Free chapter 路 Read without an account

Chapter 4

by Ummubasheer 路 CUTAR KAI

```CUTAR KAI....```馃拲



{ _Labari ne mai cike da nadama, yaudara, tausayi, tsantsar k'auna mai tab'a zuciya_ }



 _Story And Written_

        ```By```

 ```UMMU BASHEER

   &

MAIMOUNATH O.G```



 *Wannan labarin k'irkira ne, bamu yarda a sace ko ayi mana copy and paste ba, duk wanda yayi kuma bamu yafe ba*





 *Page 04*





Yau a gidan sun tashie da aiki sosai kasancewar yau ne Aminin Daddy zai zo wato Alhaji Kabeer, wanda su Nadrah suke kira da Baba Kabeer,gidan an gyara ko'ina sai tashin k'amshi yake, Abinci kuwa kala kala akayi ga Ginger Juice da Pineapple juices da akayi kasancewar yafi son irin su, Nadrah kuma tayi snacks kamar irin su Meatpie, velvet cake, Spring rolls,Samosa,sai Fried Rice and cowslow da tayi, Mommy sosai take koya ma y'ar nata girki,duk da suna da mai aiki amma tana sa Nadrah girki sosai saboda tasan gidan wani zata mace kuma ba girki ai ba mace bace  mussaman Mommy tasa Daddy ya biya ma Nadrah kud'i taje inda ake koyan duk wasu nau'in snacks ta koya,Bayan duk sun gama aikin Nadrah da kanta taje Parlour Daddyn su ta shirya komi Hisham na taya ta da kawo abubuwa, Sannan ta koma d'akin ta, kasancewar tun safe take aiki ko wanka ba tayi ba gashi ta gaji kawai sai ta fad'a toilet tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin wani riga da skirt na atamfa fitted, rigar Green colour ce mai ratsin black and golden, tayi dauri batayi make up ba powder kawai ta shafa sai lipgloss, tasa kwali, ta feshe jikinta da perfume ta fito parlour.




Da yammah Daddy ya dawo gidan domin tarbar Aminin nashi, Around 6pm Su kaji horn din mota Daddy ya tashi cikin farin ciki ya fita waje, Nadrah tana mamakin irin shak'uwar dake tsakanin su, duk da ita ta manta da Baba Kabeer din ma kusan 4yrs rabon shi da gidan su, share tunanin tayi suka Cigaba da hira da Mommy.



Wata had'adiyar mota ce Mai tsada tayi parking a Cikin gidan, Kyakyawan Mutum ne ya fito daga ciki, Bak'i ne sosai amma kuma yana da kyau, dogo ne mai fafad'ar kirji, irin Giant Mazan nan ne, Fuskar shi babu saje ko gemu a aske yake, yana da white eyes, Sanye yake cikin Shaddah Gezner, light blue dinkin babban riga tumbin shi ya d'an fito alamun hutu sun bayyana, Sanye yake da glass irin na manyan mutane, Alhaji Kabeer kenan, Daddy yana fitowa ya Mik'a mai hannu sukayi musabaha cike da farin ciki suna dariya suka nufa parlour shi, still hannun su na cikin na juna, bayan sun shiga ne, Alhaji Kabeer ya zauna Daddy kuma ya tsaya a tsaye yana cewa"Allah mai iko yau dai ga ka a Kaduna bayan wasu Shekaru"


Dariya yayi fararen teeth dinshi suka bayanna" At last dai nazo, yanzu zan huta da gorin ka"


 Dariya suka sa gaba d'aya, Daddy ya gabatar mai da abin motsa baki, yayi godiya, Daddy da kanshi ya zuba mishi Ginger Juice ya Mik'a mai yana cewa bari ya kira Mommy tazo su gaisa, Mommy tazo suka gaisa cikin mutunci Sannan ta koma Parlour tace Su Nadrah suje su gaida Alhaji Kabeer, Hisham yayi gaba ita kuma taje d'aki ta d'auko karamin veil ta yafa, zata shiga parlour Hisham ya fito zda Sallama ta shiga, suka amsa, cikin ladabi ta gaishe da Alhaji Kabeer ya amsa, ta juya ta fita, cike da mamaki yace"Wannan wace ce? ban santa ba"


 Dariya Daddy yayi yace"a haba kar dai ayi abin kunya wai Uba ya kasa gane y'ar shi"


D'an waro white eyes dinshi yayi" What, kar dai kace min Nadrah ce? "


Dariya Daddy yayi" Kwarai kuwa yaushe rabon ka da garin nan"


 Jinjina kai yayi cikin mamaki yace" Eh lalai mun tsufa, yanzu Nadrah ce ta girma haka"


 Daddy yace"Ai kuwa ka tsufa har yanzu aure shiru, kak'i aure"


Da wasa Alhaji Kabeer yace" Ai dole inyi aure ni naga iri ma ina so, ka bani Nadrah kaga shikenan anyi tuwona mai nah"



Dariya Sosai Daddy yayi" ah toh ai Shikenan indai Nadrah ce na baka ita"


 Shima dariyar yayi suka canza hirar, cike da farin ciki suke hira duk da cewa kusan kullum suna magana a waya amma ganin junan su yasa su farin ciki Sosai.



Sai bayan sunyi magrib da isha'i Sannan Alhaji Kabeer ya tafi masaukin shi Daddy yayi yayi ya kwanan nan yak'i wai ya riga yasa anyi mishi booking Hotel room, sai washegari ma zaije ya gaishe da Kawun shi, Haka suka rabu cike da kewar juna.



Daddy yana dawowa ya shiga bedroom din Mommy tana ninke praying mat data iddar da sallah, cikin farin ciki yace"Y'ar ki dai tayi Miji"


 Da mamaki tace"Miji kuma Alhaji, yaushe kayi mata mijin kuma wane ne?"


Zama yayi yana cewa" ai kya tsaya kiji tukuna irin Wannan jero tambayoyi haka My Wife"


Murmushi tayi tare da zama kusa dashi, gyara zama yayi yace" Alhaji Kabeer ne ya ganta yana So......"


Mike'wa tsaye tayi cikin tashin hankali ta katse shi" What Alhaji Kabeer kuma kasan mai kake cewa kuwa, kana nufin wai Aminin ka? "


Rik'o hannun ta yayi ya zaunar da ita" Kwantar da hankalin ki meye na rud'ewa, ki nutsu ki saurare ni"


" Haba Alhaji dole in rud'e, ya za'ayi kace wai Nadrah ta auri Aminin ka, hakan ai ba mai yuwuwa bane sai kace mun gaji da ita, ya za'ayi Nadrah yarinya y'ar shekara 18 ta auri wanda ya haife ta..... "


 D'aga mata hannu yayi" dakata bana son saurin yanke hukunci, Meyasa ba zaki tsaya kiji magana ta ba tukun"


Zama tayi"Kayi hakuri ina jinka"


 "Babu abinda Aminina Kabeer zai zo min dashi in kasa mishi ke kanki kinsan irin shak'uwa da zumuncin dake tsakanin mu, sannan kuma mene ne ai'bun shi, ba wai yana da mata bane bare kice matsalar kishiya, idan hali ke ke kanki kinsan mutumin kwarai ne, mutum ne nagari, wanda yasan ya kamata, na tabatta zai rik'e Nadrah da amana, Kuma batun shekaru ai Age is just a number, batun kuma ta auri abokina ai ba haramun bane"


Ajiyar Zuciya ta sauke amma a zuciyar ta sam bata son y'ar ta ta auri Alhaji Kabeer, sai dai tasan mijin nata kaifi d'aya ne tunda har ya fad'a to babu yanda za tayi dan akwai shi da taurin kai bare kuma yanda yake son Abokin nashi.


Ya sake cewa"Kinga kuma dama samari sun fara kawo mata hari, ga yaron nan marar tarbiyya, kinga yanzu Jami'a zata shiga,ke da kanki a baya kince kinfi son tayi aure,gashi yanzu Allah ya kawo mata miji sai dai kawai mu bisu da Addu'a"


Zuciyar ta ba dad'i dai tace" Ameen, amma kuma bana jin zata amince"


 "Itace ta haife mu?"ya tambaye ta


 "kenan auren dole za kayi mata Alhaji?"


 Tsaki yayi yace" ku dai mata baku da hangen nesa, babu batun auren dole, bazan bari ta fad'a halaka na auren saurayin nan ba, ga Miji har gida Allah ya kawo mata dan haka ki bar wani zance kawai muyi musu Addu'a, sannan tunda makaranta zata fara ki bata wayarta yana Cikin wardrobe na"


Da toh ta amsa ya fice daga d'akin.




Nadrah taji dad'i Sosai da Mommy ta bata wayarta duk da tayi mata gargad'i akan kar ta kuskura ta Kira Sufyan, amma bata Jin zata iya, sai da ta Kira shi saboda wani irin son shi da take,kamar a mafarki yaga Kiran Nadrah, ya d'auka cike da farin ciki, sun dad'e suna waya Sosai kowa na fad'a ma d'an uwan shi kalaman soyayya da Yanda sukayi kewar juna, Bayan two days Nadrah ta fara attending School, A wannan Lokacin ne Baba Kabeer ya dawo Kaduna da wasu aikin nashi, duk da aikin nashi yafi yawa acan Lagos, amma shi kanshi yanzu yana missing y'an uwan shi yayi nisa dayawa, Nadrah kuwa tunda Ta fad'a ma Sufyan tana Zuwa Kasuu shikenan time to time yakan je gurin ta, wani time din ma har D'aukar ta yake suje Restaurant ya siya mata Abinci dasu Ice cream, Sannan ya maida ta school dama Driver shine ke kai ta yana d'auko ta, haka suka Cigaba da soyayar su a fili, sosai Nadrah take jin dad'in kasancewar su tare yanzu har ta saba ko hannun ta ya rik'e bata hana shi, Haka kuma sometimes zai dinga shafa fuskar ta ko kuma yayi hugging dinta, duk bata hana shi saboda Wani irin son shi take, kamar ko da Yaushe yau ya kira ta a waya yace tana school ne tace eh, yace Yaushe zasu tashi lectures tace ai sai 5 nan yace ta jira shi zaizo 5 din, ita kuma sai ta kira Bala driver tace sai six zata tashi lectures, Ai kuwa tun kafin 5 ya kirata cewa yana Daidai inda yake D'aukar ta wato idan an fito gate din school Akwai wani kwana nan yake parking motar shi ya d'auke ta, ko lectures din bata jira an gama ba tayi taking excuse ta fita, straight gurin ta nufa tana zuwa ta hango motar shi, da sauri taje ta bud'e ta shiga front seat, murmushi suka sakar ma juna, gaishe shi tayi ya amsa Mata tare da sak'ala hannun shi cikin nata yana d'an murzawa a hankali d'ayan hannun kuma ya maida shi kan Sitiyarin motar yana driving a hankali suka bar gurin, wak'a ya kunna musu, wani dad'i sosai take ji w ranta idan tana tare dashi, kan ta ta d'aura kan shoulder dinshi, kallon ta yayi suka had'a ido ya d'aga mata gira, yana mata wak'ar dake tashi a motar, a haka suka isa wani Restaurant mai kyau, a tare suka fito, da cewa tayi ya barta kawai bata jin yunwa yak'i yarda yace sai sunje ko snacks da Ice cream tasha, haka kuwa akayi aka kawo musu Kuma ta d'an ci domin tun safe rabon ta da Abinci domin yau sun dad'e suna lectures gashi bata samu fita ta d'an siya wani abu ba, Koda suka je massalaci wata K'awar ta Khairat tace suje su siya wani abin tace Aa akwai wani note da zata k'arasa, bayan sun gama suka fito tare da shiga mota kawai taga ya nufa wani d'an unguwa inda ba taron mutane, parking yayi a wata inuwa ya kalle ta"Baby six ba tayi ba naga sai kallo na kike, hira toh za muyi"


 Hararar shi tayi cikin wasa" Hira kuma shine sai munzo nan"


Rik'o hannun ta yayi tare d'an murzawa, ya matsa kusa da ita ya kai bakin shi gurin kunnen ta yace"Baby na k'osa muyi aure fah, kina rikita ni dayawa, da k'yar nake controlling kaina akan ki"


D'an ja da baya tayi" Uhm" 


 Shima gyara zaman shi yayi tare da Kwantar da kujerar yana Mata kalamai masu rikita ta, bata ankara ba taga six har ta wuce Cikin tashin hankali tace ya maida ta school, ganin duk ta damu yasa da sauri ya maida ta Lokacin da zata fita motar ya rik'o hannun ta babu zato taji ya rungume ta sosai yana sauke numfashi, wani iri take ji a jikinta da sauri ta ankara ta ture shi tana cewa sai sunyi waya Fitowar ta babu zato kamar daga sama taji ance"Nadrah"


A razane ta daga kai was zata gani Daddyn ta ne tsaye gefe kuma Bala Driver,



 Jikinta ya d'auki rawa, Sufyan ya fito da sauri ya durkus'a zai gaishe da Daddy kawai ya d'aga mai hannu"Bana bukatar gaisuwar ka, Ina maka warning kar ka k'ara zuwa inda y'ata take, idan ba haka ba zan d'auki mumunar mataki akan ka"


 Ya juya ya kalla Nadrah ya daka mata tsawa" wuce ki shiga mota"


Jiki na rawa ta shiga motar gaba d'aya a tsorace take, Daddy na gaba ita kuma tana back seat Bala driver Yana driving, babu Wanda yayi magana har suka isa gida, Suna zuwa ta shige ciki a matuk'ar tsorace, tana shiga D'aki Daddy ya shigo Parlour ya fara kwala Mata kira a rud'e ta fito tana zuwa ya dam'ko hannun ta, a tsorace ta kalle shi, wani irin mari ya d'auke ta dashi sai data ga wani duhu ya gilma, ya k'ara d'auke ta da wani zaro Charger yayi ya fara lafta mata Mommy ta fito da sauri ta fara kokarin kare Nadrah wacce ke kuka tana bashi hakuri, rai a matuk'ar b'ace ya Kalla Mommy"Ni yarinyar nan zata cuta, ashe fita take da Yaron nan idan taje School"


A rud'e mommy tace" fita kuma Nadrah kina hauka ne, yaushe Kika zama haka? "


 Daddy ne ya k'ara dank'o Nadrah tare da cewa"Fad'a min mene yake miki, zan iya kashe ki wallahi idan har yasan ki a mace"


Cikin kuka tace" Wallahi Daddy Ban tab'a yin Zina ba, Wallahi Allah bamu komi kawai fita muke"ta k'are Cikin sakin wani kukan


Mommy gaba d'aya ranta ya b'aci ita ma ta rufe Nadrah da duka"Tarbiyyan da muka baki shekara da shekaru shine kike son lalatawa, Nadrah mu zaki watsa ma k'asa a ido? "


 Daddy Cikin b'acin rai yace" Nadrah nayi miki Miji, Alhaji Kabeer Abokina shi zaki aura, kuma daga yau na raba ki da Yaron nan"


Nadrah a matuk'ar razane ta rik'e kaf'an Daddy tana kuka da karf'i take cewa"Daddy dan Allah kar ka aura min Baba Kabeer, wallahi bana son shi, Sufyan nake so, Daddy zan iya mutuwa dan Allah ka taimaki rayuwa ta..... "


Ture ta yayi da kafar yana kallon mommy" Ki k'ara jan mata kunne na gama magana aure babu fashi tsakanin ta da Alhaji Kabeer" Yana fad'in haka ya wuce ciki.


Nadrah kuka tasa Mommy ta daka mata tsawa"rufe min baki, Kar in b'ala ki anan, kinji kuma abinda Daddy ku yace, Dan haka kiyi mai biyayya kawai" ta wuce ta barta anan.


Nadrah kuka take kamar ranta zai fita, da k'yar ta koma d'akin ta, tana zuwa ta fad'a a gado sai kuka, da k'yar ta iya yin sallah magrib da isha'i a dadafe, Sufyan sai kiran ta yake amma ta kasa d'auka, ba karamin firgici da tashin hankali take ciki ba, daren Haka ta kwana kuka. Hisham shima ya shigo yaga tana kuka duk sai ya damu juyin duniyar nan tak'i fad'a mai mene akayi mata, Tunda bai sani ba.



Cikin kwana biyu Nadrah ta shiga damuwa Sosai Daddy ya k'wace wayarta, sannan yayi mata warning akan idan har taje School ta had'u da Sufyan zai d'auki mumunar mataki akan ta, saboda dama yasa a dinga kula mai da ita a b'oye duk wani movement dinta ya sani, shiyasa ranar ma ya ganta da Sufyan, tana tsoron Daddy sosai shiyasa bata yi gigin haduwa da Sufyan ba gashi ko waya basa yi ita Babban tashin hankali ta shine wai zata auri tsoho Abokin Baban ta.













#UMMU BASHEER

#MAIMOUNATH O. G

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.