Free chapter · Read without an account

Page 25

by Amina Abubakar Yandoma · WATA SOYAYYAR

🧟‍♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟‍♀️



   *_Labari/Rubutawa_*


*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*

    ( _Meenat A Yandoma_ )

         tare da

   *ZAINAB MUHAMMAD*

      ( _Indian Girl_ )



*NOTE*

_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._



      *GARGAƊI!*

_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_



*PAGE 4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣*


..."Jidda kada kiyi mani haka ki tashi, in cikin nan ya zube Jidda kin kashe mani rayuwa."

Yazid ya riƙa sambatu a kan Jidda wadda bata masan yana yi ba.


Da dai yaga da gaske jidda bata numfashi a gigice ya sungumeta suka nufi asibiti, taimakon gaggawa aka fara bata domin ta jigata jinin ya ya zuba sosai; Yazid kuwa kai komo ya riƙa yi zuciyar shi a cunkushe da baƙin cikin wannan al'amari, indai cikin jikin Jidda ya zube ba shakka ta gama dashi cikin daya kwallafa ranshi shikenan.


Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da samun wuri ya zauna; dafe kanshi yayi da hannuwanshi biyu ya tsumayin fitowar likitocin.


An kwashe sama da rabin sa'a kafin likitocin su fara fitowa ɗaya bayan ɗaya a hanzarce ya sha gaban su; 

"Ku taimake ni ku sanar dani halin da mamata take ciki."

"Ka same ni office."

Daya daga cikin likitocin ya faɗa.


Gaban Yazid ne ya yanke yayi mummunar faɗuwa sakamakon jin abinda likitan yake faɗa fatan shi ɗaya Allah yasa cikin nan bai fita ba, jiki ba kwari haka Yazid ya shiga office ɗin; farin Glass ɗin fuskarshi ya cire tare da kallon Yazid.

"Kai ne mijin matar nan da aka kawo tana zubar da jini"?.

"Eh ni ne"

Yazid ya fada.

"Matar ka tana cikin mawuyacin hali domin kuwa yanzu haka tana buƙatar jini, shi ya sako ko izininka bamu tambaya ba musa saka mata,halin da ta tsinci kanta na firgice ya haddasa mata cikin dake jikinta ya zube."

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun."

Yazid ya faɗa tare da mikewa Tsaye.

"Jidda kin lalata farin ciki na yanzu sai da kika zubar da cikin nan, la haula walaƙuwwata illa billahil azeem."

"Bawan Allah kayi haƙuri zaku yi ku dauki wanna a matsayin kaddara domin bawa bai ta6a kaucema ƙaddarar shi."


Koma wa yayi ya zauna tare da fuskantar likitan.

"Zan iya shiga in ganta"?.

Yazid ya fada.

"Eh amma ba zata farka ba sai zuwa wayewar gari lokacin ta dawo cikin hayyacin ta."

Tamkar kazar da aka jefa da gishiri haka Yazid ya fito daga ɗakin hawaye nabin fuskar shi, ƙofar ɗakin ya tura nan yayi tozali da Jidda kwance ga jini an daura mata; gefenta ya zauna zuciyar shi na ƙuna.


Abubawan da suka faru a baya nan suka fara dawo ma shi ɗaya bayan ɗaya, kuka ya fashe dashi tamkar mace sabuwar nadama na sake lullu6e dukkan ga66an jikin shi, sai a yanzu ya sake yarda shida haihuwa har abada sakaci da son zuciya sun ja masu bala'in da har subar duniya yana bibiyar su.


A daren ranar Yazid bai runtsa ba har gari ya waye, sallar asuba yayi tare da jingina da a gadon Jidda, Iya ce ta turo ƙofar domin tun jiya Yazid ya sanar da ita halin da ake ciki.


Bayan sun gaisa take tambayar shi me jiki.

"Jiki da sauki, yanzu haka tana gaf da farkawa."

"Ubangiji ya karo sauƙi, ni kau Yazid ya batun matsalar gidan ku! Ina fatan dai komi ya dai-dai ta"?.


"Iya muna cikin tashin hankali wanda duk wanda ya ji abinda ke faruwa damu tilas ya tausaya mana, yanzu haka sun zubar da cikin dake jikin Jidda."


"Na shiga Ukku yanzu jikan nawa ne suka barar dole ne mu ɗauki mataki domin nan gaba bamu san me zai faru ba."


"Iya babbab abinda ke tayar mani da hankali kenan ni haka zan rayu babu ɗa babu jika, abun nan na matuƙar tayar mani da hankali."

Yazid ya ƙarasa maganar tamkar zai yi kuka.


"Kada ka karaya domin zamu nemi magani har inda ƙarfin mu ya ƙare wannan abu ya fara ɗaga mani hankali."

Iya na rufe baki Jidda ta farka tare da fara ƙara.


"Gasu nan! Ku ceci rayuwata sun ɗauki wani abu a cikina kada ki bari su kashe ni."

Jidda ta ƙarasa maganar tare da fizge karin jinin da akayi mata tana ƙoƙarin dirowa daga saman gadon.


A hanzarce Yazid ya rirrike ta tare da kwalama likitocin kira, ganin halin da take ciki Allurar bacci suka danna mata ba jimawa ta bingire.


Binta da ido Yazid yayi yana ji ina ma ace cikin ta na nan, wata irin soyayyar ta ce ya ji ta sake kama shi ya kasa ɗaukar duk wani mataki da yake tunanin ɗauka akan barar ma shi da ciki da tayi.


Mahaifiyar Jidda kuwa a gigice ta diro asibitin; ganin halin da ɗiyar ta ke ciki nan ta fara tambayar halin da ake ciki.


Jin bayani daga bakin Yazid sa da mahaifiyar Jidda ta girgiza, kallon Yazid tayi cike da mamaki.

"Yanzu da ace cikin nan bai zube ba haka zaku gyale ni ba zamu ji abinda ke faruwa ba, tunda ku ba zaku iya neman magani ba ni ku bani ɗiyata inje gida da ita in nema mata magani."


Sam Iya bata ji daɗin abinda mahaifiyar Jidda ta faɗa ba.

"Ina tunanin Jidda da Alkhamis duk ƴa'ƴana ne, duk abinda ya samu daya ina da alhakin kula dashi gaskiya banji daɗin abinda kika faɗa ba."

"Daga faɗar gaskiya kuma naga ai bari tayi dole ne a bani ita muje gida inta samu lafiya na maidota."

Ganin maganar zata yi tsayi yasa Iya tayi zuciya tabar asibitin.


Jidda kuwa tana farkawa ta ga mahaifiyar ta kuka ta fashe dashi tare da rirriƙeta.


"Sannu Jidda kin auna arziƙi kada ki damu ina tare dake babu abinda zai faru dake."


"Umma tsoro nike ji kashe ni zasu tace ɗaukata zatayi ta tafi dani."


"Duk karya suke ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru kinji."

Mahaifiyar Jidda ta faɗa.


Nan tayi ta kwantar mata da hankali har sai da barci ya ɗauje ta.


Mahaifiyar Jidda kuwa ganin Jidda tayi barci yasa ta fita daga harabar asibitin zata amsa waya.


Jidda na tsaka da barci

Kukan Jinjirin da taji kusa da ita ne ya saka ta bude ido da sauri, ja da baya tayi tare da dafe kirji ganin ta ko ina ɗakin ya cika da jarirai suna ta yawo tamkar turwa ta samu hatsi.


Wata irin dariya suka kece da ita tare da ambatar sunan jidda da wata mummunar murya.


"Jiddd,,,,,daaaahhh,, ba shine baki maraba damu, kizo ki ɗauke mu domin mu jinin ki ne Jiddddda."

Ɗakin ya karade da amsa kuwwa, tamkar tsuntsaye haka jarirai suka riƙe tashi saman iska suka sufo Jidda, ihu take kurmawa ko za'a samu wanda ya ji ta amma ina babu alamaun ana jinta.


Kafin tayi wani yunƙuri tuni wani jariri ya dira saman cikinta yana me bude zaƙa-zaƙan hakuran shi tare da dafa cikin ta sai ji tayi wani abu na shigewa cikin ta.


Raɗaɗi da azabar da take ji ne suka haddasa mata sakin wata razananniyar kara lokacci ɗaya idanunta suka kakkafe tamkar anyi jifa da ita sai gata kasa tim babu alamun rai a tattare da ita....



           ***

  GIDAN SU ALKHAMIS


...Safiya nayi Alkhamis ya fice yabar gidan domin ya lura in ya tsaya tabbas zai iya illata Farida domin yarinyar tayi ma shi wani irin reni.


Farida kuwa wanka taje tayi tare da gasa jikinta domin kuwa ta daku, gidan ta dan share saboda tasan yau kawayen ta zasu dawo.


Abinci me rai da lafia ta girka masu; a tsora ce ta shiga ta sake wani wanka domin jinin ta a kan akaifa yake ta rasa mike mata daɗi abu daya tasa a ranta shine sai kashe wannan auren domin kuwa bala'in yayi mata yawa.


Ƙofar da taji ana bugawa ce ta sanya ta saurin mikewa, budewa tayi domin kuwa a tunanin ta zata ga kawayen ta, turus taja ta tsaya tana kallon ta cike da mamaki.


Wata irin ragargazajjiyar tsohuwa ce tukuf hannunta riƙe da sanda kallo daya zaka yi mata sai hantar cikinta ta kaɗa.


"Baiwar Allah lafiya"?.

Jidda ta jefa ma matar tambaya.

"Ƴar nan ki taimaka mani da ruwa ƙishirwa nike ji."

Gelele Farida tayi cike da zallar mamaki domin kuwa bata iya ba wannan tsohuwar ruwa ita fa kyamarta ma take.


"Bani da ruwa domin kuwa ni amarya ce ta ya ma zani iya baki ruwa da kayayyaki na sabbi, duk unguwar nan ki rasa gidan da zaki zo sai nawa,Malama ki 6ace mani daga ƙofar gida tun kafin raina ya baci."


"Yanzu ƴar nan ba zaki taimaka mani da ruwan ba"?.


"Eh ba zani bada ba in kuma zaki shigo ne ki kwata bisimillah."

Tana kaiwa nan ta mayar da kofa ta rufe.


Falo ta dawo ta kwanta cike da haushin wannan tsohuwa ta rasa inda zata zo roƙon ruwa sai gidan ta.


Wani bugun ƙofar ta sake ji dan haka a zuciye ta mike burinta daya shine ta karasa bakin ƙofar ta wawwanka ma tsohuwar nan mari.

"Ƴar duniya; an samu gidan miji sai faman buga ƙofa muke an barmu waje kamar sakarkari."


"Amarya bakya laifi, mata daya tilo a gidan Alkhamis, ki huta ki sarara."

Tuntsirewa da dariya suka yi a tare.


Farida kuwa burinta daya su shigo ta leƙa taga shin ina mabaraciyar nan ta shige, amma sama ko kasa babu ita.


"Ummilo da zaku shigo baku ga wata mata ba a ƙofar gidan nan"?.


"Ke mufa babu wanda muka gani."

Suka fada tare da shigewa gidan.


Tamkar mayunwata haka suka rufarma abinci sai da suka karar dashi.


Gama cin abincin keda wuya suka hau iya shege suna video kowa burin ta shine su gama ta ɗora a shafinta na TIKTOK, manya-manyan sifikun ƙatuwar plasmar suka kunna tare kunna waƙar Ado gwanja ta Warrr suna warwasawa ɗaya nayi masu Video, lokaci ɗaya Farida ta manta da masifar da take ciki ta biye masu suka cigaba da chashewa a tare.


Sun kwashe rabin sa'a suna wannan rawar kafin su tsagaita, kunna Videon suka yi suna dariya ganin yadda suka chashe.

"Na shiga Ukku! Jama'a ku maido Videon nan baya."

Fauzy ta fada a rikice.


"Ke lafiyar ki naga kin wani ruɗe"

Cewar memunari.


"Iskanci Fauzy ne fa ya motsa taga duk mun fira kyau shiyasa da iya warwasawa."

Tuntsirewa suka yi da dariya a tare.


"Da gaske fa nike ku maido Videon nan baya wallahi wata tsohuwa na gani a gefen mu."

Zare ido suka yi tare da kallon junan su. 


Baya suka maido Videon cike da mamakin abinda Fauzy ta faɗa.


Ihu suka kwala tare dayin jifa da wayar sakamakon ganin wata tsohuwa tukuf a gefen su tana babbaka masu dariya.


"Fauzy mun shiga ukku ku tashi mu tafi gida, Farida gidan ki a kwai aljanu."

Tana rufe baki suka ji an kece da dariya.


"Inaaa zaaakuuu,,,ku tsaya mu taka rawar CHASSS domin kuwa zata fi kyau da Tiktok."


Cubrewa suka yi a wuri daya ido ya raina fata, fauzy ce ta fara kurma ihu kafin kace mi ƙofar falon ta rufe kanta wutar nepa ta ɗauke matsanancin duhu ya mamaye falon...









*MEENART..........✍🏻*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.