Free chapter · Read without an account
Chapter 3 nd 4
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨
Na
ZAINAB A BARDE
🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI 🗡️ WRITER'S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)
Free page 3 nd 4
****
Akan hanyarta ta komawa gida ta hadu da Safara'u ta debo ruwa, ita bama ta kula da ita ba, kudin hannunta ta daure a habar zani, sannan ta cakwali gaban rigarta, "ubanwa na kama","dan Allah Zainabu kiyi hakuri, kinga inna tace ta aike ni na daibo mata ruwa zata duro girki","cha cha cha, dalla rufe min baki kafin in fasa shi a nan wajan, dama gashinan kamar na biri, kinga sai na kara tabar dashi, sauke ruwan kanki","dan Allah kiyi hakuri","zaki sauke ne ko Aa" ta fada tana kankance ido, sauke ruwan Safara'u tayi, idonta na tara kwalla, ai tana sauke ruwan Zainabu batayi wata wata ba, ta dauki ruwan ta shaika mata shi, tundaga kanta har kasa, kuka Safara'u ta fashe tashi, ganin wannan wulakanci da Zainabu tayi mata, "gobe ma ki kara tsokanata kiga yadda zanyi maki" ta fada tana jefa mata bokitin tare da karawa gaba, durkushewa safara'u tayi ta fashe da kuka.
Tana dab da shiga gida tayi cilli da ƙwaryar tare da shigewa gida, sallama ta rangada tana kwala kiran sunan Anna, "ni wai lafiyan ki kike kwalla min kira haka?","lafiya lau Annata, dama kudin ki na karbo maki, gasu ma" ta fada tana ciro su daga habar zani, dari biyu ta bata, "ahh ni Anna yau wace rana Hannatu tayi biyan bashi ta dadin rai" ai bata gama rufe baki ba saiga Hannatu ta fado gidan kamar an jefota daga sama, "Anna ga kudin ki, ki bani wake na","wana wake kuma?","waken da Zainabu ta kawo maki mana","ni bata kawo min wani wake ba, kudine ta kawo min kuma gasu" ta fada tana nuna mata dari biyun,
"Kee! Zainabu ina wake na?","ban gane ba wana wake kike magana akai, kin bani wake ne?","waken da kika dauka a cikin ƙwarya na alalata","kinga malama ni ban daukar maki wani wake ba, kinje chan wani ya daukar maki wake zakizo ki lakabamin, banji ba ban gani ba" ta fada tana murtuke fuska a dole ba ita ta dauka ba, Hannatu zata sake magana Anna ta dakatar da ita, "kinga Hannatu tun muna shaidar juna ki fitar min daga gida, baza kizo har gida kice jikalleta ta daukar maki wake ba, bayan kuma bata dauka ba, dan kinyi biyan bashi, kuma shine harda sharri, to wayace kici bashin?","wllhi Anna wake ta daukar min da nace mata banida kudi, kuma Alalar siyarwa fa zanyi","kinga ki fitar min daga gida tun muna shaidar juna, kije ki naimi wanda ya daukar maki wake tun lokaci bai kure maki ba","Anna dan Allah kisa baki ta fada min inda wakena yake","Anna bari na fitar da ita tunda bazata fita ba" nan ta fara tura ta harta kaita kofar gida sannan ta hankadata, "gobe ma ki kara cin bashin Annata, kuma kiƙi biya kiga yadda zan maki" ta fada tana shigewa ciki,
Hannatu kuwa hannu ta dora a ka, tama rasa ihu zatayi ko kuka, a dakeka sannan a hanaka kuka, amma bataga laifinsu ba laifinta ne, da bataci bashin su ba, da duk haka bata faru ba, garama ta tashi tasan inda dare yayi mata, dan tasan kaf garin nan babu wadda ya isa ya karbar mata waken ta, har mai gari da kansa, saboda masifar Anna da jikarta Zainabu, tashi tayi ta kara gaba tana matsar kwalla.
Koda Zainabu ta koma cikin gida abincin ta taci tasha ruwa, ta godewa Allah, "Anna bari naje gidansu siyamah kafin lokacin dora abincin rana yayi, saina dawo na tayaki","sha zaman ki jikalle ta, dan nasan ma ba dawowa zakiyi da wuri ba, karki min wani dadin baki, in kuka hadu da ciyama ai baƙu sanin lokaci yayi","nace maki Siyamah ake cewa ba ciyama ba, ina gyara maki ne dan kar wataran ki kunyata mu","naki na fada yadda kikace din, yadda na iya haka zan fada, yar bantan uba" dariya tayi tana ficewa daga gidan.
Koda taje gidansu Siyama, tararwa tayi innarta batanan, ita kuma tana wanki, "ƙawata ashai dai zakizo","kin manta wace Zainabu Abu ashai, bata saba alkawari, tunda nace miki zanzo to zanzo" murmushi Siyamah tayi, nikam ai nafi kowa sanin ƙawata, kinji labarin anjima da daddare za'ayi babban wasa a dandali","wasan mai?","kin manta gobe ake aurar da yar gidan mai gari" tabe baki tayi "kinsan fa ni abinda ya dame ni nakeyi, ban shiga abinda bai dame ni ba","amma dai zamuje ko?","gaskiya ba zanje ba, amma in kinga kinason zuwa zaki iya zuwa","dan Allah ƙawata ki bari muje" zata sake magana, siyama tace "dan abotar mu fa" girgiza kai Zainabu tayi dan tasan abinda zatace kenn dama, "shknn inkin shirya ki biyo min sai muje","yauwa ƙawata ko kefa","ina Inna ko batana?"," eh taje gidansu wasila","ki gaishe min da ita in ta dawo","zataji sai mun hadu anjima"
Tana fitowa daga gidan ta ga Hansai mai tallar awara, "kee! Hansai a warar ta yauce ko kuwa kwantai zaki siyarwa da mutane?","wllhi Aunty Zainabu ta yau ce" ta fada jikinta na mazari, murmushi Zainabu tayi ganin yadda Hansai ta shiga hankalinta, ba zata manta ba tun ranar da hansai tayi mata rashin kunya, ta gudu gida, aiko Zainabu ta bita har gaban uwarta ta lakada mata mugun duka, tun daga ranar in suka hadu take kaffa kaffa kar tayi abinda zataci duka, "ajai bokitin awarar taki kije makarantar Malam Mamman ki kirawo min almajirai mutum goma, saura kuma ki zauna karki dawo da wuri kiga yadda zan maki","amma aunt.. bata karasa ba Zainabu ta girgiza mata hannu, ai da sauri ta ruga da gudu dan cika aiki karta sha duka.
Tana nan tsaye Hansai ta dawo da almajirai guda koma kamar yadda ta bukata, layi tasa suka bi, "ki saka ma kowa awara ta naira dari" zuru Hansai tayi, dan karta saka musu Zainabu ta hanata kudin ta, "ko bazaki saka musu bane?","zan zann saka" ta fada tana in'ina, haka ta amshi robarsu ta saka musu ta dari dari, kamar yadda Zainabu ta bukata, haka almajiran suka rika murna suna mata godiya, bayan ta sallami almajiran, ta dago tana kallon Zainabu, dubu dayar nan da ta daure a habar zani ta dauko ta mika mata, da sauri Hansai ta karba tana godiya kamar tayi mata sujjada, murnan da take yaudai gashi sun hadu da Zainabu kuma sun rabu lafiya, gashi kuma ta siye mata awara, yau ba saitayi yawon talla ba, haka ta dauki bokitinta ta nufi gida cike da farinciki, "nayi miki sadaka da kudinki, kinga ai kya sami lada, tunda dama bayi kike ba, sai bakar rowar jaraba.
Tana cikin tafiya taga wani mai siyar da lemo, "lemo lemo lemos, ga lemo in ba zaki ba biya","masha Allah, Malam mai lemo a bani lemo","na nawa za'a baki?","fara bani daya in taba" yanka mata lemon yayi, ya mika mata, karba tayi ta fara sha, "kara min wani" saida ta sha lemo biyar, "aikin banza ma, ashai kasan lemon naka babu zaƙi","haba yar nan, lemo na kuwa shine mai zaki","niko banji wannan zaƙin ba, dan haka bazan biya ba","aiko baki isa ba, ni nasan duka lemuka na masu zaƙi ne","sai kayi kuma, ni kaga tafiya ta","aiko baki isaba" bata kulasa ba ta fara tafiya, binta ya fara yi a baya yana fadin "ki bani kudi na nace" duk inda suka wuce kallon su ake, wasu na fadin Allah ya raba ku lafiya, a haka har tazo gida, tayi shigewarta ciki.
Sallama ya rinka kwalawa, "jikalle ta kamar sallama nakeji ko?","bawai kina ji bane, sallama ce Anna","bari to naje na gani","muje tare mu gani wane" fitowa sukayi, "bawan Allah kaine kayi sallama?","nine kudina nazo amsa da ƴarki tasha min lemo taƙi biya","to ba nan gidan bane danni banida wata ƴa","ga tanan a bayanki" jiyowa tayi ta kalli Zainabu "kinsha masa lemo ne?","Anna shine fa yace in ba zaƙi ba biya, ni kuma da nasha naji babu zaƙi","to kai kaji, lemon naka babu zaƙi","nifa nasan lemo na akwai zaƙi, bari ma kiji" lemo daya ya dauko ya yanka mata, karba tayi ta fara sha, saida ta kusa shanyewa, sannan ta furzo dashi,
"Wannan wana irin lemo kake siyarwa da mutane, abu duk bauri, babu zaƙin yau bare na gobe","nide wllhi sai kun biyani kudi na","ko sisi bazan baka ba, tunda kai kace in ba zaƙi ba biya","ku bani kudina kafin in muku akuya","kinga Anna barni dashi" ta fada tana dawowa gaban Anna, "kayi min akuya ni kuma in maka bunsuru, in ka fasa yin akuyar ka raina uwar data haife ka" zaro ido mai lemo yayi jin tana naima ta zage sa, "kinga jikalle ta, taho mu shiga ciki, kai kuma ka kwana a kofar gidan" tana gama fadin haka taja hannunta, jiyowa tayi tana masa gwalo, "wllhi Allah ya isa kudina"
Shere fisabilillah.