Free chapter · Read without an account
Page 29
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PAGE 5⃣1⃣&5⃣2⃣*
"A tare! A tare!! A tare!!!"
Shine kalmar dake fitowa daga bakin mahaifiyar Jidda da ita da maƙota sunabinta suma a guje, da kyar da siɗin goshi a ka samu wasu maza suka riƙeta tana fizge figze su kai gida da ita.
Da tirjiya aka samu aka sata a gidan a ka kulle tana surutai da birgima.
Maƙota fa an baje na mujiya sai kallo ake, sai da abu ya lafa sannan suka fice suna tsegumi da ƙananun maganganu.
Lafawar abin ya sa mahaifiyar Jidda ɗaukan waya ta kira Yazid, bai yi wata wata ba ya kamo hanya ya baro wajan aikin ya taho gidan su Jidda.
Gudu yake sosai dan ya samu ya isa gidan saka makon abinda mahaifiyar Jidda ta faɗa masa na cewa ta fita sai kamota akai aka dawo da ita tana fisge fisge, ya yi tafiya mai nisa titin ba kowa sai tsilla tsillan motoci waɗan da ba a rasa ba dake wucewa.
Yazid dake tuƙi burki yaja lokacin da ya hango jarirai kwance akan titin suna ta tsala kuka, fitowa yai bayan ya gama paking ɗin ya nufi inda jariran suke.
Amma me yana tafiya ne jariran na matsawa wanda duk shi bai san haka na faruwa ba, bai tashi ankara ba sai da ya ganshi a wani ƙungurmin daji ba gida gaba ba gida baya sai bishiyoyi da koguna.
Gabansa ne ya yanke ya faɗi zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri, zazzaro ido ya yi sakamakon ganin wani babban kogi gabansa gefe da gefe kuma wasu kalar koguna ne masu ban tsoro.
Take dajin ya hautsine da wani irin kuka haɗi da girgiza wanda yasa bishiyoyin kar karyewa suna zubowa ƙasa…
*ƁANGARAN GIDAN SU MARIGAYIYA FATEEMA*
A sai la'asar suka iso gida wanda shigar su kenan aka fara kiraye kirayen sallar la'asar , dan haka ko zama ba su yi ba suka shiga ɗaura alwala mazan suka tafi masallaci matan kuma suka tayar a gida.
Suna idarwa kafin mazan su dawo daga masallacin har sun ɗora abinci.
Ko da suka dawo kowa ɗakin sa ya yi, ya yin da Abban su Usman ya shige ɗakin Maman Fateema domin a girkinta yake.
"Maman Fateema kema kije ki huta ki barni ni zan ƙarasa"
Inna Habiba ta faɗa domin taga kamar Maman na a cikin wani damuwa da ruɗu wanda itama kanta a cikinsa take.
Maman Fateema tai murmushi kafin, Ta ce"A'a Innan Fateema a yi haka? Mu ƙarasa dai"
Itama murmushin Inna Habiba ta yi sannan, Ta ce"Ba komai kije ni zan ƙarasa"
Maman Fateema bata son ta jayayya dan haka ta wuce zuwa ɗaki.
Kishin giɗe ta samu Abban su Usman fuskarsa cike da damuwa haɗi da alhinin tuna wani abu da ya yi, zama Maman Fateema ta yi kusa da shi kafin cikin sanyin murya.
Ta ce"Abba Usman lafiya meke damunka tun da muka baro garin nan naga damuwa a fuskar ka?"
Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya miƙe zaune daga kishin giɗen kafin, Ya ce"Hadhiza damuwar dake tare da ni da wadda ke tare dake duk abu ɗaya ne ya haifar da ita domin kema na fuskanci wannan damuwar a tare dake"
Maman Fateema ta sauke ajiyar zuciya kafin wasu zafafan hawaye su zubo mata bata samu damar goge su ba, Ta ce"Abban su Usman hakane amma ya kamata wannan damuwa kar mu bata damar zama a tare damu, Abban su Usman ya kamata mu kawo ƙarshen wannan abu tun da har ubangiji ya kawo ƙarshen sa da kan sa"
"Hakane maganarki amma to kina ganin taya zamu fara kuma ta wace hanya?"
Abba ya tambaya yana mai fuskantar Mama.
Maman Fateema Ta ce"Ai hanyar ɗaya ce babu kuma wacce ta fita sannan ta inda aka fara ta nan ɗin dai za a sake farawa"
Jinjina kai Abban su Usman ya yi ya gamsu da abinda Mama ta faɗa dan haka, Ya ce"Shikenan wannan maganar taki dai dai ce, amma yanzu mu bari zuwa a kwana biyi kafin mu haɗu duka a tattauna"
Maman Fateema ta gamsu dan haka suka cigaba da hira kafin Inna Habiba ta kwalla mata kira ta fito su raba abinci…
*ƁANGARAN GIDAN LADIDI KWADAGA*
"Idan banda ma ƙaddara me za ai da baƙin ahali irin naku masu baƙar aniya"
Wata ƙanwar Maman Farida ta faɗa cike da ɓacin rai.
"Ke! karki ƙara kuskura wannan maganar ta sake fitowa daga wannan banzar bakin naki, idan ba haka ba kuwa wallahi sai kin yi nadama"
Wata itama a dan gin Ladidi Kwadaga ta faɗa a zafafe.
Haka dai akai ta cin bala'i har wajan magriba sannan dangin Maman Farida suka fita suka bar gidan kowa da ta bonta ya yin da suma dangin Ladidi Kwadaga ma haka.
Alkamis ne ya shigo gidan bayan fitar su Maman Farida ya samu su Mamansa a wujigace.
"Lafiya Mama meke faruwa na ganku duk a haka? Sannan naga su Maman Farida suma haka suka koma kuma ina zaune wajan makoki a ƙofar gida suka ce na tashi na tafi ba sa buƙata ta"
Ba wanda ya iya magana a cikin su sai wata ƙanwar Ladidi Kwadaga mai kama da itace ta shiga kora masa da bayani.
Ran Alkamis ya ɓaci ya shiga zagin dangin su Farida wanda ya yi a banza tun da ba a gaban su yai ba.
Ya gama faɗan ya juya zai fita daga gidan wata kalar iska mai haɗe da guguwa ta taso ta lulluɓe wajan, kowa ya rufe idon sa gudun kar ƙasa ta shigar masa.
A hankali wannan iskar ta shiga lafawa kafin wani razanannan kuka mai haɗe da dariya ya shiga tashi, wata murya kuma tana magana cike da kuka mai firgici.
"Mutuwa bala'i da masifa duk sun shigo rayuwarku kenan kuma ba za su bar ku ba daku da duk wanda ya raɓe ku"
Gaban kowacce macece ya shiga faɗuwa suka hau buɗe ido suna zazzare shi cike da kaɗuwa.
"Na shiga uku na lalace idona sun ƙi buɗuwa wayyo Allah na!"
Suka ji muryar Ladidi Kwadaga ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali da kaɗuwa, nan duk su kai kanta amma me sai…
*ƁANGARAN GIDAN SU JIDDA*
Maman Jidda ganin shiru shiru Yazid bai ƙaraso ba ya saka ta shiga kiran layinsa amma shuru, har ta gaji.
Miƙewa tai ta nufi ɗakin da aka kulle Jidda, amma me zata gani bala'in ya yi yawa dan haka ta kurma wani uban ihu wanda yasa maƙota masu jiran kaɗan shigowa…
*Indian Girl Ce*
Yanzu wannan ce number da nake whatsApp da ita _***_