 6uya...





Nan Daddy ya shiga sanar da ita dalla² daga asarar da yayi, wa'azajin mommah a gare shi, da zuwan Fadeel gidan, hadi da uban kudin da Fadeel ya bashi, komai dai ya sanar mata.





Ai fadin zallan mamakin fadeelah da farincikin ta bata lokaci ne, taji dadi da Daddy ya gane gaskiya, ta kuma yi mamaki kwarai da Fadeel ya bawa Daddy zunzurutun kudi amma ko sanar mata bai yi ba, in fact batama san cewa yazo estate din su ba...





Sosai ta nuna mamakin ta, wanna hakan ma ya bawa su Daddy mamaki ganin bai sanar wa fadeelah uban kudin daya bayar ba, sosai hakan yasa Fadeel kara samun waje a zuciyar su, tabbas da za a samu masu kyawun zuciya irin na Fadeel a al'ummah da an samu cigaba sosai..





Haka dai suka Shiga lallashin fadeelah har aka samu bacci ya dauke ta kan cinyar Mommah, domin duk maganar nan da suke hawaye ke zuba a Idanunta....




*****************





*AMERICA*


Hada'dd'en asibiti ne mai girman gaske, gabadaya ma'aikatan su farare ne, ma'ana masu jajayen kunnuwa ne, ko wannesu sanye da uniform farare kal, yayinda majinyacin su ke saka light blue...





Kwance Fadeel yake babu riga ko daya a jikinsa, sai wani kyalle fari da aka rufe al'auran sa da shi, yayinda wasu wayoyi masu yawa ke manne a duk wata gaɓa ta jikinsa inda jini ke yawo, an ɓula duk wani maguɗanar jini dake jikinsa an saka wayoyi a a ciki, ta nan jinin ke shiga jikinsa.


ga jini masu yawa leda-leda rataye kan wasu karfuna a tsaye irin na karin ruwa nan, luckily cikin kudirar Allah aka samu blood group O+




A yanda yake kwance zaka dauka matacce ne, domin baya motsi, banda zuciyar sa dake bugawa babu abinda ya bambam ce shi da matacce...





******************************




NIGERIA (LAGOS)


*Bayan watanin goma sha daya*


Fadin tashin hankali da damuwar fadeelah bata lokaci ne, kuka kuwa shine abokin hirar ta, sannan hoton zanen Fadeel dake part dinta shine abinda yake debe mata kewa.




Bata taba tunanin fadeel zai dauki wata uku bai dawo gareta ba, amma gashi yanzu 11month babu amo babu labarin sa, tun su Mommah na lallashin ta har suka zuba mata ido, domin suma abin ya fara damun su jin Fadeel din shiru, gashi sun sa anyi bincike har yanzu ba a gano asibitin da yake ba.







Ta bangaren ma'aikatan gidan da escort din sa kuwa, suna ganin alert duk wata hakan yasa basu damu ba, domin a tunanin su wata tafiya mai muhimmanci sukayi domin fadeelah bata koma ba, a cewar ta bata amfanin zaman gidan ba babu gwarzon ta a gare da ita, dama kuma fadeel ya kai albashin ma'aikatan sa na tsahon lokaci banki, duk da bai san tsahon lokacin da zai dauka ba, amma sai da ya kai kudi masu yawa wanda kowa zai samu albashi har na shekara daya da watanin, kana ya bada account number din kowa yace duk wata ana biyan su, zai bar kasar zuwa wani lokaci, kasancewar da bank din yake amfani hakan yasa ma'aikatan na samun salary dinsu duk wata....





*************



Sosai Fadeelah ta dawo so silent babu hayaniya, domin idan ba hirar Fadeel Mommah ko Daddy zasu mata ba, bata magana da kowa, sosai suke tausaya mata, domin ita ba jiki ba dama, gashi kuma damuwa ya kara zuketa.....




******************



AMERICA


1 MONTH LATER


A yau Fadeel yayi shekara daya da zuwan sa America, hakan kuma yayi daidai da shekaran sa daya a kwance ba tare da yasan a wace duniya yake ciki ba, likitoci sun fara damuwa ganin har yayi shekara daya bai motsa ba, sosai suka damu...


tun kafin a fara aikin sunan fadeelah'n sa ne a bakin sa, sosai suka tausaya masa, domin basa son wahalar sa ta tafi a banza, musamman babban likitan mai suna KELVIN SMART domin sai da Fadeel ya bashi labarin soyaayyar sa da Fadeelah ya amince za a yi masa aikin Saboda hadarin dake ciki, kasancewar sa bature, dama an san turawa da sanin darajar soyaaya hakan yasa ya amince domin ya yarda da reasons din fadeel din, taɓɓas samun irin wanna soƴaaƴar da wuya, koda cikin su turawa ne, ace uwa da ɗa duk sunyi sadaukarwa mai girman gaske...




Zuwan KELVIN SMART na hudu kenan a safiyar yau domin duba fadeel ko ya farka, saboda ya fara jin tsoro... a hankali ya tura kofar zallan glass din ya shiga, kamar a mafarki ya ga Fadeel ya fara motsa kafafun sa......






Share fisabilillah





Comment





✨Noor larab ce✨





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call *****

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.