Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Zeey · ASHE ƊANA NE

🙆‍♀️ASHE ƊANA NE🙆‍♀️



PAID BOOK 






LABARI DA RUBUTAWA✍️

ZAINAB SALIHU YARIMA

(SARAUNIYAR KANAWA)








Littafin nan na kuɗi ne akan Naira ɗari biyu 200, vip group kuma ɗari biyar ne 500 posting sau biyu safe da yamma, ga mai buƙata zai biya kuɗin shi kafin free page ya ƙare, masu biya ta katin waya ku turo katin wayar ku ta wannan number *** ga masu turawa ta Account kuma zasu turo ta wannan number 6019964818 zainab Salihu yarima keeystone bank, sai kiyi screen short ki turomun shaidar biyar ki ta wannan number ***.




PREE PAGE 3



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM




"Ai in faɗa miki Hajjaju aikin malam sarki kaman yankan wuƙa yake, matsalar shi kawai ki saki kuɗi zaki ga aiki."

  "Ni in dai kuɗi ne ai bai da matsala in da buƙatata zata biya."

Sun ƙariso bakin titin layin suka ajiye motar su kasancewar mota ba zata shiga lungun layin ba, haka suka gangara a ƙafa har suka isa wani gida ginin ƙasa irin ginin da ɗin nan a cikin unguwar na kusfa.

Gida ne kato in ka shiga ciki amma kuma ɗakuna uku ne a jere sai fankaɗeɗen tsakar gidan da ya cabalbale da taɓo kasancewar wanke-wanke da matar gidan ke yi, washe musu baki yamusasshiyar matan da suka gani tana wanke-wanke tayi ta na faɗin, "a'a sannunku da zuwa ku shiga malam ɗin na ciki."  

Ta ƙarisa maganar ta gyara ɗaurin kirji da tayi don zanin na neman sulluɓewa, gaba ɗaya Hajiya Uwani a yamutse take kallon gidan ji take tamkar zatayi amai saboda ita a rayuwarta ta tsani ƙazanta, haka suka ƙarisa wani akurkin ɗaki, wani gabjejen mutum suka tarar a ɗakin mutumin dogo ne baƙi ga ƙiba fuskar nan baƙaƙirin ba alamar rahma ga jajayen ido ya tasa wani katako cike da ƙasa a cikin sa yana ta wani surkulle, Hajiya Saratu ne ta kalli malam Sarki ta ce, "Malam barka da aiki, fatan mun sameka lafiya."

"Barka dai Hajiya, kun zo lafiya, ku zauna ga guri."

  Kallon gurin Hajiya Uwani ta yi ta yamutsa ido tana tunani ita ina zata iya zama a wannan ƙazantaccen guri, sai da Hajiya Saratu ta jawota ta zauna sai ƙoƙarin toshe hanci takeyi.

  "Malam wannan ƙawata ce tana da damuwa akwai wani ƙanin mijin ta da iyalin shi gaba ɗaya sun takura ma rayuwar ta gashi komai ya samu sune ga shi yana da wani ɗa gaba ɗaya sun shaƙu da ƴar ta tana tsoron kar a ce za'a haɗa su aure wataran, kuma duk uwar mijin na ta ita take haddasa komai."

  "To yanzu mai kuke so a yi musu.?

"Yauwa Malam so nake gaba ɗaya a rabashi da ƴan uwan na shi ya zama baya taimaka musu daga ni sai ƴa ta."

  "An gama Hajiya zaki bada kuɗi za'a siya manyan turarruka domin aikin na da matuƙar wahala kuma yana buƙatan turare masu tsada."

"To yanzu malam kaman nawa zan bayar.?

"Zaki bada dubu ɗari uku wannan kawai na kayan aiki ne, sannan kuma bayan an gama aiki zaki biya kuɗin ladan aiki."

   "Malam ga wannan dubu ɗari biyar ne ni dai kawai burina ya cika, ƙawata mu je."

  "An gama Hajiya nan da kwana uku zaki ga aiki ya fara."

   Fitowa sukayi suka nufi hanyar da zai fitar da su gurin da suka parker motar su.


Wa'iyazubillah shin ƴar uwa kin san girman shirka kuwa,? shin uwa kin san tarin zunubin da kike ɗauka in har kika haɗa Allah da wani.

  (Allah maɗaukakin sarki yana cewa cikin suratul Ma'ida,  "Haƙiƙa duk wanda yayi shirka da Allah, to Allah ya haramta masa shiga aljanna, kuma makomar sa wuta, kuma su azzalumai ba su da mataimaka.)

Amma ƴan uwa idon ku ya rufe kawai neman duniya ya sa ku kauce hanya da bin shawaran ƙawayen banza su ɗoraki akan hanyar kauce ma Allah da saɓa mishi, don kawai jin daɗin duniya, to ƴar uwa karki manta jin daɗin duniya na taƙaitaccen lokaci ne ba zai taɓa dawwama ba, kina da damuwa ki tashi cikin dare ki roƙa a gurin ubangiji Allah da kan shi ya ce mu roƙe shi ya amsa mana to dan me zamuje mu roƙi wanin Allah, insha Allah nan gaba akwai sirrori da addu'oi da zan kawo muku ku bini bashi Insha Allah.



   Bayan Hajiya Uwani ta dawo gida, ta shiga ƙayataccen falon ta da aka ƙawata shi da lafiyayyun funitures Ash an white sai ɗaukar ido sukeyi ga wani haɗaɗɗen carpert da ke tsakiyar falon wanda kina takawa kafar ki na lumewa gefe guda kuma zaki bi wani siririn corido ne da zai kai ki har dinning area in da tsayawa faɗa muku kyan gurin ma ɓata lokacine wani zagayayyen dining ne golding colour mai ɗauke da wasu kujeru suma golden colour sai ɗaukar ido yakeyi, gefe guda kuma sink ne na wanke hannu da aka ƙawata shi da wasu flowers suna bada wani haske kala kala sosai dining area ya haɗu, ta can gefen hannun hagu kuma wani matakala ne da aka ƙayata shi da haɗaɗen silver in ka bi nan zai sadaka da sama in da nan ma ɗin wani ƙayataccen falo ne da ya fi na farko haɗuwa, in da aka ƙawata shi da funitures royal blue da white in da walpaper ɗin ɗakin ma duk royal blue ɗin ne, tsaruwan falon dai tamkar ba a ƙasar Nigeria ba don zaku iya kiran shi da aljannar duniya, bayan ta gama ƙare ma falon kallo dining area ta nufa ta tarar da abinci gashi nan an jera su a wasu lafiyayyun kuloli, bubbuɗe kulolin ta mayar ta rufe ta bi ta wani hanya sai ga ta a falon sama direct wani kofa ta nufa ta buɗe ta shige, woow masha Allah ganin irin aljanar duniyar da aka tara a wanin bedroom ɗin tamkar bq za'a mutu ba, tana shiga ta fara ciccire kayanta ta nufi banɗaki ta sakarwa kan ta ruwa tana sauke ajiyan zuciya, sosai ta dunga dirza jikin ta domin Hajiya Uwani Allah ya yi ta da kyankyami gani take kamar dattin gidan malam sarki ya maƙale a jikin ta domin kayan da ta cire ma watso su tayi ta ce mai aikin ta ta kwashe.



BAYAN KWANA BIYU


Yau Alhaji Tahir zai dawo, Hajiya Uwani ne ta fito sanye da wani rantsattsen lace an mata ɗinkin Abuja bubu, ta yafa mayafi ta kashe ɗaurin ture kaga tsiya fuskar nan ta sha kwalliya, hannun ta sanye da warwaro da zobuna na dimond.

  "Zeeyterh zan tafi fa, kin san Daddyn ki ya kusa sauka kin tsaya kina ɓatamun lokaci ko."

   Da gudu zeeyter ta ƙariso sanye ita ma da lace iri ɗaya da na momyn nata har ɗinkin ta kalli momyn ta ɓata rai tana faɗin, "Momy zamu tsaya mu ɗauki brother ko."

  "Wallahi baki isa ba, bazan ɗauki wannan shegen yaron ba sai dai kema ki fasa zuwa."

  "Eh na ji Momy na fasa zuwa in dai ba zaki da brother ba."

Ta ƙarisa maganar tana juyawa cikin gida.

  "Yau na shiga uku na ni Uwani wai me yarinyar nan take son zama ne, duk yarinya tabi ta susuce akan yaro."

 Juyawa tayi tai shigewar ta mota ta ce ma Idi ya ja su tafi.


   BAYAN WASU AWANNI.


 Shigowar motan su gate ɗin farko Alhaji Tahir yaji kan shi ya wani sara tuni ya riƙe kan shi, "lafiya my dear.?

 Cewar Hajiya Uwani cikin kissa da kwarkwasa irin na matan da suka san kan su.

"Ba komai My dear ina tunanin gajiya ce ta sa na ji kaina ya wani saramun."

"Ayyah sorry dear mu je in tayaka kayi wanka ka ci abinci sai ka sha magani ka huta."

 Ta ƙarisa maganar dai dai lokacin da suka ƙarisa kofar falon na su idi ya parker motar, tuni suka fita suka nufi cikin gidan.

  Jaddi ne ke zaune bayan ta gama shirya ma ɗan nata Abinci mai rai da lafiya, kasancewar duk lokacin da ya dawo nan suke wutowa direct ya ci abinci su yi hira da mahaifiyar ta shi, ya faɗa mata irin tarin nasarorin da ya samu ta sanya mai albarka sai dare ya raba sosai sai su shiga gidan su hakan kuma dama yana ƙona ma Hajiya Uwani rai, Jaddi shiru shiru ta ji ba taji motsin shigowar Tahir ba kuma Zeeyterh ta shigo da gudu tana faɗa mata cewa Daddyn ta ya dawo amma gashi har yanzu bai shigo ba, ita kan ta Umman Mu'ayyid taji mamaki wannan canjin lokaci ɗaya tun Jaddi na kawaici har ta ɗauki waya ta kirashi sai ji tayi Hajiya Uwani ta ɗauka, "hello Hajiya ni ce my dear ya shiga wanka tare muka shiga ma na ɗan taimaka mai fitowata kenan na ji kiran wayar ki, nasan zaki ce mai ya hanashi shigowa gurin ko kamar yadda aka saba to daga yau ni Uwani na kashe wannan tsarin.!

  Tana gama faɗin haka kit ta kashe wayar, sororo Hajiya Asma tayi da wayar a hannun ta numfashin ta ya ɗauke na wucin gadi, wani jiri taji yana ɗiban ta yuuu tayi zata faɗi da sauri Umman Mu'ayyid ta ƙariso ta riƙeta.

  "Jaddi lafiya mai ya faru.?

Kasa magana Jaddi tayi sai kuka da ta fashe da shi.


Bayan Alhajji ya fito wanka haka hajiya ta tayashi ya shirya, ta ja shi zuwa gurin cin abinci gaba ɗaya ya mance da wata mahaifiyar shi balle ƙanin shi, ko yaron ƙanin shi, hajiya Uwani da ƴar ta kawai sune a gaban shi.


"Halima Uwani ta rabani da ɗa na kuma Allah sai ya mun sakayya, zan cigaba da faɗa ma Allah baya barci."

"Kiyi haƙuri Jaddi ba ta isa ta rabaki da ɗan ki ba, Allah yana ji kuma yana gani kuma da shi muka dogara."


 **************************



*BAYAN SHEKARA GOMA*



Abubuwa da yawa sun faru ciki har da rashin lafiyar Jaddi yau ciwo gobe lafiya, hakan ya sa ta kira Muhammad ta ce mai, "Muhammad ina so in maka wani magana mai muhimmanci ka ga in da rayuwa ta ke tafiya kana ganin halin rayuwar da muke ciki da kyar muke samun na ci da na makarantar Mu'ayyid shiyasa na ce akwai wasu kuɗi da nake son in baka ya kamata ace yanzu ka natsu duba da gashi yanzu saurayin ɗa kake da shi a gaban ka, Business nake so ka fara zan buɗe maka shago a sabon gari mun riga mun yi magana da yayana."

  "Aiko Hajiya yanzu na natsu insha Allah nima zama haka nan da nakeyi ba daɗi tun bayan korar mu aiki da akayi."

  "Kaje nan da sati ɗaya za'a kammala komai za'a zuba maka zannuwa."

   "Nagode Hajiya."

Tashi yayi ya fita, yana fita ya ɗauko waya ya danna kiran wani number, can sai ga muryan mace ce ta ɗauka cewa yayi, "hello sweetheart kina ji na lokacin auren mu yayi domin yau Hajiya take min maganar zata buɗe mun shago."

"Da gaske baby,? kai na ji daɗi ni dama wallahi na gaji da irin rayuwar da mukeyi na fi son muyi aure."

"Karki wani damu lokaci yayi, sai na kiraki anjima zamu haɗu."



   "Brother meyasa kwana biyu duk ka canza mun, na rasa me ke damunka."

  "Kinga Zeeyterh ni fa abun da kike mun kwata kwata ban jin daɗi tun muna yara ba dama in raɓi kowacce mace sai kin san yadda kikayi kika rabani da ita, wai to meye nufin ki,? kin san dai ni ba zan taɓa auren ki ba saboda irin tsanar da mahaifiyarki ta yi mun."

  Yana gama faɗin haka ya buga table ɗin da ke gaban su, ya miƙe ya fita a fusace, da gudu Zeeyterh ta biyo bayan shi tana kiran shi, ko waiwayowa bai yi ba, durƙushewa tayi a gurin ta rushe da kuka, "Momy why! why! meyasa kike son ki rabani da farin cikin raina, meyasa ba zaka fahimce irin son da nake maka ba tun muna yara, meyasa ba zaka kauda kanka akan momy ba mu gina rayuwar mu mai inganci.!

Ƙarisa maganar tayi tana ƙara rushewa da kuka, Yalwa ce ta ƙariso gurin da sauri tana faɗin, "uwar ɗakina lafiya, don Allah ki tashi ba girmanki ba ne."

  Yalwa ta ƙarishe maganar a tsorace don ta san ƙaɗan daga cikin aikin Zeeyterh ne ta disgata, ɗago rinannun idanuwan ta tayi wanda suka ƙara girma saboda kukan da tayi ta watsa ma Yalwa wani wulaƙantaccen kallo tana faɗin, "bar nan gurin munafuka kawai, ina ruwan ki da kuka na.!

  Ta ƙarishe maganar cikin ɗaga murya, jiki na rawa Yalwa ta juya har tana tuntuɓe. 

  "Ke..! zo nan, ki je ki kwaso mun kaya a garden."

  "To ranki ya daɗe."




"Umma gobe ne final day da za'a rufe karɓan kuɗin jarabawa fa gashi har yanxu ban biya ba, na ma abba magana bai ce komai ba."

  "Kayi haƙuri Mu'ayyid za'a biya ma insha Allah a goben."

"Shikenan Umma Allah ya kaimu, ina abinci na.?

  "yana ɗakin ka."


Tafiya take cikin sanɗa ta buɗe ƙawataccen ɗakin barcin na mahaifiyar ta, a hankali ta maida kofar ta rufe direct drawer mahaifiyar tata ta nufa numbobin buɗe drawer ta sa nan da nan drawer ta buɗe gefe guda kuɗi ne a jere sababbi fil da su jikin ta na rawa ta kai hannu ta ɗauki bandir biyu ta saƙe ta maida drawer ta rufe juyowar da zata yi aka buɗe kofar ɗakin.✍️✍️✍️✍️



Zeeey yar mutan zazzau follow me on Arewa book Sarauniyakanawa🥰🥰🥰🙏🙏

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.