Free chapter · Read without an account
Two house
by Azizat Hamza · ZAYTOONAH
*Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*11-two house*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Rayuwa kam ta cigaba da juyawa. Zaman haƙuri kam shi Maryam ke yi a gidan T J. Iya ta zame mu su kujeran zama, ta gina katanga tsakanin farincikin masoyan. Duk wani tuggu da munafurci da ta ke yi Maryam ba ta kulata.
Watanni kaɗan bayan haihuwar Hajjo Maryam ta fara aiki. Hajjo ta samu 'ya mace aka yiwa Iya mai suna amma Humairah ake kiranta, da wurwuri T J ya je aka gwada ta inda aka tabbatar ma sa AS ce ba SS ba, hakan ya sa hankalinsa ya kwanta. Duk kuɗin da ya kashe a wajen Suna Iya da Hajjo ba su gani ba acewarsu bai yiwa Humaira hidima ba kamar yadda yai a Sunan Zaytoonah. Lokacin hidiman ginin gidan sa ya ke yi amma a hakan ya daure ya fitar da maƙudan kuɗi akayi hidiman Suna da shi.
Yadda Iya ke tsananin ƙin Zaytoonah haka ta ke nunawa Humairah tsananin so. Ko da wasa ba ta taɓa ɗaukan Zaytoonah ba ko lokacin da ta ke rarrafe idan by mistake ta rarrafo ta wajenta to haka za ka ga ta make ta. Zaytoonah ta dinga kuka idan Auwal na kusa ya ɗauketa yai ta lallashi idan kuma Maryam ce ke kusa ta ji kukan ta ta zo da sauri ta ɗauke 'yarta.
Renon Humaira kaf a hannun Iya ya ke. Har yarinyar ta shafe watanni duk hidimar fitsari da kashinta Iya ke yi. Hajjo dama son jiki ga shi ta samu Iya ba ta iya kwaɓarta saboda ita 'yar yayarta ce kuma 'yar Fulani ba kaman Maryam Inyamura ba.
Maryam kam ta zuba mu su ido, tunda ba a son 'yarta ita tana son kayanta. And besides yafi ma ta ma da ba sa shiga harkan 'yarta kar su koya ma ta mugun abu. T J kuma sai dai ya nunawa Zaytoonah kulawa a cikin ɗaki bai isa ya nuna a waje ba.
Karon farko da Maryam ta fara fita aiki Iya ta dakatar da ita, wai yawon iskancin ya isa haka ba inda za ta je. Maryam ta yi biris da ita ta cigaba da tafiya dama T J ya tafi wani comference na kwana uku a Lagos. Daga dawowan shi Iya ta ce ba ta yarda Maryam ta dinga fita aiki ba. Daya fara ƙoƙarin yi ma ta bayanin mahimmancin aikin sai ta ce idan har bai hana Maryam fita aiki ba za ta tsine ma sa.
Ranan da dare ya samu Maryam ya lallaɓata wai ta haƙura da aikin na lokaci kaɗan kafin Iya ta huce tukunna. Ta dinga jin zancen shi har ya gama ba ta nuna ta damu ba.
Washegari yana fita ta ɗau 'yarta sai Ringim. Gaban Baffah Umar ta je ta kai ƙaran TJ da Iya ta kuma rantse ma sa cewa muddin ya ce ba za ta cigaba da aikinta ba za ta bar mu su gidan.
Baffah Umar bai yi boko ba kuma a da yana ƙin boko musamman na 'ya'ya mata amma yanzu ya fara ganin Alfanun Bokon dan kwanaki wata 'yar abokinsa da ta cigaba da karatu bayan aurenta sai gashi yanzu ta zama babbar Likita. Ya kai uwargidan sa babban Asibitin Murtala ne a Kano ya haɗu da ita, shi bai ma gane ta ba sai da ta ma sa bayani akan ita ce 'yar abokin sa Malam Saleh Audu. Har aka sallamesu yana mamakin yadda akayi Usaina ta samu baiwar ilimin magani haka. Kamar ba ita ba ce shekaru shatakwas da su ka wuce ake rigima akan aurenta saboda mijin da za ta aura ba Bafulatani ba ne, Asalin su Jarawa ne daga Dass amma kasuwanci ya zaunar da su a Kano.
Dan haka bai ga aibu acikin aikin da Maryam ke yi ba da har Iya za ta yi mummunan furuci akan sa.
Kwana biyu ta yi a Ringim suka koma Zaria da Baffah Umar ɗin. Ya je gidan ya sissille Iya, yai Allah wadarai da halinta. Dama Baffah Umar shima lokacin ƙuruciya an taɓa ƙiriniya dan haka a Umar ɗin sa ya fito ma ta.
Nan take ta sha jinin jikinta, ta sani dama duk cikin yaran Modibbo, Umar da Babbar yarsu Fatima sun fi kowa taurin rai da faɗa. Ko a da ɗin ba ƙaramin tsoron sa ta ke ji ba.
Bayan yayiwa Iya na ta faɗan ne ya koma kan T J wanda shima faɗa sosai ya ma sa ya kuma yi ma sa tuni da amanar Maryam da Baffan sa ya bar ma sa.
Daga wannan zuwan Baffah Umar ɗin ne Maryam ta samu damar komawa bakin aikinta hankali kwance...
***
Zaytoonah na da shekara uku T J ya kammala ginin sa. Gida ne da tun farkon aurensa da Maryam yai foundation ɗin yadda tsarin zai kasance sai dai kuma komai ya chanja ma sa lokaci guda tunda yanzu mata biyu ya ke aure ga kuma Iya da ta ke zaune da su babu ranan tafiya.
Maryam ya fara kaiwa gidan ta gani ta kuma sa albarka. Ɗakuna biyar ne a gidan ya gina ne da niyyar ɗakin sa ɗaya sai ɗakin Maryam sai ɗakuna biyu na 'ya'yan su da kuma ɗakin baƙi.
Amma yanzu tsarin ya chanja ya koma ɗakin sa, sai ɗakin Iya, ɗakin Maryam da Hajjo sai ɗaya ɗakin na Auwal da yara mazan da za su haifa.
Akwai babban falo sai kitchen da store.
Ra'ayin Maryam ya tambaya akan yadda za a saka furnitures ɗin gidan. Abu ɗaya da ta yi magana a kai shine a mayar da store ɗin ya koma kitchen saboda ba za ta sharing kitchen da Hajjo ba. Ko ba ta yi bayani ba ya san tana cutuwa. Bai yi musu ba ya amince da hakan dama ba ariga anyi kitchen shelves da wardrobe ba, ko kitchen sink ma ba a sa ba...
Cike da farinciki ya sanar da Iya cewa za su koma sabon gida ƙarshen wata. Amsar da ta bashi sai da ya sa numfashin sa ya ɗauke na ɗan wasu daƙiƙu.
"Iya dan Allah kiyi haƙuri, na san ba kya son Maryam amma Iya kamar yadda Hajjo ta ke matata haka Maryam ma ta ke. Idan na yi haka ban ma ta adalci ba kuma..."
"Idan kuma korata za ka yi a gidanka sai ka faɗa amma ka sani ba zan zauna da karuwar Inyamurar da ka ajiye a gida ba. Wannan zaman da na yi ma kullum cikin fargaba na ke"
Daga tsugunnen da ya ke ya zauna daɓas a ƙasa gumi na keto ma sa ta ko'ina.
Shi yanzu ya zai yi da Iya, ya zai yi da Uwar da ta haifeshi wacce ke neman rusa ma sa duk wani farincikin sa.
Ta ina zai fara kallon Maryam da zancen Iya ta ce ba za ta tare tareda su ba.
Shi yanzu kunyan kai ƙaran Iya ya ke ji saboda kullum kimarta zubewa ya ke yi a wajen 'yan uwan Baban sa.
Daren ranan da zazzaɓi ya kwana, daɗin abin ma ɗakin Hajjo ne ba Maryam ba. Da Maryam ce tsab sai ta gane yana cikin matsala. Ita kam Hajjo baccinta kawai ta sha har da mimshari.
Washegari da zai fita Maryam ta lura da yanayinsa. Ta tambayeshi ko lafiya ya ce ma ta ba komai.
Da ya koma ɗakinta kuwa ta ma sa tambayar duniyan nan akan mi ke damunsa ya ce ba komai yana tunanin yadda zai fara Phd ɗin sa ne nan ba da jimawa ba kuma ba kuɗi a hannun sa.
Maryam ta san ƙarya ya ke yi amma ta ƙyaleshi tunda baya son faɗa ma ta matsalar sa.
Itama ya sanar da ita ƙarshen wata za su koma sabon gida amma har ya saura kwana shida ba ta ga an fara shiri ba. Da ta tambayeshi sai ya ce an fasa tarewar akwai wasu ayyuka da ba a gama ba. Ta yi shiru ba ta kuma cewa komai ba, T J ɗin da ta sani has being behaving strange wanda ta san duk yadda aka yi wani abu ne daya danganci tsakanin sa da Iya.
Tunanin ƙara aure ne ya fara zuwa ma ta. Ƙila tunda ya yi gini Iya ta ce ya ƙara aure su zama su uku. To daga baya kuma sai ta fara tantamar haka. Dan Hajjo da Inna ba za su yadda da wannan ba.
To amma minene?
Ta dai bar tambayar a ranta zuwa lokacin da T J zai furta ma ta matsalarsa da kan sa.
Saura kwana uku tashin su ya sanar da Iya an fasa tashin sai wani watan saboda za'a ƙarisa wasu gurare da ba'a gama ba.
Iya ta fara masifa wai ta san ƙarya ya ke yi. Idan kuwa dan baya son bin maganarta ne to ita gobe za ta bar ma sa gidan idan ya so ya je ya tare da Maryam tunda ya fi son matar sa akan uwar da ta haifeshi.
T J ya shiga ba ta haƙuri amma fir ta ƙi.
Duk abinda aka yi a idon Auwal hakan yasa ya ji haushin Iya sosai.
Maryam na dawowa ya tareta da murna ya fara ƙoƙarin ɗaukan Zaytoonah wacce ke cin biscuit duk ta ɓata bakinta da uniform ɗin ta. Ta maƙe kafaɗa tana faɗin "leave me"
"Auwal ajiyeta kawai tun ɗazu ta ke damuna da rigima"
Nursery one Zaytoonah ta ke, da an tashi a makaranta Maryam ke zuwa ta ɗaukota ta wuce da ita office ɗin ta, idan ta tashi a office sai su dawo tare. Wani lokaci kuwa T J ne ke zuwa ya ɗaukota ya wuce da ita na shi office ɗin idan ba shi da class a lokacin.
Bayan ta yi wanka ta yi sallar la'asar ne ta fito ta shiga kitchen dan ta fara girkin dare, yanayin jikinta kwana biyun nan ba ta gane ba tana hasashen ma ko ciki gareta dan kwana takwas kenan ba ta ga jininta ba. Tana son zuwa Asibiti ta tabbatar da hasashenta amma gaba ɗaya she's busy a office idan ta dawo kuma ta gaji.
Tana yanka alayyaho sai ga Auwal da Zaytoonah sun shigo sanye da uniform ɗin Islamiyya.
Zaytoonah na cin wani chocolate baki da hannu duk yayi dumu-dumu da shi.
"Auwal yanzu sai da ka bata chocolate ɗin nan bayan na hanaka"
"Mommy cewa ta yi idan ban ba ta ba bazata je Islamiyyan ba"
"Oya come here" Maryam ta faɗa da ɗan ƙarfi
Zaytoonah ta ɓoye a bayan Auwal tana wiki-wiki da ido dan ta san yanzu za ta ƙwace chocolate ɗin.
"Zaytoonah"
Kawai ta ɓare baki da kuka. Maryam ta jijjiga kai kawai ta ce " ku je Auwal amma ka share ma ta baki da hannu kafin ku fita"
"Ke kuma zanyi maganin ki, tukunna ma chocolate nawa kika sha a office yau?"
Zaytoonah ta ɗaga yatsunta huɗu still tana maƙale da Auwal ta ƙi isowa wajen Maryam dan ta san halin mommyn na ta ba ta dukanta amma kunnenta zai sha murɗa.
Bayan sun fita sai kuma Auwal ya dawo da sauri ya fara yiwa Maryam magana ƙasa-ƙasa. Hajjo dai ba ta gida ta fita unguwa amma Iya na ɗaki.
"Mommy yau da rana kafin ki dawo Iya ta dinga yiwa Daddy faɗa, ta ce wai ba za ki koma sabon gida ba. Kuma fa Daddy har kuka ya ma ta amma ta ƙi sauraren shi, ni kam indai ba za ki koma sabon gida ba nima ba zan je ba"
Tunda ya fara maganan ta ƙura ma sa ido. Auwal yana da wayo, shekarun sa goma yanzu, yana aji huɗu a primary. Mafiya yawancin lokaci idan anyi wani abu a gidan a bakin sa ta ke ji, shima ya gane Iya da Hajjo ba sa son Maryam kuma suna ma ta munafurci, shiyasa ma ya tsanesu ya fi damuwa da Mommynsa Maryam.
"Auwal ku wuce Islamiyya" abinda ta iya faɗa kenan saboda zuciyarta da ya cunkushe.
Sai yaushe wannan Matar za ta dena ci ma ta fuska.
Ina ma Goggo ce ta haifi Tijjani, da za ta fi kowa sa'ar uwar miji.
Amma Iya, Iya, Iya sai dai kawai Allah ya rabata da ita lafiya.
Iya ta yi kishi da Goggo yanzu kuma da ita ta ke kishi.
Ba ta ga laifin Baffah da ya fi son Goggo ba lokacin yana raye. Kyawawan halayenta su suka sa ta samu babban matsayi a zuciyarta. Iya ta ƙare rayuwan aurenta acikin baƙin kishi, gashi yanzu da tsufanta ma ba ta bar kishin ba.
Illiteracy, Greedy and Envy su ne manyan abubuwan da su ke damun Iya cikin ukun ba ta san wanne ne ma yafi wani yawa a ciki ba.
At first ta ɗauka haihuwar Zaytoonah zai sassauta tsanar da Iya ta ma ta amma abun ba haka yake ba. Matar da har sheganta ma ta 'ya ta ke yi.
Tun kafin Zaytoonah ta yi wayo ta gane ƙiyayyar da Iyan ke ma ta yanzu ma da ta fara wayo ko gaisheta ba ta yi.
Countless times ta kan cewa Maryam "Mommy i hate Iya"
Maryam ta kwaɓeta akan ta dena faɗin haka.
Da sanyin jiki ta ƙarisa girkin. Ta gyara kitchen ɗin ta koma ɗaki. Tsayawa ta yi bakin hoton T J da ke jikin frame a bangon ɗakin. Sanye ya ke da kayan bautar ƙasa yana murmushi.
Yana daga cikin ƙaddararta ta haɗu da T J, yana daga ƙaddararta ta faɗa makauniyar soyayyar sa, yana daga ƙaddararta ta wahala a zama da shi.
Despite everything ko kaɗan soyayyar da ta ke ma sa bai ragu ba.
Ta jima tana kallon hoton kafin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta bar wajen.
Da dare T J bai dawo da wuri ba har goma, gaba ɗaya Maryam ta damu sosai.
Ta san maganan Iya ne ya sa shi ƙin dawowa da wuri.
Ƙarfe goma da minti ishirin da biyar ta ji shigowar sa gidan.
Ya buɗe ƙofan ɗakinta ya ga wuta a kunne. Suna ido huɗu da shi yai saurin kau da kai yana faɗin " ba ki kwanta ba?"
Takalmin sa ya cire ya sa gefen ƙofa ya zo ya zauna a gefenta.
"Sorry na tsaya duba assignment ɗin yara ne a office ban san dare yayi har haka ba"
Hannun sa ta kamo ta ce " ba sai ka yi bayani ba na san komai. Barin kawo ma ka abinci"
"No ki barshi gobe zan ci ɗumame" ya faɗa yana miƙewa dan ya cire kayan sa
"Da ka ci abincin kuwa sai na maka albishir da abubuwa guda biyu"
Ya ɗan juyo ya kalleta ya ce "Maryam dare yayi ba zan iya ci ba. Ki gaya min albishir ɗin"
Tausayin sa ta ji ya kamata, hatta maganar sa chanjawa ta yi, ga idon sa da yai jaa.
"To barin haɗo ma ka tea"
Tana da flask ɗin ruwan zafi a ɗaki dan haka fita ta yi ta je kitchen ta ɗauko cup da spoon. Ta ɗau kayan tea da ke saman drawer ta haɗa ma sa tea mai kauri wanda ya ji sugar sosai kaman yadda ya ke so.
Ya cire kaya ya sanya jallabiyar sa da ya ke bacci da shi, yana zaune bakin gado yayi tagumi, ta cire hannunsa daga tagumin da yai ta ce "ka sha tea dan Allah"
Ya karɓi kofin ya ce na gode.
Ta hau gado ta koma bayansa ta fara masa massage ɗin goshin sa a hankali a hankali daga nan kuma ta koma wuyan sa zuwa kafaɗar sa.
"Minene Albishir ɗin?"
"Ka shanye tea ɗin tukunna" ta amsa ma sa ta cigaba da danna ma sa kafaɗun sa.
"Adaeze ta miki rigima a office ko?"
"Kai ma ka san za ta yi tunda kai ta ɗauko wajen rigima"
Yai murmushi yana lumshe ido saboda yadda ya ke jin daɗin tausar da ta ke ma sa.
"Ka san dai kanada hawan jini amma sai ka dinga sawa kan ka damuwa"
"Maryam..."
"Ka bari na gama magana please. Yanzu idan wani abu ya sameka ya ka ke so na yi? Abu na daminka ba za ka faɗa ba. Its better ka gaya min tun da wuri rather than sai daga baya na ji ko kuma na ji a bakin wanda bai kamata ba"
"I'm sorry"
"Shshhhh. The first surprise is"
Ta kamo hannunsa ta sa a cikinta.
"I'm 90% sure ina tareda junior Teejay"
Ya juyo da sauri yana zaro ido
"Really?"
"Ban je na yi gwaji ba amma ina jin symptons ɗin"
"Alhamdulillah, Maryam you really make my day" ya faɗa fiskan sa ɗauke da excitement
"And the second surprise is..."
Ya ɗaga gira yana jiran ta ƙarisa maganar
"Na amince zan zauna a nan, its actually a good idea. Rather than na zauna da su Iya ina zama cikin damuwa kullum is better mu zauna gida daban-daban. You dont need to kill yourself because of that"
Jikinsa a sanyaye ya tallafo fiskarta ya ce " its not fair Maryam. Da sunan ki na fara ginin nan and"
Ta sa yatsa ta rufe bakinsa ta ce " idan Allah ya buɗa ma ka wani lokacin sai ka gina min nawa gidan ko ka siya min wani gidan. Ni ban ji haushin Iya ba, zaman lafiya ma ta kawo mana"
Cire yatsar ta da ta yi yai daidai da haɗe bakin su da yai.
"Mommy tea, i want tea" muryan Zaytoonah ya daki kunnuwan su.
Maryam ta juyo ta kalli 'yartata wacce tuni ta riga ta buɗe ido.
"Ya Allah! this girl can eat from morning till night, duk abincin da ki ka ci kafin ki kwanta bai isheki ba"
T J ya ce " kar ki takura min Princess"
Ya mirgina ya je wajen Zaytoonah ya ɗauketa. Ita kuwa Maryam ta ɗau kofin da T J ya sha tea tana ƙunƙuni tana haɗawa Zaytoonah tea. Tun tana shan nono yarinyar ke da masifar ci, duk dare sai ta yi kukan abinci, shan nonon tsakar dare jazaman ne. Yanzu ma da ta girma ci gareta kamar gara, lokaci zuwa lokaci kuwa za ka ga ta tashi da dare wai a haɗa ma ta tea wani lokaci har da bread ake haɗa ma ta ta ci musamman idan T J ne ya haɗa ma ta...
Ba kunya ba tsoron Allah Iya da Hajjo su ka koma sabon gida. Auwal ya ce ba zai bi su ba. Iya ta ce bai isa ba. T J ya roƙeta akan ta barshi zuwa ya ƙarisa makaranta sai ya koma gidan su idan ya so sai ya fara Jss 1 ɗin a cikin gari. Da ƙyar dai Iyan ta bar shi.
Neighbors ɗin su sunyi mamakin rashin tarewar Maryam musamman wanda su ka je su ka ga gidan kuma su ka tabbatar gida ne Babba da zai ishi dukkan su. Maryam ta kan ce mu su sabo da zaman quarters ya sa ba ta son tafiya. Ko daƙiƙi ya san wannan ba hujja ba ne.
Bayan kwana biyu da tafiyar su da ta kama Saturday Maryam da Auwal su ka shiga gyara gidan. Ɗakin Hajjo da na Iya duk sai da su ka wanke shi su ka goge, sosai su ka gyara gidan ya fito yai tsab da shi. Duk wani tarkacen su da su ka bari sai da su ka yi waje da shi.
Da T J ya zo yai ta faɗa akan za ta yi aiki bayan ba ta da lafiya. Ta ce mishi dole ne ta yi dan tun asali haƙurin yadda gidan ya koma ta ke yi. Hajjo irin matan nan ne da duk kyaun gida sai sun ɓatashi saboda ƙazanta.
Rayuwa ta dawo mu su sabuwa. Zai zo yai kwana biyu a wajen Maryam ya je yai wa Hajjo kwana biyu. Ɗakin Maryam da ke chan kullewa yai saboda bayaso a ɓata ma ta furnitures ɗin ta.
Maryam ta ma sa halacci shiyasa ya shiga neman gidan da zai siya a anguwar na su. Ba shi da kuɗi dan shanunsa ma duk ya siyar saura ɗaya da ƙarami ɗaya. Amma duk da haka idan ya samu gida ko nawa ne zai nemo ya siya hankalinsa ba zai taɓa kwanciya Hajjo na zaune a sabon gida ita kuma Maryam na quarters ba.
Bayan wata biyu da tarewan su ya samu Alhaji Iliyasu Mai Auduga. Alhaji Iliyasu na ɗaya daga cikin mutanen da su ka fara zama a anguwan. Yana da gidan sa da ya ke zaune yana kuma da kusan gidaje takwas da ya gina flat flat yana bayarwa haya.
Ɗaya daga cikin gidajensa ne wasu su ka tashi dan haka T J yai maza ya samu Alhajin akan yana son siyan gidan. Gidan da gidan T J ɗin gidaje shida ne tsakanin su.
Alhaji Iliyasu ya ce ba zai sayar da gida ba. T J yai yai da shi ya ƙi.
Ganin ya ƙi ne ya sa shi fayyace ma sa abinda ya faru da kuma dalilin son siyan gidan da ya ke son yi. Baya son iyalen sa su kasance suna nesa da juna saboda sauƙin samunsa idan wani abu ya faru baya gidan ɗaya.
Alhaji Iliyasu yai shiru sai kuma daga baya ya ce " ka ci albarkacin kai mai sunan Shehu ne. Zan siyar ma ka da gidan"
Alhaji Iliyasu yana bin mazhabar ɗariƙan Tijjaniyya shiyasa ma tun lokacin da ya fara zuwa anguwar da ya haɗu da Alhaji su ka gaisa su ke mutunci ba ya taɓa kiran sa da Tijjani sai dai Shehi.
Bayan sun tsaida ciniki T J ya wuce Ringim ya sayar da gonakan sa ya haɗa da babban saniyar sa ya siyar. Still kuɗin bai cikata ba Goggo ta siyar da Sa ɗin ta ta bashi kuɗin ya ce ba zai amsa ba. Tayi-tayi da shi ya ƙi ƙarɓa.
Ta ce ma sa indai bai karɓa ba ya nuna Iya ce uwarsa ita bai ɗauketa a matsayin uwa ba, hakan ya sa ya karɓi kuɗin yana ƙara jinjina kyawawan halayen Goggo wanda ta shi Uwar ta rasa.
Da kuɗin da kuma aron kuɗi da yai a wajen abokinsa Suleman kuɗin gida su ka cika. Ya je ya biya Alhaji Iliyasu kuɗinsa.
Bayan ya samu makullen gidan ya je ya duba gidan ya ga irin gyaran da za a mishi. Gidan dai zai kai shekaru shabiyar da ginashi, ginin na da kyau kuma mutanen da su ka zauna a ciki na ƙarshe sun kula da gidan sosai.
Da ya tafi ya je ya kira ma su gyara su ka duba abunda za a gyara su ka faɗi kuɗin da za su karɓa.
Cikin sati uku gida ya gyaru har da sabon fenti aka yiwa gaba ɗaya gidan.
Duk abunda yai bai gayawa Maryam ko Iya ba. Sai da ya kammala komai na gida sannan ya gayawa Maryam ta shirya za su je wani waje gobe. Ba ta kawo komai ba ta ce to.
Su na zuwa ya damƙa ma ta makullin gidan ya ce gidan ta kenan kafin Allah ya hora ma sa a gaba ya gina ma ta wani gidan.
"Love ba ka da kuɗi fa" ta faɗa cike da tausayin sa.
"Ba abinda zan ce sai dai ki yi haƙuri. You deserve more than this amma for now kiyi haƙuri da wannan"...
***
Sai da Maryam ta koma sabon gidan ta kafin ya sanar da Iya. As usual dai sai da ta yi ƙorafi, tare da Hajjo su ka je su ka duba gidan wai ko gidan Maryam ɗin ya fi na Hajjo. Gida ne madaidaici daya ke ɗauke da falo da ɗakuna uku kowanne yana da banɗakin sa. Su ka karkaɗa ƙafafuwan su suka tafi.
Duk wasu mahimman abubuwan sa gidan Maryam ya kai ya ajiye.
Auwal kam ganin sun dawo anguwa ɗaya ya sa ya ƙi komawa gidan Hajjo ya zauna a gidan Maryam. Iya ta yi masifan ta yi zagin amma ya ƙi komawa wajen su dan haka dole ta haƙura ta ƙyaleshi.
A hankali cikin Maryam ya girma wataranan Asabat su na tareda T J ta tashi da naƙuda T J ya kai ta Asibiti zuwa ƙarfe huɗun Asuba ta haifi ɗan ta namiji, kamanninsa sak T J.
Wannan karan a Zaria aka yi suna kuma kamar yadda Iya ba ta halarci sunan Zaytoonah ba haka wannan ma ba halarta ba. Ita dai Hajjo ta je sunan.
Wannan karan ma Goggo ce ta zauna ta yiwa Maryam wanka. Bayan sati shida ta koma Ringim. Maryam da T J sun so ta cigaba da zama da su amma ta ƙi ta ce ta fi so ta mutu a ɗakin aurenta. Duk da Baffah ya jima da rasuwa amma har yau a matar Baffah ta ke jinta ba a Bazawara wacce mijinta ya rasu ba.
Har Goggo ta zo ta tafi Iya ba ta zo ta gaisheta ba. Ita kuwa Goggo har sau biyu tana zuwa gidan da za ta tafi ma sai da ta je ta ma ta sallama.
Wannan karan T J bai yi gigin yiwa ɗansa mai sunan wani ba. Maryam ya ce ta zaɓawa ɗansu suna ita kuwa ta zaɓi SALMAN.