Free chapter · Read without an account
Page 30
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PAGE 5⃣3⃣&5⃣4⃣*
Faɗowa wata bishiyar kuka gabansa ce ta dawo da shi duniyar saboda da bai ma san me yake ba, bai san wace ƙaddara ce ta kawo shi wannan waje ba domin har ya zo bai san ya zo ba.
"Hhhhhhhhhhh Yazidu maci amana azzalumi ƙarshenka ya zo"
A kai maganar cikin wata razananniyar murya.
Cike da firgita Yazid ya shiga waige waige a dajin, wasu kalar kawuna ya gani suna yawo a sama sun zagaye shi wasu babu ido wasu hanci ga dai sunan babu kyan gani.
Wata irin kwasa akaiwa ƙafafun Yazid aka damfara shi da ƙasa aka dinga tumurmusa shi a cikin ƙasar ana azabtar da shi ana lankwasa shi.
Banda ihu babu abinda Yazid ke iyawa saboda azabar da yake ji a jikinsa.
Wani mummunan jariri ya ga ya nufo shi babu ƙafafu da hannaye a jikinsa sannan idon sa ɗaya a tsakiyar goshi babu hanci sai baki gadan gadan Yazid ya nufa.
Ƙirjin Yazid dukan dubu dubu ya dinga yi zuciyarsa tana fat fat ya runtse ido domin ya saddaƙar mutuwarsa ce ta zo.
Jikinsa ne ya sandare ya kasa ko da kwakwkwaran motsi sakamakon jin wannan halitta ta jaririn a jikin yana ihu yana, Ce wa"Baba! baba!! baba!!!"
*ƁANGARAN GIDAN SU JIDDA*
"Maman Jidda lafiya muka ji kin kurma ihu ko jikin Jiddan ne?"
Wata daga cikin maƙotan ta faɗa cike da kaɗuwa na yadda suka sami mahaifiyar Jidda itama a kiɗi man.
Cikin tsananin ta shin hankali da kaɗuwa Maman Jidda ta shiga nuna musu ɗakin ta window.
Kowacce a cikin su so take taga mene dan haka suka shiga leƙawa, da sauri suka ja da baya sakamakon abinda idanunsu ya gani tashin hankalin ba ƙara mi bane.
Jidda ce a ɗakin sai wani abu take kamar wadda take yi da wasu abubuwa tamkar na aljanu, abinda ba su sani ba kuwa shine azatar da ita aljanu suke.
Da kyar kowacce ta iya jan ƙafafunta ta fice cike da tsoro suna ba za su ƙara zuwa gidan ba domin Jidda ba mutum ba ce.
Itama mahaifiyar Jidda baya ta mara musu zata fita su kai karo da mahaifin Jidda dake shigowa.
Cike da mamakin halin da ya samu matar tashi ya dubeta, Ya ce"Lafiya Maman Jidda meke faruwa na ganki haka?"
Cikin zazzaro da idanu Maman Jidda ta dube shi kafin, Ta ce"Wallahi Malam shiga ka gani da idon ka dan ba ma zan iya siffanta maka masifar ba, ni nan da ka ga ma bar muku gidan zan"
Mamaki ya kama mahaifin Jidda, Ya ce"Amma mene ne wannan da har zaki ce ba zaki koma gidan ba?"
Maman Jidda ganin mahaifin Jidda zai ɓata mata lokaci ya sa ta kwasa za tai waje amma bai bata damar hakan ba yai saurin riƙo hannunta ya dannawa gidan sakata ya jata su kai ciki.
Ɗakin da ya gani a kulle yasa ya kalli Maman Jidda zai magana amma sai ya fasa ya nufi ɗakin ya leƙa ta taga, ai ba shiri yai yo baya saboda jin wasu maganganu da kuma alamar ana buga mutum da ƙasa.
"Mariya kinga ko? Kinga halin da kika jefa min ƴa ko? To wallahi ke da Allah"
Yana gama faɗar haka yai waje tare da kulle gidan yai tafiyarsa.
Maman Jidda ta taɓa ƙofar da zummar itama ta fice amma sai taji ƙofar a kulle hakan yasa ta zauna bakin ƙofar tana kuka domin ta san idan har wannan hau kan na Jidda ya bada damar buɗe ƙofa to kashinta ya bushe gashi ɗan iskan mijin nata an masa waya yaƙi zuwa tun ɗa zu.
Shi kuwa mahaifin Jidda ko da fitar sa kai tsaye wajan wani malami ya nufa domin ya ga alamar abun na Jidda da shaiɗanu a ciki, bayan sun gaisa da malamin mahaifin Jidda ya ƙora masa bayani haɗi da halin da yarinyar take ciki.
Sosai malamin ya tausaya musu tare da faɗan me yasa ba sa neman malamai da addu'a, nan dai Baban Jidda ya bada haƙuri suka nufo gidan shi da malamin…
*HAYIN NA ILLO ƁANGARAN SU SABUWAR FATEEMA*
"Talatuwa dole ne fa ɓoyayyan abu ya bayyana"
Malam Jauro mahaifin sabuwar Fateema ya faɗa yana mai fuskantar mahaifiyar sabuwar Fateema.
Haɗe rai mahaifiyar sabuwar Fateema ta yi kafin, Ta ce"Gaskiya malam kaga bana son wannan maganar kawai mu barta domin tada bara bana ba zai ba"
"Aikwa Talatuwa ta da wannan bara da banan shine zai yi domin ko da munci gaba da ɓoye fa to dole ya bayyana wataran"
Mahaifin sabuwar Fateema ya sake faɗa yana yinsa da fuskarsa duk cikin damuwa.
Cikin faɗa mahaifiyar sabuwar Fateema ta fara magama, "Wallahi Jauro wannan maganar ba za a ta she ta ba domin su nanta matacciya kaga kuwa mataccen baya tashi"
Mamaki ya kama mahaifin sabuwar Fateema, yau shi Talatuwa take ambatar sunan sa akan abinda ta tabbata bata da gaskiya ciki kuma ba zai taɓa ɓoyuwa ba.
Miƙewa yai ya sake fuskantar ta kafin, Ya ce"Talatuwa ni kike kira da sunana gatsal akan maganar gaskiya"
Talatuwa a zafafe Ta ce"Na kira ka da Jauro tun da sunan ka ne kuma kai ka janyo saboda nace maka bana son maganar banza da wani kake iƙirarin maganar gaskiya"
Mahaifin sabuwar Fateema da ya buɗe baki zai magana sai ya fasa sakamakon ganin Fateema ta shigo tana bin su da kallon tuhuma duk sai su kai tsamo tsamo suna sussun kuyar da kai…
*ƁANGARAN GIDAN LADIDI KWADAGA*
Ga dai idanunta a buɗe suna gani amma tana iƙirin ta shiga uku to meya faru da ita?.
Ƴan uwan Ladidi kwadaga suka shiga faɗa a ran su.
Cikin kuka Ladidi kwadaga ta shiga magana, "Wai ku bakwa gani ne na makance bana gani idon na duhu wayyo Allah"
Gaban kowacce mace na ya shiga faɗuwa jin abinda ƴar uwar su ke faɗa, yanzu fa suke zaune lafiya da idonta rasss amma tace bata gani? Anya karfa maganar jama'a ta tabbata.
Shine abinda kowacce ta shiga rayawa a zuciyarta.
"Kuma ku shige ku bar gidan nan idan ba haka ba hmmmmmmm!"
A kai maganar a razananniyar murya mai cike da firgici.
Ai a guje suka dinga rige rigen fita Ladidi Kwadaga tana kwalla musu kira tana ihu amma ba su ji ba su kai ficewar su.
Wuri wuri Alkamis ya shiga yi yana mai tunani a zuciyarsa ya fice ne shima koya zauna amm ina ba zai iya zama ba shima masifar ta same shi *(Kunji fa shi da sana din sa masifar ta samu😄😄)*.
Hanyar fita yai shima a million amma sai ƙofar tai garam aka shiga dariya da wata irin murya mara daɗin sautin sauraro.
Cikin jagulalliyar murya aka shiga magana.
"Kai ka cika mara albarka ko da yake duk baku da albarkar kai da uwar taka mai baƙar zuciya mai zuciyar karnuwa amma shine kake shirin ka gudu to kaje ina? Ka fa sani duk inda kake muna biye da kai"
Gama maganar ke da wuya Alkamis cikin girgici da inda inda, Ya ce"Dan…dan…dan…Allah…ku…ku…ku rufan asiri ku taimaka min kar ku makanta ni nima ita ɗin ma ya isa tun da ai mahaifiyata ce"
Sosai dariya ta dinga tashi cikin murya tamkar ta kuka kafin ace, "Ai kai sai an maka abinda ya fi makanta kuma ba zaka mutuwa ba sai ka gwammace ba kai cin amana a rayuwarka ba"
"Fateema! Fateema!! Fateema!!! Fateema wallahi yanzu ma nayi nadama dan Allah ki kyale ni"
Alkamis ya shiga faɗa amma ina bai san komai ya lafa ba dan sai komai ya dawo normal.
Kuka ya fashe da shi yana, Ce wa"Wallahi Mama duk ke kika ja min wannan bala'in kika sa na ha'inci Fateema"
"Kai dalla rufe min baki ni baka ga masifar data saman ba nace me?"
Maman Alkamis ta faɗa cikin kuka har da majina…
*Indian Girl Ce*
_*****_