Free chapter · Read without an account

Aduniyar mu 7&8

by Khadija Umar · A duniyar mu

A DUNIYAR MU

7&8

Khadijah Umar Abdullahi

(Garkuwar Jarumai)


Bismillahir'rahmanir'raheem


""Dole  zamu buɗe wani account ne da zamu dnga fallasa a bubuwan da suke yi, na tabbata koda ba duka mutane ba wasu zasu fahimta sannan sai mn dena nuna adawa da halin su azahiri,

 kamar yanda suke wa talakawa kisan mimmiƙe to muma shi zamuyi musu,


""Na fahimce ki amma a kwai buƙatar mu haɗu ko ?

""eh gaskiya kam amma yaushe ya kamata mu haɗu? alhamdllh tinda kai ƙwararre ne wajan sanin yanar gizo nasan bazamu samu matsala ba,


 saidai fa amma ina hango mana baƙar wahala a cikin wannan aikin,

 amma dole haka zamu haƙura tinda muka ɗakko in sha Allah sai mn kaishi,


Yanzu ka buɗe mana wani sicret account kasaka masa matakan tsaro sosai saidai fa dk sanda muka ɗora wani abu akai zamu rufe account ɗn gaba ɗaya sannan mu karya sim ɗn sai a buɗe wani,


 ma'ana dai kowane labari da sabon account zamu yaɗa shi daga nan amfanin sa ya ƙare,



amma yaushe zaka fara aiki? !"" Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "" na gama trayning  an bani office zuwa kawai zan fara yi kuma ina saka ran fara zuwa on monday, saidai hanklin dadi be kwanta da aikin ba "


"nasan dama bazeso ba kana matsayin ɗansa kuma kana mamallakin manyan kamfanoni a nigeria da maƙotan ƙasar mu sannan kace zaka zama bawan ƙasa,


 kamar yadda mukayi da daddy na kafin ya amince na fara aikin jarida,

 shima kuma gani yake kamar ya samu damar da zai dnga al'amuran sa yanda yake so saboda yana da ni a cikin ƴan jarida,


 saidai da farko naso nuna masa ba haka zanyi ba amma daga baya na gane ba'a fito na fito da iyaye,


 amma nayi alƙawarin sadaukar da farin ciki na da na iyaye saboda ceto miliyoyin alumma kuma ina da yaƙinin ubangji zai taimaka mana,


 "" in sha Allah Kamal yace yana jinjinawa basira irin ta Khadija, da haka sukayi sallama bayan sun tsaida ranar da zasu haɗu

--------------------------


ikon Allah ne kawai yakai nura gida wani irin jiri yake ji saida ya dafe bango sannan ya iya kaiwa ga ɗakinsa,

 yana shiga ya kwanta kan katifar sa zuciyar sa na masa zafi ya kasa mantawa da yanayin da yaga jamila  



""Meyasa rayuwa take mn haka? meyasa sai lokacin da zanji daɗi sai wahala ta shigo ta katsemn farin ciki? meyasa ? ya Allah ka ciremn som jamila a raina Allah ka kawomn ɗauki ,



wasu zafafan hawaye ne suke sintiri a gefen idon sa suna sauka kan katifa,


Ƙanin sa ne ya shigo kiran sa


 turus ya tsaya ganin halin da yayan nasa yake ciki da sauri ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin mahaifiyar su ya sanar da ita halin da Nura yake cik



 da sauri mama ta fito tana gyara ɗaurin zani tayi hanyar ɗakin nasa,

 koda ta shiga ta same shi kwance har zazzaɓi ya kamashi cikin damuwa ta dubi ƙanin na sa tace "" maza Aliyu kaje ka kirawo najib,

 da to ya'amsa ya fice daga ɗakin,

 be zame ko ina ba sai bakin titi wani ɗan ƙaramin chemist ya shiga da gudu yana haki

 wanda ke zaune cikin chemist dn da hanzari ya miƙe tsaye yana tambayar Aliya lafiya?


 "" yaya nura ne Aliyu yake ta faɗa yana haki ba tare da najib ya tambayi abinda ya samu nura ba ya harhaɗo kayan aikin sa sauri sauri ya fito daga chemist ɗin inda ya barwa yaron sa wajan ya nufi gidan su nura,


 shigar sa keda wuya ya samu nura dafe da ƙirjin sa yana wani irin tari mai ban tausayi yayin da mama ke zaune gefe tana share hawayen tausayin jarumin ɗanta,


 allura najib ya ciro yayi masa guda biyu sannan ya dubi mama yacs "" yaci abinci ""eh yaci da magrib ""ok to Aliyu kawo ruwa yasha magani da sauri Aliyu ya ɗakko ruwa ya miƙawa najib,



 nura da baima san najib ya shigo ba najib ya ɗago shi ya bashi maganin ya bashi ruwa ya haɗiye sannan najib ya maida shi ya kwantar,

 ya maida kallon sa ga mama yace "" amma mama ya'akayi aka tsokano masa wannan wahalallen ciwon dn ma Allah yasa abin beyi tsamari ba tnda be fara amai ba


 "" ajiyar zuciya mama ta sauke tace "" wllh najib kawai ina zaune ina lazimi Aliyu yace nura bashida lafiya shine na taso na ganshi


 nace ya korawo ka to kafin kazo ne jikin ya zama haka amma nafi tinanin daga waje ne ya taho da ɓacin ran,


 cike da tausaya wa najib ya dubi nura wanda zuwa yanzu ya ɗan ji relief bacci ya ɗauke shi yace "" sannu nura Allah ya yaye maka wannan ciwon Allah ya baka lafiya 


""amin mama tace tana goge hawaye,



------------------------


Misalin ƙarfe uku suka shirya suka tafi gidan hajiya samee basu sha wata wahala ba wajan shiga gidan saboda me gadi ya gane su, tana nan zaune kan kafet tana shan fruit sukayi sallama,


 washe baki tayi tare da cewa ""oyoyo ƴan uwa sannun ku da zuwa,


 ladidi mai aikin ta ta ƙwalawa kira ta bata umarnin a kawo musu abinci,


 aiko ba jimawa aka shirya dianing hajiya samee tace "" to muje kuɗan ci wani abu babu musu suka bita suka zauna akayi serving ɗin su suka fara ci,


Sai da suka ci sukan ƙoshi snnan suka dawo palo hajiya samee ta dube su tace 


"" nasan koda baku ce komai ba zuwan ku ya nuna amincewar ku yanzu abnda ya rage ku shiga ɗaki na kuyi wanka ku ɗauki kayan da kuke so daga cikin kaya na ku saka,


 sannan ta dubi maman nabila tace " zamu bar nabila wajan me kulamn da yara kafin mu dawo zata kula da ita sosai fiye da ke sannan ina so ku sani bafa dawwama zamuyi muna wannan harkar ba,

 jari zamu tatsa a wajan su misali idan muka mallaki irin moll moll manya ko textiles ka restuarent,


 sai mu janye daga gare su kunga lokacin munfi ƙarfin komai koba haka ba?


 yanzu zaku bani sunayen mazajen ku zan kira malam zan faɗa masa da zarar kun koma duk abinda kuka faɗa musu sn zauna,


shewa suka saka suna tafawa sannan suka faɗa mata sunayen mazajen su suka haura sama inda ɗakin ta yake don yin wanka


Daddy ne zaune cikin wani ƙungurmin daji tsakiyar dare baka jin komai face kukan tsintsaye sai kuma wani sauti mara ɗadin ji dake fitowa cikin wata bukka,


"" a samo yara ƴan ƙasa da shekara goma guda goma a yanka su,


 a tare maka jinin nan da kwana uku kayi wanka da jinin sai ka dawo mana nan kana ƙarnin jinin shi muke buƙata "" wannan ai ba komai bane sarkin aljanu ga yara nan kamar famfo aka murɗa suka zubo zan sa a shiga unguwoyin talakawa za'a samu koda sama da guda goma ake buƙata "'tashi kaje ka aiwatar "" angama sarki Daddy yace yana miƙewa daga wajan ta fara tafiya da baya da baya



SHARE FISABILILLAH


MAMAN SHARIFA CE

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.