Free chapter 路 Read without an account
A DUNIYAR MU 9&10
by Khadija Umar 路 A duniyar mu
A DUNIYAR MU
9&10
Maman Sharifa ce
(Garkuwar Jarumai)馃挭馃徎
Jarumai writers association
Bismillahir'rahmanir'raheem.
Da baya da baya Daddy ya dinga sakkowa daga dutsen da bukkar sarkin aljanu ke kai har yazo inda yayi perking,
yana shiga mota yaja yabar wajan zuciyar sa fal farin ciki, sakamakon tabbacin da sarkin aljanu ya bashi dangane da mulkin sa,
tinda ya fara tafiya yake sa茩awa da warware wa a zuciyar har yazo gida,
direct 蓳angaren sa ya nufa yana shiga ko zama beyi ba ya fara kiran waya ,
Kamal da tun fitar Daddy yake safa da marwa a palon sa yana ayyana irin rashin tsoro na Daddy da kuma inda ya nufa hankalin sa be kwanta da tafiyar ba,
dn haka yayi maza ya haura saman Daddy yayi sa'a part 蓷in abu蓷e yake haka ya shiga ciki da sand'a
wata 拼ar 茩aramar camera ya 蓷akko cikin aljihun sa ya manna ta jikin bango tsakanin labule ta yanda babu wanda zai kawo wani abu aka saka a wajan,
sannan ya koma part 蓷in sa ya zauna yana jiran dawowar sa,
akan idon sa Daddyn ya dawo ya shige ciki,
Kallon agogon hannun sa yayi k'arfe biyu da rabi
Ganin zeyi nisa da sauri ya ta shi ya bishi a baya yana la蓳ewa a bayan labule,
Daddy gaba 蓷aya hankalin sa be kawo masa cewa a kwai wanda ze kasance ido biyu cikin gidan ba,
shi yasa yake yafiyar sa hankali kwance,
yana zuwa shiga 蓷akin Kamal ya shige bayan labulen palon sama kamar alamun motsi Dady ya ji yayi saurin juwo yana waiwaye saidai baiga kowa ba,
ya s mur蓷a handle 蓷in ya shige ciki ya turo 茩ofa,
jikin 茩ofar Kamal ya jingina daga ciki banda tsaki babu abida Daddy yakeyi, yayin da Kamal keji ta wata 拼ar 茩aramar na'ura daya saka a kunnen sa gefe guda kuma tana masa recording,
wanda Daddy ya ke kira ne ya amsa wayar,
nan da nan Daddy ya rufe shi da fa蓷a mutumin yana bashi ha茩uri kafin ya tsaya da fa蓷an yace
""na baka kwana biyu ina bu茩atar yara 拼an 茩asa da shekara goma maza biyar mata biyar ka shiga unguwar talakawan nan,
daga can 蓳angaren mutumin ya amsa da cewa
"'excellency yanzu fa talakawan sun fara wayewa basa barin yaran su a waje sannan koda an samu sai an yaudare su tukun,
ma'an saidai na shiga da alawa na raba musu kamar ta kwana uku kafin nan sun sake dani ,
wata irin tsawa Dddy ya daka masa yace"" ni jibi nake so idan ba zaka iya ba zan sa wani "" ayi ha茩uri ranka ya da蓷e ko gobe kake so za'a samo tnda monday ce idan an taso 拼an primary za'a samo a ciki, Allah ya huci zuciyar excelency
ba tare da Daddy ya ce komai ba ya ajiye wayar ya shiga toilet Kamal da jikin sa keta rawa hankalin sa yakai 茩ololuwa wajan tashi yana le茩en Daddy ta jikin 茩ofar,
yana jin wata tsanar Daddy na shigar sa tare da nadamar kasancewar sa 蓷a a gare shi ,
A hankali ya bu蓷e 茩ofar da san蓷a ya shige yana jiyo 茩arar ruwa daga ban蓷akin ya 蓷auki wayar Daddy yayi copy numbern wanda sukayi waya da shi sannan ya 蓷auki cameran sa yafice,
a hankali ya turo 茩ofar da sauri sauri yake sakkowa daga saman Daddy ya nufi part 蓷in sa yana zuwa ya jiye wayar sa da camera a gefen bed,
ya cigaba da zagaye a 蓷akin ganin ya rasa mafita gashi dare ne bare ya 茩ira Khadija yasa ya shiga toilet ya 蓷auro alwala ya fito ya shimfi蓷a pray mat ya tada salla.
---------------------------------
Tnda gari ya waye umma da jasmin suka fahimci tsantsar farin cikin dake tare da jamila,
dk abunda take yi tana yinsa ne cikin nisha蓷i,
hankalin umma ya 蓷an kwanta tana tinanin adduar ta ce ta samu kar蓳uwa
misalin shabiyu na rana Aliyu ya shigo gidan da sallama amsawa umma tayi ya ce wa " to yau Aliyu ne a gidan? kwana biyu ka 蓳uya har ina cewa zanzo biko murushi yayi ya gaishe da umma amsawa tayi tana nazar tar yanayin sa tace
"" Aliyu baka da lafiya ne?"" lafiya ta 茩alau umma yaya ne ciwon sa ya tashi zaro ido umma tayi ta ce"" innalillahiwa innailaihirrajiun yaushe ciwon ya tashi? yana ina?
"" jiya bayan isha ya fito daga gida to daya koma ne ya koma da ciwon,
ina ga 'a inda yaje ne aka 蓳ata masa rai,
amma jikin da sau茩i yana gida yanzu ma ya koma bacci,
Aliyu ya fa蓷a yana yiwa umma sallama a fice daga gidan, umma da ta daskare a tsaye ko Amsa sallamar da Aliyu yayi mata bata yi ba zuciyar ta ke sa茩a mata abubuwa da yawa,
a hankali ta zauna ta maida kallon ta ga jamila ta ce "" me kika yiwa Nura?
cike da rashin gaskiya jamila ta ce ni? ""kefa !! cewar umma ranta a 蓳ace """ wasa da 拼an yatsun hamnunta ta farayi sannan ta ce nifa gaskiya na fa蓷a masa "" wace gaskiyar ? ke har wata gaakiya gareki !!!? mekika ce masa?
"" cewa nayi bashida abin da ze aure ni kawai ya nemi wata,
da sauri umma ta mi茩e tana nuna jamila da hannu tace
"" anya jamila anya ke mutumce?, wani jiri ne ya fara 蓷iban umma da sauri jasmin ta ri茩e ta ta zauna tana maida numfashi
"" karki mata kuka umma hawayen ki masifa ne a gare ta kiyi ha茩uri umma na kar wani abu ya same ki ,yanzu muje gidan mu duba shi,
da sauri umma ta mi茩e ta kasa magana kallon Jamila kawai takeyi
Jasmin ta 蓷akko musu hijabai suka saka suka fice daga gidan,
Suna zuwa suka samu Nura ya tashi yana sha kunu,
da 茩yar,
cikin 茩an茩anin lokaci gaba 蓷aya ya rame gaisawa umma da mama suka yi mama ta ce "" oh yanzu saida aliyu ya fa蓷a miki kema da ba lafiyar gare ki ba murmshin ya茩e kawai umma tayi tace "" nice nace masa ya dinga fa蓷a mn duk abinda ya faru,
kallon nura umma tayi ta ce"" kayi ha茩uri Nura ka yafe mana ha茩i茩a jamila ta cutar da kai amma nasan kaima Allah ba zai barka hakaba nan dai umma ta kwashe abinda Jamila ta ta fa蓷a mata ta sanar wada mama,
zuciyar mama tayi zafi amma saita dake ta ce
"" bakomai dama ai wani baya auren matar wani,
wannan ciwo kuma ba lallai se dalilin Jamila ba Allah ya 茩addara zai tashi a wannan lokacin ya茩e kawai umma tayi tace "'sai kuma wata alfarma da nake so kuyi mn ke da Nura,
ahankali Nura ya dubi umma ya ce
"" babu abinda bazan iya miki ba idan har ina da ikon yi,
jinjina kai mama tayi alamar tabbatarwa """ saida umma ta gyara zama sannan tace "" so nake nan da wata biyu a 蓷aura auren ka da Jasmin,
ina fatan zaka amince gaba 蓷aya suka 蓷ago kai suka kalle ta mama ce tayi 茩arfn galin cewa
"" amma Jasmin yarinya ce shekara goma sha shida fa,
""haka ne nasani cewar umma saidai nasan jasmin ba zata watsamn 茩asa a ido ba sannan ta maida kallon ta ga jasmin tace
"" jasmin na yanke miki wannan hukuncin ne badon bana son ki ba sai do nagar ta da kyawawan halayen irin na nura na tabbata wata rana zakuyi farin ciki keda shi,
sanan ta maida kallon ta ga nura tace ka amince?
murmushi kawai nura yayi yace
"" ba komai umma Allah yasa haka shi yafi alkairi,
amma umma bana so ayiwa jasmin dole a kaina,
kallon jasmin umma tayi tace "" kin amince ? sunkuyar da kanta Jasmin tayi tace
"" koda wani kika ce na zauna da shi wanda ban sani ba zan zauna da shi kuma nayi masa biyayya iyakar iyawa ta,
bare kuma yaya Nura,
gaba 蓷ayan su babu wanda Jasmin bata burge ba,
mama ce tace Allah yayi miki albarka Jasmin sannan ta dubi umma tace sai musa ranar da zamu je zariya ko? "
"eh nima abunda nake tinani kenan inaga nan da kwana uku se muje ko?
sannan in sha Allah Nura yaji sau茩i sai mu tafi tare da su, haka ne cewar mama,
to Allah yanuna mana ranar...
Share fisabilillah