Free chapter · Read without an account

CHAPTER 7-8

by salmeert sani salman · NAZLAH

☘️☘️NAZLAH☘️☘️





    *DAGA ALƘALAMIN*



SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️.




*WANNAN LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF)WANNAN LITFAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KI YI YARDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI , YA KUMA KARA RUFA ASIRI , DUNIYA DA LAHEERA........*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

    {R.S.W.A}


***

 *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




بسم الله الرحمن الرحيم

 






7-8.






"""""""""""""Yana tafiya Jamseey ta tattaro kayanta gaba daya ita da Ƙanwarta Jasmin suka dawo gidan, tunda suka dawo komai a gidan sukeyi, basa ko dan zuwa gidansu su zauna, sai dai su ɗibi abin ci su bada akai,basa mata aikin komai, kwana biyu kawai gida ya fita daga hayyacinshi, mai aikin da take zuwa tana gyara palon ma Jamseey ta hanata zuwa, Sadiyya kuwa kamar wadda aka Asirce bata iya yin komai, kullum tana tule, duk abi da suka ce mata shi takeyi, bata son ganin bacin ransu ko kaɗan biyayya take musi kamar uwarsu...........






      *********



       



       Tsabar kukan, Ummu ko leqowa waje bata yi ba saboda kawar da kai ga Yaranta, haka Nazlah ta mike ta shiga ɗakin tana kuka, kan jikin Maryama ta zauna tana shasheƙar kuka , tare da nuna mata hannunta, hannun ta rike tana dubawa, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba ganin hannun gaba daya ya tashi, sharw mata hawayen idanunta ta shigayi, ita kuma nata na zubowa, ganin Ummu na kuka yasa itama ta kara fashewa da kuka, dan duk da bata wuce shekara daya da rabi ba amma gaba daya batason ganin Mamarta na kuka..............





      yakice Labulen dakin Lawan ya yi, tare da cewa "wane shege ne yakeson mayar min da gida filim mutuwa, kumin shiru ko na tattaka ku gaba dayanku", ya fada yana daka musu tsawa................






       Shiru Ummu tayi, kanar ruwa ya cita, Nazlah kuwa kara fashewa tayi da kuka tana boyewa jikin Ummu dan gaba daya bata son ganin Lawan ko kaɗan dan kallon mugu take mishi, "dan Ubanki rufemin baki ko nazo na tattaka ki", ya fada yana shirin shigowa ɗakin ,da sauri Ummu ta sanya tafi hannunta ra rufe mata baki, (Allah Sarki Mahaifiya, bata son duk abunda zai faru ga Ɗanta, tana iya jure dawainiyar Yaro tun daga ciki har izuwa haihuwa da raino, kashinka futsarinka, da komai naka ita take gyarawa, ko dan ciwo kaɗan bataso kaji, balle ta kai ga wani yaci zalinka, sai dai kawai tayi kawaici ta kyale bawai dan bataji ciwo a ranta ba, kawai dan mutunci da zaman tare, Allah ka tsare mana Mahaifanmu ka shirya mana Mahaifanmu sannan kaji ƙansu, ka gafarta musu zunubansu, Alfarmar Annabi da Al-qur'ani , Ameeen).






       sakin labulen ya yi, tare da ficewa yana banbamin bala'i, ganin ya fice da sauri ta dauki, Nazlar ta daurata akan gado tare da fara bincikar in da zataga maganin wuta, tasha wuya sosai kafin ta nemo maganin, tana kuka, Nazlah na kuka haka ta ciccire mata fatar da ta tashi, ta barbada mata maganin, bayan ta gama, feeding dinta ta fara yi tana shafa,mata kai tare da busa mata iska a hannunta, bacci mai nauyu sosai ya dauketa, ganin bacci ya yi awon gaba da ita yasa ta sauke numfashi da karfi, tunanin rayuwa ta fara yi, batayi aune ba taji ana kiran Magrib..............






         Sallah tayi, lokacin da zata gama Haleem ya dawo daga aikin kanikancin da aka sanyashi, cikin murna ya matsa gareta tare da cewa "Ummu kalli, Oga na ya bani wannan", ya fada yana nuna mata wata sabuwar naira Ashirin da ya fitar a Aljihunshi, murmushi tayi tare da cewa "Allah ya mata Albarka, kaima Allah ya maka Albarka dama Ƴar uwarka," ta fada tana shafa kanshi, "Ameeen Ummu", ya fada yana jingina da jikinta..............







        idanunshi ne ya hasko mishi ƙunar hannun Nazlah , da sauri ya mike ya nufeta , yana cewa "Ummu mai ya samu Nazlah", ya fada cikin rudu, yana kara kallon hannun, tuni kwalla ta cika mishi idanu dan bayason ganin ciwo ko ya yake a jikin Mahaifiyarshi ko Ƙanwarshi dan yana tsananin Ƙaunarsu fiye da komai, shafa kanshi tayi tare da cewa "Ƙonewa tayi dazun", girgiza kanshi ya yi, tare da cewa "kuma duka hannunwan Ummu ?", ya fada ya kara kallon hannun, "bana son surutu tunda dai ta ƙone ai shi kenan", ta fada tana kawar da kanta daga kallonshi, shiru ya yi bai kara cewa komai ba...............  






            Chan kuma yace "Ummu mai zamu ci da dare", shiru tayi sai kuma chan tace "ga goma chan dauka ka haɗa da kuɗin hannunka ka siyo muku garin kwaki na ashirin sugar ta goma sai kusha", ta fada tana nuna mishi kabet dinta , mikewa ya yi, yaje ya dauka ya fice, minutes kadan sai gashi ya dawo da duk abin da tace,karɓa tayi tare da jiƴa musu, kallonshi tayi tare da cewa "sha ka rage mata", suna cikin maganar ta bude idanunta da suka jaajir , idanunshi na kanta hakan yasa da sauri ya dauketa ya sanyata a jikinsa...........






          fita ya yi da ita ya wanke mata baki, tare dawo da ita, garin ya fara bata,yana bata yana sha, surutu ta fara bashi tana cewa "Abbu! Abbu!! Abbu!!!", "shine ya ji miki ciwon", da sauri ta gyaɗa kanta ,shiru ya yi, dan shi tunda yaga ƙunar zarginshi ya ta'allaƙa ga Mahaifinsu, ganin Ummu bata son zance yasa bai kara magana ba............






         ko rabin garin basu yi ba, Lawan ya shigo baaaga-baaaga, kwace kofin garin ya yi, tare da zama ya fara shaa, Nazlah na ganinshi kamar taga mala'ikan mutuwa, haka ta ringa ƙanƙame Haleem , taƙi yarda ko ido su haɗa.............





    shafa kanta ya shigayi yana karanto mata Addu'ar neman tsari dan har wani firgita takeyi, Lawan na gama shan garin ya kwanta sai bacci, dama ya gama shaa ya bugu.............







     ~********~




        Bayan shekara daya da rabi, a lokacin Nazlah na da shekara ukku chass, ta ƙara zama wata cute gal, tayi wayau sosai ga karatu a bakinta, hakan yasa Iya ta kaita Makarantar tayani gantali dake chan bayansu, ba wata shahararriyar makaranta ba ce, dan sai Yaro na da mugun ƙoƙari kafin ya iya gane abun da ake koyawa saboda cunkushewarsu da rashin Malaman koyarwa, sai dai duk da haka tana ganewa sosai dan bata zama sai layin gaba, sai dai ba halin nan an na kwaɗayi, dan in taga abu miyanta har zubowa yake, tana tanɗar baki, hakan yasa mutane da yawa suka tsaneta, dan da taga mutum na cin abu zata je ta sanyashi gaba tana kallo, ko ta mika mishi hannu.............






      Umma na iyakacin bakin ƙoƙarinta na ganin ta hanata, amma abun ya faskara Haleem ma ya yi iya bakin ƙoƙarinshi, amma abun yaƙi ci yaƙi cinyewa hakan yasa suka barta...........






     sai dai da taga Lawan ko mai tale take take komawa cikin hayyacinta, ana cikin haka aka sanyata wata Islamiyya chan gefen Unguwarsu, Islamiyya ce mai kyau, wadda Fisabillilah wani Bawan Allah ya ginata, domin Gajiyyayu da Marayu, hakan yasa aka kaita chan, Haleem na zuwa aikinshi Ummu ma tana zuwa wani gidan Masu kuɗi tana musu aikatau suna biyanta, sai dai ko kusa bata taɓa zuwa da Nazlah ba dan tasan duk ranar da ta kuskure taje da ita, to wallahi ranar ta tashi aiki, dan korarta zasuyi, dan Nazkah bata gani ta ƙyale ba kuma taga abu batayi kamar ta fada ba, hakan yasa suke iyakar ƙoƙarinsu na ganin sun siya mata abubuwan Makulashe duk san kar ta gani hannu Yara ta roƙa, sai dai ko akwai abu a hannunta da taga na wani sai ta mika mishi hannu, in taga Yaro ne in bai bata ba, ta kamashi ta duka, dan fada gareta sosai ko dage ya shafa matw lafiya a faɗa.............






     Kamar Kullun Yau ma an tasosu daga Makarantar Boko , tana tafe tana karanta A B C D, tana gyada kai da taɓa hannu, idanunta ne suka hararo mata Wata Yarinya da Alale a hannunta tana ci, kamar Walƙiya baga ta kwasa a guje, gaban Yarinyar ta tsaya, tare da cewa "Kandala", ta fada tana murmushi tare da haɗiyar miyau.............






       Harara ta dalla mata tare da cewa "lafiya zaki tsayamin aka", ta fada tana ci gaba da cin Alalenta, murmushi tayi tare da zama kusa da ita tana cewa "ai abun ba na fada bane, Ƙawata", ta fada tana dafa kafaɗarta, sauke hannunta tayi tare da cewa "wace ce Ƙawar taki?, yanzu ne kikasan da ni a matsayin Ƙawarki, yanzu da kika ga abun duniya ko, to wallahi ahirrr dinki, dan ko zaki mutu ba zakici Alalen nan ba", ta fada tana dauke kwanonta ta mayar gabanta, "ke Dalla ki ajiye muci nima anjima in na siyo abuna zan baki", ta fada tana mika hannunta cikin kwanon.................






       kwaɓe hannunta tayi tare da cewa "Cire kin hannunki a cikin abuna", ta fada tana mikewa, cikin jin haushi tace "to wallahi sai na ci ko zaki mutu dan ma in binki cikin lalama", ta fada tana dalla mata harara.........





     ta fada tana fige kwanon hannun Kandala, wawushewa tayi tare da turata baki duka, wani azababban Mari Kandala ta sakar mata, tare da riketa mata wuyan riga tace "Wallahi ko da wannan Uban naki dan caca kike yawo sai kin biyamin alalena", ta fada idanunta na tara hawaye...............






     Tsalle Nazlah tayu tare da ƙifa mata wani wawan mari tare da cewa "ke dan Ubanki har kin isa ki zagi Ubana, naga ai tare da ubanki suke cacan dan haka babu kin ga ba sauran gori", ta fada tana dukan kirjinta tare da kama wuyan rigarta............







         fada ne sosai ya kaure a tsakaninsu, gashi unguwar babu yawan mutanen da suke zirga - zirga hakan yasa babu wanda ya rabasu, Hannu Nazlah ta daura akan Kandala, Jelar gashin dokin da aka sanyawa Kandala ta kama, tare da ja cisgowa gashin dokin ya yi , tare da gashinta gaba daya, jini ne ya fara zuba, ganin haka yasa da sauri Nazlah ta saketa tana zare ido, shafo kanta Kandala tayi ganin jini yasa ta zaro idanunta...............






     Sakin Nazlah tayi tare da dafe kaiiii, ganin ta saketa yasa ta falla da gudun tsiya ba inda ta tsaya sai gidan Iya dan tasan ta koma gida Ummu batanan kuma ko dafata za'ayi sai ayi a gama bata dawo ba, da gudu ta shiga gidan Iya, Iya da take bakin murhu tana ƙoƙarin hada wuta da sauri ta mike tana cewa "Kayya! Kayya!! me ne ne?", ta fada tana zare idanunta, sai da ta kai kofar dakin Iya kafih tace "Iya fada muka yi da Kandala har na cirw mata taura(jelar gashi) daya kuma wallahi ga jini na zuba " ta fada tana sakin futsari saboda tsoron da take ciki...............







       "Mtswwwww wace Kandala, ita abun da takeyi a cikin garin nan ai sai a daure Ubanta, kema ranar ba ta duke ki ba, dama ai rama cuta ga macuci ibada ne, ni da in kai karar Ɗa gwara a akawo min kararshi, " bata rufe haki ba Delu Uwar Kandala tayi Sallama, da gudu Nazlah ta banka karkashin Gadon Iya ta shige tare da rike bakinta tayi lakur.............







Huci Delu ta fara yi tare da cewa "In wannan shegiyar Jikar taki take?",ta fada tana kallon Iya , cikin fada Iya tace "kul kar ki kara shegantamin Jika in ba haka ba zan nakaɗa miki tsinannan duka a cikin gidan nan", ta fada tana harararta, tula mata jelar gashin tayi tare da cewa "gashi nan ta cirewa Kandala jelar gashi kuma wallahi gidan mai gari zan kai, dan bazan yarda ba", ta fada tana dafe da kan kandala da take ta kwaɗa ihu.............






      yar dariya Iya tayi tare da cewa "kim dade baki kai gidan Sarki ba, ke in ana biya ta Ƴarki ai da yanzun an kasheta har laheera Ƴar da har ƙarƙashin gadon Uwar Yaro take binshi ta dukeshi, shine dan an taɓata zaki ringa wa mutane zancen banza, to kin dade baki kai kara ba, ni kuma daga nan har bangon duniya zanje domin kare jikata

", ta fada tana shigewa ɗaki, dan haushi ficewa Uwar Kandala tayi, bata ƙara cewa komai ba, dan tasan in bala`i take ji dashi Iya ta fita...............





    **************





    Tun da ya dawo aiki yake fama da matsanancin ciwon mara da ya rasa yarda zaiyi, har wasu hawaye ke zubo mishi,yanzu haka kwance yake rike da mara yana juyu cikin fitar hayyaci, Wayarshi ce ta fara ring , dakyar ya iya gangarawa gefen da take ya dauka, dakyar ya iya cewa "Hello!", daga chan ɓangaren akace "hi Buddy ya kake?", jaan numfashi ya yi da azabar karfi tare da cewa " ba lafiya ba ", cikin dan damuwa Khalil yace "mai yake damunka", numfashi ya sauke tare sa cewa "matsanancin ciwon mara dakyar na iya dawowa daga aiki", dan tsaki yaja tare da cewa "har yaushe zaka yi ta fama , tunda matarka ta ƙi zama a tare da kai kawai kaima ka ɓalle bushashaeka ko haka zaka zauna kana cutar rayuwarka in zaka tsaya ka bude idanuka ka shiga duniya ka shiga, in ba haka ba ka mutu a banza wallahi, y...............






*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, KI DAURE KI BIYA KUƊINKI HAJIYA, DOMIN BA ZANYI FREE PAGES DA YAWA BA, CMPLT DINSHI #400 NE, TURAWA PC #300, GROUP #200, SIYAN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA , DAGA ALƘALAMIN SALMAJI/SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️*





   1499884120

    UMMASALMA SANI.

    ACCESS BANK.





*KU TURAMIM SA SHAIDAR BIYAN TA HANYAR YIN SCREEN SHOT KU TURAMIN TA NUMBER TA KAMAR HAKA...*





***.





~DAGA ALƘALAMIN SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE~🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol