Free chapter 路 Read without an account

Episode 23-24

by Aisha Ma'aruf 路 馃尲馃尲ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲

馃尲馃尲ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲


STORY AND WRITTEN BY


GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒


ELEGANT ONLINE WRITER'S 馃摎


PAID BOOK

FREE PAGE


PAGE 11


_____________________________Da misalin karfe 8 na dare, Nasreen ce ke tafiya da sauri sauri tana waige,maza uku taga suna bin bayan ta,sauri ta Kara tanayi tana waige,ta danyi tafiya Mai Dan nisa taga still suna binta dan har sun kusa cin mata,Kara saurin tafiyan ta tayi,chan taji wani daga cikin su yace,wai bazakuyi sauri mucin Mata ba ko so kuke ta sere Mana,"Nasreen najin haka tace kafa Mai naci ban baka ba,gudu ta Fara Yi tuni Suma suka Mara Mata baya a guje,gudu take suna binta kaman masu yi tsere, da gudu yayi gudu batasan sanda ta cillar da parantin hannun ta ba tana gudu tana hawaye,tana juya baya taga tazaran dake sakanin su kadan ne,baza hannun ta tayi ta yarda duk abin da ta rike hatta kudin dake hannun ta,tattara kayan ta tayi ta Kara gudu sai Nishi take kaman zata hadiye zuciya,gudu take suna binta,"da yake Imani ya musu Karanci, Mai koman su hakura tunda sunyi gudu Mai tsawo amman sun kasa cin Mata shine su kaki,'banza ta Fadi sha-sha na biki' ",gudu take harta apka kan titi,ji kake kiiiiiiiiiiiiiiiiiii!gummmmmmmmm!,iko en iskan naganin abin da ya faru su ka juya Suka nufi inda zasu................



Kai baba Amman fahh! banji Dadi ba da bamu samu yarinyar nan ba,ya fada Yana zukan sigari,daya daga cikin su ma yace "wlh kuwa ba hago Nima abin ya ban haushi,nayi mamakin da yarinyar nan ta iya tsere Mana,ace mun kasa cin Mata,ko da yake Dan wani ya bige tane da mun cin Mata","Sabo yace wlh gudun yarinyar ya ban mamaki,kaga yanda take gudu kaman jirki,Ni wlh gudun ta ma yaban mamaki,I ko ba'a bige ta ba zaiyi wiya mu iya cinmata","bazuka yace I Naga alamun ta gaji,kadan yarage mu cin Mata sai wannan mutumin daya bigeta ya Mana kwapsi" "bahago yace har na hango yanda zannnnnn! Kaiiiiiiiii! Ya fada yana daura yatsa daya a baki,dariya duk sukayi suka buso hayaki a tare sukace sai wani jikon Kuma,"Allah yakai buzu ga harawa,ya Sha Romo".



Yana bige ta sai data yi sama kafin ta dawo ta fada saman motan shi kanta ya bugu da glass din motan shi har sai da glass din yayi alamun fashewa,fitowa yayi da sauri dan ya dauketa zuwa Asibiti,da yake a kife take sai ya juya ta,Yana juyata wa zai gani Angel,zaro Ido yayi Yana salati,"kanshi yaji ya mishi nauyi,jijjigata ya farayi Yana Angel Angel Angel!!!,daya ga alamun dai Bata motsi shine yasa hannu ya cincibe ta yasa ta a bayan mota sai Asibiti.Wani babban Asibiti ya kaita inda Nan family doctor su ke aiki,ko da ya kawo ta family doctor sune k da duty,da sauri ya amshe ta a hannun Arif ya kaita daki na musamman Arif na biye da shi sai share zufa yake, doctor na shiga Shima ya bi bayan shi zai shiga aka Hana shi,tura kofan su kayi,tuni doctors har uku Suka rufa akan ta aka Fara Bata taimakon gaggawa,tsayawa Arif yayi a jikin kofan Yana kallan duk abinda sukeyi a ciki da take kofan na da wani Dan glass a jikin shi Wanda zaka iya ganin dum abin da k gudana aciki, sun shafe Awa biyu suna kanta,wayan Arif ne yayi ringing,Yana Jin ringing tone din yasan na wayene,tashi yayi daga wurin kofan ya zauna akan kujeran dake gaban dakin,amsa wayan yayi tare da gaishe da mummy,amsawa mummy tayi sannan tace lafiya son Mai ya Sami muryan ka Kuma Mai yasa baka dawo gida ba har yanzu,kasan karfe nawa kuwa girgiza Kai yayi kaman mummy na gaban shi Yana duba agogon dake daure a hannun shi,zaro Ido yayi daya ga time yace" mummy is to 12" "mummy tace fyn! Mai kake Yi da baka dawo gida ba then" bude Baki yayi muryan shi a sanyaye yace" mummy I had an Accident,na bige wata yarinya" mikewa mummy tayi saye ba tare data sani ba tana salati tace a wani asibiti kuke jikin ta sai rawa yake,"Gaya Mata sunan Asibitin yayi",tana gama Jin sunan ta katse wayan,daddy me yace what happened to son,drawer mummy ta nufa tana bashi amsan abin da ya faru,salati daddy yayi Shima ya mike da sauri ya dauko wani jallabiya Baki Mai dogon hannu ya zura sannan ya saka hulan Nan Mai suna" tabani kaji hadisi"key mota ya dauka Suka fita da mummy dama mummy ba wani shiri tasaya yi ba hijabi kawai tasaka a saman kayan barcin ta,key daddy Yana ma mummy ta nufi wurin motan da za'a fita da shi ta shiga ta Mai key ta tuko shi har zuwa wurin gate,daddy ko wurin Mai gadi ya shiga yamai bayanin zasu fita zuwa asibiti Amman Bai Gaya mishi Mai ya faru ba,adawo lafiya Mai gadi ya musu tare da musu Allah ya tsare,mummy ce ta fito daga driver seat ta nufi bangaren Mai zaman banza daddy Kuma ya shiga driver seat ya ja motan suka bar gidan,baifi minti 15 ba Suka Isa katafaran Asibitin saboda gudun da daddy yayi,daddy me ya Kira Arif ya tan baye shi ward din da suke,kashe wayan yayi sannan ya nufi ward din da aka Gaya Mai"EMERGENCY WARD" hango Arif sukayi a zaune ya bugs uban tagumi kaman maraya,su daddy na Isa inda Arif yake wani likita ya bude kofa,kallan dakin duk su kayi, doctor ne yayi saurin karasowa Yaba ma daddy hannu Dan yasan daddy sossai,kafin daddy yayi magana Arif ya riga shi tan bayan Mai jiki,Dan Jim doctor yayi sannan yace muje office nayi muku bayani,bayan sun Kai office kowa ya zauna,wani plain A4 doctor ya dauka Yana musu bayani Yana Dan wasu rubutu,jijjiga Kai duk suke har doctor yagama bayani,Babu Wanda yakai Arif shiga damuwa,mummy ma ta damu dan tun kamin taga yarinyar taji son ta ya shiga zuciyan ta,tashi duk sukayi zasu fita,sai Arif yace zamu iya zuwa muga patient din,da ehhh! doctor ya amsa,Amman Kar ayi wani hawaniya ko Kara a kusa da ita Dan a yanzu ba'a San Kara a kusa da ita saboda condition din ta,daddy ne yace insha Allah za'a kiyaye,dakin da aka gama Mata aiki su ka nufa Suka tarar Bata ciki, doctor su Suka tanbaya inda take ya Kai su har dakin da aka Kai ta,shiga duk su kayi da sallama a bakin su,samun ta sukayi a kwance kanta made da bandage har fuskan ta sai hannun ta na hagu ma ansa mishi bandage,shiga duk sukayi jikin su a sanyaye,"mummy ce tace karamar yarinya ce,Ina iyayen ta suke da Suka Bari ta fito waje daddare,Babu inda zata samu amshoshin tanbayoyin ta sai a bakin yarinyar"zuwa tayi ta zauna a gefen gado tana kallan Nasreen,kallan farko datayi Mata sai da zuciyar mummy ta buga,kallan ta ta dingayi a zuciyar ta tanajin kaman tasan fuskan nan". Haka Suka zauna a dakin jugum jugum kowa ya buga tagumi,dukkam su sun kasa barci,da misalin karfe 2 Arif je yayi sallah sai da yayi raka'a 11 kafin ya tashi daga kan sallayan,daddy ma yayi sallah Amman raka'a 4 yayi haka ma mummy duk barci ya gagari idan su yanda sukaga Rana haka sukaga dare har garin Allah ya waye,bayan su Daddy sun dawo daga masallacin dake cikin Asibitin,dakin da take sukayi da sallama Daddy na gaba Arif na biye da shi a baya,samun mummy su kayi akan darduma tana Addu'a hannun ta na sama,bayan ta Gama Daddy yace ta tashi suje gida tayi musu breakfast tayi wanka sai tadan huta kafin ta dawo anjima,jayayya zatayi Daddy yace ununnn! Karma ki Fara tashi kawai,da Mai Aiki tazo Arif ma zai dawo yayi wanka,ya fada Yana kallan Arif,da toh!daddy Arif ya amsa Yana girgiza Kai,ta shi yayi yaraka su mummy sai da suka tafi kafin ya dawo cikin Asibiti.



Bayan kaman misalin 2hours,Mai aikin tazo,Arif ne ya fita yayi Mata jagora suwa dakin da suke tare da tayata dauka basket daya,shiga sukayi Suka ajiye basket din,sannan Mai aikin ta Kara gaishe da shi tare da Mai jiki," amsawa yayi da lfy lau,jiki Kuma Alhmd"Zama sukayi na sawon minti Sha biyar,taga dai Bai da alamun ta shi ya tafi gida,bude Baki tayi a hankali tace yallabai,Alhaji yace ka dawo gida idan nazo,kallan ta yayi baice komai ba,shiru tayi Bata Kara magana ba,bayan kaman misalin minti 5' biyar' ya tashi ya dau wayoyin shi da key din motan shi ya nufi bakin kofa harya bude kofan zai fita sai ya tsaya yace ki kula da yarinyar nan da kyau,Kar komai ya sameta duk maganar Nan da take ki kallan ta baiyu ba hasalima yaba ma dakin baya gaba daya,Yana Gama magana ya give daga dakin tare dajan kofan a hankali Dan Bai manta da kashedin doctor ba,wurin doctor ya nufa yace "doctor haryanzu Bata farka ba Kuma tayi awa 10'goma' tana barci" doctor yace ehhhh! Dole kaga haka,a sakamakon buguwar da tayi,ta Dan bugu so ana bukatar kwakwalwan ta huta sossai,Dan zai iya yuwa ta Kai kwana biyu kafin ta farka," zaro Ido Arif yayi yace kwana biyu fahhh! Kace doctor" girgiza mishi Kai doctor yayi yace ehhhh! Tabbas haka take kaman yanda kaji dai nace. "Kuma in ta tashi zai iya yuwa ta rasa duk wani abin da ta sani a baya,"wato ta rasa memory ta a turance",Amman a binciken da mukayi ko an samu akasin ta rasa tunanin ta toh! Abin bazai yi tsanani ba,Dan iyaka,tayi wata shida '6' zuwa shekara daya '1' da wannan laluran,sai dai kawai ki cigaba da Addu'a,Allah yasa ta tashi lafiya kalau ba tare da ta rasa tunanin ta ba." Ajiyan zuciya Arif ya dauke sannan yace Allah yasa mu dace,ta shi yayi ya Mika ma doctor hannu sukayi sallama ya wuce.



A hanyyan shi na komawa gida Babu abin da yake tunani kaman inda zaiga en uwan ta,sai Kuma abin da ya fito da ita a daran Nan,Kuma da alamu binta ake da har take wannan gudun ,Kuma kaman yaga alamun mutane Amman Sam hankalin shi bai Kai kan su ba,haka dai ya cigaba da tunani zuci har ya Kai gida.




Bayan sallah Azahar Arif ya kwanta bashi ya tashi ba sai karfe uku da minti 45 ya tashi,farkawa yayi da Addu'a a bakin shi,tashi yayi ya shige bayi, baifi minti 10 ba ya fito daure da bathroom da Dan karamin towel a hannun shi,share ruwan kan shi yayi da sauri sannan ya shafa man shi ya saka boxers da singlet kafin ya saka jallabiya,bayan an idar da sallah ya tashi ya Rama Wanda bai samu ba.bayan ya Gama yayi Azkar din shi yayi ma Angel din shi Addu'a,Bayan ya kammala ya tashi ya fita,gida ya nufa ya cire jallabiyan jikin shi, drawer ya bude ya dauko wani yadi kalan dark blue riga da wando jumper,shirya wa yayi bayan ya Gama ya bude case din shi na agogo,ya dau wani agogo Kiran Rolex Mai ratsin blue, a cikin shi,Tulare ya dauka ya feshe jikin shi da shi,wani hula ya saka wanda en barni me Kira da kinde,daukan wayoyin shi yayi yasa a Aljihun sannan ya dau car key ya fita a dakin,dakin mummy ya nufa ya tarar ba ta ciki,na Daddy yaje,sallama yayi a bakin kofan aka amsa Mai,samun su duk yayi a shirye,yace" Daddy Kuma Asibitin zaku" da ehh! Daddy ya amsa yace we are done self ya karasa ya na daukan car key",fita sukayi a dakin mummy ta kulle kofan,dakin ta ta nufa ta kashe bulb ta ajiye makullin Daddy a cikin dakin ta inda duk binciken ka baka gani shi.Basket din da aka jera akan dining Arif ya dauka ya fita da shi,booth ya bude ya saka shi a ciki, Daddy ya zauna a wurin Mai zaman banza while mummy ta zauna a back seat,Arif ne ya jasu har Asibiti,su mummy Suka sauka Suka nufi cikin Asibiti,Arif ko bude booth yayi ya saukar da basket din ya kulle motan,dauka yayi ya nufi cikin Asibitin,shiga yayi da sallama,ya taddasu duka Azaune, doctor ya samu Yana duba ta,daya gama duba ta ya cire stethoscope daga kunnen shi ya dube su yace,lafiyan ta kalau insha Allah zata tashi anytime daga yanzu zuwa dare insha Allah,Allah ya Bata lafiya,Yana Gama fada ya fice daga dakin........................



COMMENT AND SHARE.


BY GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒.



Normal Group #200

VIP #400

Complete Novel #600


Account Name:Aisha Maaruf

Bank Name: UBA

Account Number:2245462427

Evidence of payment via whatapp:***.


Karku Bari a Baku labari is very interesting.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.