Free chapter · Read without an account
CHAPTER 17( WHY DOES IT HURT)
WANI RABON.........🦋🦋🦋
Elegant Online Writers ( E.O.W)
Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)
In dedication to all single ladies out there........
Arewabooks @ deejasmah
WhatsApp @***
N.B WhatsApp only not call😁
CHAPTER 17 ( WHY DOES IT HURTS........?)
Dear Ummkulsum Arabiy you have been supportive throughout the course of writing WANI RABON.........by sharing which helps the book to reach audience more than i ever imagine jazakillah for everything dear Allah ya bar zumunci this chapter is wholely yours enjoy it❤
Grill🔐❤
Do everything with a good heart and expect nothing in return and you will never be disappointed.🌹
Tun daga randa na bashi hak'uri komai ya fara daidaita tsakaninmu ya kuma rage yi min tsawa ko masifa saidai kunsan mai hali dai bai tab'a canjawa a rayuwa saidai ba kaman da ba kusan yanzu shi yake kaini gida in zan wuce wani lokacin ma shi yake cewa in jira shi mu tafi tare ban wani damuwa akan hakan tunda nasan dai shi baida wani intention akaina domin har in sauka daga motar magana d'aid'aiku ne take shiga tsakaninmu
Fav da shegen iyayi saida ya tabbatar yasan waye ke kawoni gida don kusan duk randa ya ajiye ni sai ya taho wurin motar ban bari su gaisa nake jan hannunshi mu tafi don na lura baison hakan moreover babu wata alak'a a tsakaninmu dashi so banga amfanin nuna shi ga 'yan gidanmu ba
Yau kam da ya kawoni locking motar yayi ba tare sani na ba saida na fara kiciniyar bud'e motar ne naga ya bini da wani irin kallo turo baki nayi kafin ince wani abu har Fav ya iso bakin motar baiyi knocking ba saidai yana tsaye a wurin idonshi akan motar kallonshi nayi yayinda shikuma yaiwa Fadeel hon alamun ya zagayo cikin nutsuwa ya zagayo whining glass d'inshi yayi a dai-dai isowar shi
Da murmushi a fuskar shi yace " hii guy " washe hak'wara yayi yana mai kallon fuskar shi kafin ya maido idonshi kaina hararar shi nayi ina kauda kaina gefe " Good Evening sir " ya furta cikeda girmamawa gyad'a kai yayi yana cewa " evening.....ya kake? Ya karatu ?" Alhamdulillah ya furta yana mai kallona
Kallona Arshad d'in yayi tareda cewa " Malama ki daina hararar shi " sake kawar da fuska nayi ba tareda na kalle su ko ce musu uffan ba "my friend I'm Arshad Bello Matawalle" yana maida akalar maganar shi kan Fadeel tareda extending hannunshi don su gaisa mik'o mai hannun yayi shima a hankali yace " Fadeel Abubakar Sadauki but they call me fav " murmushi yai ya rik'e hannun ganin sun fara fira sun manta dani ne yasa na bud'e motar and luckily ya cire lock d'in fita nayi na d'auki jaka ta nai cikin gida
Arshad's POV
Ganin farko da nai mata zuciyata ta buga da k'arfi ban tab'a jin abunda nake ji akanta da wata mace ba when she talked kuma her voice got registered directly to my mind har banso ta gama maganaba sanda ko ta fara min bayanin reports d'in kuwa ban iya gane komai ba hakan yasa nace mata ta bar su I'll go through it anjima
A tunanina ko rashin sabo ne amma kuma kullum abun sake zama sabo yakeyi ban tab'a damuwa akan hakan ba sai randa na shiga office d'in nata da niyyar sanar da ita ta fito mu tafi zuwa meeting d'in da na tura Mukhtar ya sanar mata wanda nai mummunar ganin da ban fatan abunda naji in sake jinshi har abada
Akan hannunsu da yake sark'e da na juna idanuwa na ya sauka wani irin fad'uwar gaba ne ya sameni yayinda nakejin kamar in shiga ciki in cisge hannun nashi daga jikinshi marin da tai masa kuma ya k'ara min k'unci a zuciyata domin ji nayi kamar in b'alla nata hannun how dare she let him feel the softness of her hand a face d'in shi why didn't she just warned him bayan ta k'wace hannun nata amma ta d'auki precious hand d'inta ta d'aura a shegiyar face d'inshi a sanyaye na sanar da ita cewa ta shirya muna da meeting shi kuma ya biyo ni
Na kasa zaune na kasa tsaye shigowa yayi ya sameni na bawa k'ofar baya tsayawa yai a bayana cikin sanyi yace " emmmm.....here I am boss" cikeda masifa na fara cewa " ai na ganka ko?.......Mukhtar this is stupid of you.....taya zaka shiga wajenta har ka rik'e mata hannu.....tayi maka kalar 'yanmatan da ake shashanci dasu ne ko yaya ?"
D'agowa yayi ya kalleni cikin k'asa da murya yace " nima ba ina nufinta da shashanci bane sir......I really love her but tak'i ta yarda da hakan!" Kamar saukar guduma haka naji zancen nashi yanzu kam na tantance abunda nakeji akan Mukhtar wato KISHI!! kuma mai matuk'ar tsanani da zafi duk yanda naso in danne kasawa nayi don haka nace " then stay away from her !! " cikin mamaki yace " but sir....." Katse shi nayi tareda cewa " you've heard me quite well stay the f**k away from her!!!"
"OK sir I'll try to " ya furta cikin rawar jiki don muryar tashi tayi mugun razana shi bai tab'a jin voice d'in daga gareni ba k'ofa ya nufa yana cewa "have a nice day" lumshe ido nayi ina jefan shi da mugun kallo don nafi kowa sanin cewa he ain't a nice guy kuma bazan yarda ko da wasa ya shiga rayuwar Faheemah ba ko da ita d'in secretary ta ce(......... ko ba secretary ba 🙄?)
Shigowarta ne ta k'ara min zafi don nunawa tayi she can fight on her own kuma she misunderstand me as someone da yake wulak'antarwa ga martaba da 'yancin mata hakan yasa itama na sallame ta kuma ba tareda damuwa da hakan ba ta nufi k'ofa ta barni nan zaune kasa aikin komai nayi a ranar tsaki kam nayi yafi cikin carbi ganin cewa bazai fisshe ni bane yasa nai watsi da tunanin nasu ta hanyar tilastawa kaina aikin dole
A daren ranar kuwa bacci b'arawo ne ya saceni domin zafin ne ya taru ya dawo min a zuciyata yayinda hoton hannunsu kuma yake ta replaying a idanuna juyi nake tayi hakan ya haddasa min ciwon kai mai tsanani ban runtsa ba sai gab da subhi hakan yasa the next morning na tashi da mugun jin haushinta da ma kaina like why do I care that much me yasa tunaninta ya sark'afe min zuciya ne ko da naje office nunawa tayi like I don't exist
Hakan ya tab'a pride d'ina cos yanda mata kullum suke mutuwa akaina amma ita a wurinta I don't matters at all hakan ya ninka haushinta a raina yayinda a can k'asa kuwa I'm feeling something strong for her wanda ba zan iya explaining wa kowa har ya fahimce ni ba
A cikin kwanakin nan na rasa what's wrong with me tunaninta baya barin min kaina gashi kuma na k'i mata magana which is so killing me inside duk tsawar da nake mata bata ko kallona har in gama masifata gajiya nake da ganinta in koreta daga office d'ina
Tun d'azu nake juya teaspoon a cikin coffee'n da aka kawo min na kasa ko sha Ammah da tun d'azu take tsaye ne ta tab'a ni ajiyar zuciya na sauke ina d'ago kaina zama tayi a kujerar dake gefena tace " what is it.....me yake damun zuciyar jarumin d'ana ne har hakan ?" girgiza kaina nayi nace " Babu komai Ammah it is just stress shiyasa ma zan sha coffee nasan zai sauka in shaa Allah "
Murmushi tayi tareda cewa " this is not stress my dear, I've been noticing you kafi sati a haka what's wrong ?" "FAHEEMAH CE!!..."naji bakina ya furta ba tareda na shiryawa hakan ba kallonta nayi ina mai dafe bakina cikeda kunyar abinda na fad'a " Faheemah.....who's that?....sirikata?" duk'ar da kaina nayi Ina cewa " Nope......ni ba budurwa ta bace she's just my secretary " (keep deceiving yourself yaro 😒)
Murmushin manya tayi " amma shine kuma damuwarta take damunka.....OK then what's about her ?" A hankali na fara fad'a mata abunda nakeji akanta d'in don ni ban yarda cewa wai sonta nakeyi ba kawai dai I like her personality ( kaji d'an k'walllll........ba zaaji a bakina ba😅😷) shiru tayi tana mai nazarin fuska na da kalamai na kafin ta nisa tana cewa " you are so jealous a kanta.....kana son jin muryata.....kana damuwa saboda ita d'in bata damu dakai ba.....yet you want her to be noticing you amma kuma kai ba sonta kake yiba....you just like her personality.....wow just wow"
Shiru tayi sai kuma tace " ohkkk then let's do this.....tunda ba sonta kake ba.....ka rabu da ita mana.....why like something you don't love?......ka daina jin haushinta and stop being wanted to be noticed by her.....shikenan kaga sai ka huta" cikeda damuwar jin kalamanta nace " but Ammah I can't do that!!" girgiza kai tayi tareda cewa " then admit it.....tell her you love her there's nothing much there in kuma ka tsaya wasa a d'auke ta daga gareka don na tabbatar ita d'in abu ce mai matuk'ar tsada "
Kalamanta na kusa da k'arshe sun rusa min k'arfin gwuiwa ta wai a d'auke daga gareni ai duk wanda ya sake yai tunaninta ma bazan barshi ba balle har yai tunanin rabata dani kallonta nai da kyau nace " I can't just say I love her when I'm not even sure of what I'm feeling towards her " kallona tayi kafin tace "if you want to know your feelings toh zab'i d'aya ne gareka which is non-other than getting close to her....be friend her till when you are sure of your feelings" tsalle nayi ina rungumeta "yessss Ammah...yes" daga haka na juya na nufi k'ofa ina barinta da al'ajabi
Hakan yasa na had'ata da paperwork wai ko zata sakko saidai haka ta yiwo shi ta kawo min cikeda masifa na fara fad'a akan aikin da na batan dukda cewa I was impressed but she worsen the matter by walking out on me k'iris ya rage banyi kuka ba but Allah ya taimaka ta ban hak'uri shikenan kuma duk zafin da na d'auka ya tafi kamar ta sani a aljannah
Hakan yasa na fara getting too close to her na tsiri maidata gida though har mukai ban cika mata magana ba but having her by my side mean everything to me dukda ita na lura a takure take da hakan kusan kullum ina noticing yaron dake yawan dauk'ar mata jakarta from all indication bata son hakan saidai ba yanda zatayi da gayya yau nai locking d'inta tareda kiran yaron ya kuwa taho he's very respectful and I like him tun daga ganin farko unlocking motar nayi without her knowledge fita tayi da jakarta ta nufi gidan nasu da ido na bita ina mai jin wani irin shauk'i a k'asan raina
Cikeda nishad'i nake driving zuwa gida na yarda cewa love is the sweetest feeling ever yanzu da ba ma tare ji nake kamar in koma wurinta kamar nayi shekara bana tare da ita lumshe idanu nayi ina mai tuno kyawawan hazel eyes d'inta masu matuk'ar haske gefen da ta zauna shafa wurin nayi a hankali tare da cewa " Sweetest Apple "
Yau Friday cikeda nishad'i na tashi wanka nayi tareda yin dukkan aladun rayuwata na yau da kullum taje gashina nayi da saje na tareda shafa musu mai kallon madubi nayi ina murmushi closet na nufa setin kaya na zurawa ido ina tunanin kayan sawa gefen kaftans na nufa ina zaro wani filtex mai taushi Navy blue inner wears na zura tareda d'aura kayan kallon mirror nayi ina murza hula Dara maroon colour Navy blue Julio Caesar Italian leather shoes na zura wa k'afata wristwatch na companyn chopard na d'aura kafin na fesa turarukana jakata na d'auko da key ina nufar waje
Kasancewar Daddy da Mommy basa k'asar yasa na nufi part d'in Ammah ina baza k'amshi a dining na tarar da ita da yaran gidan su Zeezah,Seeyamah sai Maaruf da shirin fita school da murmushi a fuskarta tace " Jarumi da alamu an dace " nuna yaran nai da ido ina murmushi gaishe ta nayi ina zama suma gaishe ni sukayi na amsa cikeda kulawa tareda tambayar su ko suna da matsala amsa min sukayi cewa komai lafiya daga haka kuma ban sake magana ba tea kawai na sha na mik'e tareda nufar k'ofa bayan na ajiye musu kud'i ina jin suna godiya
Na hawo floor d'in cikeda k'warin gwuiwa haka nan naji I want her to see me office d'inta nai knocking amsawa tayi na b'ude k'ofar a zaune take sanye da Atamfa peach da coffee brown sai touches na cream a ciki d'inkin A line ne sai Chantilly veil da ta yafa a kanta ta kafa d'aurin nan a gaban goshi kafewa nayi na kasa shiga ciki hakan yasa ta d'ago kanta tana kallona zura min ido tayi hakan ba k'aramin sanya min farin ciki yayi ba wato she notice me
K'arasowa nai cikeda murmushin ina wara idanuna a kanta " like what you see?..." Na fad'a ina kashe mata idanu kawar da kanta tayi tace " Whatttt!?" Tana dariya raina ya b'aci da maganar ta saidai na daure nace " yeah admit it hajiya..... I look good...nay I'm handsome" tab'e baki tayi tace " and so.......?" kawar da kai nayi ina jin kamar in mata kuka " Never mind" na fad'a tareda dosar k'ofa yayinda k'unci ya cika min zuciya can't believe i look this good for this girl only for her to do this to me tabbas inda ina da saurin kuka da yau sai nayi kuka zama nayi a kujera ina jinjina masu cewa love is sweet bayan ni d'acin ta kawai na sani ba dad'inta ba
As usual at about 30 mins bayan shigowata sai gata nan d'auke da files a hannu " Good morning Sir" morning nace ina kauda kaina gefe " Sir you really look good today,u have no idea yanda kaftan suke maka kyau wlh " ta fad'a da murmushi " this girl will surely be the end of me ! So take ta maidani kamar mahaukaci " ajiyar zuciya na sauke don naji dad'i though ban jishi at the right time da naso ba but I can tell she's saying nothing but truth so I do appreciate that murmushi nai mata ina bud'e files d'in da ta ajiye min bayanai tayi min tareda fita ido na rakata dashi a k'asan raina nace" kin kusa zuwa hannu babe.....and I'm not letting you go if you do.......
Awnnnnn..........su Arshad an fara amsa Faheemah ta ciri tuta muje zuwa dai.........
#vote
#comment
#share
#add
Love y'all😍
Deejasmah🦋🔐❤