Free chapter · Read without an account

chapter 10

by salmeert sani salman · ABUL-KHAIR

ABUL-KHAIR👬



(THE IDENTICAL TWINS)





TSARAWA DA RUBUTAWA SALMEERH SANI SALMAN TRIPPLES S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)





*WANNAN  LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIKIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI* 



https://arewabooks.com


           

*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.*







Page 11.








""""""""""""""""”Bude idanunta tayi ta na kallon tulin matan dake palon kowa yana harkar gabanshi, lumshe idanunta tayi tanason tuna abinda ya kawota gurin......





cikin minutes Kad'an ta fara tuna abinda ya faru da ita da sauri ta mik'e ta na furta "Twin" duk binta suka da kallo babu Wanda ya iya cewa da ita uffan, tsoro ne ya Fara kamata dan ita tunda take bata tab'a ganin manyan Mata haka ba, gashi babu Wanda ya kulata , wasu manya manyan Mata ne farare Sol suka shigo cikin palon sai karas karas sukeyi da chewing gum, tunda suka shigo Palon daya ta kafe Muneebat da ido, ko d'aukewa batayi ganin hakan yasa itama Muneebat din ta kafeta da ido ko kyaftawa batayi, gurinta matar ta nufa , ganin tana share hawaye gashi da alama babu wanda ta sani a gurin, su kuma y'an gurin sun shareta, zama tayi tare da kama hannunta ta rike tana kallonta, kafe juna sukayi da ido, Matar ce ta fara cire idonta a kanta , dan ta lura Yarinyar duk abinda aka Mata bata bari koda kuwa kallo ne, Cikin yanga da iyayi ta furta "shiitt Beb daina Kuka," ta fad'a tana dan dukan bayanta Alamar rarrashi, amma inaaaa kamar zugata take cigaba tayi da kukanta abinta tana murtsuke ido, alamar zallar Yarinta da rashin wayau......








hannun ta cire Mata a idon tana bata Baki, ganin bazatayi shiru bane yasa ta ciro sweet a jakarta ta b'are tare da mika Mata karb'a tayi, Amma still bata daina kukan ba....... 







Zawota jikinta tayi tana dan dukan bayanta tare da cewa "cry, cry baby, menene kike so?", ta fada tana shafa kanta , duk binsu akeyi da kallo babu Wanda ya yi magana,ita kuwa bata damu ba, tana had'a ido da Muneebat, taji ka'unar Yarinyar ta dirar Mata cikin zuciyarta, "My twin", ta fada tana lafewa jikin matar, zaro ido tayi, dan ta fahimci , yau aka daukota, sannan kuma tana neman Y'ar uwarta, "shiiiiit to daina Kukan haka, za'a kaiki gurin twin din", ta fada tana dan rirrigata, matan gurin kuwa duk tab'e Baki sukayi.......









*WASHE GARI, MASARAUTAR NRI*








"Ere Orin! Ere!! Lododun ajoyo (shagali! Shagali!! Shagalin bikin shekara", wasu matasan samari suka fito daga wani guri cikin shagarsu ta alfarma sai dai jiya E yau dan shigar dai sai a hankali.









Cike da farin ciki, duk sauran mutane suka fito, suna dariya da farin ciki, Fadar Sarki aka bude gaba daya ahalin masarautar suka Fara fitowa, tun daga kan Oba Eri da gimbiya Ochchi, Agulu, Boka Shikra, da duk sauran yan cikin masarautar, duk kansu cikin shiga ta alfarma Shiga irin ta Sarauta, takawa sukeyi cikin takun kasaita har suka karaso cikin rumfar da aka had'a dominsu, guri duk suka Samu suka Zauna wani mutum ne ya k'araso gurin faduwa ya yi k'asa yana cewa "A Ki Oba Nri toro omo toro Nrin Egun Oloruno ,pelu idile yin, a mo kiyin(an gaishe da Sarkin kasar Nri ,toron d'an toron giwa , La'ananne abin Bauta ya albarkace ka tare da iyalanka muna kawo gaisuwa)" ya furta yana zubewa k'asa , jinjina Kai kawai Sarki Eri ya yi na tare da yace komai ba.........







Matsawa ya yi, gurin Gimbiya Ochchi ya yi, k'asa ya d'uƙa tare da Fara cewa" Ë kí Ömo _binrin öba Ochchi Odin tum tin (an gaishe Dake, gimbiya Ochchi , barka da zagayowar bikin she Kara)" murmushi tayi tare da dan Kad'a kanta alamar ta ansa gaisuwar.









Juyawa ya yi , gurin tarin gungun makid'an dake gurin tare da cewa cikin harshen ~Yarbanci~ "Ölorin bare sí í séré"

(masu kiɗa, ku fara kiɗa), ya fada yana wani juyi kamar jira sukeyi gaba daya suka saki gangunansu , suka fara kiɗa irin nasu na ~Yarbawa~ , tuni duk suka mike suka fara gwangwajewa har da Oba Eri........




*BANGAREN MUƊI'AT*





tunda aka sanya Muɗi'at a mota bata kara sanin inda kanta yake ba, har aka karaso da ita Masarautar Nri, bata sani ba, har inda ake ajiye wa'inda aka kawo aka kaisu , duk fifita sukayi, ita kaɗa aka bari a motar batasan mai takeyi ba, saboda sumar da tayi, motar aka jaa, har zuwa bayan part din Gimbiya Ochchi wanda, achan ne ake ajiye motar, sai in za'a fita ake daukarta, kasantuwar kowa ya fita a motar yasa , aka rurufe motar da tampol driver ma ficewa ya yu, zuwa harkar gabanshi...






driver na fita a motar aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan akeyi sosai fiye da tunanin mai tunani, ruwan ne yake kwarara takan tampol din da akasanya a motar, kasantuwar ba'a rufe boot din motar ba, yasa ruwa fara zuba ciki, a hankali ruwan yake malala har ya samu nasarar shiga cikin motar, gangara ya farayi, gar ya da aka fara



cikin jikinta ruwan ya fara gangara, har ya jiƙa kayan jikinta, kamar a mafarki , ta fara bude idanunta a hankali, har ta karasa budesu tarrrr cikin motar......






kuka ne ya kubce mata, kukan ta shiga rerawa kamar ranta zai fita , ganin kukan ba mafita bane yasa ta fara gangarawa , gurin da take ganin ɗan hasken walkiyar dake haska gurin......






hannunta ta kai gurin, jin wani abu kamar labule yasa ta sanya hannunta ta yaye, a hankali ta sulala ta fita daga cikin boot din........






zare idanu ta farayi ganinta, tsaya gurin wani tankameman gini, mai tsawo na gaske, kallo take karewa gurin.....







walkiyar da aka karayi ce, ta haska mata wata kofa, dake like jikin wani gini, ta jima tana kallon kofar, umarnin zuciyarta tabi, ta nufi kofar..........






turawa tayi ga mamakinta taga kofar ta bude, wani haske ne ya mamaye gurin, mai masifar haske har wani kashe ido hasken yakeyi, shiga tayi cikin gurin, karewa gurin kallo ta farayi, tsare fes gurin yake, babu alamar dirty ko kaɗan tar tar, haka gurin yake........







*NEW YORK...*





kaya ya siyo mishi set hudu , ko wane daya kwara biyu har colour da komai, kafin ya dawo har ya gama wanka ya futo, yana zaune kan bed din daure da towel, gashin jikin nan ya yi, luf luf ya kwanta kan farar fatarshi, sai golwing takeyi, ya yi wani gaske.







da Sallama ya karaso cikin room din, zama ya yi, kusa da Khair din , da kanshi yake ɗuƙe tun bayan da ya Amsa mishi sallama, kayan ya mika mishi, karɓa ya yi, ya fara sawa......







yana gama sa kayan Ammie ta turo kofar room din, tana tafe wata kyakyawar Yarinya mai masifar kama da ita na binta a baya, cikin room din suka karasa da Sallama, Abul ne ya mike tare da cewa "Sannu da Zuwa Ammie", ya fada kanshi a ƙasa.






batace mishi komai ba har ta karaso gurinsu, matsawa ya yi, ya bata guri, zama tayi kusa da Khair din tana kallonshi, matsawa Abul ya yi, kusa da Yarinyar tare da dan mangarar mats kanta yace, "ke baki iya gaisuwa bane", ya fada yana dan harararta....







dan taɓe baki tayi, tare da cewa "Ayya Yayah, sannu ya mai jikin?", ta fada tana dan tsare Abul din da ido.






rausayar da kanshi ya yu, tare da cewa "da sauki My Ƙanwaty, ya school", ya fada yana dan murmushi, itama murmushin tayi, tare da cewa "Alhamdulillah", bai ƙara cewa komai ba, itama kuma batace komai ba.......







"how did you feeling now"Ammie ta fada tana kallon Khair, ya mutsa fuska ya yi, tare da cewa "Alhamdulillah", bai kara cewa komai ba, shima kuma baice da ita komai ba, babu wanda ya kara cewa komai.






ajiye basket din hannunta Yarinyar tayi, tare da cewa "Sannu Yayah Khair", baice komai ba, sai rausayar da kanshi da ya yi, itama bata kara cewa komai ba, sai kujera da ta samu ta zauna.







shiru ne ya biyo baya,ba wanda ya kara cewa komai ba, ganin shirun ya yi, yawa yasa Ammie ficewa, tabar Samha anan.......







Abul ne ya zauna kusa, da ita tare da fara janta da fira, fira suka fara sosai, kamar ba gobe, Khair dai ko inda suke bai kalla ba, kamar ma babu shi a ɗakin...........







ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , wanda kuma suka bari har na gama free na fara paid to zasu biya #400, zaku iya fara biyan kuɗinku ta wannan account number din👇.






1499884120

Access bank.

Umma salma sani.






ko katin waya ta wannan number din 👇.






***






ku tabbatar kun turomin da shaidar biyanku ta number ta kamar haka 👇.





***






Salmeerh Sani Salman Tripples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.