Free chapter · Read without an account
3
by Badeelah Yakubu Mahdi · JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)
CIGABAN LABARI
Ranar Monday, daddy ne zaune a cikin mota, Fa'eez da Hisham suna zaune a Baya suna Hira duk su ukun, Daddy ne ya nisa yace "Wai mene ne Alisha take yi a cikine? shiyasa fa na nema muku driver sabida bana son Kuna 'bata min lokaci"
Hisham yace "Daddy kaine fa ogan kanka ko kaje letti ko kaje da wuri duk d'aya"
Girgiza kai yayi kana yace "Yaro dai yarone, Wai dama haka Alisha take yi idan zaku tafi school d'in?"
Fa'eez yace "A'a Daddy , inaga mummy ne ta sata yin wani abun, Hisham kaje ka Kira ta Mana zamuyi letti fa"
Hannu Hisham yasa ya bud'e marfin motan bai Kai ga fita ya hango fitowar ta, komawa ciki yayi ya rufe marfin motar had'e da fad'in "Gata Chan ma tana zuwa" duk suka kalli inda yake kallo, tafiya take a hankali duk jikinta a Sanyaye kana ganin fuskar ta zaka karanci tsantsan damuwa da yake kwance a Kan fuskar ta,ganin ta kusa da inda motar take ta saki ranta had'e da sakin Kirkirerren Murmushi duk suna kallon ta , cike da tausayin daddy ke kallon ta har ta shige cikin motar bai bar kallon ta ba, Murmushi tayi kana Tace "Daddy mu tafi Mana, Kar muyi letti"
"Kin San da hakan Kuma kikayi zaman ki?"
"Mummy ne Tace Na goge mata kaya kala d'aya shine na tsaya...... "
Kallon da yake mata ne yasa ta kasa karisa maganar yace "Yanzu duk kayan dake cikin wardrobe d'inta Basu ishe ta ba sai ta sa kin mata guga, Kuma tun ranar Saturday kuke gidan babu inda kuke zuwa Bata saki ba sai yanzu don neman magana, a gaskiya na Fara gajiya da halin haleema" yayi saurin bud'e marfin motar da niyan fita, da hannu biyu Alisha tayi saurin rike shi girgiza Masa Kai tayi had'e da fad'in "Daddy please mu tafi" ta fad'i hakan ne acikin harshen yarobanci.
Fa'eez yace "Dan Allah ki kyaleshi yaje idan baya nuna Mata abinda take ba dai dai bane Taya Za'ayi ta gyara Shirun da Daddy yake yayi yawa kamar ba na Miji........" Baiyi aune ba sai Jin saukar mariin da yaji Alisha ta masa, rike kuncin sa yayi cike da mamaki yace "Sis Mari?" Rai a mugun 'bace Tace "Eh mari Kuma idan ka kuskura na Kuma Jin bakin ka Wallahi Sai na Kara maka" ta maida kallon ta ga daddy Tace " Daddy please kayi hakuri muje kaga zaka je wurin aikin ka,gashi kuma zaka min registration zaka d'auki lokaci kamun ka gama" baice Mata kala ba ya sa wa motar ki, Yana tada motar suka hango motar mummy har ta fice daga gidan.
Girgiza Kai Daddy yayi gami da jaan Motar suka fice daga gidan, su Fa'eez ya fara dropping kasantuwar makaranta tasu ba d'aya bace, kai tsaye suka zarce makarantar su Alisha, Bayan sun isa ta Shiga class ayayin da Daddy kuma ya Shiga office d'in principal domin biya mata kudin wa'ec and neco ya d'auki kusan mintuna 30 kana suka kammala, Bayan sun kammala ya wuce office d'insa.
Daddy kasa gane kansa yayi gaba ki d'aya duk da yayi kokarin cire damuwa a ransa Amma ya kasa, Yana mamaki gami da Dana sanin bud'e wa Haleemah boutique don ya tabbata daba don Shagon Nan ba zata basu kulawar da ta dace daga shi har 'ya'yan sa ta zame musu tamkar dodo, Yana cikin wannan tunanin ne Ja'afar(Aminin Daddy) ya turo kofar office d'in had'e da sallama, sau uku yana sallama Amma daddy baiji ba, girgiza Kai yayi hannayen sa duka biyu a konkoson sa yana kallon aminin nasa cike da tausayi sabida yasan matsalar d'ayace baza ta wuce matsalar Haleemah ba, ya d'auki kusan dakika 20 yana kallon sa kana ya d'an buga table d'in dake gaban daddy had'e da Jan kujera ya zauna.
A zubure daddy ya d'aga Kai ya kalli Ja'afar yana ganin Ja'afar ne ya saki Murmushin da bai San sanda yayi ba, girgiza Kai Ja'afar yayi a karo na sau ba adadi yace "Hameed na fad'a maka ka daina yawan tunanin Nan zaka ja wa kanka matsala fa"
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Ja'afar Wallahi abin yafi karfina na rasa yanda zanyi kullum lamarin Haleemah Kara gaba yake yi, could you imagine yanzu Fa'eez baya gaida ta sai yaga dama, hatta ganin ta baya son yi? Ina tausayin yaran Nan Wallahi musamman ma Matan and idan tana wani abun ma sai gani nake kamar ta tsani Alisha,Wallahi idan wani abu ya sami yarana a dalilin negligence (Sakaci) d'inta bazan tab'a yafe mata ba"
"no no haba, insha Allah babu abinda zai same su da yardan Allah, bazaiyu ba taya Za'ayi ta tsani Yar da ta tsuguna ta Haifa da kanta? Kawai dai tayi busy ne dayawa,sai kace ka manta wace ce Haleemah?"
Murmushin gefen baki daddy yayi yace "babu wani busy wannan ma Sam ba hujja bace, akanta aka fara bud'e boutique? Wallahi zuwa yanzu ina da na sanin bud'e mata Shagon Nan, Kuma a gaskiya na fara gajiya Dole ne ta zab'a ko Ni da yaran mu ko neman kud'i"
"Na san ka da hakuri abokina ka cigaba da hakuri insha Allah komai zai dai daita, zata daina Insha Allah"
"babu alamun hakan a tattare da ita, Saida fa na zuba mata Yan aiki a Shagon Wanda idan taga dama tana zaune kud'i zasu Rika Shigo mata Amma inaa idan ta fita tun safe sai dare sometimes har 10 take kaiwa a waje"
"Ya Isa hameed, ya Isa please Dan Allah ka bar maganar Nan ,yawan mai-maita maganar kara tada maka hankali zaiyi, shawarar da zan baka shine ka cigaba da hakuri sannan ka cigaba da kula da yaran Nan"
"Nida always ina office ta ina Zan iya yin hakan? Nifa a gaskiya na fara tunanin ko aure zan karane"
Gyara zama Ja'afar yayi yace "Taaaaab" nisawa yayi kana ya ce "problem upon problem Kenan? (Matsal kan matsala),to Wallahi Kar ka Soma tafka wannan kuskuren, ai Wallahi ka kara aure matsalar da kake ciki sai ta ninka wannan, ko kamanta haleemar ta ka ce? Inaga ka manta"
" Ina fa zan Manta?"
"To ka bar ma zancen nan, let's keep on praying (mu cigaba da addu'a) insha Allah komai zai dai daita."
Iska mai zafi daddy ya fuzar ya amsa da amiin.
Da gana suka cigaba da aikin da ke gaban su, zuwan Ja'afar din ba karamin taimakawa daddy yayi ba sabida Yar maganar da sukayi sai yaji kamar an sauke Masa wani dutse ne Akan sa, sau dayawa idan muna cikin damuwa mukayi shiru bamu fitar dashi ba kullum karuwa zaiyi Amma da zaran ka sami Wanda ka yarda dashi ka fad'a masa ko da kuwa bazai baka mafita ba zakaji saukin abun sosai da yardan Allah.
*Bayan wasu awanni*
Driver d'insu ne yayi parking a bakin gate d'in school d'in su Fa'eez da Hisham, kana suka wuce makarantar su Alisha tana tsaye tana jiran su tana hango motar ta gane tayi saurin Shiga motar, cikin girmama mawa ta gaida shi ya amsa fuska a sake, ta sanar dashi GRA zasu fara zuwa don d'auko Nawal bisa ga umarnin mummy suka nufi GRA, gidan kakanin su take na 'ban garen daddy su.
"Haba Alisha meyasa kike abu kamar yarinya Yar shekara biyar ne? ki tashi ki cire uniform din Nan kici abinci sai ki zauna kallon"
Turo baki Nawal tayi kana Tace "Granny Dan Allah ki kyale ni Mana baki San dad'in Encanto bane shiyasa,idan na gama zanyi"
"to sallan fa wa zai Miki?"
" Nayi a school" tace mata idanunta tar Akan makeken TV dake makale a Jikin bangon d'akin.
A dai dai Nan su Alisha suka shigo duk su ukun bakinsu d'auke yake da sallama, granny na ganin su cike da murna da farin ciki Tace "Ah ah oyoyo oyoyo Yan makaranta, bakine a gidan namu?"
Nawal na hango su da gudu ta nufe su tana fad'in "Oyoyo Aunty Alisha" ta rungume ta, Murmushi Alisha tayi had'e da shafa kanta Tace "Oyoyo Little kina Lafiya?"
"Lafiya Lau" had'e da riko hannun ta suka zauna, Fa'eez yace "Little mu ba a ganmu ba Kenan ko?"
"Am sorry Ya Fa'eez Wallahi tsabagen farin cikine and nayi kewar ku sosai"
Tab'e baki yayi ba tare da yace mata komai ba.
Cike da girmawa Alisha da Hisham Suka gaida granny ta amsa had'e da tambayar su ya makaranta da Kuma mummy da daddyn su ta amsa da Lafiya kalau.
Fa'eez kuwa nad'e kafa yayi ya d'aura kafa d'aya Akan d'aya ya maida hankalinsa Akan TV, rike hab'a Granny tayi kana Tace "kai Fa'eez abinda uwar ka da uban ka suka koya maka Kenan baza ka gaishe Ni ba?"
" Mtsww..... " Kallon Alisha yayi kana yace "Kin gani ko sis? shiyasa nace miki Ni bazan Shigo ba, bata da aiki sai masifa da ita ta haifi mummy da Wallahi da sai ince abun a jinin sune"
"Iyeee lallai to Wallahi Fa'eez uban ka zakaci kaji ja'irin yaro Ni zakayi wa rashin ta Ido?"
Alisha Tace "Granny kyale shi Dan Allah, haka yake na rasa yaushe Fa'eez ya Zama Haka....... Yauwa granny dama mummy ce tace muzo mu d'auki Nawal driver Yana waje"
Cike da mamaki granny Tace "Oh ikon Allah cinye ta zanyi ne kome da har sai kun bi Bayan ta? dudu sati d'aya fa tayi anan, to babu inda zataje, Hisham" ta Kira sunan Hisham.
Ya amsa da " na'am" a dai dai Nan ya d'auki remote ya canza channel zumbur Nawal ta Mike ta fashe da kuka tana fad'in "Ni ka maida min Kallo na..." Kuka take sosai had'e da bubbuga kafa,shi ko Hisham abun nema ne ya samu dama ba barinta yake ba, Alisha Tace "Amma yaushe ne kace min kana kewarta Ashe dama abinda kake Shirin yi mata Kenan ko?"
Mikewa granny tayi ta kwace remote d'in ta maida mata tashar da take kallo,Nawal na ganin an canza mata shiru tayi kamar anyi ruwa an d'auke, Granny Tace "Kaje ka cewa Driver d'inku ya tafi gida sai anjima zaku koma gidan"
Rai a 'bace ya fita Yana kananun maganganu Granny Tace "Au kaima rashin kunyar zaka min kamar na Mai Kan agwagwan Nan?"
Baice mata kala ba yayi ficewar sa ba dad'ewa ya dawo, Granny Kiran Daddy tayi ta Sanar Masa da yaran suna Nan idan ya tashi daga aiki yazo ya d'auke su da to ya amsa.
Mikewa Fa'eez yayi ya nufi d'akin Papi, Granny Tace "Ina Kuma zaka je?"
" 'dakina"
" 'dakin ka? dama kana da d'aki anan ne ban sani ba?"
" 'dakin Papi d'akina ne"
" Manyan gari to sai ka zauna kaci abinci tukunna ko d'an masu gida" sosa keya yayi yace "kamar kin sani dama Wallahi yunwa nake ji"
Girgiza Kai tayi ta Fara Kiran sunan Yar aikin ta,fitowa tayi cike da girmawa Tace "Gani Hajiya"
"Yauwa altine ki sa ma yaran nan abinci" ta amsa da "Toh hajiya"
Granny ta ce "ku tashi kuje dining kuci abinci" duk suka nufi dinning d'in Amma banda Nawal da tasa kallon gaba kamar zata shiga cikin TV.
"Ba laifinka ba bane Dan liti ince maka ka d'auko min yarinya shine ka Kama ka baro su duka a chan sabida Ni ban Isa na fad'a muku magana kuji ba,ba da Kai zanyi ba bari Alisha ta dawo yau zata gane kuren ta." Ta karasa naganar tana huci,Tun da Mummy ta Fara masifa kansa na kasa sai da ya ta gama kana yace "Kiyi hakuri hajiya wallahi,Hajiya babba ce ta ce sai anjima Alhaji zai taho da su shiyasa Amma ba laifin Alisha bane"
"To sannu munafuki algumgumi,na Tambaye kane? Dallah fita ka bani wuri ko na tsaba maka" da sauri ya juya ya fita daga parlor.
Kiran wayan daddy tayi Yana ganin Kiran ta sai da yaji Fad'uwar gaba kallon wayan yake kamar bazai d'auka ba har ya kusa tsinkewa Ja'afar yace ka "d'aga mana"
Yace "Haleemah ce fa"
"And so? Dallah Malam ka d'aga kana damin kunnuwana da karar wayar ka" hannu ya d'aga ya Kara a kunnen sa daga d'ayan 'bangaren ta fara surfu bala'in da ta Saba "Yanzu hameed ni Kenan ban Isa ayi shawara dani ba? Akan me daga zuwa su d'auko Nawal zata rike su duka a chan? Wani ne ya Haifa min yaran nan ne? Da za'a Rika min iko dasu?nifa na gaji da gadara da Isar da matar Nan take min yauwa"
Mikewa yayi had'e da buga table d'in dake gaban sa yace "What!! Har Saida Ja'afar ya tsorata ya d'ago Kai yana kallon sa cikin 'bacin Rai da tsawa yace "Haleemah Mahaifiyar tawa Kika cewa haka? Kin gaji da abinda matar Nan take miki? Bata Haifa miki su ba Amma ta haife uban su,To wallahi kinzo layin da bazan lamunta ba duk iskancin ki ya tsaya akaina wannan Kuma shine last warning idan Kika sake magana makamancin wannan koda da wasa ne Akan Mahaifiya ta Wallahi Wallahi sai na nuna miki cewar ke karamar Yar iska ce"
Tunda ya Fara maganar baki a bud'e take sauraron sa kamar tana kallon sa cike da mamaki ta ce "Hameed ni kakewa tsawa amma ko ka manta da wacce kake magana ne?"
"Oh kin d'auka shirun da nake miki tsoron ki nake ji ko? To ki sani ina d'aga miki kafa ne sabida yaran Nan Wallahi da na dad'e da tura ki gidan ubanki, wawayi shasha wacce bata San me takeyi ba, kiiiiit ya kashe wayar.
Da Kallo tabi wayar tana mamaki anya Abdulhameed d'inta ne kuwa?
_______________________
Milhaat ce✍🏻
Yar Terawa
Please comment and share