Free chapter · Read without an account
Anorexia (ku karanta kafin ku karanta Confessions)
by Azizat Hamza · ZAYTOONAH
Ku karanta wannan kafin page 16 (Confessions)
(Idan baka son dogon bayani kaje chan ƙasa)
*15-Anorexia*
Bismillahir Rahmanir Rahim
Name calling shine abu na farko da ke ɗagawa ma su ƙiba hankali. Wasu kan kau da kai su nuna sunan da ake kiran su da shi baya damun su alhali kuma deep down abin na ƙona mu su rai.
Wasu kuma tun suna damuwa har sun mai da abun jiki sun dena damuwa da hakan, sun rungumi halittar su kuma suna son kan su a yadda su ke duk da kuwa kullum ana cigaba da judging na su.
Akwai wanda kuma yadda ake kiran su da sunaye mabanbanta wanda ke nuna izgili da cin mutunci yana karya mu su confidence da courage ɗin su. Sai ka ga maimakon ka gan su suna kazar-kazar kamar kowa sai ya zama ba su da wannan kuzarin. Su na jin zafin maganganun mutane, idan sun shiga wajen da mutane sirara su ke sai su dinga ganin kan su kamar ba su cika ba kamar sauran, kaman su ɗin daban ne da waɗancan mutane, kaman su ɗin abun aibu ne a cikin Jama'a.
Zaytoonah ta faɗa cikin irin waɗannan mutane. Despite the fact Daddynta na yawan nuna ma ta ƙibanta ba shi da yawa sannan tanada kyau a yadda ta ke hakan bai boosting self esteem ɗin ta ba.
Ga Humairah ma da ke ji da tashen balagar ta kullum su ka haɗu sai ta tsokaleta 'yar ɓukuta,'yar kitiɓirɓir, Tindirƙa, Sukumbiya. Ko a ina ta ke samun ugly sunayen nan oho.
Tun Zaytoonah na iya maida ma ta Martani har ta dena.
Humairah wani jiji da kai ta ke yi a shekarunta shabiyu. Ga shi ta fara period ita kuwa Zaytoonah da ke shauku ba ta fara ba. Falli da tashen balaga haɗe da kwaɗayi ya sa ta ke ƙin zaman gidan su. Sai ta je ta wuni a gidan Uncle Muntari, ta ci cima mai daɗi. Daga baya ma cewa ta yi wa Iya su koma gidan Uncle Muntari gaba ɗaya. Iya ma dai na son komawa kawai tana ganin Tijjani ba zai ji daɗi ba ne idan ta bar gidan sa ta koma gidan Muntari zai ɗauka saboda gidan Muntari ya fi na sa kyau ne shiyasa ta bar gidan.
Amma da Humairah ta takura sai gashi Iya ta yiwa T J maganar, shi kuwa yace Allah ya zaunar da su lafiya. Bai ji daɗi ba kam tunda ya riga ya saba da zamanta a gidan sa.
Ɗakunan ƙasa aka ba su, ɗakin Iya daban ɗakin Humairah daban, Humairah sai murna ta ke ɗakinta na yanzu ya fi na da girma da kyau.
Ba su da matsala da Anty Hanne dan ba ta shiga harkan su. Tana da mai aiki da ke mu su girki da duk wani hidiman gidan. Ita sai dai ta ci ta sha ta kwanta. Ta ma nemi gurbin karatu a ABU amma ba ta samu ba saboda result ɗin ta na secondary bai yi kyau ba hakan ya sa ta ce za ta sake zanawa.
Zaman su a gidan da ɗan kwana biyu ne Iya ta fara sa ma ta ido akan shiru da ta ji har yanzu. Ranan da ta isheta da tambaya wai ko ta yi planning ne.
"Iya ki tambayeshi sau nawa ya ke nemana a wata. Idan ya baki amsa sai ki dawo na gaya mi ki dalilin jin shiru da ki ka yi"
Jin amsar da ta ba ta ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru, da Hajjo da Hannen duk da ta ɗauka 'ya'yan uwanta ne babu wanda ya ɗauketa da wani daraja amma a hakan ba ta iya yi mu su komai sai ma tsoron su da ta ke ji. Sai Maryam Inyamura ne aka renawa hankali.
Da ta samu gogan da maganar haihuwa kuwa cewa yai shi baya son sa'ido. Idan lokacin haihuwan Hanne ya yi za ta haihu.
Dama shi ɗa nagari, ɗan ƙwarai wanda ya san hakkin iyaye shi ake tanƙwarawa amma ɗa marar tarbiyya kamar Muntari sai dai a bishi da ido da addu'a. Duk wani mulki da ta ke zubawa a gidan Tijjani babu shi a gidan Muntari, tana magana zai ce "Iya ba na son sa'ido"
Zaman Hanne da Muntari kuwa gashi nan gashi nan ne. Ran da ya bushi isha zai nemeta amma idan bai nemeta ba ko ta zo da kanta koranta ya ke yi ya ce shi baya son jaraba. Yana dai bata kuɗi dan duk wata tana jin alert. Zaman shiru da ta ke yi ne ma ya sa ta yi tunanin komawa karatu.
Mummunan halin sa ta shan giya kuwa tun watannin farko na auren su ta gane. Ita kam tana zargin bayan giya ma yana haɗawa da wani abun. Randa ya fara sunbatun Maryam kuwa har tsorata ta ke yi. Ita dai ta rasa wace Maryam ce Muntari ke mutuwar so haka.
***
Inter school competion za su yi daidai ƙarshen zango na shekarar wanda ya kama su Zaytoonah na gab da zana jarrabawan su na JCE.
Rehersals za a fara yau, wanda aka zaɓa za su fito su yi rehersal a gaban ɗalibai.
Wannan ne karo na farko da Zaytoonah za ta yi debate tunda ta shiga JSS. Ta kan representing ɗin makarantar su a Maths competion amma indai debate ne ba ta yarda ta yi. A nursery da primary school she used to be excited duk lokacin da aka zaɓe ta cikin ma su yin debate amma yanzu komai ya chanja ma ta, ba ta da wannan confidence ɗin.
Wannan karan ma Mr Adebayo ne ya dage sai ta shiga ciki.
Ita ce first speaker dan haka sunan ta aka fara kira Tijjani Zaytoonah Abubakar.
Cikinta ya ba da ƙululu, jiya a gaban Auwal ta presenting points ɗin ta ba tareda wata matsala ba amma yanzu da aka kira sunan ta har ta fara jin gudawa.
A hankali ta taso ta fito tsakiyar filin, gaba ɗaya an ƙura ma ta ido wasu na dariya ƙasa-ƙasa.
Bayan ta yi gaisuwa sannan ta gabatar da topic ɗin sannan ta introduncing kan ta. Tana cewa "standing before you is Zaytoonah Tijjani Abubakar, I'm..."
'aka Mama Zaytoonah' muryan Sadiya wata 'yar class ɗin su ya doki kunnen ta. Sadiya ta so a saka sunan ta a cikin ma su competition ɗin amma ba a zaɓeta ba, shiyasa ta ke jin haushin Zaytoonah.
Shiru ta yi saboda yadda sunan ya taɓata
"Yes continue" MC ɗin ya faɗa ma ta
Murya na rawa ta cigaba dan ta ruɗe "firstly, I'm.."
"Amoeba" ta sake jin an ambata da ƙarfi. Wannan karan hawaye ne ya zubo daga idon ta wanda ya sa wasu ɗaliban su ka fara dariya. Aka shiga yiwa yara ihu akan su yi shiru amma inaa sai ma ƙarawa da su ka yi saboda yadda su ka ga Zaytoonah ta bar hall ɗin da gudu...
***
"Ni ba na son kame-kame, gaskiya na ke so, za ka iya yi min aiki ko ba za ka iya ba?"
"Indai ba ka yarda da mu ba babu yadda za ayi aikin da za mu maka yai tasiri" mutumin da ke zaune kan wata tsohuwar tabarmar kaba ya faɗa.
"Kuɗi ba su ne matsalata ba, indai zan samu biyan buƙata zan iya biyan ko nawa ne. Wannan ne karo na uku da za a min kwatancen waje na je amma ba na samun biyan buƙata"
"Ai ka sha kuruminka kawai Alhaji, aikin ka an riga an gama. Sai dai dole za a yiwa baƙaƙen Aljanu yanka saboda su ne kaɗai za su iya aikin nan. Za a yanka mu su Ɓaunan da be taɓa yiwa mace barbara ba, sannan za yanka Zakaran da yai wa Kaza 'yar kwana bakwai fyaɗe sannan..." yana maganar yana zazzare ido a dole shi malamin tsibbu mai magana da Aljanu.
"Ba sai ka je da nisa ba ka yi lissafi ka faɗi nawa zan baka kawai, ni buƙata na ta biya shine damuwata"
"Dubu talatin"
Muntari ya ciro bandir ɗin kuɗi daga aljihun rigan sa ya ajiye a gaban Malamin tsubbun ya ce " ga dubu hamsin nan. Idan har buƙata ta biya zan dawo na ƙara maka wani alkhairin"
Malamin tsubbun yai saurin ɗauke kuɗin yana faɗin "ai ya saketa ma an gama. Ai yadda za a ɗasa mu su ƙiyayyar junan su ko inuwa ɗaya ba za su iya zama ba"
Da wannan Muntari ya bar rumfar mutumin yai gaba.
Shikuwa Malamin tsibbun dama na bogi ne, yawo ya ke yi ƙauyuka-ƙauyuka ya damfari mutane idan ya samu 'yan kuɗin sa sai ya ƙara gaba ya je wani wajen ya kuma damfarar wasu shashashun.
Bayan tafiyar Muntari ya shiga harhaɗa 'yan komatson sa, zuwa yamma ya bar ƙauyen.
Shi kuwa Muntari ya tafi da zubin nan da kwanaki kaɗan Tijjani da Maryam za su rabu. Dan ya ɗan yadda da bayanin Malam Nabakin kura da alama shi zai yi gaskiya ba kaman sauran 'yan tsubbun da su ka damfare shi a baya ba.
***
*Anorexia nervosa*
Anorexia: wannan kalma ana alaƙantata ne da wani yanayi da mutane ke tsintar kan su ciki musamman ma su ƙiba. Yanayin shine tsoron ƙiban su, wanda ba su da ƙiba kuma ba tsoron yin ƙiba. Ba anan matsalar ta ke ba, matsalar shine a duk lokacin da ka ke tsoron ƙiban da ka ke da shi ko kuma ka ke tsoron yin ƙiba za ka zama kana aiwatar da wasu daga cikin abubuwan nan ko kuma ka dinga jin wasu daga cikin abubuwan nan:
1-ko yaushe za ka dinga lura da yanayin jikin ka kana duba shin ka ƙara ƙiba ne ko yanene. Ko kuma dai ka rage ƙiba ne
2-za ka damu da ƙiban ka da kuma siffar ko kuma dirin ka musamman ma mata.
3-idan kana da ƙiba za ka dinga ji a ranka cewa sai ka zama siriri ne zaka yi daɗin ganuwa, sai ka zama siriri ne za ka zama accepted a idon mutane. Za ka alaƙanta ƙimar ka da kasancewar ka siriri, wato idan kanada ƙiba za ka dinga gani kamar kimar ka ya ragu.
4-za ka iya yin komai dan kawai ka rage ƙiba. Ko kuma za ka iya yin komai dan kar ka yi ƙiba (saboda kana gani kamar idan ka yi ƙiba shikenan ka kaɗe)
5-za ka dinga hana kan ka cin abinci, ka ɗauki azumin da ba lada sai wahala (wato ka dinga Azumi dan kawai kana so ka rage ƙiba). To the extend koyaushe ka gwammaci ka wuni da yunwa saboda ka sa a ranka idan kana ƙin cin abinci automatically za ka rage ƙiba.
Ko ka ga mutum ya hana kan sa cin daɗi, ya tsiri tsirface tsirfacen cin wasu abincin yana ƙin cin wasu simply because a dole yana son rage ƙiba by fire by force.
6- idan mutum ma'abocin yin excercise ne (motsa jiki) to za ka ga zai dinga yi babu hutu babu kakkautawa. Zai dinga yin excercise da ya fi karfinsa duk dan yana so ya rage ƙiba da wuri
7- idan mutum na fama da Anorexia za ka ga duk yadda ya kai ga rage ƙiba ba zai taɓa haƙura ba shi dai zai dinga ganin kaman baya rage komai. Hakanan za ka ga koyaushe yana cikin gwada nauyin sa.
8-ko ya ci abinci mai yawa sai ya tsiri ƙaƙarin amai akan dole sai ya amayar da abinda ya ci.
9-shine neme-nemen maganin rage ƙiba. Ko me aka ma sa tallah sai ya siya ya gwada ko zai dace ya rage ƙiba
10- kullum cikin jin haushin kan sa ya ke simply because Allah ya halicce shi mai ƙiba. Kullum aka yi comment akan ƙiban sa sai ya ji haushi har ya ji a zuciyar sa inama,inama. Inama inada jikin wane ko inama inada sirantaka irin ta wacce, etc.
*Matsalolin Anorexia:*
-Yana sa mutum ya kasa taɓuka komai sai ya zamana rayuwar sa ta ta'allaƙa ne kawai da son rage ƙiba ko tsoron yin ƙiba.
-Garin hana kan ka cin abinci ka je ka rasa kuzari ƙarshe ka fara fama da malnutrition idan ya zo da ƙarar kwana mutum ya mutu.
-A neme-nemen maganin rage ƙiba ka je ka sha abunda zai kashe ka ko ka sha abunda zai jawo maka wata cuta ko wata matsala daban.
- Saboda damuwa da ka sa a ranka sai ka iya samun hawan jini.
*Yadda za ka yi yaƙi da Anorexia:*
- ka so kan ka a yadda ka ke. Kafin wani ya so ka sai ka fara son kan ka tukunna. Idan ke macece kamar ni, ki sa a ranki duk ƙibar ki akwai mazan da su haka Allah ya yi su mata ma su ƙiba su ke so ba sirara ba (dama number one problem ɗin shine kina tunanin maza sun fi son sirara shiyasa ƙibar ki zai dinga sa ki damuwa. Hell no baby girl. A yadda ki ke za ki samu masoyin ki na asali wanda shi mace irin ki ma ya fi so). And idan ya complain akan ƙiban ki ki ce ma sa 'go hug transformer'.
- ki dena yin gasa ko kishi da wata 'yar uwar ki ko ƙawar ki da ta ke siririya. Babban abunda ya ke ƙara propagating anorexia shi ne yadda Media ta ke nuna models sirara, ko jaruma 'yar film za a zaɓa anfi son siririya. Ma su tallen shayin rage ƙiba ko maganin rage ƙiba sai su dinga potraying ma su ƙiba a matsayin ma su matsala amma sirara kuma su ne dai dai (akwai ƙiban cuta ko na rashin lafiya. Ina maganan ƙiba da ya ke naturally haka Allah yayiki ko yayika kuma ba ka da wani unhealthy habit da zai sa ƙiban na ka ya jawo maka wani illah). Ita ƙawarkin da ki ke burin ki zama kamarta may be itama akwai wani abu da ki ke da shi da ta ke bala'in burin ta same shi amma ke ba ki sani ba. The moment kika dena kishi da kuma gasa da sirara za ki ji zuciyar ki wasakai ba wani damuwa. You'll live happily.
-Babu magic powder ko magani da zai sa ki rage ƙiba cikin ƙanƙanin lokaci. Rage ƙiba is a gradual process, ba wai dan kin sha wani abu ko kin yi wani abu lokaci guda sai kawai bayan kwana biyu ki ga kin tashi siririya ba. Ba haka abun ya ke ba, rage ƙiba tafiya ce mai ɗaukan lokaci idan kin jure. Matuƙar za ki rage ƙiba ne dan wani ko dan wata kina ruwa. Domin indai dan wasu za ki rage ƙiba to ba ki da kwanciyar hankali, domin abu ɗaya za ki dinga hangowa shine kina son ki zama siririya dan ki burgesu. My Sister and My Brother ba za ka taɓa burge ɗan Adam ba, sai ki sha slimming tea ɗin ki sha haɗe-haɗen ki zama siririyan still a zage ki. A nuna ai yanzu da ki ka zama siriya ba ki yi kyau ba. Wa su su ce ma rashin godiyar Allah ya sa ki ka koma siririya ta ƙarfi.
- idan har kina son rage ƙiba ne bisa karan kan ki. Misali, kwana biyun nan na fara yin nauyi fa gara na ɗan zama fit kaɗan (may be nauyin na ɗan sa ki kasala ko ma dai wani issue ɗin daban. Ko kinga kamar ƙiban ki ya fara zama unhealthy) to wannan dalili daga karan kan ki ne kuma ke hangen ki ba wai ki zama siririya ba ce kamar ƙawar ki Zeenatu ko kamar 'yar film Rahama Sadau ko Nargis Fakhri. Abun da ki ke so shine kina son rage nauyi ko kina son ki ɗan sake kaɗan. Then my Sister my brother you just need to change your life style kaɗan ko na ce ka adjusting wasu abubuwa a lamuran ka na yau da kullum. Weight loss is 70% diet and 30% workout or excercise. Ba wai ki ce daga yau na dena cin abinci da yawa ba. Ba haka abin ya ke ba. Za ki saka wasu abubuwa ne cikin abincin da ki ke ci wasu kuma ki rage cin su, a hankali kina inganta lafiyar jikin ki ta hanyar yawan cin vegetables da fruits fiye da carbohydrate. Sannan kina motsa jikin ki daily walau yoga ne kike yi a gida ko kuma dai kina da Gym a gidan ki ne ko kuma kina fita trekking ne ko gudu ko tsalle etc (idan namiji ne buga ball yana da advantage sosai. Idan macece ke kamar ni musamman ma matar aure akwai yoga da za ki iya yi a gidan ki,a ɗakin ki ko falon ki ko ma tsakar gida. Minti 15,20 ko 30 ya isheki a rana depending on your tight schedule. Dancing (rawa) shima yana da fa'ida sosai domin shima motsa jiki ne, ki girgije ƙugu ki girgije jiki za ki ji jikin ki ya yi saƙayau. ( ba wai ki yi sau ɗaya sau biyu ba ki ce ke ba ki ji chanji a jikin ki ba. My Sister ba kwana ɗaya biyu na ke magana ba, ba kuma kiyi sau uku a sati ki share sai bayan sati biyu ki sake yi ba. Ina nufin ki ware minti 15 zuwa 30 a rana ki dinga motsa jiki walau rawa ne ko yoga kiyi haka na sati huɗu ki ji ko za ki ji chanji a jikin ki, ki cigaba ki yi ya kai wata uku ki ga how your body will feel. Ban ce ƙiba za ki rage ba miraculously. Aim ɗin ki ba rage ƙiba ba ne, aim ɗin ki rage nauyi ne da kuma jikin ki ya samu benefits na excercise wanda za ki ji ko malaman lafiya suna emphasizing akan a dinga motsa jiki. Ko mutum siriri ne ma ba a bar ka a baya ba ana so ka riƙa excercise. Yana rage kasala, yana rage stress yana yana yana)...
Chaaiii na gaji da bayani
Domin ƙarin bayani kya iya browsing more akan anorexia don samun haske sosai.
Ina ga ma ya kamata na buɗe fitness group Lol
Dear 'yar uwa ko ɗan uwa ma su ƙiba kamar ni. Za'a kiramu da sunaye na izgilanci, za a zolaye mu, za'a aibata mu kar ka taɓa bari wannan ya dameka. So what dan muna da ƙiba, so what idan sun zolaye mu da suna ma su muni. We get better things to do than responding to stupid people.
Kar mu koma gefe mu yi kuka ko mu ɓata rai dan ance mana ƙato ko ƙatuwa, Lukuti ko Lukuta etc wanda ya gaya mana mu zare ma sa ido mu yanka ma sa magana har sai ya ji dama bai buɗe shaddar bakin sa ya kiramu da sunan nan ba.
***
" Azumi ki ke yi ne?" Mommy ta faɗa lokacin da ta ga Zaytoonah ta mai da hankalin ta ga kallo ta ƙi cin abinci.
"Zan ci anjima Mommy, yanzun ba na jin yunwa ne"
Salman ya fashe da dariya Mommy ta ma sa dundu a baya
"Mommy wai Zaytoonah ne ba ta jin yunwa caɓɗi"
"Ba na son shirme Salman ka fita a hancin Zaytoonah dan idan ta waiwayeka ba ruwana"
Ya cigaba da cin abinci yana dariya ƙasa-ƙasa.
Lokaci zuwa lokaci tana leƙa su. Yawunta sai tsinkewa ya ke yi yadda ƙanshin jollof rice ɗin ke bugan ta.
Bayan abin da ya faru a wajen reheasal ɗin nan Zaytoonah ta ci kuka sosai. Ƙarshe ma cewa ta yi ta haƙura da karatun gaba ɗaya amma da ta isa gida sai ta rasa bakin yin magana dan tana fara furta maganar rashin zuwa makaranta ƙila Mommy sai ta zaneta. Haka dai ta dinga daddafawa tana zuwa makarantar har su ka fara exams na su, batun debate kam ya sha ruwa dan sai wata aka ɗauka.
Sati biyu kenan da ƙarisa Junior Waec ɗin su. Abinda ya faru ranan ya sa ta tsani makarantar ta su, ranan suna tareda Daddy ta ma sa maganar ba za ta koma wannan makarantan ba a chanja ma ta wata. As usual bai tambayi dalili ba ya ce ta zaɓi wace makaranta ta ke so. Maryam da ke jin su ta ce "tunda ba ta son makarantan inaga boarding school za a kaita ta ƙarisa karatun a chan"
T J ya ce "ba inda za ta je tana nan kusa da mu"
"Ka dai cigaba da sakaltata ni ba ruwana. Yarinya ba abinda ta sani sai ci"
"Ba ruwan ki da 'ya ta. Adaeze ki ci abinci ki ƙoshi sosai kin ji?" Zaytoonah ta gyaɗa ma sa kai...
Zuwa dare ta galabaita, abincin da aka ajiye ma ta flushing ɗin sa ta yi a banɗaki amma sai da ta ɗauke naman ciki ta cinye. Ta yi challenging ɗin kan ta cewa za ta rage cin abinci za ta dinga ci sau ɗaya a rana saboda tana so kafin ta fara SS class ta koma kamar Humairah. Ga sabon makaranta ga sabuwar Zaytoonah. Zaytoonah siririya wacce ba za a dinga tsokala ba.
Da dare ba yadda ta iya dodging dole sai da su ka haɗu su ka ci abincin dare kamar yadda aka saba.
Wasa-Wasa ta cigaba da skipping abinci da safe sai ta ƙi karyawa da wuri idan Mommy ta wuce office shi Salman ya fita ball sai ta flushing abincin ko idan ta ji Almajiri yayi bara ta fita ta zuba mai. Tunda Iya da Humairah su ka koma gidan Muntari T J ya ce Auwal ya koma gidan Hajjo dan gidan zai mata faɗi daga ita sai Sadiq musamman idan T J na gidan Maryam.
Daga gidan Maryam ake tura ma sa abinci ko kuma ya zo ya ci ya tafi. Yanzu ya gama jarrabawar WAEC ɗin sa saura NECO hakanan yana ɗan taɓa ɗinki a shagon Ogan sa. Tun yana JSS3 ya fara fita yana koyon ɗinki gashi shekaru uku ya iya sosai ba laifi.
Da rana ma haka za ta nemi ƙaryar cin abinci tareda su ta ce sai daga baya za ta ci alhali ba ta ci. Ita ba Azumi ba balle ta samu lada sai rashin cin abinci.
A hankali jikinta ya fara weak har Mommy ke tambayarta ko lafiya ta ke ta ce lafiya ƙalau. Sai ta koma dan tana wajen Mommy sai ta daure ta nuna kaman tana nan da ƙarfinta idan ta koma ɗakin ta ta dinga murƙususun yunwa. Daurewa kawai ta ke yi dan it has not being easy musamman saboda yadda Mommy ke chanja salo salon girki ma su daɗi. Wani lokaci har kuka ta ke idan za ta zubar da abincin sai ta lallashi kan ta da cewa nan da lokaci kaɗan za ta dawo siririya kamar Humairah sai hankalin ta ya kwanta. A kwana na biyar ne kuwa ta fara period ɗin ta. Ciwon ciki ne ke ɗan fizgarta kaɗan kaɗan sai ta ɗauka na yunwa ne ta cigaba da dannewa abun ya zo yai yawa. Ta tashi ta wuce banɗaki ko cikinta ne ya ruɗe, ta fita a ɗakinta za ta shiga banɗaki kenan ta ji Mommy ta kirata "Adaeze come here"
Da ta zo gaban ta Mommy ta juyata dan ta tabbatar da abinda ta gani. Jini ne a bayan doguwar rigar da ta sa, jinin ba da yawa ba ne amma kasancewa rigan fara ce sai ya nuna.
Nan Maryam ta mai da ta ɗaki ta ma ta bayanin abinda ya faru da ita. Ta ɗan ji wani iri musamman yadda Mommy ke karanto ma ta dokoki ma su yawa duk da kuwa an mu su karatun a Islamiyya a Babun Fil Haidhi a littafin Akhdari amma saboda ba ta fara ba ya sa duk ba ta wani sa karatun a ranta sosai ba.
Da T J ya dawo da dare ta ma sa albishir da cewa Adaeze ta zama cikakkiyar budurwa.
"You know what? Nima @14yrs na fara fa"
T J ya ce "ai ba ta cikata 14yrs ba"
"Mi ya saura kuwa tunda saura 21days ne"
T J ya rungumota jikinsa ya ce "barin karɓi tukwuici tunda na zama Baban budurwa"
Kafin Maryam ta yi magana ya fara birkitata da zafafan salon shi ma su rikitata.
Bayan kwana shida.
Tana zaune a falo tana kallo ta ji mai tallen magani yana kirarin maganin sa. Irin. Ma su yawo a cikin motan nan ne suna aza loud speaker a saman mota suna kunna tallen magungunan su.
Yadda ake ta kururuta maganin ƙiba ya sa Zaytoonah ta fara tunanin fita ta siya. Ba kowa a gidan sai ita ɗaya, Mommy da Daddy duk sun fita aiki shi kuma Salman dama indai ana hutun makaranta to ƙafar sa ba ta zama a gida, daga ya je ƙwallo ko ya je shagon su Auwal koma ya je neman tsokala tareda abokanan sa ma su ƙiriniya irin sa.
Maganganun mai tallen na ratsata sosai har ta fara hango kan ta ranan birthday ɗin ta wanda ta ke ganin sai ta bawa su Humairah mamaki harda su Nuratu ma da 'yan islamiyyan su musamman Na'ima mai cin tosono lokacin suna yara.
Ɗakin Mommy ta shiga ta ɗau kuɗi ta fita da sauri. Hamsin-hamsin ne maganin amma sun ce za su bar ma ta uku ɗari dan haka ta sayi guda shida a naira 200.
A jikin ledar maganin an yi bayani kan yadda za asha. Za ka iya zubawa a shayi marar sugar ka sha ko kuma ka zuba shi a ruwan zafi zalla. Ko wani leda ɗaya za ka sha shi sau biyu a rana wato da safe da kuma dare.
Zaytoonah was so excited, a lokacin ta haɗa guda ɗaya ta shanye da ƙyar saboda ɗaci gashi itama kaman T J ta ke, son zaƙi ne da ita kamar me.
A lokaci guda ta shanye leda ɗaya ta je ta wanke kofin ta kai maganin ɗakin ta ta ɓoye a ƙarƙashin pillow.
Da dare kafin ta kwanta ta kuma haɗa wani wannan karan leda biyu ta haɗa a ƙoƙarin ta na son zama siririya cikin sauri.
Baccin awa ɗaya ta yi ciki ya birkice ma ta. Ta shige banɗaki da gudu sai gudawa fuyaaaaa. Ta gama ta fito amma kafin ta ƙara kwantawa wani ya kuma zuwa ta sake komawa da gudu.
Cikin minti talatin Zaytoonah ta galabaita sosai gashi dama 'yan kwanakin nan da ba ta cin abinci sosai jikinta yayi weak.
A karo na biyar da ta fito daga banɗaki ne ta yanki jiki ta faɗi tunma kafin ta kai ɗakin ta...