Free chapter · Read without an account

15-16

by salmeert sani salman · NAZLAH

Jaawo Hijab dinta taji anyi, dunƙule hannunta tayi tana juyowa ta bugarwa Hasina baki, da sauri ta sakar mata hijab din, tana tarba gaba daya hannunwata a bakinta, ihu ta fasa lokacin da taga jini na fitowa daga cikin bakin, wani abu taji ya faɗo guda biyu, tana ciro hannun ta duba sai ta ga haƙoranta guda biyu a hannunta.



    cikin mugu²n ta shin hankali ta laluba, zaro idanunta tayi jin haƙora gaba babu su, kuma ta tabbatar da cewa sune suka fita, ihu ta kwada tare da cewa "Wayyo na shiga ukku ta ciremin Haƙora da sanyi safiya", ta fada tana daura hannayenta bibiyu aka.



     Wata muguwar dariya Nazlah ta kwashe da ita tare da cewa, "ai ba haka na so ba, so nayi gaba daya haƙoran su zube, Allah ne ya soki, amma gaba ki ƙara tara ta ki ga ikon Allah", ta fada tana ci gaba da tafiyarta.




     baki washe take tafiya, tana cikin tafiyar taji ta ci tuntuɓe, dan tsayawa tayi ta duƙa, kusan 2 minutes sai kuma ta mike ta ci gaba da tafiya fuska a haɗe kamar an aiko mata da sakon mutuwa haka ta ringa tafiya har ta ƙaraso gida, ba ko Sallama ta sanya kai cikin gidan, Ummu ta tarar zaune tana kiciniyar haɗa wuta, bata ko kalleta ba ta shige chan ciki ta samu guri ta zauna, tare da haɗa kai da guiwa ta fara gunjin kuka mai ban tsoro da tayar da hankali.



      a tsorace kuma cike da mamaki Ummu take kallonta, kamar daga sama Abba ya yakice labulan Dakin Umma ya fito da dorinarshi, yana cewa "wani sabon iskancin ne kika zo dashi yanzu da sassafen nan?, " ya fada yana ware bulalar, shiru tayi ta ci gaba da kukanta, da kana jinshi kasan ba nata bane, "Yau zaki ci ubanki, zan gyara miki zama, tunda baki san mutunci ba", ya fada yana daga bulalar zai zula mata.




    idanunta da suka rine suka koma jaaazir kamar jini ta watsa mishi, tare da ce wa"doke ni to", ta fada tana kallon cikin idanunshi abun da tunda take bata taɓa yi ba kenan, tun daga nan ya sha jinin jikinshi, "nace ka duke ni", ta fada cikin tsawa, sauke bulalar ya yi, tare da cewa "Allah ya soki kinyi magana yau da kinci ƙaniyarki", ya fada yana jura takalminshi, bai ko tsaya ba ya fice da sauri.




    Yah Haleem ne ya fito daga ɗaki, kallon inda take ya yi, kallo daya yay mata ya daka mata tsawa, ɗagowa tayi ta kalleshi, suna haɗa idanu tayo maza ta sauke idanunta ƙasa, "zo nan..!", ya fada tana ya fitota, ba musu ta mike izuwa gareshi, tana zuwa gareshi ta zube ƙasa , riƙe kanta ya yi, tare da cewa "mai ya kawoki yanzu da sassafe lau?", ya fada cikin sigar tambaya, cikin kuka tace "tabo mu akayi," ta fada tana kara dukar da kanta ƙasa, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "to kuyi haƙuri ku tafi", ya fada yana sakar mata kan.




      babu musu ta girgiza kanta alamar to, kafin ta yi mika a hankali da wata sanyayiyar hamma, sai kuma ta fara bin gidan da kallo, inda ta tashi ta koma batawa kowa magana ba, tana kuma zama sai ga Mamar Hasina da Hasina sum shigo Haƙora a hannu, sai zazzaga ruwan masifa suke.




    Haƙuri Ummu ta fars bawa Maman hasina ,amma kamar ana ƙarawa wuta fetur, sai kaucewa take zata kamo Nazlah, ita kuwa tana inda ta tashi fuska a turɓune in kasar da take gurin ta tanka itama ta tanka,gajiya Ummu tayi da bawa Maman Hasina Haƙuri tayi, ta ce "ga tanan yi mata duk abun da kike jim zaki mata tunda ba zakiyi haƙuri ba",,ta fada tana komawa gefe ta ci gaba da yunƙurin haɗa wutarta a murhu.




    Mamar hasina kuwakan Nazlah tayi gadan², kafin ta ƙarasa gareta taci tuntunɓe , kafin tayi wani yunƙuri, an yi sama² da ita an bata fettt a ƙasa, tare da fara mulmulata a gurin kai da ganin aikin ƙasan ba ƙaramin ɓata rai ba akayi a gurin, haka Mamar Hasina ta ringa mulmula tana ihu dakyar aka samu ta tsaya, sai da Ummu tayi ta bawa Nazlar haƙuri , Hasina kuwa tuni ta ari na kare, dan tun ɗaga Ummanta tayi waje, bata tsaya ba sai da ta kai gida tana haki, Nazlah kuwa bata ko taɓa Maman Hasina ba Hasalima tana zaune daga inda take ko kallon Maman hasina batayi ba da ta shigo..




     dakyar Maman hasina ta mike tare da taimakon Ummu ta fita tana kuka tare da jaan ƙafa, sai da Maman Hasina ta fita kafin ta mike ta shige banɗaki wanka ta sheƙo da ruwan sanyi ta fito , ɗaki ta shiga ta shirya cikin sabbin kayan Makarantar Islamiyya da suka mugun karɓi jikinta suka mata kyau sosai, naɗe gashin kanta tayi,ta mishi kamar acuci maza, fitowa tayi daga ɗakin tana dai-daita sanyin hijab dinta.




    da tsananin Mamaki Ummu take kallon Nazlah dan ita a iya saninta basu chanja mata Uniform ba kuma bata ga ta shigo dasu ba, kallonta tayi tare da ce wa "Ke..! ina kika samu wannan kayan?", ta fada tana tsura mata idanu cikin wata murya da take nuni da cewa basu tafi ba tace "tambaya ko neman sani?", tunda Ummu taji haka sai ta jaa bakinta tayi shiru.




     miƙa mata dan gutun koko da ko rabin cup baiyi ba ta ce "Ungo", kallon cikin kofin tayi, dan murmushi tayi tare da ƙarma, matsaw tayi ta jaa kujera, kafa cup din tayi a bakinta , kusan 3 minutes ta sauke cup din tare da sakin sanyyayiyar gyatsa, ajiye cup din tayi, kallon cikin cup din Umma tayi tare da kallonta, jinjina kanta tayi cikin tarin mamaki ganin yarda ta bata kokon haka ta ajiyeshi gashi kuma wai har da gyatsa tayi, mikewa tayi sai da ta kusa ƙofar tace "mun taf..!", tana fadar haka ta fice , tana fita Ummu ta sauke numfashi tare da cewa "Allah gamu gareka..!", kafin ta dauki sauran kokon ta shige ɗaki dashi.




     A hankali take tafiya, cikin wata natsuwa da ta shigeta Yau din, haka har ta isa Islamiyyarsu da yan tsurarun mutane suka zo Yau din, dan kowa tsoro yake ji, da Bissimillah ta taka cikin Makarantar, batawa kowa magana ba har ta shiga cikin Ajinsu da babu kowa a jiki, layin gaba da shine layinta ita daya ta zauna.




     Cikin natsuwa tayi Bissimillah tare da fara rero karatuj Al-qur'ani mai girma cikin bawa ko wane harafi haƙƙinsa, bata bari ta shiga haƙƙin ko wane, haka ta ringa rerowa wanda da,kaki zakasan Allah ya mata baiwa bayan baiwar tata kuma akwai taimakon wasu mutaman daban.




    tana cikin Karatun Yan ajinsu suka fara shigowa, nayi mamaki na ganinsu, dan manya² ne yan Ajin nasu, dan wasu ko hasu haifeta ba, to sun girme mata nesa ba kusa ba, zama sukayi tare da fara labarinsu suna shewa da dariya, tsayar da karatun nata tayi tare da cewa "Amma nasan kunji da kunnanku karatu muke ko?", ta fada cikin sanyin murya, Hauwa'u ce tace "to sai me dan karatu kike, kinsan dai ba zaki hanamu labarin Saukarmu ba ko k...", idanunta ne suka fara ƙaƙƙafewa maganar da ta fara ta kasa karasawa, wata kumfa ta fara fitowa daga bakinta, da sauri duk yan ajin suka fice suna ihun neman taimako, ita,kuwa Oganninyar Zamanta ta gyara tare da ci gaba da karatunta, cikin suratul ```BAQARA``` dan har ta,kusa kaiwa karshen shafin karshe.




    Malam Abbakar da ya,kasance shine Malamin Ajin mai koyar dasu Al-qur'ani ne ya shigo cikin ajin, yana kallon yarda Hauwa'u ta kaƙƙafe yasa aikin Nazlah ne da yake sun mishi bayanin abun da ya faru, kuna shi yasan Nazlah na da mutanan Boye tun ba yanzu ba, duba da yarda yake musu karatu ta dauke a jikin biyawar farko gashi in zata bashi hadda har sai ta ƙaranta inda bai musu ba, wannan kwazon nata yasa aka daukota daga ajin da take aka dawo da ita wannan ajin dan tafi Ɗaliban ajin karatu da mayar da hankali, har mamaki take bawa Malamai gurin karatu dan har gyara take cinsu.





    " bana son haka, Saketa...!", ya fada yana zama kan kujera, dukar da kanta tayi dan tana tsananin jin kunyarshi da ganin mutuncinshi, cikib siririyar murya ta ce "in har bata dai na surutu ana karatu ba, wallahi ba zata ƙara magana ba har duniya ta naɗe", ta fads tana juya idanunta, sai ga Hauwa'u tana zazzzare ido an sakar mata maƙogwaro.




     dan murmushi ya yi , tare da fara amsar karatun da zasu gurin Sauka, bai karɓi na Nazlah ba dan yasan bashi da matsala da ita, sai dai sai kallonta yake, dan yajin labarin abun da ya faru jiya da Malamai, sai dai bai yi wani jimami ba sai Allah kara da ya musu dan Malam, basa da,kirki babu abun da suka ajiye sai cutar Yara.



.

     baya sun gama Karatu aka tattauba yarda abubuwan sauka zasu kasance a gobe, kafin a tashesu su fice, direct gida ta nufa cikin farin cikin da ta rasa ko na me ne ne.




  tana zuwa ta faɗa jikin Ummu da take tunanib, yarda zatayo da su dan Yau basu da ko kwayar hatsi da zasu ci abin ci gashi tasan Nazlah da yunwa zata dawo firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, kallonta tayi tare da cewa "har kin dawo..!?", gyads kanta tayi tare da cewa "Ummu Saukar mu fa gobe banga ana shirye² ba", ta fada tana kallon cikin gidan.



    Dan murmushi da bai kai ciki ba tayi tare da cewa , "muna nan muna yi", ta fada tana shafa kanta, shiru tayi bata ce komai ba, haka suka ci gaba da zama shiru, sun ɗan jima haka kafin Ummu tace "tashi kije gidan Iya kice ina gaisheta", mikewa tayi tana murna da tsalle ta fice, bin bayanta da kallo tayi tana jinjina irin wannan Yarinta ta Nazlah shekara 10 cikin ta sha daya amma bata daina sakalci ba, tana tsoron ranar da zata faɗi (period) batayi hankali ba.




      ba tayi 5mimutes da fita ba, ta shigo da kaya riƙi² a hannunta, har tana zubar da wasu da babbat kula, ajiyewa tayi a gaban Ummu tare da cewa "gashi...!", tana ajiyewa ta shige ɗaki, Ummu na magana amma bata tsaya ba, mikewa tayi ta bita ciki da niyyar tambayarta daga ina.




     tana shiga ta nemeta sama ko ƙasa babu ita babu labarinta, duddubawa ta shiga yi har ƙasan gadonta amma batanan, gabanta taji ya faɗi , dandanan wani tunani taji ya darsu a ranta, hakan yasa ta fice tare da zarar gyalenta ,tayi gaba zuwa gidan Iya.




    tana fita Abba ya shigo, ganin kaya zube a banza, sai ya kwashe ya fice, kai tsaye dandalin cacarsu ya nufa, yana zuwa ya tarar da wani ya sanya kuɗi duba biyar, kawai shima sai ya miƙa kayan, ya zauna aka fara bugawa dashi.





     ko da ta ƙarasa gidan Iya zama tayi suka fara firarsu, suna dariya tare da wani gwaranci da su kaɗai suke iya gane kanshi ,ko ince mutanansu ne kawai suke iya gane kanshi, dan mutanan kan Iya sune suka koma kan Nazlah saboda kaunar da take mata.




     cikin sauri Ummu ta tura kanta cikin gidan, ganinta zaune yasa ta ja burki tana sauke numfashi, cike da tsoro wace ce wacchan din?, ta tambayi kanta cikin ruɗu,shi ko mutanan Nazlar ne har suka chanja mata salo da haka?, kallonta Iya tayi tare da cewa "Ƙara so mana", girgiza kanta tayi, tare da ce wa "Iya bai san na fito ba", ta fada tana juyawa ta fice.




    Ummu tana zuwa ta tarar babu kaya , iya tashin hankali ta shiga, tasan dai ba mutanan suka zo suka dauki kayan ba , sai dai in Abba ne zai shigo ya dauka, bata ko zauna ba sai gashi ya shigo, bashi ga tsuntsu bashu ga tarko, dan ya zuba kayan am cinyeshi, shi kuma bai cin komai ba ,kasa ta zube tare da gaishe shi , amsawa ya yi a yatsine cikin fusata, dukar da kanta tayi tare da cewa "Dan Allah ko kaga kaya ɗazun akan taburma?" ta fada kanta na karayin ƙasa.





      wani banzan kallo ya watsa mata tare da ce wa "Eh na gani kuma na zuba su A caca, ko a kwai yarda za'ayi da ni," da bala'in sauri ta dago idanuta , sai dai bata iya cewa komai ba, bata san yarda zata fada mishi haɗarin kayan ba, bayan Sallah Isha Nazlah ta tattara komatsanta ta tafi gidansu.




   ``` Washe gari```




    Tun Asuba Nazlah ta farka, tana ta yan tattare- tattarenta , bayan ta gama ta tashi Ummu dama Abba ba gidan ya kwana ba, bayan sunyi Sallah da Azkae din sade, tayi Karatun Al-qur'ani.



     bayan ta gama ta kalli Ummu tace "Ummu ina Kayan Abin ci a daura kar lokaci ya kure mana?", shiru Ummu tayi bata ce komai ba, ƙara tambayarta tayi, juyowa tayi ta kalleta kafin tace "Babanki ya daukesu, a harzuƙe ta kalli Umma sai kuma ta fice, bata jima ba, Ummu taji ƙarar ɓuruntunta , tana fitowa ta tarae tana kiciniyar daura tukunya ga kanyan Abincin na zube a gabanta.




    iya tashin hankali Ummu ta shiga, dan bata son Abubuwan ban su bude wa Nazlah ido, dama ta lafiyar kura balle kuma tayi hauka, tayata tayi suka daura, dandanan suka gama duk abun da ya dace, har wanka da sauransu.



       bayan Nazlah tayi wanka Ummu rasa kaya da zata bata ta sanya tayi, dan bata mata Ankon Saukar ba, haka yasa ta kasa shiga ɗakin da ba tasan mai zata ce mata ba, tana tsaye ta fito cikin shigar Atamfa super da ta mata kyau kwarai da gaske kalar green da farar hijab dinta da takalminta, tayi kyau sosai sai walwali take, dan ma wai babu kitso balle lalle, dan mutananta bata so ko kaɗan.




     Karo na farko da tayi Alfahari da mutanan Nazlah dan sun fitar da ita kunya, ko da ta shiga itama sabbin kaya ta gani ajiye, da ƙin sawa tayi, sai kuma wata zuciyar ta ce "Allah ne fa ya cida ki ki sa kawai" ,sawa tayi itama ta fito garau da ita, Yah Haleem ma cikin kyakyawar shiga ya shigo gidan da wasu Yara, su suka dauki Abincin suka tafi gurin Saukar.



     cike damkam suka tarar da gurin dan saukar bata mutum daya bace ta kusan mutum Ashirin ce, ga kuma gayyar manya mutane, dakyar suka samu hanyar shiga cikin taron, Nazlah sai wangale baki take tana magana ita daya, nikam nace ```tab wannan taron ai dole ma da Gayyarki ciki```…





     Guri suka samu suka zauna, ita kuwa gurin Ɗalibai Yan uwanta ta nufa, zama tayi kafin su gaggaisa, cikin Yar raha.





     *********



    tun da sassafe Hajiya ta kira Hameed ta shaida mishi batun Saukar da za'ayi, haka yasa ya turo da kyautarshi ta Malamai da wuri, tare da manyan kyatutuka da ya shirya domin bayarwa ga Daliban sa sukayi saukar , Duka yan Uwanshi suma sai da suka sanya gudumuwarsu a ciki, dan dama makarantar kusan haɗin guiwa ne dasu, sai dai kuɗinshi sun fi yawa a ciki , dan shi yake biyan Malam duk wata.



      


     shi kuwa sai misalin 10am ya shigo cikin gidan da Sallamarshi sai baza kamshin turaren Giorgio Armani, yake cikin kwarjini da cikar haiba yake takawa zuwa cikin palon, inda suke zaune suna jiranshi, gaishesu ya yi Ƙanan suka gaisheshi, amsawa musu ya yi,yana zama kusa da Hajiya tare da daura kanshi a kafaɗarta, shafa kanshi tayi tare da cewa "Auta ka taushe hannu, kai kawai muke jira tun dazun", ta fada tana yunkurawa zata mike, kallon Adda Zainab ya yi, tare da ce wa "Adda ki ɗiba kin break fast mana",ya fada yana binsu da kallo.




    kallonsu suk Adda Zainab tayi, suma suka kalleta kafin ta ce "To ina matar gidan? da ta bar mijinta da yunwa..!", shiru ya yi alama baya son zancen hakan ya tilasta mata yin shiru itama, sai da ta diɓar mishi kafin su fice, mota huɗu sukayi Adda Zainab da Hameed daya, Hajiya da Adda Nabila da Adda Nafisa daya, sai Haleesa da Yaran su Adda daya, sai dayar kuma Sojojin Hameed ne a ciki .




     kai tsaye makaranta suka nufa , basu dau wani dogon lokaci ba suka ƙarasa dan tsakanin Unguwarsu Hajiya da Makarantar ba nisa sosai,suna shiga ciki aka basu hanya, suka shiga, ganinsu yasa gaba daya Malaman suka mike zuwa taryarsu, bayan gama gaishe-gaishe aka samu gurin da aka tanadar musu mai AC da Fanka, cikin rumfa, Nazlah tun da taji karar shigowar Motoci zuciyarta tayi wani mugun bugawa da karfi, hakan yasa ta dafe saitin.




     bayan gama bude taro da Addu'a wanda Nazlah tayi , da gabatar da baƙi da Malam Abbakar ya yi, sai aka danyi drama ta larabci wanda shima har da Nazlah wadda ita take jaan ragamar drama ,bayan ta gama aka fara karatun sauka, wanda Nazlah aka fara kira ,,cikin natsuwa ta hau kan munbari, fuskarta a bude tar ta,karayin wani fari, sauran kuwa duk da niƙaf ita kuwa bata sanyawa dan numfashinta daukewa yake in ta sanya, cikin ƙira'arta mai dadi ra fara karatu wanda duk wanda yake gurin hankalinshi da idanunshi na kanta ,amma banda Hameed da kanshi na ƙasa saurararta kawai yake, har ta gama ba'a cita gyaran ko wasali daya ba,balle akai ga fidda kalkala dan tasan inda haƙƙoƙinsu suke, kuma tana kiyayesu .




    bayan ta gana aka kikkira Abokan saukarta, suma sukayi, sai sai Yawan cinsu duk da akwai kura-kurai a cikin karatunsu, bayan sun gama aka basu kyauttuka, wanda Nazlah tafi kowa samun kyauta mai tsoka, bayan bada kyattutuka da bada shahada, aka kira Nazlah again domin gabatar da Nasiha ga mutane, cikin gajiyawa ta kara hawa munbarin, cikin wata murya mai dadi ta fara magana, muryar da ko baka kaunar Uwarka da Ubanka in ka jita sai ka kaunaci mai ita ta fara magana, wanda yasa Hameed ya dago idanunshi ya dubi inda ake maganar, sai da gabanshi ya faɗi, dan kamar ance su kalli juna su biyun, kusan 30 seconds idanunsu na cikin na juna kafin ta jaanye idanunta, shi kuwa bai iya daukewa ba dan zalar mamaki ya cika mishi zuciya ganin Yar Yarinyar da take raira wannan karatu da tafseer duk a lokaci daya gashi komai za'ayi sai an kirata.





    bayan ta gama Adda Zainab da karɓi Laundspeaker ta jaaddada godiya ga Iyayen Yaran da sukayi Sauka da bada kyauttutukanta, da jaddada Albarka a gesu, duk a cikim harshen larabci, sai da ta gama kaf kafin ta kira sunan Nazlah Lawal, a hankali Nazlah ta dago da gajiyyayun idanunta ta kalleta, alama ta mata da tazo, mukewa tayo tazo har gabanta kafin ta sunkutar da kanta kasa alamar girnamawa.



    Cheack din 2 millions ta damƙa mata a hannu, tare da kara sanya mata albarka, dan Yarinyar ta bala'in burgeta ta kuma shiga ranta, har ƙasa Nazlah ta duƙa tanawa Adda Zainab godiya...........






***




```DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROTAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️```

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol