Free chapter · Read without an account

14

by Safiyya Haruna · DAMUWATA



A tare muka jera zuwa cikin asibitin duk kuwa da yarda naso ya yi gaba na biyo bayarsa ya k'i. D'akin ba kowa sai wata nurse domin na yi zaton zan sami su Baba a ciki. Nurse d'in na ganin mun shigo ta mik'e ta fice, na matsa ina lek'en fuskan Mama wacce har lokacin barci ta ke yi, a kwana da yini har ta rame sosai sai dogon hancinta tare da fuakanta suka k'ara tsayi, haske kam wannan ba'a magana domin sai ta koma tamkar balarabiya wanda da ganinsa kasan bana lafiya ba ne. Sumba na sauke mata a goshi ina maida kwallan da ke neman zubomin.


"Ya rabbi ba dan halina ba ka bawa baiwarka lafiya alfarman Annabin karfo da k'arshe."


"Amin ya rabbi, insha Allah zata sami sauk'i burina ki cire damuwa domin ita kanta bazata so ta farka ta ganki cikin yanayi mara kyau ba."


"To Uncle zanyi k'ok'arin cirewa."


"Hakan ya kamata."


Shiru ya ratsa na minti biyu zuwa uku.


"Da alama wannan d'an ka iyan bai bar kowa ya shigo ba sai Malam."


Uncle ya ambata yana waige-waige kamar mai neman wani abu.


"Har shi ban bari ba." 


Muryan d'an fitinan ya ratso, na juyo da sauri na tsira masa ido ya sanja sutura zuwa manyan kaya akan d'azun da ya ke sanye da k'anana.


"Kai wallahi Brother over acting d'in ka ne wata rana ke sanya mu b'ata da kai, yanzu har mijin nata ka hana shigowa ya ganta? To me kenan kayi fisabilillahi?"


"Eh fa har shi d'in banbari ba saboda kiyaye dokan Likita kuma a gabansu ya zo ya kuma tabbatar musu da kada wanda ya shiga ko waye nata."


"Wannan plan d'inka ne Brother domin nafi kowa sanin waye kai, inaga makaranta zaka koma ka zamo Likita akan Engineer tunda ka shiga rigarsu ta zartar da hukuncin da ko su basa yinsa wato hana murarrami ganin halalinsa."


Dariya ya fashe da shi yana rawa da kai na kuma zuba masa ido ina kallon dimful nasa da suka lotsa duka biyun.


"Yaya wallahi na yarda kafi kowa sanin halina shi yasa Abba ke had'ani da kai dan gano gaskiyan abinda na b'oye a ruhina."


"Ba dai ka kyauta ba Brother, a ce har mijinta ka hana shigowa ganin iyalinsa, haba dan Allah me yasa wata rana lamuranka baka sanya tunani cikinsa?"


"Kaima zaka fita idan ka cigaba da mita."


"Au har da ni?"


"Eh har dama Matarka mai kallon tsiya kamar goyon k'auyawa."


Uncle ya kalleni na juya baya ina mai maijin kunya.


"Kaga Brother zanci gidanku in ka ce zaka sanyawa iyalina ido."


"To ka sanar mata ban son kallo in ba haka ba zan tsire mata idanu sai ka zamo d'an jagora."


"Amsa naka na ce Sa'ad."


Jin Uncle ya ambaci sunarsa yasa na juyo da sauri na kuma tsira masa ido kamar mai son gano tawayarsa.


'Dama shi ne Sa'ad d'in?'


"Khadijatu meet my blood brother Sa'ad."


Maganar Uncle ya katsemin zancen zucci, kauda kai gefe na yi tamkar banji me ya ce ba saida ya sa ke mai-maitawa.


"Ok, ina yini?"


Na furta ina kuma kallon cikin idanunsa. 


"Fine mai kallo k'urillah."


Murmushi na yi dan nafahimci yana da son raha kuma shima ya tsani kallo kamar yarda na tsana amma sai gashi yau ina yi har ana sanarmin da ba'aso lamarin da ya zamo karan farko cikin rayuwata.


"Kaga Brother zan sanya Abba ya yi maka aure da yar daji mai tallan Nono in har baka daina takurawa iyalina ba."


"Wallahi na bari Yaya domin ban shirya kashe 'yar mutane ba, good night, iyalin big brother Allah tashemu lafiya.."


Ya fice da sauri, kallon Uncle na yi ya girgiza kai tare da janyo kujera ya nunamin da yatsa na zauna ya dawo bayana ya dafa kujerar na kalleshi ya jinjinamin kai tare da cewa.


"Kinga na kori mai takura miki cikin ruwan sanyi."


Shiru na yi tare da kallon hawa da saukan numfashin Mama.


"Alamun ta samu lafiya kenan insha Allah wani abin cutarwa ya bar k'ara shigowa gidanku balle ya nemi tab'a ku."


"Allah ya amince hakan Uncle."


"Amin iyalina."


Murmushi mai sauti na yi saboda tun d'azun sunar ke bani dariya.


"Insha Allah ke iyalina ne Khadijatu."


"Uncle ka tafi gida kaga dare ya soma yi."


Na sauya akalar maganar saboda yarda ke bani kunya.


"Tare zamu kwana."


Idanu waje na ke kallonsa.


"Ko tun yanzu kina son nunamin Maman ke kad'ai ke da ita?"


"A'a fa kawai hakan bai kamata ba ne dubi da kana da iyali kuma na tabbata suna can suna dakon dawowar ka musanman ganin baka saba kaiwa dare a waje ba."


"Sun san inda na ke to ba damuwa."


"Uncle dan Allah ka tafi kada fa ka zamo mara adalci tun ba'ayi nisan zango ba."


"Oh da haka Kuma fa, nagode da tunatarwa, na tafi ki kula da kanki tare da Mama dan Allah."


Kai na motsa ina kallon fuskansa ya yi da ya ke tafiya da baya da baya saida ya kai bakin k'ofa ya d'agamin hannu cikin cewa "Good night Iyalina."


Da kallo na raka bayarsa ina hasko wal-walar da ke kwance saman fuskansa abinda ya sanyani murmusawa tare da jin sanyi na shiga cikin ma'adanar halittar zuciyana.


"Uhm Uncle manya, sam baya duba girmansa sai ya yi tayimin abinda matasan samari ke yiwa 'yan mata."


'Shi ne So wanda ake kira mai maida tsoho yaro.'


"Aikam in haka ne to So babban kalubale ne a cikin rayuwar bil'adam, tunda yana maida mai natsuwa zuwa kishiyarta."


'Ke dai Deejah ki taka a sannu ka da reshe ya juye da mujiya.'


Idanu na zaro ina jinjina amsan da zuciyata ta bani. Gyara zama na yi cikin k'ok'arin kauda tunanin tun ban soma zamowa mahaukaciya ba. Sai dai abin mamaki fuskan Uncle da na d'an fitina su ne ke tamin gizo a idanu duka na kaiwa goshina ta ke na saki yar k'ara ina liliya wurin saboda zafin da na ji.


Cool music na jiyo nesa da ni mai taken soyayya, inda wayar ke haske na tsirawa ido saboda tun daren jiya rabona da ita.


"Uncle yazomin da ita kenan ko wa?"


Ringing wayar ta kuma na tafi da sauri na d'auka duk kuwa da bak'uwar number ce. Sallama na yi maimakon a amsa sai saukar ajiyar zuciya akayi tare da datse kiran baki d'aya.


"Wa ye?"


Ganin zan sanyawa kaina ciwo akan son gano ko waye sai na watsar da lamarin na koma gaban Mama na zauna na tsirawa hawa da saukan numfashinta idanu tamkar mai irgawa. Addu'a na yi ta karantowa Ina tofa mata zuwa wani lokaci barci ya soma kamani na tashi na kulle k'ofar tare da tofe ko wani sak'o na d'akin da Ayatul kursiyu na haye gado na kwantar da fuskata a kirjin Mama ba jimawa barci ya d'auke ni.


***

Uncle Muhseen ko da ya isa gida bai shiga gidansa ba a k'ofar gidan su Deejah ya tsaya ya kira wayar Beebah bata daga ba ya nemi na Bintu a kashe , sai da ya kira duka wayoyinsu duk ba wanda ya yi dacen an d'aga, fitowa ya yi ya tura k'ofar gidan ta bud'e ya yi jim saboda tunaninsa a kulle zai sami k'ofar. Hasko shi akayi da filita mai mugun haske ya kare fuskansa hucin duka ya jiyo ya sunkuya da sauri hakan ya yabawa mutumin damar ficewa gidan a guje bayansa Uncle ya biyo amma ya nemesa k'asa ko sama ya rasa, kirjinsa na dukan uku-uku ya nufi cikin gidan, d'akin Deejah ya shiga ya samesu suna ta barci ajiyar zuciya ya sauke ganin babu alamun an tab'a su, ya fito waje yana haskawa da fitilar wayarsa buhunan waken suya ya ciki karo da buhunan waken suya an fito da su an jera.


"Ikon Allah wato barawo ne ya shigo sata, to wa ya bud'e masa gidan? Domin na tabbatar su Bintu sun kulle gidan tunda suka kwanta barci."


Komawa d'akin ya yi dai-dai lokacin Fanta ta tashi zatayi fitsari ganinsa saida ta tsorata dan batayi zaton ganin mutum ba, kiranta ya yi da hannu suka fito waje saida suka kai zaure ya ce "Kulle gidan ki tofa addu'a na shigo duba ku ne."


"To Uncle amma ta ya ka shigo alhalin mun kulle k'ofa?"


"Nima abude na gansa shi yasa na shigo duba ku."


"A bud'e kuma?"


"Kinga kulle ki tafi ki kwanta securities zasu zo gadinku insha Allah bakomi sai khairan."


"To Uncle saida safe."


"Ok mu kwana lafiya."


Yana tsaye ta kulle gidan shi kuma ya kira waya kimanin mintoci goma shabiyar 'yan sanda uku suka zo a mashin sun jima suna magana kafin ya barsu ya shiga motarsa zuwa gidansa.


Sallama ya yi a falon duk da yaga da duhu alamun babu kowa amma bai sanya ya shigo kai tsaye ba. Makunnin wutar ya latsa haske ya gauraye falon zama ya yi cike da gajiya ga yunwar da ta addabesa, mik'ewa ya yi dan samawa kansa abinda zai kori yunwar. Ja baya ya yi cikin razana da ganinta domin sam bai jiyo takunta ba sai gaminta ya yi tsaye gabansa.


"Dole ka razana mana saboda ka san baka da gaskiya, wallahi Abban Hafiz wutar Allah sai ta cika in har ka ce wannan mugun halin zaka tsiro da shi na yanke zumunci tare da munafunci. Wai ina matarka baka damu da ni ba kamar yarda ka damu da d'iyar makwafta, na rantse da Allah ba zan tab'a yafewa aljanan yarinyar nan Deejah ba domin ta rabani da dangina tare da mijina to wallahi Allah sai ta biya dan bata ci banza ba, zan nuna mata ainihin kalata wanda ta ke da duhun kai akansa Dan sai na wulak'antata da duk kan gatanta, sai ta yi kukan jini bana hawaye ba, billahil azim kukan da ta sakani sai ta yi ninkin baninkin nasa indai ina numfashi, sanann kaima ban ya... 


"Ke! Banson sokanci da rashin natsuwa maza b'acemin da gani tun kafin ranki yafi dare duhu."


Ganin magan-ganun Nafisa bana k'are ba ne shi yasa ya dakatar da ita cikin fushi amma hakan baisa ta tsagaita da tijarar ba saima haukacewa da ta yi cikin daga murya tana kuka tana fallasa mygayen alwashinta akan Deejah muryanta sai sark'ewa keyi tamkar zatayi amai.


Shiru ya yi yana kallonta domin yasan ya tab'ota, bai kyauta mata ba saboda tunda ya fita sadda Beebah ta sanar masa da halin da Mama ke ciki bai kuma waowayen gida ba ko kayan da ya sanja Sa'ad ya turo ya d'aukan masa kuma ya tabbata sunyi halin nasu da ita saboda basa zama inuwa d'aya dalilin kenan da baya zuwa gidan saida babban dalili. 


"Kiyi hak'uri Mom Hafiz, yanzu hutu na ke buk'ata, tafi ki samomin abinda zanci wallahi yunwa ke damuna." 


Ya yi furucin cikin laushin murya saboda maganganunta na daf da sanya masa ciwon kai, dole dibarar lallab'ata ya zo masa.


"Ai da ka dauko dadiron naka ta huce maka gajiyan kuma ba mai sakani shiga cikin da wannan daren salon in d'auko aljannu ka barni da wahala, ai saidai ita d'iyar Bokann tazo ta dafa maka abin da zaka ci amma ba dai Nafisatu ba jinin bare-bari."


Runtse ido ya yi yana jan addu'ar samun nutsuwar zuciya saboda kada ta tunzirashi ya aikata abinda zai damesa, musanman kalman dadiro da ta ambata 


"Abban Hafiz yau fa sai ka zab'a ni ko d'iyar makwafta domin nagaji da hak'uri akan cin kashin da kakeyimin akanta, wallahi yau sai ka sanarmin da hakikanin alak'ar dake tsakaninku."


"Fine, kina son sani ko?"


Ya furta cikin wata murya mai kaushi daga ji ranta ya kai k'ololuwar b'aci.


"Eh."


"Iyali ta ce."


"Me!?"


"Ban hanya in wuce ko in aikata abinda ba zaiyi mana dad'i ba duk kanmu."


Fad'awa kujera ta yi jikinta na rawa saboda yarda ta hango komi na iya faruwa idan har bata kauce ba.


"Na shiga uku ni Nafisa d'iyar Boka ta gama min da miji, shi da ke rarrashinna idan na tubure masa irin haka yau shi ne ya komamin horror, Allah ya isa tsakanina da ke Deejah wallahi sai na koya miki hankali, saina b'ata miki fuskan nan mai kama da ta aljannu inga ta inda zaki kuma d'aukan hankalin mijina."


"Aikata hakan dai-dai ya ke da yanke alak'ar aurenmu da ke na har abada sannan ko da habaici kika tozarta min Khadijay ban yafe miki ba."


Yana ambatar haka ya haye sama ranta tamkar wuta, yunwarma da yakeji nemarta ya yi ya rasa, sai bugawa zuciyarsa keyi da k'arfi.


"Hak'ik'a Aurenki shi ne kaddarata Nafisa, ya Allah ka bani ikon cinye jarabawan nan ka kuma yimin dacen samun mace ta gari mai kwantarmin da hankali ko da ba wacce raina ke burin mallaka ba ce."


Hawaye ne masu dumi suka zubo masa burinsa ya jiyo muryan Deejah wannan dalilin ya sa ya kirata da number da bata san shi da shi ba tana d'auka ya datse kiran. Abin mamaki yana jin sallamarta cikin taushi ya sami kansa cikin nutsuwar ruhi, hamdala ya yi tare da cigaba da ambatar sunar Allah AL-GAFURU. A haka yana zaune saman kujera barci ya soma kamasa sai kawai ya gyara kwanciya.


***

Kiran sallar asalatu ya farkar da ni na sauka a hankali na ji Mama ta rik'eni da sauri na kalleta ta sakarmin murmushi a hanzarce na koma jikinta na rungumeta k'am-k'am ina dariyar murna.


"Uwata Allah ya yi miki albarka mara iyaka, Allah ya inganta rayuwarki, Allah ya rabaki da ganin tijarar rayuwa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa."


"Amin ya rabbi Mamana."


"Tafi kiyi nafila idan kin sallaci subahi sai ki taimakamin inyi wanka."


"To Mamana."


Ina idar da sallah aka kwan-kwasa k'ofa, na bud'e cikin jin faduwar gaba, Baba ne tsaye fuskan nan kamar an aiko masa da sak'on mutuwa. Russunawa na yi na gaisar da shi ya amsa a dak'ile na maida k'ofar na kulle na koma saman sallaya na cigaba da jan carbi amma hankalina na kan su Baba wanda na fahimci Mama bata so ganinsa domin yana ta kiran sunarta tak'i amsawa, ta yi kamar mai nisan barci alhalin ganin shi yasa ta koma kwance.


"Ke! Uwani tun jiya bata farka ba ne?"


"Ta farka."


"Da yaushe?"


"Tsakiyar dare."


"Alluran hutun suka sa ke yi Mata ko me?"


"Magani dai suka bata inaga shi ne ya kuma sakata nauyin barci."


"Me suka ce na damunta?"


"Hawan jini."


"Kin gani ba, ai dama na sanar mata indai tana tare da ke sai ta gamu da ciwon zuciya bama hawan jini ba."


"A'uzubillahi! Baba ni d'in?"


"A'uzubillahi akanki shegiya mai bakin jini gayyar ta zu...


Tarin da Mama ta sark'e da shi yasa Baba dakatawa da yimin tijara. A guje na hau gadon na kamota ina kiran sunarta bata amsa ba amma ta daina tarin. Kallon Baba na yi ya zabgomin harara kwantar da ita na yi na sauka na fice zuwa kiran Likita. Tare muka dawo da Likita tare da nurses biyu, cewa sukayi mu basu wuri, muka fito ni da Baba sai zagina ya keyi zuwa can ya koma kam Uncle na antayo masa zagi tamkar ba malamin ilimi ba.


"Alla wannan munafukin Alhaji Muhseen ya ke ko wa, k'ara zan shigar da shi akan shigamin safgar iyali kai tsaye batare da neman izinina ba, duk kudinsa idan na saka masa ido wallahi sai ya koma mai gyaran talkalmi ya fisa arziki, muzuba mu gani shege ka fasa ba dai aurenki ya ke son yi ba, Uhm."


Nidai kai na juya gefe ina saurarensa hakalina na ga halin da Mamana ke ciki.


Ban aune ba na ji an zabgamin carbi a kai na kwalla ihu wasu nurses suka taho wurin a guje ganinsu Baba ya bar wurin tamkar bashi ya aita dukan ba.


"Kiyi hak'uri Mamanki zata sami lafiya kinji."


Motsa kai ba yi domin d'aukansu halin da Mama ke ciki ne ya sanyani ihu, su suka kamani na zauna saman bencin da Baba ya tashi sai bani baki sukeyi, muna a haka Likita ya fito tare da nurses ya dubeni ya ce "Ina Babanki?"


"Ya tafi ya dawo."


"Ok shiga tana son ganinki amma ki kula kada ki yarda maganar bacin rai shiga tsakaninku saboda zuciyarta na daf da samun matsala."


'Shi kenan bakin Baba zai tabbata.'


"Tana son hira mai sanya nishad'i dan haka ki lula sosai."


Maganar Likita ya dawo dani tunanina.


"To." 


Na amsa cikin rawar murya.


Ina shiga Mama ta d'agomin hannu na isa da sauri na kama.


"Malam ya tafi ko?"


"Eh."


"Kin sanarwa da Baba Umaru kuwa?"


"A'a."


"Maza kiramin shi."


"To."


Na tafi in d'auko wayar inda na barta jiya babu ita ba sanmatarta, shiru na yi ina nazarin inda na jefata.


"Uwata." 


Mama ta kirani cikin wata murya mai kama da ta yara masu tsamin baki. Da hanzari ya juyo wurin batare da na amsa ba sai dai abinda na yi arba da shi ya kusa sanya zuciyata bugawa.


Mama ce ke d'agomin hannu cikin son furta kalma tamkar ba yanzu ta kirani da muryan yara ba. Kallon yarda bakinta ya koma gefe na ke yi jikina na rawa, ga wani irin jijjiga da ta soma ruwan kumfa na fitowa daga bakin tamkar wacce taci guba.


"K'alu innalillahi wa Inna ilaihin!."


Kalmar da na ambata kenan da k'arfi ina mai nufar Mama da wani irin k'arfi na cukumeta ina zabga ihun kiran Likita da muryana wacce ta soma dawowa hayyacinta daga dushewa, nurses suka shigo a guje wanda na ke zaton dama suna hanyar zuwa d'akin ne saboda muna da tazara da inda suke. Cikin dibara sukayi nasarar rabani da jikin Mama. Na juya musu baya ina wani irin kuka wanda na ke jin zafin fitarsa har cikin tsokar naman zuciyata.


"Mama kada ki tafi ki barni wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, in kika tafi zan biki ne a birnemu tare, wayyo Allah rayuwata!. Hasbunallahu wal ni'imal wa kil!, La'ilaha illa anta subbahanaka inni kuntu minal zalimin!."


Na zame k'asa na zauna dirsha ina cigaba da mai-maita addu'o'in cikin k'araji. Saukan hannu naji a saman kafad'ana yasa na tsaya tsak tare da kallon wanda ya dafanin, zubawa Likitan ido na yi wanda ban san sadda ya shigo ba.


"Kiyi hak'uri duk mai rai...


Ban gama jinsa ba wani sautin dim ya sauka cikin kunnuwana abinda ya haifar da toshewarsu kuma alokaci d'aya idanuwana suka daina ganin komi, duhu ya mamayesu, ji na yi tamkar ina yawo a sararin samaniya, zuwa can naji kamar ana janyoni zuwa k'asa al'amarin da ya sanyani jin ina fizgar numfashi da k'yar kenan daga haka ban kuma sanin me ke faruwa ba.


*Zaku iya soma booking kafin zuwan k'arshen free pages, send #300 only a 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, aturo shaidan biya ta ***.*


*TALLA.*


*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*


Sabulu (molato and black soap)

Scrub

Face cream

Oil

Body lotion

Shower gel

Kulachan

Humra (White and black)

Turaren tsugunon

Turaren kaya

Turaren wuta na d'aki

Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)


*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in *** ko ***. Sai munjiku.*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.