Free chapter · Read without an account
BAKAR FURA CHAPTER 12
by Fadila Lamido · BAKAR FURA
🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 56- 57
Komawa Baffah yayi ya zauna yana cike da bacin rai, yayin da Momy take fadin, " kayi hakuri kabi komai ahankaali.
Aliyu kuwa kansa akasa ya juya ya koma dakinsa tare da fadawa kan godo yai ruf da ciki yana fadin, koma me Baffah yake zargina dashi nasan bazai wuce kan wancen auren bane
dan haka sosai yaji hankalin sa ya tashi, addu'a yake Allah yasa aunty ta dawo, domin yasan dole Innawo zata aikota gurin Baffah, sai dai itama besan yadda zata dauki zancen ba.
Washegari tashi yayi da matukar zazzabi sabo da yadda yake Jin damuwa sosai, gashi agobe yake son zuwa Cameroon amman Ina, yana tsoron yadda zai fad'awa Baffah.
Daker ya iya daurewa da yamman ya fito misalin karfe 5, bemasan inda zashiba kawai dai fitowan yayi, motarsa ya shiga ya zauna yana kokarin tadata yaga an bude gate din gidan, motar gidan su aunty Ruqayya yaga tana shigowa, take ya sake ajiyan zuciya batare data sani ba, domin yasan duk yadda akayi aunty ta dawo kenan.
Jira yake yaga danta Abba ya fito amman abun mamaki ita da kanta ya gani tana saukowa.
Cike da zullumi ya bude motar ya sauko, ya nufeta, yayin da tana ganin shi ta sake murmushi.
Dafda ita ya tsaya aunty yaushe kika dawo?
Jiya da Yamma, ance min kaje, Ina ta Allah Allah karka kama hanya.
Gobe nake da niyar tafiya, wani aikine ya taidani.
Ka makara matarka nata fushi dakai.
'Dan kawar takai yayi domin zuwa yanzun yasan tasan komai, cike da sonji yace, " kinje ne?"
Eh bama sau daya ba.
Sunanan lafiya ko?
Lafiya Lau, to Kai yaushe ka dawo?
Jiya da safe, nadawo ma nasamu Baffah sai fad'a yake yi, yana nuna wai yana zargina bani da gaskiya, jiyan ma shine yace in Kira masa ke.
Dan takatawa tayi da tafiya tana fadin, wani ya kawo masa labari ne?
Shine ban sani ba Aunty.
Jimmm tayi zuwa can tace, " ai yana gida yanzun ko?
Yana nan.
Barin je karka shigo, idan ba kiranka yayi ba .
Amsawa Aliyu yayi sannan ya koma cikin motar sa ya zauna.
Ruqayya ko ciki ta shiga cikin fara'a Momy ta tareta, bayan tace mata gurin Baffah tazo aka kaita har falon sa, Baffah na sauke ajiyan zuciya suka gaisa da Ruqayya, sannan yace mata, daman Ina son ganin ki, jiya na aika Haydar ya kiramin ke yace kinyi tafiya.
Eh Baffah Ina Cameroon, jiya da daddare muka shigo, toh daman Innawo ta bani sako tace Ina dawowa inzo in isar mata da sakonta gurin ka.
Toh toh naji, nima Ina son nai mgn dake, amman kafin nan bani sakon na Mama.
Shiru Ruqayya tayi tama rasa ta Ina zata fara, zuwa can tace, nima zuwa Cameroon din kirana tayi, tunda naji kira nai saurin tafiya, toh daje sai take min bayanin cewa akwai yariya data sauka a agidan nan watannin baya, wadda Aliyu yazo da ita.
Eh tabbas matar abokin Aliyu ko?
Eh toh, Innawo tace kayi hakuri kuma ka fahimci zancen dakyau dan Allah.
Inajin ki, muje, muje Ruqayyatu.
Toh Baffah wannan yariyar ba matar abikon sa bace kamar yadda ya gaya maka.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Baffah ya fada sannan ya tsare Rukayya da idon sa yana fadin inajin ki.
Baffah wannan yariya ta dalilin ta Ummi ta koro Aliyu daga can Cameroon ya dawo nan da zama, domin sun nuna suna son juna, Kuma anyi anyi su rabu sunki, a yadda suka bani labari family yariyar ba inda basukai mgnr ba har kotu anshiga, amman sunki rabowa da juna, dan haka ta turoshi gurin ka kawai.
Subuhanallahi, kinji irin abun ko?, amman da Aliyu yazo nan, ba yadda banyi dashi ba inji dalili yaki fada min, daga karshe nabarshi kawai tunda Naga bason fada yake ba.
To Kuma Baffah sai gashi ya kumayin wani kuskuren agaba, domin da yariyar ta biyo shi nan kasar bayan shekara biyar da rabuwan su Ya kamata ya sanar maka sabo da abashi shawaran abun da ya sace.
Shiru Baffah yayi yana jinjina zancen, cikin ransa zuwa can yace, " a'a ikon Allah, bana mantawa lokacin na mishi fada akan zuwanshi da ita, amman saiya rufemin baki da fadin ajiyansa aka bashi Kuma ma matar Aure ce, toh abun da yasa ban damu ba lokacin, yariyar cikin su Meenat ya barta, daga baya yace min Mijinta ya dawo, tazo tamin sallama na mata alheri, duk ta saba da yara, yanxun haka ko jiya sunata cewa zasu zasu Cameroon gurin ta.
Ai Baffah da yace maka Mijinta ya dawo mota yasata ta koma gida, Innawo tace dan Allah Kai hakuri karka dauki zancen da zafi dan kafin ta koma gida wani abu ya shiga tsakanin sa da yariyar........
Batakai ga karasawa ba Baffah ya dafa kansa yana fadin Innalillahi wa inna ilaihir raju'un.
Yana rike da kansa aunty Ruqayya tace Baffah dan Allah kayi hakuri abun da suka guda kenan suka turoshi nan, amman dake kaddara ta riga fata soyayya najanta, saida ta biyo shi nan, bayan Kuma ta koma da wata uku iyayenta suka gane tana dauke da ciki, wadda aka rasa inda ta samushi, domin bata kula kowa, Baffah saida yariyar ta haihuwa aka tabbatar d'an na Aliyu ne, domin jinin sa ya nuna sosai Koda yariyar bata fada ba yaron yayi kama dashi kamar an tsaka kara.
Motse baki Baffah yayi idon sa akasa sannan ya dauke gilashin sa dake gefen kujera yasa a idon sa, daker ya iya bude baki yace, shikenan sai ya aureta kawai.
Jimmm, Aunty tayi sannan tace, " eh bayan yaje lokacin ta haihu kotu suka kaishi, nan ta kwashe komai ta gaya masa har tahowan da tayi da yariyar.
Bayan ya gama sauraron Ruqayya yace, " shikenan Ruqayya bakomai, ni musulmi ne dole in amshi kaddara mekyau da mara kyau, ni daman naji kishin kishin din yayi aure a Cameroon, naji daga wani abokina da nake bawa sako na musashi, ganin wani ya sake min mgn nace barin tuntube ki, su Kuma iyayen yariyar ai bekamata suyi watsi da ita ba, wannan auren da akayi shine maganin abun, Kuma wannan ya Isa yasa zuciyar su ta huce, Amman fa laifin na Aliyu ne, inda ya gaya min tunfarko da ke zan nema kisata agaba ki mayar da ita gaban iyayenta, su Kuma iyayen idan suna da hankali lokacin zasu gane auren shiyafi dacewa dasu.
Ai Baffah iyayen yariyar nan banjin kome za'ayi zasu bada ita.
Toh shikenan, abun da ya faru ya riga ya faru, yanzun abun da za'ayi tunda Aliyu beda gurin zama, besa zaiyi aure ba bare ya nema, wancen part din daman can danshi na gina shi, yariyar tazo ta zauna aciki amman fa duk abun da zanma Aliyu yanzun zan masa domin yariyar ne, domin yariyar ce abun tausayi idan bata samu farin ciki ba akwai matsala dole Aliyu ya riketa dakyau, idan har yana son in huce dashi ya kyautatawa yariyar nan, akanta zan bashi mamaki matsawar yace zai wulakantata. Tun shine silar lalata mata rayuwarta, Ina da 'ya'ya mata idan aka masu bazanji dadi ba, dan haka itama yariyar nasoko cikin yarana idan ya nemin ya wulakantata zan rufe idon incimai mutunci, wannan shine sharadina.
Cike da farin cike Aunty tace toh mungode Baffah insha Allahu zasu zauna lafiya.
********
Aliyu taganin tahowan Aunty ya fito cikin motar, yadda yaga fuskanta yasashi ya sake murmushi yana fadin, " kungama?"
Eh, ya fahimta, amman kasan dole zaiji babu dadi, ya Kuma ce babu wulakanci, Kuma a kanta zai iya saba maka, yana nufin dai beson rigima, yana son ka rike ta amana.
Ba rigimar da zamuyi aunty, ko munyi ma babu meji kanmu.
Murmushi tayi sannan tace Allah yasa, amman ai koni yanzun najiku, tunda Aysha bakaramin fushi take dakai ba, samunta nayi fa ta hada akwati zata shiga duniya, sabo da fushin da take dakai.
Nashiga uku, ya fada yana zare idon, tare da fadin, har kin Kara min tashin hankali, Anya kuwa baxan tafi yau ba?, toh aunty kinji dai nayau, amman insha Allahu wannan ne nafarko da kikaji kanmu kuma na karshe.
Dariya aunty tayi sannan tace, zafi kowa farin ciki da hakan kuma lokacin ne zan tabbatar daku masoya ne, Aysha kuma daker na dakatar da ita, Amman zakazo gidan mu da daddare ko?
A'a kam, muyi sallama kawai yanxun?
A'a kaxo.munyi da ita zam bada sako ka Kai mata.
Kansan ya sosa kadan sannan yace saina zo toh.
Motar ta shiga suka bar gidan yayin da Aliyu ya koma cikin gida yana sauke ajiyan zuciya.
Misalin 8:00pm Aliyu ya fito da nufin zuwa gidan aunty saidai yana son ya sanar da Baffah gobe zai wuce Cameroon dan haka ya fara zuwa falon sa, da sallama ya tura kofar ya shiga, Islam da Meenat ne suka amsa Baffah ko juyar da kansa yayi can gefe.
Zama yayi agefen sa yana fadin Ina wuni Baffah.
Lafiya, kawai ya iya cewa fuskan sa babu alamar walwala, Su Meenat ne suka gaidashi ya amsa sannan ya sake kallon Baffah yace, " gobe zanje Cameroon.....
Tun be rufe baki ba Baffah yace, " ka gaishe su.
Kasa tashi yayi domin ba haka suka saba sallama ba idan zaiyi tafiya, ya dade zauna sannan ya tashi jiki ba kwari ya fito.
Baffah kuwa Aliyu ta nafita ya mikawa su Meenat key din part din da Aliyu zai zauna yana fadin, " ku rike wannan masu aiki zasuzo gobe su karba.
Baffah na meye ne key din?
Na wancen part din ne, yayan ku zaizauna aciki da matar sa.
Baffah zaiyi aure ne??
Yamayi a Cameroon.
Idon suka zaro saidai sun kula kamar Baffah bayajin dadi dan haka sukayi cikin gida.
Basu dade da fita ba Momy ta shigo lokacin Baffah yana dafe da kansa, kallon sa tayi sannan tace Alhaji wani lbr naji abakin yara, wai da gaske Haydar yayi aure a Cameroon??
Eh, yayi.
Amman Alhaji kana nuna min iyakata agidan nan, wato sabo da banice uwar shi ba bazaka gaya min komai da ya shafe shi.
Kiyi hakuri, cikin bacin rai nake, abu me dadi shi kake rawar jikin gaya, Ina wannan yariyar da ya taba sauka agidan nan?
Eh naji matar abokin sa.
Karya yamin kawai matar sa ce.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, lallai ma Aliyu.
Baffah da beson zancen yai nisa mikewa yayi kawai ya nufi dakin gidan mahaifiyar sa.
******
Ai danaga har 08:30pm baka zoba na dauka baza kazo ba.
A'a aunty, na tsaya gurin Baffah ne, kince ya fahimta amman naga daker yake min mgn.
Cikin ido ta kalleshi sannan tace karka damu da wannan, Kai inda ace da yariyar da 'Dan kazo mishi ai da kun kwasa 'yan kallo, karka damu ai abun ma yayi kyau, kama godewa Allah, har cewa yayi fa ga guri nan ka zauna kafin ka nemi wani.
Karyar dakai Aliyu yayi yana fadin, toh yanzun aunty bani sakon in wuce sauri nake yi"
Toh shiga daki yana nan gefen gado ka dauko.
Mikewa yayi yabi hanyar data nuna masa, be taba shiga dakintaba amman Kai tsaye ya tura kofar.
Babban dakine me dauke da wawakeken gado, idon sa ya sauka akan wani yaro dake ta wasa da kafarsa da hannunsa, sai kushin kushin yake, tsintan kansa yayi da saurin karasawa, saidai idon shi na sauka akan yaron yaga kamar gizo ne dan haka yasa hannun sa yana kokarin daukan yaron tare da saurin juyawa yana Kara kallon yaron.
Cak ya atsaya alokacin da yaga Aysha ta fito daga wanka towel daure bisa kirjinta yayin da ta yafa wani a kafadanta.
Binta da kallon yayi sosai yake mamaki yana Kuma tsareta da ido.
Itako Aysha ganinsa ya sata daure fuska sosai, tasan dole ne yasan tana gidan Amman bata zaci zasu hadu da wuri haka ba, ganin inda yake binta da kallo tundaga sama har kasa yasa tai saurin komawa toilet din yayin da yai saurin takowa tare da mika hannun sa, adaidai wannan lokacin ta bugo kofar tare da fadin, wayyo aunty!!!
Runtse idon sa yayi saboda zafin da yaji sosai kofar ta matse hannun sa, yayin daya kara rike Khalipa dakyau da hannun sa daya yana fadin, "Aysha menene haka?, daman kun taho tare?, Aysha ki bude kofar mana"
Arikece Aysha ke Kiran sunan aunty ganin haka Aliyu yace, " ki bude ki fito, kibar kiran aunty haka.
Nika fita, bana son ganin ka.
Ni din?
Eh.
Haba Ayaha nine fa yaya Aliyu malamin ki, daman d'aliba tana fushi da malaminta ne???
Toh bakai bane saikamin alkawari baka cikawa dan kawai kaga bana gurin, ka manta dani😭
Nidin?, akasi ake samu Aysha, tayaya zan mance ku, arana bana iya kirga so nawa nake tuna ku, kiyi hakuri kinji.
Ni ba kalmar da zaka gaya min.
Toh naji, yanzun fito ki amsa Khalipa.
Ka ajeshi inda ka ganshi.
Toh zan ajiyeshi, sai yaushe zan ganki to??
Ni karka sake min mgn.
Kawar da kansa yayi daga kallon kofar, Khalipa ya zubawa ido sannan yace, naji bazan sake miki mgn ba, amman kibani rana da lokacin da zan miki mgnr.
Jinta shiru yace mgn nake fah.
Ni babu ruwana dakai
Lumshe ido yayi sannan yace, aure muka yi fah Aysha, kinta ganin mata tace babu ruwanta da Mijinta alhalin tana karkashin ikon sa??
Wannan karon batace komai ba,dan haka yaci gaba da cewa, ," baya ga haka Kuma ke dalibata ce, Kuma har yanzun ni malamin ki ne dan haka ki fito kawai.
Yana gama fadin haka ya koma bakin gadon ya zauna yana me zubawa kofar ido, zuwa can yajita cikin kasa da murya tace, " ka dan miko min hijjabina.
Akwai yaro a hannuna kizo ki dauka.
Ka ajeshi mana
A'a, ya fada sannan ya dauke kansa yana cigaba da fadin, Idan sabo da nine na juya baya na ki fito abun ki.
Lekowa tayi taga ya juya bayan kamar yadda yace, dan haka ta fito tai saurin daukan hijjabinta ta sanya, shiryawa tafara, yayin da Aliyu ya maida hankalin sa kan Khalipa tsayon lokaci sannan yace, " idan kin gama zan wuce.
Can kasa tace nagama.
Juyawa yayi ya kwantar da Khalipa tare da tufa masa addu'a sannan ya mike har ya wuce ya miko hannunsa ya jawota ya hada ta da kirjinshi ya rungume.
Sosai ya rungumeta tamkar wani zai kwace ta, ajiyan zuciya yake saukewa da karfi yayin da numshin sa yake sauka a tsakar kanta lokacin daya yake kewaye duk ilahirin jikinta, nan danan taji jikinta na amsawa, bata so ta sauko da wuri haka ba dan haka ta kokarin ta dake, daker take iya turesa take kaimasa duka.
Duk inda ta nemi ta kubce rokota yake, gashi tanayin abun ne cikin kuka gaba daya.
Aysha kiyi hakuri, bason bacin ranki nan, gaba zaki tabbatar da haka, Ina tsananin sonki fiye da tunanin ki, kuma zanyi kokarin insaki farin wadda ba'a iya kwatantawa, kibar zargina akan rashin cika alkawari, na farko nasan da gangan nayi, saboda tun ranar da kika gayamin jiya kika gama al'adarki na rubuta na ajiye, Kuma saidana kirga wata tara sannan na kamo hanya, amman wannan karon akasi aka samu, dan Allah ki nutsu ki gaya min matsalar ki ayanzun dani, nikuma zanyi kokari in gyara komai, zama nake son muyi mekyau, Ina son ki bani hadin kai, ya kasance ni dake har abada babu mejin kanmu, ko wani abu ya faru tsanin mu ne kowa banson wani yaji, nasan halin ki kinsan nawa, nasan kina da taurin Kai, ni Kuma ina da zafi idan raina ya baci, yanzun kinsan me nake so dake???
Tana kwance akirjin sa ta kirgiza kanta.
Bani shawaran hukuncin da zan dinga miki idan kin kureni da taurin kanki, nikuma zan baki shawaran abun da ya kamata kiyi idan fushina ya tashi har kika rasa inda zakiyi dani......
***
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 58- 59
Tsintan kanta tayi da sakin murmushi tana kwance a kirjin sa, saidai ta gaza cewa komai.
Ganin haka Aliyu yadan dagota yana me kura mata ido yace, " inajin ki, kibude baki mu nemi mafita kinji.
Kwace kanta tayi ta koma ta kwanta jikin shi, ahankali tace, ni bani da taurin Kai yaya Aliyu.
A'a, banson sonkai Aysha, ni na yadda Ina da zafi, idan raina ya baci, kema ki yadda da taurin kanki sai mu nemi mafita kawai.
Jimmmm tayi, zuwa can tace to ai abu me saukine ya Aliyu, kawai cemin zakayi dauko littafin ki cikin buga irin wannan tsawar taka dake rudar dani, danaji haka zan shiga hankalina.
Murmushi yayi sannan ya Kara rungume ta tare da sumbatan Kumatun ta, sannan yace, "cemin zakiyi danaga kin fara tirjewa sai in hade fuska in koma Malam Yaya Aliyu?
Kai ta daga tana mejin wani farin ciki na shiganta cikin zuciyarta, ahankali tace kaifa ya zan yi dakai toh.
Kanta ya rungume sosai akirjinsa, yana Jin saukan numfashin da take har cikin zuciyar sa, sannan ya fara fadin, " idan Kinga raina ya baci har na fara fada, kinsan me zakiyi??
Kaita girgiza tare da fadin, " a'a"
Ahankali yace, " kurma zaki zama, duk abun da zance karki kulani, idan Kuma tambaya ce nayi, amsa kawai zaki bani, iyaka gaskiyar ki, har sai kin Bari na gama sai kice Allah ya huci zuciyar ka mijina abin alfahari na.
Cikin sauri Aysha ta dago ta kalleshi cikin idon, Yaya toh ai wannan wayo ne kamin, idan Kuma maganganun ka sun sauka daga kan layi fah???🤔
Eh duk da haka dai hakurin Zaki bani, idan akwai kalmar da kike ganin batai miki ba, bayan kin tabbatar da na huce saiki same ni da ita, nikum insha Allahu zan miki a dalci.
Ciki da gamsuwa tace shikenan.
Yauwa Aysha barin zo inje gida Kinga dare yayi sosai, gobe zan zo, me zan kawo muku??
Babu"
Akwai, kiyi tunani da kyau.
Allah babu, idan Kuma akwai goben sai in gaya maka.
Amsawa yayi, cike da gamsuwa ya saketa sannan ya juya ya fita.
Koda ya fito falon Abba kawai ya samu, tambayan sa yayi Ina aunty, amsa ya bashi da tana falon Abban mu, dan haka yace masa kace mata na tafi da safe zan dawo.
****
Gida Aliyu ya koma cike da tunanin Aysha, sosai yakejin nutsuwa na shigarsa mara iyaka, rabon da yaji irin sa ya manta, bacci yayi me dadi, hakama bayan ya dawo sallah Kara kwanceya yayi wadda har ya dauke sa 11:30 sannan ya tashi, wanka yayi sannan ya shirya cikin manyan kaya da hula, fitowa yayi da nufin zuwa gidan aunty, saidai yana fitowa suka hadu da Baffah, cikin sosa kai ya gaida shi bayan ya amsa ya wuce ya shiga motarsa ya zauna, harya tada motar yaji Baffah na cewa Hajiya na neman ka.
Amsawa yayi da toh sannan ya fito agidan.
Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce, afalon ya sameta cikin tsananin Jin nauyinta ya gaidata, fada ta fara masa akan baya kula mutane ko zuwa gidan ta yanxun baya yi, yayin da ya bata uzurin aikin sa ne baya bashi daman haka akarshe yace zai dinga kokartawa yana zuwa.
Jinjina Kai tayi cike da gamsuwa sannan tace, jiya Babanka yazo min da wani labari mara dadi, duk da cewa kaddarace amman babu dadi Sam, Kuma baka kyautawa iyayen ka ba damu baki daya. Kaga na farko daga mahaifin ka har mahaifiyar ka sun jaka ajiki, suna nuna maka kauna, basuki su mika komai nasu agareka ba dan me zaka rufe su?, Ran Baban ka ya bacci, amman natunatar dashi cewa idan ka gaya mishi Yaya za'ayi agujewa kaddara, nabashi hakuri dan haka kaima ka sameshi ka bashi hakuri, dan kayi kuskure gaskiya.
Kawar dakai yayi ya fesar da ajiyan zuciya sannan yace, " toh nagode Hajiya, na karma kuskurena kuma Ina tabbatar maku ba abun da nayi da gangan kawai na tsinci kaina acikin kaddara ne, insha Allahu zan kiyaye.
Allah ya baka iko, dan Allah ku dinga neman shawara, yanzun acen matar taka tana gidan Yayarka ko?
Eh tana can.
Toh ya kake gani, babu matsala?, Idan da matsala ka kawota nan ta zauna dan gaskiya yariyar tana bukatan kulawa.
Babu wata matsala Hajiya insha Allahu.
Allah yasa, duk wadda yai maka fada cikin 'yan uwa kabashi hakuri, domin jiya Baban ka dun ya tarasu yace masu kayi aure har matar da haihu babu sanin sa, wasu daga ciki ransu ya baci nima nayi fushe dakai lokacin saidaga baya yamin bayani, dan haka duk ma wadda yazo maka fada ka saurareshi kawai bayan ya gama ka bashi hakuri.
Nagode Hajiya.
Toh shikenan, Sai Kuma mgn ta gaba, Abbas yace baka taba lekawa gidan shiba tunda yai aure?
Juyowa yayi ya kalli Hajiya sannan yace, " lallai ma yaron nan ya raina ni, me zanje gidan shi inyi?, auto zuwan da nake ma gurin aikin sa mu gaisa be ishe shi ba har ma so yake Kuma in dinga zuwa gidan shi.
A'a to meye dan kaje gidan nasa?, Baka so kuyi zumunci ne??
Haba kanina ne fah Hajiya..
Wani irin kallo ta masa sannan tace ta yaya ya zama kanin naka?,🤔 kenan Kai baka da azumunci.
Ni ba haka bane Hajiya gidan sane dai bazanje ba, duk sanda nabi ta office din su in shiga, amman kawai saina tashi gotai gotai dani inje gidan sa.
Waini Tsaya in tambaye ka kaita Abass din waye gaba ne??
Cikin sauri yace, nine Hajiya.
Bakai bane, ai inajin Abbas yayi shekara da watanni yana shakar iskan duniya sannan aka haifika.
Wai da gaske Hajiya??
Sosai ma kuwa, kaje ka tambayi iyayen ka, shi bece ya girme ka ba yake son zumunci sai Kaine zakace wani wai gotai gotai son girma kamar gyanbo.
Dariya Aliyu yayi sanan ya mike yana fadin karma ki gaya masa wai ya girmeni dan Allah Hajiya, idan na samu lokacin zanje.
Da haka sukayi sallama da hajiya, masallaci yaje daganan bayan yayi sallah ya wuce gidan aunty yana me cike da farin ciki.
Tun kafin ya shiga falon yakejin muryanta ita da Sadiya suna hira cikin fulatanci dake aunty najin yasa itama Sadiya ta iya, sallama yayi ya shiga, yayin da duk suka waigo suka kalleshi cikin girmamawa, Aunty ya gaida yayin data amsa cike da sakin fuska, itama Sadiya gaidashi tayi yayin daya sata kallon Aysha dake durkushe gaban aunty tana rufe wata roba.
Kawar da idon sa yayi adaidai lokacin data ce Ina wuni?
Lafiya Lau ya fada kansa agefe yayin da yaci gaba da cewa Aunty me kuke hadawa ne naga duk hankalin ku ya dauke?
Kanina turare ne irin na wuta, jiya kuma saika wuce babu sallama bare godiya.
Murmushi yayi sannan ya maida da hankalin sa kansu yana cewa, "aini aunty baki taba sani farin ciki kamar yadda kika Sani jiya ba, sai jiya na dada tabbatar da cewa lallai bakaramin so kike min ba.
Dariya Anuty tayi tare da fadin, " gara daka gane, ai Ina son ka, Kaine kaita shareni agarin nan, Kuma abun da yasa ban gaya maka ba, Aysha cewa tayi indai gunka zan kawota bazatazo ba, dan tana fushi dakai....
Satan kallon Aysha yayi sannan yace, " aunty wannan mgnr fa babu ita, an dade da wuce gurin ko Aysha??
Satan kallon Aunty Aysha tayi sannan ta sunkuyar da kanta.
Cike da murmushi Aunty ta dubi Aysha tace wai babu ita Aysha??
Cike sauri ta kawar da idonta sannan ta daga Kai.
Aliyu ne yace da baki Zaki gaya mata.
Cike da Kunya Aysha ke buye fuskanta yayin da aunty tashiga tafa Hannu tana fadin, "yanzun duk wannan uban fushin da kikayi tashi daya kanina ya rugujeshi🤔
Shiko Aliyu fadi yake, "Aysha ki bude baki kiyi mgn, ganin tana kara boye fuska ya mike yana kokarin zuwa gurin su, ganin haka Aysha tai saurin mikewa tana fadin nafa amsa.
Ai dakai kika amsa bata gani ba.
Cikin kukan shagwaba tace, ai tagani so kake kawai inji kunya.
Dariya Aunty tayi tana fadin, " Kanina rabo da ita.
Komawa yayi ya zauna ganin tana shirin guduwa, gaban aunty ta koma yayin da aunty tace, " dazon munje Asibitin da Aysha, yanayin wankan jegon datayi ne ban yadda dashi ba.
Cikin kawar da Kai yace, sannu Aunty Amman to ba matsala ko?
Babu insha Allahu sundai bata wasu dan magani.
Sadiya ya kalla dake goye da Khalipa yace, bacci yake ne?
Eh Uncle, tun da aka masa wanka yake bacci
Agogon hannun sa ya kalla, kusan daya da rabi ake nema dago kansa yayi yace ma Sadiya toh baccin nan na lafiya ne kuwa?
Lafiya Lau, yaji dumi ne kawai.
Toh ai yakamata a tada shi, Sadiya kawo shi.
Zuwa Sadiya tayi gurin ta sauke shi a hannun Aliyu yayin da Khalipa yai saurin ware idon shi tare da kuka gaba daya.
Cikin yamutsa fuska Aliyu yace Kuka Kuma, kujimin yaro, nifa banson kuka, a kafa yasashi yana fadin, " yi shiru mana"
Hmmmm ai tunda ka tasheshi Kuma saiya sha nono tukun ko zaiyi abun arziki.
Zaiyi shiru Aunty, mikewa yayi yana mishi wasa saidai karama tsandarewa da ihu yake dan haka ya Karasa gaban Aysha ya mika mata shi yana fadin, " bashi Nono.
Amsan sa tayi sannan ta sashi cikin hijjabinta, tsayon lokaci.
Zuwa can Aliyu ya kalleta yace," ya haka ne, kin wani takureshi babu ta inda numfashin sa ke fita.
Juyawa ta karayi domin kaucewa ison Aliyu yayin da Aliyun ya shiga fadin, " aunty wai haka take yi ne daman ko ganina ne??
Haka take Aliyu, ai Naga kanwar tawa akwai kunya.
Kawar da zancen Aliyu yayi da fadin, aunty naga an fara gyaran fah.
Cikin kallon idon Aliyu tace, " da wuri haka?, koda idan an gama sai arufe duk ba matsala bace,
Bangane sai a rufe ba aunty?
Eh mana, kafin lokacin da za'a yaye Khalipa.
Dariya Aliyu yayi harya fitar da sauti, sannan yace' " haba Aunty, kina nufin bazataje can gidan ba sai anyi shekara nan gaba? ai wannan bama abun da zai yiyu bane.
Au haba?
Allah aunty, ni ko yau banki mutafi ba.
Jin haka Aysha ta mike tabar falon yayin da aunty da Aliyu sukaci gaba da tattaunawa tsakanin su.
Hakace ta cigaba da kansacewa kullum da yamma Aliyu ke zuwa gitan aunty, hira suke sosai tsakanin su, dan haka shakuwa takara shiga me karfi, yayin da ya dada sabawa da aunty Rukayya da yaranta hakama Fahat.
Satin ta Uku a Nigeria, Daddyn Ayaha ya yazo ganin inda take, gidan aunty Rukayya ya sauka kamar yadda Innawo ta bashi adireshin farin ciki Ayaha ta shiga mara misaltuwa wadda har saida ta fara kwalla, sai dare Aliyu yazo ya kaishi gurin Baffah sannan ya fita ya basu guri.
Tattaunawa sukayi ta fahimta tsakanin Baffah da Daddy, inda akarshe ya dauki kudi daidai gwargwadon iyawarsa ya bawa Baffah acewarsa a sayawa Aysha kayan daki, nan Baffa ya shaida masa ya saya mata komai amman duk da haka yaki karba.
Washegari Daddy yayi sallama da Baffah cikin girmamawa da mutunta juna, Aliyu ne ya dauke sa ya sake komawa dashi gidan Aunty sukayi sallama da Ayaha sannan yakai shi Tasha.
Bayan kwana biyu da tafiyan Daddy Aliyu yazoyiwa Aysha Sallama dan washari zaiyi tafiya wadda sun gama tsarawa da aunty yana dawowa zata tare.
*********
Yaushe zaka dawo??
Sati 6
Zaro ido Aysha tayi cikin baccin rai tace nifa banson tafiye tafiyenan, Kuma yaya Aliyu har sati 6??
Kanta ya rike da duk hannun sa biyu, sannan yace, " kiyi hakuri yanayin aikina ne, ki shirya dana dawo ko kwana daya bazan bari ki karaba zamu wuce gidan mu, nakosa na ganki cikin farin ciki.
Yaya Aliyu ko yanzun bana cikin damuwa ai, damuwata daya Mamana.
Karki damu mucigaba da addu'a insha Allahu za'a daidaita, hannun sa yasa ya cire mata kwallar data taro agefen idonta sannan yace, " kimin murmushi karkisani in tafi da damuwa.
Dagowa tayi daga jikinsa tana murmushi me kama da yake tare da lankwasa hannunta.
Ganin haka Aliyu ya mika hannun sa ya ruko nata, kibar dan lankwasa hannun nan, wannan karon bazan Kara kwanakin ba insha Allahu, sunbatanta yayi sannan yace kimin addu'a.
Adawo lafiya Allah ya tsare.
Ameen ya fada sannan ya saketa ya juya.
Tunda Aliyu ya tafi aunty gyara Aysha take dan ta kula ya zaku ta tare, har mamakin Aliyu aunty take, gashi dai Aysha goyone da ita amman rawar kafar da yake akanta bashi da banbanci dana wadda za'akai masa sabuwar amarya dal, abu daya ke kwantar ma aunty da hanka idan ta dubi Aysha taga yadda Allah yayi mata surah mekyau, babu me kallonta yace wai ta haihu, sau daya aunty ta taba ganin nonon Aysha yayin da tayi mamakin kamar ba shayarwa take ba, sosai ta yaba hallitan Aysha wadda take tunanin ko kyanta ne ke ruda kanin ta, yaron ma ba me kallon shi yace nata ne kasancewarta fara tass shikuma baki, gashi bata nuna wani damuwarta akanshi.
Ranar da Aliyu ya cika sati 3 da tafiya Aysha ta tashi da kewanshi sosai, gani take kamar shekara yayi, Kuma wai yanzun nema yayi rabi, kwalla ta share sannan ta debo kayan Khalipa ta fito tana kokarin wankewa, kallonta Sadiya tayi dake bakin fanfon tace, " Aunty Aysha ki barsu na wanke.
Barin wanke Sadiya, nagaji da zama ne.
Tahowa Sadiya tayi suka shiga wankin tare sunayi suna hira, tas suka wanke sannan suka shiga dauraya.
Jimmmm Aysha tayi, Sadiya naji Karan mota ta shigo gidan nan.
Nima naji aunty halan Abbanmu ne tunda Uncle baya na......
Cak ta tsaya ganin Aliyu tsaye a bayan Aysha yayin da taga yasa mata Hannu abakin shi alamar tai shiru.
Kokarin sunkuyawa take domin tacigaba da daurayan yai mata nuni data koma daki da hannun sa, dan haka cikin sauri ta maida kayan cikin bahon tana fadin aunty Ina zuwa.
Aysha da batasan me yake faruwa ba ta cigaba da wankin ta, shiko Aliyu bokitin ruwan dake bayan Aysha ya sunkuya ya dauka ahankali sannan ya koma nesa da ita ya rage ruwan akasa sannan ya juyo ya daga bokitin ya shikoshi jikin ta.
Shiiiiiiiiiiiii, wayyo Allah na, Ayaha ta fada tare da gantsarewa, runtse ido tayi tanajin sanyin ruwan na ratsata, yayin da doguwar rigarta ta dame jikinta gaba daya surarta ta baiyana, cikin tsananin mamaki ta juya bayanta dan sanin dalilin zuwan ruwan nan jikin ta.
Aliyu tagani rike da bukiti yayin da yake kashe mata ido cikin fara'a sosai yake kare mata kallo.
Kaikakai lalalala wlh bazan yadda ba cikin saurin ta wuwuri bahon da kayan gaba daya tayi kanshi yayin da yai saurin daga hannun sa sama yana fadin, " yi hakuri, yi hakuri, karki jika ni, cikin dariya yake maganar ganin ta nufoshi yasa gudu, cikin dariya sosai, saidai be aune ba yaji ruwan da ka kayan ajikin shi dan haka ya tsaya cak yana kallonta tare da riko rigar kakinsa ta baro jikin shi.
Karan gudun Aliyu da dariyar da yake har yanzun yasa aunty fitowa tsakar gidan cikin zare ido.
Cak ta tsaya tana kallon gidan, duk ya jike ga Aysha sharkaf, hakama Aliyu, kasa ta kalla taga kayan Khalipa akasa, baho, bokiti nan danan gidan ya hargitse.
🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 60- 61
Yau naga abun da ya ishe ni, Aliyu menene haka?
Daker ya iya danne dariyar sa aunty wai daka inai mata wasa shine ta shi'ka min ruwa.
Shine ya fara aunty bukiti days ne ya juye min shi ajiki.
Jikin Aysha aunty ta kalla tayi tsamo tsamo sannan ta kalli Aliyu wadda gaban rigar shine yajike tace, " lallai akwai aiki, Aliyu daman haka kake?🤔
Wasa fa na mata Aunty.
Tsugunawa aunty tayi tana kwashe kayan yayin da Aysha ta shiga tayata, aunty kuwa fadin take, " dan Allah ji, yanzun wannan haukan zakuje kunayi agidan naku, naso da ace Ummi taga wannan haukar taka.
Dariyarsa ya fadada tare da fadin, Allah sarki Ummi na.
Nan danan yaji tunanin Ummin sa ya dirar masa , cikin sauri ya juya aunty natafi inyi wanka daman banje gida ba.
Mikewa aunty tayi tabi bayan shi tana fadin ajike zaka tafi?
Toh yaya zanyi aunty, banso yara su ganni ajiki.
Har bakin motar aunty ta biyoshi, yayin da ya shiga motar ya zauna aunty tace, "amman dai bayau bane tarewar taku, yau satin ka Uku da tafiya.
Yaune Mana aunty.
Sati fah shidda kace zaka yi.
Eh amman Aunty Aina gaya miki nadaina gaya mata gaskiyar ranar da zan dawo karawa zan dinga yi saboda gudun matsala.
Eh toh amman duk da haka ka Kara mana ko sati daya ne.
Ya mutsa fuska yayi, haba mana aunty, ko tausayina bakiji, yanzun idan wata tafiyan ta taso min nan da Sati daya natafi kuma kikasan yaushe zan dawo?, Nidai anjima zanzo mu tafi inyaso idan San tafi saina kawota ku karasa kafin indawo.
Murmushi aunty tayi tare da fadin, " ai indai ta riga ta tare shikenan Kuma, jeka anjima zan rako ta.
Aunty gara dai inzo ke zaki iya dadewa baku zoba har nagaji da jira.
Juyawa aunty tayi dan takula Aliyun bawata kunya gare ba, fadi take nidai nace karkazo zan kawo ta.
******
Misalin takwas da rabi na dare Aysha ce Da Aunty Ruqayya acikin dakin Hajiya mahaifiyar Baffah.
Khalipa rike a hannun Hajiya tana kare masa kallo idon ta cike da kwallah take fadin, "bawan Allah, Allah yama rayuwarka Albarka.
Ameen aunty ta fada yayin da Aysha tai kasa da kanta ko iya dagowa bata yi.
Hajiya ce ta cire kwalar dake idonta sannan ta kalli Aysha tana fadin, "to ki dago min fuskarki inganki mana ko matsoraciya ce ke me tsoron kishiya.
Sosai Aysha ta karayin kasa da kanta tare da wasa da hannun ta tana zaune cikin hijjabi yayin da take zuba kamshi.
Aunty ce tai dariya tana fadin, Ina ba tsoro sai dai kunya hajiya.
Kunya ko Kuma kishi dai, Kinga ni bana kishi, ki saki jikin ki, nan ma gida ne, Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a masu albarka.
Ameen aunty ta sake fada, yayin da hajiya tafara daga murya tana Kiran sauran jama'ar gidan, babban gida ne sosai Kuma duk family ne, nan danan kuwa suka iso yayin data masu nuni da Aysha tana fadin, ga matar Aliyu, ga Kuma d'anshi sun iso.
Cike da farin ciki suka amsa d'an yayin da kowa ke tofa albarkacin bakin shi, yaron yayi kama da Aliyu sannan suka koma kan Aysha, nan ma ca suka mata yayin da da yawan su suke fadin Masha Allah yariyar son kowa, abokan wasa kuwa suka shiga janta sai dai Aysha ta kasa sukuni, kauna suka nuna mata sosai kamar zasu lashe ta yayin da wasu daga cikin su suke fadin, " su Aliyu suke Nima suci kaniyar sa dayai aure har matar ta haihu be gayawa kowa ba sai kace muna makiyan sa.
Hakuri aunty taita basu, cikin raha da wasa da dariya ganin dare nayi aunty ta masu sallama suka fito.
Har motar aka masu rakiya daker suka bada Khalipa, bayan sun kamo hanya aunty ta kalli Aysha tace, Wannan hajiyar Itace maman Baffah kakar Aliyu kenan, sauran Kuma duk iya lanta ne, basu da matsala ki saki jikin ki dasu, Amman ki iya bakin ki, na kula basu San komai ba, hakan bakaramin dadi yamin ba, dan Allah kiyi wasa da dariya da kowa amman Banda sakin cikin ki.
Nagode aunty zan kiyaye.
Lokacin da suka Isa gidan Baffah kuwa kai tsaye cikin gidan ta nufa da ita, yayin da duk ta samesu duk afalon,.
Cikin mutunci nan ma aka taryesu, yayin da Baffah yai mata nasiha cikin hikima, Momy ce take ta dan dandaure fuska Islam da Meenat kuwa tuni suka koma kusa da Aysha suna janta da mgn saidai ta kasa sakewa sabo da Baffah.
Daga falon Baffah kuwa part din dasu Aysha da zasu zauna suka nufa, cikin rakiyar momy, dasu Meenat, wadan da farin cikin su yaki boyowa.
Sosai yanayin tsaren da akama wajen ya burgesu, kaya ne masu kyau da tsada aka zuba, daki biyu ne aguri sai madaidaicin falo.
Duk gidan suka leka saidai suna tura kofar dayan dakin suka hangi Aliyu aciki, Cikin sauri su Islam suka juya Momy ma joyowa tayi, aunty Ruqayya ce kawai ta shiga.
Momy kuwa tana fitowa falon tace dasu Meenat kuzo mu tafi.
Aysha kadai ta rage agurin, misalin 10 sannan aunty ta fito, au ke kadai ce, su Momy duk sun koma ne?
Amsa ta bata da eh, yayin da aunty tace ton Nima barin tafi dare nayi, Allah ya zaunar daku lafiya ya albarkanci rayuwar ku, Aliyu dake bayan Aisha ne yake amsawa da Ameen, har mota Aliyu ya raka Aysha yayin da Aliyu ya nufi cikin gidan su, Baffah zaune kadai afalon dan haka ya tsuguna agaban Baffah bayan ya gaishe shi yace, " Baffah nazo ne in Kara baka hakuri dan Allah kayi hakuri ka gafarceni.
Dagowa Baffah yayi ciki da fushi yace, " nace ma wani abu ne?, Konama baki ne??
A'a Baffah, nidai nasan kana fushi Dani ne.
Toh Ina zuwa Aliyu, barin tambaye ka, zakaji dadi danka da kake tsananin so kake jansa ajikin ka yai maka abun da kamin?
A'a Baffah bazanji dadiba,Kuma bazan soba Baffah, nasan ban kautaba shiyasa nake baka hakuri, wlh Baffah tsintan kaina kawai nayi acikin matsalar.
Shikenan, kaje kawai dare yayi, kabar yariya ita daya, agurin da bata saba ba, ni ban rike ka arai ba, amman abun na bani takaici, sharadi daya ne zan gaya maka, tunda ka raba yariya da iyayenta karka wulakanta ta, nagaya ma Rukayya ma, banson ka wulakanta yariyar nan, ko kace zaka juya mata baya, kasa aranka amanar ta nabaka.
Insha Allahu Baffah zan kiyaye.
Mikewa Baffah yayi yana fadin Ina zuwa.
Dakin sa ya shiga sa nnan ya fito ya dawo ya zauna tare da mikewa Aliyu wata leda yace, " wannan kabawa matarka Babanta yabani in saya mata kaya, dan haka ka danka mata ahannun ta.
Zuciyar Aliyu fari Kar ya karba yayi godiya sannan ya koma part dinsa ya samu Aysha zaune cikin yanayin tagumi.
Kafar ya kulle sannan ya dawo kusa da ita ya zauna, cikin fara'a yace Yaya dai.
Kawar da kanta tayi cikin wani irin yanayi daya bijiroma ta, bada jimawa ba.
Aysha meyasa na ganki wani iri?
Fashewa tayi da kuka ya Aliyu Ina tunanin Mamana sosai.
Kiyi hakuri komai zai wuce, yau ranar farin ciki ne agare mu, idan zuciyan su yayi sanyi zan kaiki ki basu hakuri.
Hawayen ya share mata sannan ya karbe Khalipa dake hannunta yace, " tashi muje d'aki"
Mekewa tayi har yanxun tana cike da zullumi da tunani.
Gadon yara dage gefen gadon sa ya Isa ya saka shi tare da tofa masa addu'a tsayon lokaci ya dauka yana kallon sa sannan ya waigo ya kalli Aysha da har yanxun take kwalkwal da ido
Kallonta yayi yai murmushi sannan ya nufi toilet, alwala yayi ya fito, tsaye yayi gaban Aysha yana fadin, abar tunanin haka kije kiyo alwala.
Mikewa tayi babu musu, Koda ta fito har ya hau kan sallaya, nuni yai mata data matso sunyi sallan a hankali ta karasa, sai dai duk jikinta a sanyaye yake.
Bayan su idar ya kama kan Aysha yayi addu'a sannan ya sauke hannun sa yana fadin Allah ya kade fitina a tsakanin mu yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Idon Aysha cike da hawaye tace Ameen.
Kallonta yayi yaga duk inda jikinta yayi sanyi yace, " Allah ya sanyayawa Mama zuciyarta, ya kuma sa ta fahimci wannan al'amarin kaddara ce bayin kanmu bane......
Cikin sauri tace Ameen Yaya Aliyu, 😭 hawayen da take makalewa ne suka zobo yayin da take fadin, " abun na damuna yaya Aliyu sosai.
Jikin sa ya jawota ya rungume, yana fadin, " kibar sa abun azuciyar ki yana damun ki, wannan rayuwar ba mutum bane yake tsarawa kansa, wlh Aysha Ina kyamar zinah tun Ina karatu, nasamu damar da zan iyayi amman sabo da nasan haramun ne banta ba ko da wasa. dan haka da abun ya sameni na dauke shi kadara tace, nasani akwai damuwa akwai kunya, duk naji su, amman dole na dake, dan haka kema ki dake ki maida komai ba komai ba mu rungume kaddarar mu, Kuma Ina ganin nan gaba kadan komai zai wuce insha Allahu.
Ya Aliyu, bana tunani komai zai wuce, yayyen Mamah suince sun cireni acikin su, sunce basu bani inaji ajiki kamar indai Umma na raye mmn Sadam na raye bazasu sake bari na taka cikin gidan nan ba bare ma har Naga mama.
A hankali yake shafa bayanta, yana sauke ajiyan zuciya tsayon lokaci sannan yace, " muje mu kwanta., Ki Kuma bar irin wannan tunanin, asalima bana son kina Kira min sunan Umma ko mmn Sadam anan, ni babu ruwana dasu, kema Kuma Ina son kibar sasu cikin lissafin ki.
Dagata yayi yana rike da hannunta suka Isa bakin gadon, sakin hannunta yayi sannan ya rage kayan dake jikin sa, juyowa yayi ya kalli Aysha data hada kanta da guiwa yace"
Kigan bana son haka fah, tashi ki rage kaya kizo ki kwanta dare nayi.
Mikewa tayi kamar yadda yace, " cikin hikima ta shirya sannan ta koma can gefe ta kwanta, tare da mike hannunta ta rike gadon da Khalipa yake kai.
Kallonta yayi yai murmushi har cikin zuciyarsa yakejin tausayin ta, gasu kwance inuwa daya amman zuciya ta rasa nutsuwa, yana kwatanta yadda takeji cikin ransa, saidai yasan dole ne su jurema hakan, har zuwa lokacin da abun zai lafa, dan haka ya fara matsawa gareta ahankali har ya Isa ya rungumeta, lumshe ido yayi yana mejin dumin jikinta tsayon lokaci, ahankali ya fara sarrafa hannun sa jikinta cikin kwanciyar hankali.
Aysha bata yi yin kuren hanawa ko gardama ba, saidai har yanzun mamanta ne cikin zuciyarta dan haka ta kasa nutsuwa.
Ahankali yace, " Aysha menene haka?, Na rakokeki dan Allah ki dawo da hankalin ki nan, dan Allah koma me ke damun ki kicire shi cikin ranki ki ajeshi gefe.
Jin haka tayi kokarin bashi hankalin kamar yadda ya bukata, yayin data lura ya shiga cikin wani yanayi domin zuwa wannan lokacin jikin sa har wani rawa yake yi, hadin kai ta bashi suka shiga faranta ran juna, Aliyu daya susuce gaba daya yayin da yai wurgi da rigar sa kasa ya fara zame kayan Aysha.
Adaidai wannan lokacin Khalipa ya farka cikin wani irin tsandara uhu, lumshe ido Aliyu yayi tare da fadin, Subuhanallahi kashhhhh ahankali kamar me rad'a
Cikin sauri ya sauka yayin da ya nufi toilet, sannan ya dawo ya dauki rigar sa ya sanya, gurin gadon Khalipa ya nufa ya daukeshi sannan ya dawo bakin gadon yana fadin, ki tashi mana.
Toilet din ta nufa, itama sannan ta fito tazo ta zauna gefen Aliyu cikin sauri da karfi yaron tana fadin toh ya Isa, shiko Khalipa ne rufe bakin ba har saida ya runtasa nonon sannan ya kama mamula babu kama hannun yaro, da ido Aliyu yabishi tare da fadin lallai ma yaron nan, kallon Ayaha yayi yana fadin yanzun Kuma har minti nawa zai dauka yana sha??
Awa biyu ne zuwa uku, tabashi amsa tana Satan kalon shi, yayin da ya tabe baki yace, lallai, gadon ya kwanta ya daura sandar hannun sa kan fuskar sa.
Satan kallon sa tayi, sannan ta d'anyi dariya har ya fitar da sauti.
Yaya dai?, Aliyu ya fada cikin tsareta da ido
Babu. Aysha ta bashi amsa.
Akwai, naga kina min dariya ne.
Ba dakai nake ba.
A'a, dani kike, kuma nasan ne kike ma dariya.
Toh meye?
Kina min dariya ne saboda Khalipa ya tashi.
Dariya Aysha tayi wadda har tasa Aliyu ya dara yana fadin, " zan kamaki Aysha yau dinan basai gobe ba"
Dariya ta sake yi, idan Khalipa ya yadda ba.
Zaima yadda Bari ki gani, Kuma daga yau hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu.
Kana nufin bazai sake farkawa ba da daddare?
Eh.
Cikin dariya tace, " maganin bacci zaka bashi ne?
A'a amman bazai sake shiga hakkina ba.
Rufe ido Aliyu yayi be sake cewa komai ba, tsayon awa daya Khalipa ya dauka sannan ya koma bacci, mikewa tayi ta kwantar dashi sannan tahau gadon, ahankali ta kwanta sai dai tana numfasawa taji saukan hannun sa jikinta.
Yaya Aliyu bakayi bacci ba.
Waya gaya miki sabon ango na bacci, bayan yana son ya amsa hakkin sa.
Lumshe ido tayi tana fadin, " nafa gaji ya Aliyu.
Dan Allah fa?, Khalipa ne ya gajiyar dake da tsotso ko?
Kanta ta daga.
Toh bari in sauke miki nawa sai kiyi baccin gajiya gaba daya.
Ni a'a Yaya Aliyu kabari sai gobe.
Aysha bazan iya ba, tsoron me kike?
Zafi ya Aliyu.
Kokarin cire kayan jikinta yake yana fadin bari bazai miki zafi ba wannan karon
Yana kokarin kai hannun sa jikinta Khalipa ya sake farkawa, wannan karon ma cikin kuka sosai, Hannu Aliyu yasa ya dafe kansa tare da sake fadin kashhhhh