Free chapter 路 Read without an account
FREE PAGE 2
*_K I K U L A N I_*
_(MALLAKIN ZUCIYA)馃挄_
_N A N A H A F S A T_
_MSS XOXO_
_F R E E - P A G E :002_
______
*A* darare ta kashe dan kyandirin da ke ci ahankali ya kusa cinyewa. Ta dubi yaran nata su biyu maza. Sun zuba mata idanu.
Ta yafito daya da hannu yana matsowa kusa da ita ta goye shi a baya. Ya yinda ta dauki dayan a hannu.
"Kuyi shiru. Kar wanda yayi magana.. "
Sikif ta fice daga cikin dakin zuwa bandaki bayan tayi adduar shiga. Dan ruwan da ke cikin bokitin da ta sakaye shi a bakin kyauren ta dakko. Ta saka hannun ta aciki da dan dumi kadan.
Nan da nan ta sabule musu kayan jikin su duka. Cikin rawar jiki ta shiga yi musu wanka tanayi tana juyawa tana duban kofar wajen bandakin. Kasancewar dare ne. Ga fargaba da ke cunkushe a kirjin ta. A 'darare take cudasu tana dauraye wa da ruwa.
Tana kammala wa ta dauki dayan da dazu daukar sa tayi ta goye shi. Yayin da ta dauki dayan data goya dazu ta rike shi a hannu.
Da sauri ta fito da su daga cikin bandakin ta shige dasu cikin daki. Nan da nan ta rufe kofar dakin da dan kyallen da take rufe wa.
"Bacci yazo ko Hammadu?" Ta tambaye su tana goga musu basilin.
"Haidar kai ma bacci ko? Kunga Hadiyyah sai baccin ta ta ke. "
Suka juya a tare suna kallon Hadiyyah da ke bacci tana sakin munshari.
"To zo nan ka kwanta kai ma. Kai Hammadu dawo ta nan... Yauwa yaran albarka. " Ta kwantar da su duka akan wata yaloluwar yar katifa bayan ta tofe su da addu'oi.
Ta janyo muhuci ta shiga yi musu fifita tana mai kade musu sauro. A haka har sukayi baccin su ma.
Tsayawa tayi tana bin su da kallo. .. su ukun duk sunyi bacci. Ta sauke ajiyar zuciya tana kokarin mayar da hawayen da ke shirin gangaro ma ta kan kumatu.
Sai da dare ya kara ja tukun sannan ta tukwikwiye yar jakar data ke matashin kai (pillow) da ita ta kwanta daga gefen su bayan tayi addu'oin kariya. Ba dadewa kuwa bacci ya dauke ta..
脳脳WASHE-GARI脳脳
Da asubah tana tashi bayan tayi sallah ta shiga gyara dan tsukakken dakin da yake a matsayin nata dana yaranta su uku.
Ta tattare shara ta zubar. Kana ta zauna tana jan carbi har lokacin da gari ya waye rana ta fito.
Soyeyyen dankalin hausa da kwai ne ke tashi daga dakin Ladiyo. Ta sake sakaye kofar dakin don kada kamshin ya shigo su Hammadu su shaka. Tunda haramiya ce domin ba ci zasuyi ba. Kar su zo suna mata kuka. Batada inda zata samu dankali bare kwai.
Don haka da sauri ta mike ta gyara zaman hijabin jikin ta. Ta fita daga cikin dakin.
Tana fita sukayi kicibus da malam mai gidan su. Ya shigo da ledar kosai a hannun sa.
"Barka da safiya malam.."
Ta tsugunna har kasa ta gaishe shi.
Ya dube ta a yatsine yana mai cigaba da sakatar hakoran sa da wani tsinke.
"Ke Murjanjan ungo kai wa babar ku." Ya mikawa wata yarinya ledar da ke handama dankali da kwai cikin bakin ta. Yayinda gefe daya ruwan shayi ne a kofi tana korawa da shi...
Ta bi ledar da bayar da kallo. Tarasa wano irin rashin imani ne da shi. Da sam baisan hakkin iyalin sa ba akan sa. Iyalin ma su kadai kawai.
Ta goge hawayen da ya gangaro mata da kasan hijabin ta da sauri ta mike ta fice daga gidan.
Wajen Asabe taje mai suyar kosai da kunu. Suka gaysa ta shiga matse yatsun hannuwan ta . Tana neman kalaman da yau ma zata gaya mata ..
Asaben ta dakko daurin bakar leda cike da kosai aciki da biredi na sittin ta mika mata.
Ta tsugunna har kasa ta karba tana mai sake kwararo mata addua kamar ko da yaushe.
"Nagode Allah ya saka da alkhairi.... Allah ya karo kasuwa mai albarka Amin."
"Amin Fadila. Wannan sadaqa na gayan ki ba ni ke bayarwa ba. Wani bawan Allah ne kasko daya yake sa a toya ayi masa sadaka da biredi na dubu daya kullum. "
"Na sani Asabe. Shiyasa baki yayi kadan wajen nuna godia ta agare ki. Tunda kece kika saka mu a jerin masu karba kullun bakya gajiyawa kuma bakya canzawa... Allah ya saka da alkhairi "
"Amin Fadila.. Ya yaran?"
"Na baro su suna bacci.."
"Allah sarki. Ki tashi ki koma. Ungo kunun nan ki basu ba yawa. " Ta karasa fada hadi da mika mata wata bakar leda cike da kunu sai kayan kamshi ne ke tashi daga ciki.
"Allah ya saka da alkhairi... Nagode nagode..." Ta saka hannu biyu tana mai sake yi mata godiya.
Sannan tayi mata sallama ta tafi. Tana tafe tana kwararawa koma wanene da ke sadakar kosai da biredin nan addu'oi hadi da albarka.
Tana sallama cikin gidan kunnuwan ta suka fara jiyo mata kukan yaranta. Da sauri ta karasa dakin ta shiga. Ta janyo su jikin ta tana lallashi. Kafin ta janyo yar roba dake dauke da ruwa kadan aciki ta dauraye musu bakunan su.
Kafin ta sunce yar ledar kosan da biredi ta shiga basu tana mai hada musu da kunun. Har suka cinye tas.
Sai da ta tabbatar sun koshi tukun sannan ta cinye ragowar ta kurbe kunun. ..
Tana kokarin dauraye abunda suka bata su Hadiyyah suka fita wajen tsakar gidah...
Sai jin kukan su tayi. Ta fita da sauri. Ladiyo ta gani a tsaye ta talle keyar Hammad. Ta dumawa Haidar dundu hadi da lankwasa kunnen Hadiyyah.
"Sattin ta mai duka. Idan yaran nan masu kayuwa kamar gorar ruwa suka sake shigo mun daaki Allah sai na dau babban mataki. Ai kin kawai" Ta karasa fada hadi da rafkawa Fadila harara.
Da sauri ta janyo su jikin ta tana lallashin su duka. Hawaye na tsiyaya daga nata hawayen.
Malam Haladu ya fito daga dakin sa yana jera tsaki.
"Kukan menene hakane.?"
"Su wa ka sani malam? Shafaffu ne da mai mana...Hammadu da Haidar da Hadiyyah.." Ladiyo ta bude murya daga tagar dakin ta tana bashi amsa.
"Mtscccew" Yaja dogon tsaki kafin ya koma daki. Can sai gashi da warin takalmin sa daya ya nufo su zai kai musu bugu kenan Fadila ta kwashe su har tana dauje gwiwarta ta shige cikin daki da su...
Ladiyo ta kece da dariya har tana sakin guda. Yayin da malam Haladu ya koma cikin dakin sa yana mita....
*RUMBUN K'AYA*馃敟
*DAUDAR GORA*馃敟
*IDON NERA*馃敟
*A RUBUCE TAKE*馃敟
*KI KULANI*馃敟
*_uhmmmm_*馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉馃槉
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*鈽猴笍鈽猴笍
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*馃敟馃敟馃敟馃敟馃敟
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
***
馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜馃嚦馃嚜
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*馃敟