Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA BIYU

by Hassana Suleiman · YARDA CE SILA

YARDA CE SILA.

Sanah S Matazu.


BABI NA GOMA SHA SHA BIYU.

1⃣2⃣

Lokacin da Saif ya ajiye waya dafe kai ya yi yana tunani, tabbas ya san ya ɓatawa mahaifansa rai da yawa amma suna kawaici sai dai a wannan yanayin da ya ji mahaifinsa ya ɗaga masa hankali. Ko babu wasa cikin lafazinsa da duk ƙarfinsa ya ke maganar da alamu ransa a ɓace ya ke matuƙa. Babbar damuwarsa furucin Mommynsa kansa ya ji ya yi nauyi ya dinga _(tray)_ maimaita kiran wayarta a kashe ta _Colenel_ Kanal kuma ya ki ɗagawa haka ta su Mima duka a kashe takaici ya kashe shi haka ya zauna jigum. Washegari sukuku ya tashi hata Tina kasa fuskantar shi ta yi har gara a office Angeli ta ɗebe masa kewa ita ma bai wani jima ba ya tureta ya miƙe yana tsaki duk duniyar ji yake ta yi masa zafi.


***

MAIDUGURI

Tun a washegarin al'ammarin iyalan Kanal su ka ta shi a baƙon yanayi musamman rashin wayoyinsu kowa ya tambayi Mommy amsar ɗaya ce Daddynku babu wadda ke ƙara magana, Mimi ce ta samu Mommy a ɗaki tana tambayarta abin da ya faru ba ta yi la akari da 'yar za ta iya jin zafin uban ba ta kwashe komai ta faɗa mata KUSKURAN WAƊAN SU MATAN ke nan wurin bayyana sirrin zamatakewarsu ai duk yayin da ɗa ya ɗarsa uba ko uwa na cutar ɗayansu an sami raunin tarbiya da taɓarɓarewar zamantakewa. 

Ai kuwa ta shaƙa iya shaka ta. Ta ɗauki tsanar duniya ta ɗorawa Shukuriyya tun kan ta ganta, ba ta ƙara tsanarta ba ma sai da yamma yan class ɗin su su ka zo mata da korafin anyi (test) ba ta nan rashin waya kuma ya hana tasan da afkuwar hakan. An kirata a kashe. 


***

Saif ya kasa nutsuwa gaba ɗaya musamman samun wayoyin ahalinsa a kashe, ga shi in ya kira Kanal ba ya ɗauka hakan ya sa ya soma shirya-shiryan baro ƙasar ba ƙaramar damuwa Angelena da Tina su ka shiga ba da kyar yana lallashinsu yana komai ya haɗo kayansa tare da ɗaukan _(excouse)_ uzuri a wurin aiki. 


KOWA YA BAR GIDA...

Ƙarfe goma na safiya jrgin sama ƙirar kamfani *Fikra airline" a sauka fillin jirgin Maiduguri _Internation Airport_ a hankali mazauna jirgin suke fitowa cikin nutsuwa can sai gashi ya fito ya haɗe cikin suit baƙaƙƙe ya rufe idanunsa da ma adanar ɓoye idanu daga nesa in ka hangobshi zam bature amma daya matso kusa da kai za ka kirashi da cikakken Kanuri a tsaye ya ke ƙyam yana da faɗin ƙirji da murɗaɗun damatsa sak! Ƙirar zaki. 

 Sassanyar iska ya shaƙa ya lumshe idanunsa farare da ratsin ja kaɗan ƙwayar baƙa siɗik da ita da galgasa masu tsayi zara-zara, ya dinga mamaki tare da jin wata irin kewa na ɗibansa tabbas duk wanda ya bar gida-gida ya bar shi. 

 Kai tsaye ya sami abun hawa ya tara ya sanar da shi inda zai kai shi tsaki ya fara ja ganin yadda duk garin nasu ya hargitse a zuciyarsa yana ai yana ban da furucin Daddy mai zai hana shi dawowa (Nigeria). Har su ka iso bai dawo duniyar tunanin da ya lulaba sai da ya yi masa magana ya yu firgigit ya dawo daga tunanin yana dubansa. 

 "Mun zo."

 "Ok!"

Ya furta ta re da ba shi gudar naira dubu ɗaya ya wuce abinsa, duk da an sauyawa barikin tsari hakan bai hana shi gane arearsu ba sai da ya nuna _(identity card)_ katin shaidar ɗan ƙasa su ka barshi ya wuce, ya dinga dariya ƙasarsa ta fara samun tsari mai kyau. Sai da ya yi tambaya sannan ya samu gane gidan ya kutsa kai kansa tsaye.


Da sallama ya shiga gidan gaba ɗaya suna zaune a fallon duk da ba wani daɗin yanayin suke ji ba, gaba ɗaya yaran su ka miƙe kamar an yi fasta haka su ka ƙaƙƙame cike da mamaki suna kallonsa Kanal kuwa tasbihi kawa ya ke ga ubangiji wasu kurtayene su ka dinga shigo da jakunkunan kayansa kimanin guda shida manya. 

 Da gudu su ka ƙarasa su ka rungume shi Falmata ta yi sakaro tana dubansa tana ayyana ko dai wannan ne Saif ɗin? Ai kuwa idan shi ne ita kuwa ta yi babban kamu lokaci ɗaya wani irin nishaɗi ya sauka a ƙirjinta ta samu kanta da sakin murmushi mara tushe. Cike da ƙauna ya ke shafa kansu yana faɗin _(miss you)_ naɓyi kewarku Kanal kuwa yana gefe ya harɗe hannayansa a ƙirji yana satar kallon Mommy da ke murmushin ganin gudan jinninta ta kasa komai cike da nutsuwa Saif ya ƙaraso ya zube gabansa tare da rike kafaffunsa,

"Daddy ku ya femini."

Mommy ta ji daɗin hakan amma da ta tuna abin da ya yi silar dawowarsa wani ƙuncibne ya mammaye ma ta zuciya da sauri ta yi sashinta tana matsar ƙwala. Duk su ka yi saroro Kanal ya sunkuya ya ɗago shi zuciyarsa fall farin ciki wani sashin kuma na tuna masa bai kyautawa Hauwa ba ba ta cancanci haka ba za ta ga kama yana nuna mata iko ne akan abin da in ma iko ne ya ci ace ta fishi iko da shi cikin dabara ya maida ƙwallar da ta tarar masa yana bubbuga bayan Saif,

"Ka wanke kanka Saifullah amma ka je ka ba wa Mommyn ka haƙuri ka ga ta yi fushi."

Daga haka ya zare jikinsa ya nufi sashinsa kansa na tsananin ciwo zuciyarsa fal damuwa ko da wasa baya san ganin Hauwa u cikin damuwa amma ya ya zai yi? Shukuriyya tamkar wata amana ce haka ya ke kallonta a cikin r rayuwarsa idanunsa na masa gizo zuciyarsa na yi masa wani hasashe amma ya ƙasa tantance gaskiyar lamarin.


Kwanan Saif uku da dawowa ya samu ya daidaita da mahaifansa suna walwala da komai amma kannansa sun fara shiga taskunsa saboda akidarsa ta kyara da tsangwama in dai bashi yaso wasa dasu ba to babu hakan tsakaninsu ba kamar Falmata da ya ɗorawa ƙin jini musamman da ya ji ita ɗin YAR GUDUN HIJIRA CE ga kuma wata da Daddy ke son jajjuɓo masu hadda tsayawar shari a lamarin ya ɗaga masa hankali ita ɗin ya rasa wacece? Wana matsayi ta taka wurin mahaifinsa. Da fari ya ɗauka ita zai tsayawa kan lamarun daga bisani Mimi ta bayyana masa komai ya yi mamaki kwarai sai lokacin ya ɗan rage kyarar da yake mata saboda yana hangen wani feeling cikin idanunta kuma ya hangi akwai mamora tare da ita.


  A ɓangare guda kuma Mommy ta tatara lamarin Kanal ta watsar gaba ɗaya ta yaranta take ko shigowa ya yi suna hira za ta miƙe tabar wurin. Mimmah ta fi kowa baƙin cikin abinda Mommy take amma ta lura Saif da Mimi ke tunzurata shi ma sai ya tattara ya watsar da su ya cigaba da shirye-shiryansa a cikin sirri ya shirya komai har Kano ya je ya dawo ya samu zantawa da Ahmad ba tare da kowa ya sani ba ana saura kwana shida komawarsu Shukuriyya kotu ya samu kira daga Ahmad da bayanin komai. 

 Ya ji daɗi sosai dan haka bai jinkirta ba ya shirya musu tafiya shi da Falmata da Saif ba tare da sanin Mommy ba saboda tama ki sauraransa bale ta baɓshi fuska su tattauna muhimman abubuwa shi kansa Saif sai ranar tafiyar da asuba ya sani hakan ya sa ya hau shiri gadan-gadan gudun ɓacin ran Kanal ɗin da safe kawai sai ta shi mutan gidan su ka yi su ka samebsu cikin shirin tafiya kasa jura ta yi ta hau tambaya,

"Kanal ina zabku kuma kai da Saif...?"

Kafin ta rufe baki Falmata ta fito cikin lafaya _(Sky blue)_ kalar sararrin samaniya abinka da farar mace ta yi kyau sosai. Hoda ta shafa ta kawo kwali ta tisa biy-biyunta tar ya fito ta hade gashin kanta ta saka barimar hanci _(dark blue)_. Sak! Kanuri, wasu turarruka ta dinga bin jikinta dabsu masu matuƙar ƙamshi ta fito kwas da ita Saif ya dinga satar kallonta yana haɗiyar yawu kamar maye. Ta fito bayan ta yane jikinta da lafayarta sai da gabanta ya faɗi zahiri yarinyar ta yi mata kyau kai tsaye ya ba ta amsa cikin taushin murya,

"Kano!"

Yanayin da ya ba ta amsa ya karya guiwarta ganin ba bu annuri kan fuskarsa ya sa ba ta sa ke tankawa ba, yaransa ya dinga bi yana tambaya duk mai buƙata ya sauke masa ita sannan su ka yi sallama su ka tafi zuciyarsa babu daɗi ya tafi ya barta ya amince Hauwa farin cikinsa ce.

 Bayan fitarsu ne ta faɗan gidan Maman Safiyya da kukanta. Hankalinta ya tashi ta dinga mamaki yar lelen Kanal guda na zubda hawaye abinda ta daɗe tana burin gani sai yau? Ji take kamar ta zuba zuwa a ƙasa tabsha cike da kulawa take tambayarta babu musu ta bayyana mata komai abinda ya ke faruwa, jim ta yi tana wani tunani a ranta daga bisani ta tanka.

"Na ji ba bu daɗi Maman Saif amma fa na fi ganin laifinki ya ya ya za ki bari Kanal ya raina ki bayan ke kika yi masa komai a rayuwa? Ya manta sanda ya ke wahalniyya waya ɗaga darajarsa duk bariki idan ba ke ba shi ne zai saka miki da wannan? Kai namiji ma a barshi."

"A'a Maman Safiyya wannan tsakaninmu ne, duk abinda na yi masa YARDA CE SILA kuma bai kamata ya zamo abin gori da tashin-tashina ba don mu samu matsala kawai na zo ne ki ba ni shawara ya zanyi?"

A ranta ta ji haushin furucinta so ta yi ta ɗorata ta ɗoru amma taki bada kai bori ya hau numfasawa ta yi,

"Shawara ɗaya ce duk yadda za ki bayan ya gama tsayawa yarinyar karki yadda a ajiye miki ita a gida wallahi domin na lura wannan yarinyar Falmata ba ta gaban Kanal kawai tausayinta ya sa ya kawo miki ita amma wacan na tabbatar za ki ji zuwan da dawowar duk a gama nasan ke zai kawowa ita saboda YARDA CE jigon zamanku ya amince za ki amsheta tunda ya yarjewa hakan ya sa lagonki ya san yadda yake sarrafaki ya sha kanki ki bishi a hakan ku zauna cikin YARDA amma sai kisan yadda za ki amfani da YARDA ya amince cewar ba za ki zallunceta ba sai musan shirin da zamu yi a kanta."

"Tabbas Maman Safiyya na gode sosai, Allah kawo bazawari na gari."

"Amin ke dai ni har yanzu na rasa na kamawa wallahi."

"Sai addu'a ai lamarin "

Da haka su ka ƴlyi sallama ta koma sashinsu.bMaman Safiyya ƙawar Mommy ce, tun zuwanbsu barikin ba ta da kawa sama da ita. Asalinta yar garin garin Emo ce ita ɗin Bendal ce. Ko ɗaya ba ta da kirki mace ce mai ƙyashi da hassada. Gata da mugunta ba ta son tabga wani ya ci gaba musamman wanda ya zo a bayanta a fuska tana da faram-faram a zuci kuwa halinta sai ubangijinta. Mijinta tsohon soja ne ya daɗe da rasuwa da daɗewa, yaransu uku da shi Safiyya ce babba ta rasu sai biyu masu shekaru goma sha huɗu duk maza. Duk wata shawara da ita Mommy take yi babu abinda ba ta sani ba na tarihin rayuwarta da Kanal hadda labarin auransu da gwagwarmayar rayuwar da su ka fuskanta.

***

Washegari Kanal ya ɗauki Falmata zuwa ainihin sansannin da su ka fara zama, an samu wasu tsiraru cikin 'yan gudun hijirar da su ka zauna tare cikin hikima Kanal da Saif su ka dinga yi musu tambayoyi kan rayuwarsu har su ka gangaro kan maƙasudin zuwansu ta samu kyakkyawar shaida. Ya tausayawa rayuwar da suke sai dai sun iske da dama gwamnati na tallafawa wasu cikinsu. Wasu ma sunyi aure. Abin gwanin tausayi daga bisani ya yi musu alkhairi mai yawa musamman marasa lafiyarsu ya kaisu asibiti marasa abinci kuma ya ba su kuɗi. 

 Ya zanta da dama daga cikinsu ya ji ra'ayoyinsu masu buƙatar komawa Jiharsu ya yi musu alƙawarin komawa da su. A ranar kwana ya yi yana juyi da tunanin rayuwarsu. Washegari ne da safe su ka sake komawa yaji daɗin yadda su ka samesu babu taggayara kamar zuwansa na farko bayan ya gama duba su ne su ka ƙarasa wurin Lado ba nijare ba tare da bayyana Falmata a idonsa ba su ka sakayata cikin mota. 

 Sun yi masa tambayoyi da ɗan dama daga bisani su ka wuce sun sami ganawa da mutane da dama ɗaga nan su ka wuce gidansu Ahmad sun so su karɓi Nawaf amma ya kƙ amincewa sun jima tare daga bisani su ka fita zaga gari bayan Kanal ya yi wa mahaifiyar Ahmad alheri mai yawa su ka dinga yi masa godiya. Kai tsaye wucewa su ka yi manyan shagunan garin Kano aka yi wa ƴNawaf siyayya mai yawan gaske su ka maudashi wurin mahaifiyar Ahmad. 


Washegari su ka nutsa bincike ba su fita da Falmata ba da Ahmad su ka fita, sun sami muhimman bayanai kan waye Faisal a haka har su ka sami ganawa da yaronsa Anas bayan ya shaƙi manyan kyautuka ya zauna ya kwance musu waye Faisal da aihin halayyarsa har club-club ɗin da yake zuwa ya kaisu inda a asurce su ka sami tattaunawa da wata amintaciyar yarinyarsa. Ranar sun gaji sosaai don haka washegari ba su je ko ina ba su ka huta saboda jiki da jini ana saura kwana biyu su shiga shari'a ne su ka sami zuwa wurin Shukuriyya don ganawa da ita.

 

Tun daga sama har ƙasa Saif ya ke ƙare mata kallo shi kam bai ga abun tada jijjiyar wuya anan ba duk da yana da ra ayin auran mace jiri (ƙabilarsa) ya kuma lura ita ɗin cikakkariyar (jiri) ce ƙabilarsa ta haɗa komai da yake so amma tashi ɗaya ya ji ya yi mata wata muguwar tsana tsana tun daga zciyarsa har zuwa ƙwayar idanunsa ta gaza ɓoyuwa murya a kausashe ya dinga watsa mata tambayoyi waɗanda su ka da ce da waɗanda ba su da ce ba ban da idanun Ahmad dana Dattijon da ta kasa mancewa ta kuma hau tunanin mene ne hujjarsa ta zuwa taimakonta amsar da ta gagara samu ke nan don ba ta da wanda zai bayyana mata hakan da babu abun da zai hanata yin shakulatun ɓangaro da shi ba.

 Cike da mamaki take dubansu haka su ka gama su ka miƙe su ka barta daga ita sai Kanal sunyi shiru dukkansu ya kai mintuna goma yana yi mata nasiha mai ratsa jiki bai gushe ba har hawaye ya taru cikin idanunta kaunar Dattijon ta kwanta mata lokaci ɗaya mamaki ta ke dama akwai mutane irin Kanal a duniya mutum ne shi _self contained_ mai wada tar zuciya _(well dressed)_ mai kyakkyawar halayya gaɓshi kuma _(soft heated)_ mai tausayi. Tabbas da ace duk ma aikata haka su ke da saukin kai da ansami kyakkyawar alaka tsakanin ma aikaci da kuma ɗan ƙasa. Ta amince akwai ira-iran Ahmad a doron ƙasa.

 Haka su ka ƙarasa masauki Saif duk ya jigata sai tsaki ya ke a ɓoye yana yatsina fuska lokaci-lokaci yakan amsa kiran mahaifiyarsa dana su Mimi, Mimi ta fi kowa yi masa ƙorafi tana zuga shi duk yadda za ayi ya yi silar yankewa Shukuriyya hukunci kar a kwaso musu jaraba duk abunda suke bai san Kanal yana ji ba sai da ya gama amsa wayar ya juyo ƴya yi arba da shi ƙlokacin karfe takwas na dare duk sai ya dirirrice ya hau kame-kame. Murmushi kawai Kanal ya yi wanda ya kasance ɗabi'arsa ne kodayaushe.

Ya dafa kafaɗarsa ta re da bashi umarnin zama bayan ya zauna ya dubeshi ya kira sunansa,

"Saifullahi."

Ya amsa a sanyayye,

"Duk wata hallita da za ka gani a doran ƙasa to ubangiji yana da manufar hallitarta kuma badan baya santa ba ya ke iya jarrabtarta da duk wata nau in jarrabawa da ya so a kuma lokacin da ya so. Dan Adam hallita ce da babu kamarta a doran ƙasa kuma ubangiji yana fushi a taɓabmasa bayinsa. 

 Ina nusar da kai ka sani cewa duk abunda ka aikata wala a ɓoye ko arubuce ko a bayyane akwai ranar bayyanarsa a idanun alumma, ranar da wayau ko dabara ba za su ƙwace ka ba face kyakkyawan aikinka. YARDA CE SILA da ta sa na ɗauko ka matsayin ɗana na ɗoraka ka kula da shari ar Shukuriyya. Kasan ina da kuɗin da zan iya ɗaukar duk wani lauya da na so kuma ya tsaya mata koda ba ta da gaskiya tunda shari ar yanzu ta koma kuɗinka gaskiyar bale kai da kanka matsayinka na cikakken Barrister ka riga ka fahimci inda gaskiya ta ke magana ta ƙarshe ga Shukuriyya nan na YARDA da kai na baka amanarta ka tsaya mata ba wai buƙatar ka kareta na ke ba kawai kai amfani da gaskiyarta iyawarka ba ita na ke buƙata ba idan kuma ƙasan zalluntarta zaƙka yi tun wuri ka samar da ni in samu mai tsaya mata na barka lafiya ruwanka ne ka fitar da ita ko kuma ka dulmiyar da ita."

Tsam! Ya miƙe ya bar masa ɗakin ba tare da ya saurareshi tun daga ranar Kanal ya sauya tsari Saif bai sake ganinsa ba sai ana gobe za a shiga kotu da ƙyar ya su ya ba shi haƙuri ya yafe masa bayam ya kira Mimi ya yi mata tas! 


WATA SABUWA.

Tun zuwan Kanal na farko hankalin Ahmad ya tashi. Zahirin gaskiya yana jin wani abu game da Shukuriyya amma ya kasa tantance mene ne? Sai dai zuwan su na biyun nan da furucin Kanal na a ba shi Nawaf ya ɗaga masa hankali musamman daya ga Falmata wadda ya kasa raba ɗayan biyu ko 'yar uwar Shukuriyyar ce a yadda yake jin Shukuriyya na hirar Jiharta kodayaushe ya san babu makawa bin Kanal za ta yi. Babbar damuwarsa ina zai kai nauyin da ƙirjinsa wanda ke kan Shukuriyyan? Yayi nisa cikin tunanin mahaifiyarsa ta shigo sai da ta yi masa magana sama da uku sannan ya amasa tare da yin firgiggit.

"Lafiya Ahmad?"

"Lafiya lau Umma, kaina ne yake ciwo."

Jim ta yi daga bisani ta furta,

"Karfa ka ɓoyemini damuwarka"

Kansa a ƙasa ya na jin a duniya ba shi da kowa sama da ita dan haka idonsa jajjur ya runtse su duk da rashin hango tauraruwar nasara da yake cikin lamarin,

"Umma kina ganin idan aka zama shari'ar nan Shukura ta yi nasara Kanal zai bar mana ita?"

Tambayar ta ba ta dariya ta kuma kaɗa mata ciki tare da tsinka zuciya.

"Me kake nufi? Idan ya barta ka yi yaya da ita? Ai barazanar ma Dr da mahaifinsa ta isa ka yi tunanin koda sun barta ka ce a tafi da ita. Wai ma idan ta zauna me za ta yi maka?"

"Umma ina santa auranta zan yi!"

Ya faɗa da bugun zuciya kamar za ta yi tsale ta fito saboda kiɗima da damuwa. Ta dinga watsa masa kallo alallace kamar ta ga kashi,

"Lafiya Um...m..a?"

Ya samu kansa da rawar murya,

"Hmmm! Zaman ne naga babzai yiwu ba mai iyayi ya tarad da mai kinibibi ita fa kowace zabuwa da ka gani da zananta take tafe. Karma ka soma wallahi zanɓyi mugun saɓa maka ka rasa waza ka jinginamin a matsayin suruka sai 'YAR GUDUN HIJIRA?Ina Amakata karma ka soma..."

 Fu! Tabar masa ɗakin ya cije leɓe yana tuanin hallayar Mama wani lokacin yana mamaki rikiɗa take kamar hawainiya tafi kowa tausayin yarinyar amma kuma taƙi amincewa da kudurinsa. Baudaɗɗan hali ne da ita sosai ya tabbatar ya kwanto wutar rigima. Kwana ta yi tunani yana miƙawa Allah lamarin abu. Ilai kuwa da safe daya gaisheta a cuɗe ta amsa bako walwala har sakeal ja masa kunne take kan Shukuriyyar.

***

Washegari da safe tsakanin Kanal da Saif gaisuwa ce kaɗai ta haɗasu ya buɗe mota su ka shiga su ka ɗauki hanyar gidansu Ahmad don zuwa kotu. Ya lura sosai da rashin walwalar Ahmad harma mahaifiyarsa yana ta wasa da Nawaf yana son yaron sosai saboda bashi da ƙaramin yaro yanzu sai Aliyu Mommy Hauwa kuwa ta ce ta gama haihuwa aikinta ya isheta na hidimar kula da maigidanta. 

 Ya dinga mamaki yadda ta sakar musu fuska a jiya amma yau babu hakan bai ƙara mamaki ba sai suna gab da ƙarasawa kotun ya ji tana cewa Falmata ta wuce da Nawaf idan an tashi shari' a wai jiya kuka ya yi ta yi yana nemanta. Matar da su ka yi ta naci ta ba su yaro taƙi saboda sabon da su ka yi amma ita ke faɗar kuka ya ke? Jinjina kai kawai ya yi yana satar kallon Ahmad da ya yi sukuri da shi ya kasa tankawa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.