Free chapter · Read without an account
Page 17
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 17*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call ***
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Juwairiya ta yi tsuru da jakarta ta na kallon Mama da ke tsaye a gefen ta riƙe da hijabin ta a hannu ta na ƙoƙarin saka wa a kanta sai ta ji hawaye sun ƙara wanke mata fuska,ta share da sauri domin Mama tun ɗazu take mata ƙorafin kuka yanzu ma da taga ta na hawaye sai ta yi tsaki ta ce." Gaskiya kukan nan na ki ya fara siƙe ni Juwairiya na ga ke da Baba Sani kuka shirya hakan,amma kin bi kin dame ni da kuka in da kin san ba za ki iya ba uban wa ya ce ki amince."
Sai ta rungume Mama ta ƙara fashewa da kuka ta na jin wani irin baƙin ciki da fargaba ga gabanta da yake faɗuwa a kai akai don ji take kamar ta ce a ta fasa.
"Mama akan ki sami lafiya na amince amma ki yafe min in na ɓata miki na ga kamar ran ki ba ya son na tafi."Ta ce da ita cikin hawaye fuskarta ta tura shi a jikinta.
" Ki na ganin in da bai yi wa rayuwarmu halacci ba wallahi Baba Sani bai isa ya saka ki ƙara wani aikatau ba,don kullum na yi sallah sai na roƙi Allah ya raba ki da shi saboda irin cin mutuncin da kika fuskan ta."
Share hawayenta ta yi ba ta ce komai ba ta shafa kan Ibrahim tare da riƙe hannun sa suka fito tare.
" Mama ji nake kamar kar na tafi sai kun tare a sabon gida."Ta faɗa tare da fuska.
Mama ta kalle ta ta ce " Gara ki tafi Juwairiya saboda yau aka yi zaki tafi kuma kin ga mutumim nan ya yi ma rayuwarmu hallaci wanda dalilin haka ina matuƙar girmama shi."
" Humh." Ta ce a cikin zuciyarta sannan ta ɗora da ce aranta jin abin da Mama ta ce." Da kin san abin da ya ƙulla da ba ki girmama shi ba,shi ɗin macuci ne sosai ya fiye son kan sa da rayuwar matar sa da kin san dalilin da ya sa ya yi mana wannan abubuwan da kin tsane shi har iya ƙarshen rayuwar ki."
A lokacin da suka yi nisa mama ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye ta ce." Juwairiya ki riƙe mutuncin kan ki a duk in da kike kuma, duk abin da ki kai kin san Allah ya na kallon ki mutunci na ƴa mace shi ne zai zama ado a rayuwarki,ba wai ina zargin ki ba ne a' a ina miki nasiha a matsayina na uwa wacce ƴarta za ta yi nesa da ita,sannan ya zama dole na saki a hanyar daidai don kar ki ga mutum zai aikata abu a ɓoye,ya na tunanin ya kauce idon mutane bayan ya manta mahaliccin sa ya na ganin duk abin da ke"
Jikin Juwairiya ya ƙara sanyi kamar ƙanƙara haka kawai sai ta ji ta fara tsarguwa yadda Mama take ta mata wasu irin maganganu, wanda take shan jinin jikinta don in ta yi mata irin waɗannan maganganun ko kallonta ba ta iya wa.
Yanzu haka ta kasance ta yi ƙasa da idanunta ta ce."Mama an ya ba zan."
Katse mata hanzari ta yi tare da taran ɗan mashin ta karɓi jakarta da ta riƙe da ta yi tsumu ta ɗora a kan mashin ɗin sannan ta kalle ta ta ce." Ma za ki tafi Allah ya tsare da kin sami lokaci ki leƙo."
Juwairiya ta haye mashin jikinta babu karsashi hawayen fuskarta sun ci gaba da kwaranya yayin da ɗan mashin ɗin ya fara tafiya a kan titi.
Wani ƙarin abin da ya ƙara zubar hawayenta cikin ƙunar rai da ta tuna yau gidan mijinta za ta akan mashin da ƙullin kaya a jaka, ba tare da an kawo mota kamar yadda ko wace mace mai gata wacce mijinta yake son ta ake mata,duk lokacin da ta tuna wannan sai ta ƙara sakin kuka har ɗan mashin ɗin ya juyo ya kalle ta ya na faɗin."
Lafiya Hajiya?"
Amma ba ta kula shi ba kuka sosai take har suka isa gidan Atine,a lokacin da ta isa ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo sallah ta yi suka kama hanya.
Wani irin faɗuwar gaba take yi har sai da ta dafe ƙirjinta.Kasancewar a kwai tazara sosai da gidan Atine sai da suka hau nafe.
A lokacin da suka iso ƙofar gidan da Juwairiya ta saka a ranta na A.m ne hankalinta ya yi matuƙar tashi matuƙa gaya.Kawai sai ta ji ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba ta sani A.m suna da kuɗi amma ko kaɗan ba ta taɓa tunanin haka gidan sa yake ba.
" Dole ka ce baka sona kuma ba zaka taɓa sona ba saboda ba mu dace ba ni kai na sheda ne."
Ta furta cikin karayar zuci don ta san ya fi ƙarfinta na har abada.Gaskiya fasalta gidan sa abu ne da zai ɗau lokaci saboda gida ne mai matuƙar girma, da tsari ga shukoki masu kyau waɗanda suka ƙara ƙawata gidan,don haka mai karatu na bar maka aikin tsara fasalta iya tsaruwan gidan,A.m a hannun ka don in na ce zan yi zan ɗauki lokaci ni dai na yi wa gidan suna da aljarnar duniya.
Lokacin da suka shiga cikin falon Juwairiya ku san neman numfashinta ta yi ta rasa, don barazanar shiɗewa yake yi saboda tsaruwar falon da ke ɗauke da ku san set huɗu na kujeru mabambanta.
Duk lokacin da ta ƙara taku a cikin falon zuciyarta karaya take da son A.m da ya shige zuciyarta saboda ta haƙiƙance ma kanta da yaudarar kanta take yi A.m babu abin da zai yi da ita.
A ƙasar kafet ɗin dake zagaye a tayas ɗin da ya sha guga ya na ta ƙyalli da ɗaukar ido ta zauna tare da rintse idanunta,hakan ta ji ba ta son idanuwarta su yi tozali da matar A.m don ta san zuciyarta za ta buga.
Atine ta zaro wayar ta ta yi kiranta sai dai cikin takaici ta ije wayar ta kalli Juwairiya ta ce." Ba ta dawo aiki ba amma ta ce mi jira ta za ta duba patient ta dawo."
Sai Juwairiya ta sauke idanunta daga kallon Atine saboda kiran sunan ta da ta yi,ta ci gaba da kallon ƙasa yayin da zuciyarta yake bugawa tamkar za ta fito.
Kusan waya biyu suka shafe suna zaune a falon sai kowa shiru jefi-jefi Atine take sakin tsaki,amma Juwairiya iya tsawon lokacin ko tari ba ta yi ba sai sautin bugun zuciyarta da yake ta ƙara tsanantuwa.
Ƙwas!Ƙwas!!Ƙwas!!! Suka ji sautin takalmi wanda Juwairiya ta sadaƙar da matar gidan ce ta dawo,bayan iya tsawon lokacin da ta ɗauka ta shanya su zaman jiran ta kamar wasu dussa.
Bugun takalmin Zainab ya na tafiya tare da bugun zuciyar Juwairiya da take jin tamkar za ta fito,ta rintse idanunta ta na burin a ce ba Zainab ɗin ba ne take ƙoƙarin shigowa,domin tsoro ya bayyana a fuskarta sai take ganin kamar za ta gane dalilin shigowar ta gidan.
Koda ta shigo waya take yi zama ta yi ba tare da ta ce musu komai ba ta ci gaba da wayar ta.
Juwairiya ta kasa ɗago idanunta ta ga matar mijinta na wucin gadi wanda take cikin zuciyar sa yake fifita ta fiye da komai har ya zaɓi ya cutar da rayuwarta duk akan ya farnta mata.
Amma idanuwanta sun kasa haɗa ido da ita hasalima ko ɗagowa ba ta yi ba, duk da ta fahimci ta gama wayar da take yi bayan ta ɗauki rabin awa.
" Am Atine na ɓata miki lokaci ko?"
Tambayar da ta yi mata kenan ta na kallon matar da ta kusa jika da ita a yatsine.
" Ba komai Hajiya dama me aikin ne da muka yi magana da megidan ki na kawo miki."Ta ce mata ta na kallonta.
" Ok."
Abin da tace kenan ta janyo wayarta ta kunna data yayin da tsaƙwanni suke ta shigowa ta na duba wayar har na tsawon lokaci,daga bisani ta kashe ta kalle su duka daidai lokacin da Juwairiya ta yi sa'ar yaƙar idanunta, na tsoron haɗa ido da ita da suke ta kalle ta, don ta ga wannan mace mai ji da kanta da wulaƙan ta mutane.
Karab idanun su duka suka haɗu da juna Juwairiya da ƙyar ta yi nasarar daƙile gangar jikinta da yake shirin tashi da zura da gudu ganin kalar matar da A.m yake aure.
" An ya ƴar Nigeriya ce?"
Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki domin yanayin ta da kyanta surar ta gabaki ɗaya ya tsorata ta,saboda hasken ta har wani kashe ido yake yi sosai da ta yi duba ga kalar fatar jikinta sai ta ga ta yi baƙa wuluk kamar gawayi,duk da ya ba kyan fatarta da ƙawayenta suke yi.
Zainab kuwa wani irin tsanar ta ya shiga ranta haka kawai sai ta ji ba ta kwanta mata ba,ba wai kuma kyan da ta gani ba ne ya tsorata ta a'a ita sheda ne akan A.m ko ƴan mata larabawa za ta kawo mishi ba zai yi dubi garesu ba, duba ga yadda ta sha wahala kafin ya amince da ita sannan tun da su kai aure ba ta taɓa jin ya yi maganar wata ko wata ta kira shi ba.
Amma sam Juwairiya ba ta yi mata ba saboda daga ganin ta za ta yi munafunci ganin yadda take duƙar da kanta ƙasa-ƙasa.
" Atine an ya wannan ƴarinyar kina ganin ta yi?Kin san A.m a kwai shi da ƙyanƙyani ji yanayin shigar ta da wani zumbulelen hijabi kin san ya na da tsafta, kar ta zo ta na ma na girki ya na shiga sannan wallahi zubin ta bai yi min ba don ni na daina ɗaukar ƴan aiki gidahumai ƙauyawa,bai gaya miki ɗakin sa da komai na shi ita za ta din ga gyarawa ba?A can zo wata kawai."
Juwairiya ta yi ƙasa da kanta jin abin da ta faɗa duk da ranta ya ɓace,amma ta yi tunanin fiye da hakan a gurin ta saboda ta karance ta tsaf mace ce mai ɗagawa da nuna ta isa,musamman ga talakawa ƙasƙantu irin ta.
Sai kuma ta ji daɗin abin da ta ce ranta ya yi fari ko banza ba za ta zauna agidan wannan mai kama da canis ba sai ya zo ya san yadda zai yi da ita,ai dama abin da ya shirya a yi mata kenan shi ya sa ya aure ta ya kawo ta kuma ita ta sai ma kanta don in da ƙwaɗayi a kwai wulaƙanci!
Atine ta ji jikinta ya yi sanyi sosai har ta fara tunanin in da za ta samu kuɗin A.m ta mayar masa don ya na ba ta ta kai ma mai kujeru akan bikin ƴarta marainiya wanda mijinta ya mutu ya bar mata.
Sai ta ji kamar ta ce ai mijin ta ne ma ya buƙaci ta kawo ta,amma da ta yi tunanin ba ta san dalilin da ya sa ka shi ya buƙaci hakan ba sai ta kama bakinta ta guntse ta ce." Ai Hajiya Juwairiya a kwai aiki da tsafta sosai ta yi aiki da dama shi ya sa na kawo ta,kuma za ki ya ba sosai sai kin gode min,amma ki gwada ta in ba ta yi miki ba sai a kawo wata.Kin sai an gwada akan san na ƙwarai.
" In ko haka ne ta na buƙatar gyara don sai na canza mata tufafi ba za din ga mana girki da shi ba,ni ban san daƙiƙanci da rashin wayewa."
Ta ce ta na kallon Atine da ta yi hamdala a ranta jin ta amince da ita,sai kuma ta kalli Juwairiya ta na mata kallon tsaf irin na ciki da waje har mutum ya gano munin ka.
" Ina yini"
Juwairiya ta ce mata ganin ta na mata kallon ke ba kya gaisuwa ne.
Ɗauke idanunta ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk da ta tabbata ta ji gaisuwar da ta yi mata.
Sai ta miƙe ta kalli Atine ta ce."Wash na gaji ba ri na shiga ciki."Har ta fara tafiya sai ta tsaya.
" Ina fatan Atine ta yi miki bayanin aikin da za ki din ga yi a gidan nan? Ina da da tsohuwa da take share-share da ƴan abin da ba'a rasa ba.So ke aikin ki kula da ɗakina da na mijina da wankin underwears ɗin mu da girki.Kasancewar ba zama nake ba don yanzu waje zan fara fita na baki amanar gidana, da mijina duk sanda ba na nan ki rinƙa kula da abincin sa ruwan wankan shi kayan sawan shi da wanda ko ina nan ke zaki kula da wannan."
Ta ɗan numfasa ta ɗora da ce wa " Game da kayan sawar shi irin wanda yake so ina fatan ke ba daƙiƙiya ba ce kuma ba' a yi asaran tara ba na yi mishi time table a ɗakin sa na kayan da yake saka wa sai ki din ga dubawa ki na cire masa."
Wani iri Juwairiya ta kanta ya yi mata take wani irin zafin kishin mijinta A.m ya taso ya mamaye zuciyarta,har ya hana ta jin abin da Zainab take ce wa sai kuma tausayin sa ya kamata matuƙa jin irin ballagar mace da yake aure.
Ta ƙara rintse idanunta ta na jin kishin iya adadin masu aikin da Zainab ta yi waɗan da suka gama kallon mata miji,kuma a haka yake iƙirarin ya na sonta lallai ta yadda so halitta ce kuma makaho ne.
" Ki na ji na ina magana kin yi banza da ni!"
Zainab ta daka mata tsawa ganin ta tafi duniyar tunani.
" Yi haƙuri ina sauraren ki ne."
To ba na son shashanci in ina magana duƙar da kunnin ki saitina za ki yi kuma duk na yi magana ki ɗaga kanki."
Ta ce sannna ta ci gaba da tafiya ta na faɗin." Atine ba ri na ɗauko miki abu."
" Kut! Na shiga uku A.m ya san halin matar sa ya kawo ni cikin gidan nan."
Ta faɗi ta na jinjina kanta tare da tunanin irin zaman da za su yi da ita .A jiyar zuciya ta saki mai ƙarfi jin sakacin da Zainab ta yi da mijinta.
Kuɗi masu yawa ta miƙa ma Atine wacce ta sandare da jiranta,saboda har wanka ta yi ta saka kaya shara-shara wanda al'dar ta ce zama da irin wannan kayan a gida.
A lokacin Juwairiya ta gaji har ta fara gyangyaɗi ga yunwa dake ta ƙwaƙwular cikinta.
" Kin ga na jima ban dawo ba ruwa na watsa ga shi ki yi haƙuri."
Ta ce da Atine sannan ta kalli Juwairiya ." Ke ki tashi ki fara aiki kuma na manta ban gaya miki ba! Ba na son raini da ƙazanta."
Sai kuma ta ƙwala ma Baba mai aikinta kira da gudu sai ga shi ta ƙaraso mari ta zabga mata.Banza daƙiƙiya ba na ce miki za'a yi sabuwar mai aiki ba? Da kika gan su sai ki fara nuna mata aikin gidan ko sun yi miki kama da irin baƙin da zan yi ne?"Ta tambayeta ta cikin zafin rai.
"Ki yi haƙuri Hajiya ai ba ki bani umurnin haka ba kuma..."
" Rufe min baki banza maza ki je ki nuna mata."
" Allah ya huci zuciyar ki."
Ta ce tare da kallon Juwairiya sannan ta ce ." Mu je na nuna miki aikin."
Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye ta dafe ƙuncinta don gani take kamar ita ta mara.Zainab ciki ta koma tare da ɗaukar wayarta ta yi kiran rabin ranta.
Tsananin tashin hankali Juwairiya ta shige shi ji ta yi tamkar ba za ta iya rayuwa a cikin gidan ba,a tare suka share hawaye da Baba suka kuma kalli juna.
" Ki yi haƙuri Baba haka matar gidan take miki?Gaskiya ba ta da mutunci a matsayin ki na wanda kika haife ta.Wai mai masu da shi suka ɗauki talaka shi ba mutum ba ne don kawai ya na nema a ƙarƙashin wani sai wulaƙanci."
Baba ta share hawayenta ta kama hannun Juwairiya ta ce " Humh ba zaki gane ba ne!Hajiya Zainab ta wuce tunanin ki ina tausaya miki wallahi Allah ya sa kin iya girki."
Ta ɗan ƙara matsowa kamar ta na tunanin Zainab za ta yi musu laɓe ta ce." Ina gaya miki wacce ta kora ta kawo ki da ta yi abinci juye mata ta yi a jikinta,ta rufe ta da duka wai mijinta ya ce ba ta iya girki ba.Ni fa ban taɓa ganin mutum irin maigidan nan ba,ya tsane mu sai dai shi baya duka."
Duk da Juwairiya ta san matsayinta a gidan amma sai da gaban ta ya faɗi ras!Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Da Juwairiya suka shiga kicin kusan ruɗewa ta yi kamar za tai hauka,irin dukiyar da aka narka da kayan na'ura,duk da ta yi aikatau gidan masu kuɗi ta san yadda ake sarrafa na'ura amma a ranar yar ƙauye ta dawo.
Abinci mai rai da lafiya Juwairiya ta shirya sannan ta shiga ɗakin da aka ba ta wanda Zainab ta yi mata umurnin duk ta yi girki ta yi wanka.
Juwairiya ta da fari kasa amfani da kayan bayin ta yi sai daga baya a hankali ta fara gane yadda ake amfani da shi bayam ta ɓata lokaci ta na ƙauyanci.
Juwairiya ta yi mamakin irin kayan da ta jibga mata da sunan ta dun ga amfani da shi,haka dai ta shirya ta na ta tunani barkatai a ranta yayin da kewar su Mama ya kamata, matuƙa har ta ji hawaye na zuba a ƙuncinta.
Juwairiya na zaune a ɗakin da ya zama mallakinta bayan ta idar da salla sai kuma ta miƙe da sauri jin kamar Zainab na kiran ta.
Ta na baƙin ƙofar fita daga ɗakin suka yi kicibis da ita za ta shigo." Ke kurma ne ina kira kin yi banza dani."
Ta faɗa cikin ɗaga murya." Ki yi haƙuri ban ji ki ba ne."
Ta ce ta na kallonta amma kuma a tsorace take saboda kar ta kai mata mari.Tsaki ta yi." Maza ki je ki shirya dinning za mu ci abinci mijina yanzu zai shigo.Kuma ki cire wannan ƙazamin hijabin na ki don na san ina ya gani ba zai iya cin abincin ba."
Juwairiya ta ji jikinta ya yi sanyi jin umurnin da ta ba ta domin ba za ta iya fita a haka ba,amma sai ba ta ce komai ba ta saɓule hijabin ta koma ciki.
Hankalinta ya kwanta da ta tuna a kayanta a kwai hijabi wanda bai kai wancan tsawo ba,da sauri ta ɗauko ta saka a jikinta bayan ta saka turare kamar yadda ta murceta.
Juwairiya na gyara dinning ta ji dirin mota alamun an shigo da mota,gaban ta ne ya faɗi ras! Don jikinta ya ba ta masoyin ta ne ya dawo haka kawai sai ta ji gaban ta na faɗi.
Da sauri take shirya dinnnig ɗin saboda ta gama ta kauce ma ganin sa,amma sai kafin ta gama ya riga ya shigo ya na takun sa da sarsarfa irin na ingarmar namiji mai jini a jika.
Shigowar sa ya yi daidai da fitowar Zainab daga cikin ɗakinta cikin wata irin shiga ta alfarma,amma fa a gurin sa wanda kuma Juwairiya ta ga bai kamata ta fito da irin wannan shigar ba,sanin a kwai ta a cikin gidan don har tafi shigar ɗazu rashin kyan tsari.
Da gudu ta faɗa jikin sa ta na dariya cikin farin ciki.
Shigowar sa ya sa Juwairiya ta gane ashe tafiya ya yi saboda direban sa da yake janye da troley ɗin sa guda biyu kuma masu girma.
Duka suke dariya sannan suka faɗa kan kujera suna bayyana iya kewar da sukai ma junan su.
A hankali A.m ya zura ma Juwairiya ido shi har ya manta sun yi da Atine yau za ta kawo ta.Ya ɗauke idanun sa da sauri ganin Zainab ta bi in da yake kallo.
" Hubbina sabuwar mai aikin da Atine ta kawo mana ne,Allah ya sa ta yi maka sai dai na ganta kamar gidahuma ce ko ina yawo da hijabi,amma haka zamu yi haƙuri da ita don gaskiya na gaji da ɗaukar masu aiki."
A hankali Juwairiya ta ɗago idanunta ta ɗara su akan A.m duk da ba ta son hakan,amma ta na son ta ji mai zai ce mata.
Ga mamakinta sai ta ga ya taɓe bakin sa ya kalle ta kamar ya ga kashi ya ce." Uhm na gan ta sai dai ki yi mata magana ta kiyaye sosai in kuma taƙi dole ki canza wata don kin san halina."Ya ce a taƙaice sai kuma ya canza maganar ya na kallon Zainab ya ce." Na yi missing ɗin ki babyna sati ɗaya da na yi kamar na yi shekara,yanzu haka ma ban gama abin da na ke yi ba na baro A.k a can na dawo na ga kyakykyawar fuskar ki."
Ya faɗa kamar zai yi mata kuka yayin da idanunsa suka bayyana hakan ga Zainab da take kallon sa da wani irin murmushi ta na kashe masa ido.
" Allah ko zauji ka san ni da kai kamar hanta da jini ne ɗazu ina ma wani operation, ka san Allah saura kaɗan na yanka sa ba in da ya kamata ba kuma fa kai na ke tunani."
Dariya suka yi duka ya riƙe hannunta ya ce." Na san za ki yi fiye da hakan akai na amma ki kula rai ya wuce wasa."
" Ke banza wawiya!Ba ki da tarbiya ko?Ko baki ko ya a gida ba in ma'aurata suna magana ki ba su wuri maza wuce daga nan stupid kawai!"
Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da A.m ya shige ta nemi hankalinta ta rasa ji take kamar ta ruga da gudu ta faɗa jikinsa.
Gabaki ɗaya ta manta a wace duniyar take wasu irin zafafan hawaye ta ji ya wanke mata fuska, saboda tsananin son da take masa wani irin kishin sa ya tokare mata maƙogaronta, har ta ji ta na son ta yi aman sa don ta na jin ɗacin sa ya na hawowa bakinta.
Muryar Zainab da ta daka mata tsawa ya fargar da ita halin da take cikin da sauri ta ruga da gudu,ta shige ɗakinta har ta na bugewa da bango ƙum!Amma ba ta kula ba don tsoron Zainab take yi sosai a ranta.
Ta na shiga cikin ɗakinta ta fasa kuka sai kuma ta toshe bakinta tuna ko a ina take daga ƙarshe toleit ta shige, ta kulle ta ƙara sakin kuka ta na buga kanta a bango amma ba ta kula ba ko kaɗan.
" Na shiga uku a haka zan rayu a gidan nan? Na tabbata zuciyata ta kusan kamuwa da hawan jini!Allah na roƙe ka ka yafe min laifin da na yi maka ka haɗa ni da A.m wanda da ma burin sa ya kawo ni gidan sa kishin sa ya yi ajalina!"
TO FA JUWAIRIYA AN YA DAI? GARA DAI KI TSAYA A MATSAYIN KI KISAN KE FA AUREN GWANGILA CE AKAN KI AMMA BA MATAR SO BA.INA JIRAN COMMENT TSAKANIN FANS ƊIN ZAINAB DA JUWAIRIYA.
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.
MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.