Free chapter · Read without an account

Episode 6

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · AZIZAN BABA

Agogon ya duba sha ɗaya da mintina ya ajiye wayar ya kwanta yana tunanin ko yau she zai samu nasarar shawo kan Baba.


Da asuba Daddy ya duba ɗakin AZEEZ samu yayi idonsa biyu, ganin Daddy ya sa AZEEZ gaishe da shi, "barka da asuba"

Daddy ya ce " ya jikin naka?" AZEEZ ya ce" da sauƙi" 

"Allah ya ƙara lafiya, ka kintsa dan tafiyar safe zamuyi" AZEEZ ya ce"to Daddy" ja masa ƙofar yayi ya nufi ɗakin Mami,ita ma ta tashi dan sanin halin Daddy haka kamar gaske,amma muddin aka taɓo shi anan ake gane shi ɗin jinin BABA ne.


"ku shirya da wuri zamu tafi" Mami ta ce" da wa zaku je, kasan dai yau E.D.D ɗin Kausar zai cika, a gabanka Hajiya ta ce in kula da ita, yanzu kuma ka ce da ni zaku je, ba zai yuyu ba wallahi" Daddy ya ce "okay yau ne ko na manta ne to Allah ya raba lafiya a shirya mana breakfast early in the morning" ya juya.

Mami ta ce" kai ka sani haka kawai inje sanyi ya kamani a wannan jejin na su" ta cire hijab ta koma baccinta.


Siyama da Maryam da Mannir kuwa tun dare suka haɗa kayansu suna ta ɗauki.


AZEEZ kuwa kamar ya mutu ko baccin kasa komawa yayi tsaki kawai ya ke yi. Har takwas bai da niyyar ta shi ya shirya.

Daddy ne ya fito cikin shirin tafiya, shadda milk ya sa, babu wanda zai ce ya na da saurayin yaro kamar AZEEZ, su Mannir ne suka fito a shirye hakama Siyama da preety.



"Good morning daddy" Siyama ta gaishe shi, hannu ya ɗaga musu, yana cin tuwon acca miyar egusi wacce ta wadatu da naman kaza, black tea ya sha wanda aka haɗa shi da girfa da na'a-na'a. 

"ina yayanku ko sai mun zauna jiransa?" Pretty ce ta ce" bari in kira shi" ta yunƙura zata ta shi, Mami ta ce"shi fa ba lafiya ce da shi ba,yana kwance mai zai hana a haƙura da zuwan nan da shi?" 

Daddy ya ce " kira min shi"pretty ta nufi sama.



Yana inda yake ko tashi bai yi ba, pretty ta turo ƙofar "yaya ka fito inji daddy".

 "Bar nan dan uwarki, munafukar banza"pretty ta juya da sauri, ta koma, tashi AZEEZ yayi ya faɗa toilet, wankansa yana ɗaukar lokaci sosai, sai yafi minti hamsin bai fito ba.


Pretty ta koma ta ce "ya ce gashi nan zuwa" ta nufi cikin parlour wajen su Mannir.

Tun Daddy na kallon stairs dan ganin fitowar AZEEZ har yagaji ya ce" wai me yakeyi ne har yanzu?" Mami ta ce"ai kasan dai ba lafiya ce da shi ba Alhaji bari in gani,Allah ya sa ba jikin ba ne"

Daddy ya ce" wallahi ko zai mutu sai munje idan ya so, ayi jana'izarsa acan" abun ya yi mugun ɓatawa Mami rai.


Ƙamshin turaren AZEEZ ne ya ziyarci hancinsu, shima sanye yake cikin yadi black kansa ɗauke da black ɗin dara, sandal baƙi ya sa hakama agogon hannunsa.


Ba ƙaramin kyau yayi ba, ko zama break ɗin bai yi ba, ya durƙusa ya kuma gaishe da daddy, bala'in ladabi ne da shi, a gaban daddy.


Ku tashi mu je, " haba Alhaji bai yi breakfast ba, kuma Katsina ba nan ba bama can ba shiga Dauran ma aiki ne bare garin Alhaji ko dai an turaroka ne akan zuwa garin nan?" cikin faɗa Daddy ya ce " banason zancen banza Hadiza" ya fita daga parlour'n hakama su Mannir suka ce " Mami sai mun dawo, me za'a tawo miki da shi?" 

Mami ta ce" a'a ni babu abinda nake buƙata, Allah ya kiyaye hanya" 

Har zata koma sama ta fasa,ta ce" bai kamata in nuna rashin kulawa ba, ta bi bayansu da sauri dan yi musu a dawo lafiya, Daddy da AZEEZ da Siyama da Pretty  ne a back seat Mannir ne a front sit sai driver.


Da sauri Mami ta ƙaraso ta ce " Allah ya tsare idan kun isa ku kira ni, a gaishe su da kyau, tafiyarce babu shiri ban sai musu komai ba" Sosai Daddy ya ji daɗi, ya ce" babu komai zasu ji insha Allahu" hannu ta ɗaga musu bye, suma suka yi mata bye-bye.

Addu'ar tafiya sukayi suka ɗau hanya.



AZEEZ baya um baya um-um kawai duba group ɗin su yake, bayason yayi wani abu wanda zai sa daddy yayi faɗa.

tafiyar 2hour su kayi, suka isa garin Mazoji.



MAZOJI


Da sassafe AZIZAN BABA ta tashi, da ke akwai boko,Inna Gaji ce ta fito ganin AZIZA ta na tsakar gida ta na shafa mai, baƙi ƙirin da ita, dan jiya  batayi wanka ba.


"Ke meye haka kike yi?" AZIZA ta ce "makaranta zanje, dan na zama ƴar karota Gwaggo ta ce, sai da karatu ake iya cika buri a rayuwa" Inna ta ce" akwai ruwa a flask ɗauko ki yi wanka, kafin na gama abin karin" AZIZAN BABA ta cuno baki ta ce" sai na dawo zanyi, haba Inna baki gani sanyi akeyi" Baba Tabawa ce ta fito ta ce" Yaya ina kwana?" Inna Gaji ta amsa tana tambayar ya ta tashi, ta amsa da lafiya kalau, ta ce "ina ruwan yake?" Inna Gaji ta ce "kina shiga rumfa za ki ganshi" 

Baba Tabawa ta shiga ɗakin Inna ta ɗauko flask ɗin, aikuwa AZIZA sanin wankan dole Baba zatayi mata, ta hau matse kwalla, Ina Gaji ta ce" me za'a dafa miki kafin ki tafi dan ni yau ƙosai zan yi da koko" AZIZAN BABA ta ce "kut koko wallahi bazan sha ba, ƙwai da shinkafa zanci irin na gidan Kawun burni" Baba Tabawa ta sirka ruwa suna tsaye ta nufi AZIZA dan kamota.

Inna Gaji ta ce" to bai aiko da kwan ba, kuma bazan dafa shinkafa da sassafen nan ba, ni banason almubazzaranci" duk abin nan da suke BABA yana masallaci, suna tare da dattijan unguwar dan su ba su zama wasu suna gona wasu kasuwa, shi kaɗai ne Aminu (Daddy) ya hanashi zuwa gona, ya ɗaukar masa ma'aikata. 

To sunfi haɗuwa da safe suyi hira zuwa takwas sai ya koma gida.


Baba Tabawa ta kamo AZIZA ta na faɗin "idan kin dawo zamu tafi suna tare" AZIZA ta ce "ni na fasa zuwa, ba na son wanka Baba" sai hawaye sharrr.


Baba Tabawa ta ce " au ba za ki je ba kenan, to ai kin yi wa kanki" da tsiya akayi wankan, wankakken uniform blue ta ɗauko a ɗakinta dan duk yawancin kayan AZIZA yana ɗakin Baba Tabawa.


Dan kowanne ɗaki kwana take, sai ta fara bacci anan cikin dare ta koma can.

Tsaf ta shiryata sai kyan AZIZA ya fito ta sha farin hijab ɗinta.

Inna da ta ajiye waken ta soyawa AZIZA irish ta zubo mata a plate da koko ta ce " zo ki karya" AZIZA na ganin da gaske ba shinkafar da ta ce ba ce, ta sa ihu, haɗi da ture dankalin kokon ne ya zube, ran Inna ne ya ɓaci, cikin fushi ta wankawa AZIZA mari tass, " abun naki har ya kai haka, in yi miki abin kirki ki zubar" AZIZA da marin ya shigeta gigicewa ta yi, ta fasa uban ihu,  

Tun daga waje BABA ya jiyo ta, a ruɗe ya shiga yana faɗin " innalillahi yau ba sa'a an sa marainiya kuka" 

Jiyo faɗan Inna Gaji ya ji, nan da nan ya ji ɓacin rai, Aguje AZIZA ta nufo BABA tana faɗawa jikinsa, cikin kuka na fitar hankali.


"Ni zakiyi wa shashanci, in ajiye komai dan ki ci ki zubar bazan ɗauki iskanci ba" BABA ya kalli yanda AZIZA take kuka ya ɗago fuskarta dan ya rarrasheta shatin hannu ya gani a fuskarta, cike da mamaki ya ce "waye ya bige ta?"

Inna ta ce "ni ce nan Malam"

"Sa'adatu. Kinsan hukuncin azabtar da maraya, zamu bar miki gidan, daman ba tun yanzu ba na gane baki kula da AZIZA ga shi nema kike ki kashe min jika" Baba Tabawa ta ce " kayya Malam ba haka ba ne kayan kari aka kawo mata, ta zubar da gangan" 

Baba ya hau faɗa, "waye baya kuskure, iye waye ba ya ɓari, wannan abun da kukayi shi ya ƙara tabbatar min da ba za ku iya riƙe marainiyar Allah ba, yau zamu bar muku gidan"

Nan fa hankalin tsofaffin ya tashi, ganin BABA ya kama hannun AZIZA sun fita.

 Tafiya suke dan neman mafita, AZIZA da ta ke ta faman sauke ajiyar zuciya ta hango makarantarsu yara suna ta shiga, tsayawa tayi ta ce" ni makaranta zanje" BABA ya ce"makarantar me ni fa daman ba son bokoko a wutan nan nake ba, Aminu ne ya dage sai kin zama irinsa nasara, asarar duniya, ki bari mu je wajen Inusa dillali ya samo min gida ko da hayane sai mu zauna ni kaɗai zan iya kulawa da ke"

AZIZA ta girgiza kai  tana faɗin "ni bazan bar Baba Tabawa ba, ka ba ni kuɗin makaranta in tafi" ganin ta kafe BABA ya ciro naira ɗari ya ba ta ya na faɗin " to mu je in rakaki" har ƙofar gidan ya rakata, dan makarantar gida ne, ita ce ta kuɗin da Aminu ya sa akaita(private) har ciki BABA ya raka AZIZA, wacce fuskarta tayi jajir, saboda kukan da tayi.


Headmaster na zaune ya hango shigowar AZIZAN BABA, sanin halinta ya sa ya zargi ko wani abun ne ya faru ta sa BABA zuwa.

Daga office yake hango AZIZA na yi wa BABA bye-bye ta juya ta shige class ɗinsu primary 4.


Ƴan class ɗinsu da suka sake kwana biyu, suna ganinta kowa ya shiga hankalinsa dan har monitor ɗin tsoron masifarta suke, ganin yau ba hura hanci ko ɗagawa, ya sa suka yi tunanin ko dukanta akayi aka korota, ƙawarta Fadila wacce halinsu ya zo ɗaya ta kalleta ta ce" baki da lafiya ne?" AZIZAN BABA ta girgiza kai ta ce "Inna ce ta dake ni, dan na zubar mata da koko" cikin mamaki Fadila ta ce "ita Innar da kanta?" AZIZA ta ce " ai bar mata gidan ma zamuyi ita kaɗai, dan ba zan zauna da ita ba, Baba Tabawa tafi so na" Fadila ta ce" Allah sarki, ki yi haƙuri kawai dan anga Babanki ya mutu ne" AZIZA ta ce "ke ai nasani" suna tsaka da hira Malamin Agric science ya shigo.

 Gaba ɗaya aka tashi tsaye dan gaishe da Malam. 

Rubutu ya fara yi musu sannan ya juyo ya ce " our last period discuss about balance diet, who can tell me the meaning of balance diet?" tsit ajin yayi AZIZAN BABA da take wasa da jelar rigarta, ta yi shiru ta na tunani, washe baki tayi ta na ɗaga hannu.


"Okay stand-up" Malam ya faɗa yana harɗe hannu.

AZIZAN BABA ta fara bayani " A balance diet is a meal that contains all the essential food subtances in the right proportion"

Malam ya ce "clap for her" gaba ɗaya a hau tafi AZIZAN BABA sai ta manta da abinda Inna tayi mata ta saki ranta, har malam ya gama yi musu revision ɗinsa AZIZA ta na participating sosai. 

Dan akwaita da kwanya nan da nan tayi catching abu.


Break aka fito anan ne cikinta ya fara kiran yunwa, danasani ta shiga yi, na zubar da kokon da ta yi, ga dankalin ya soyu yawu ta haɗiya na kwaɗayi, wajen break ɗin suka nufa, duk abinda ta gani sai ta ji batason siya, ƙanƙara ta siya har guda biyar ta hamsin sai ta sai agwaluma ta ashirin, magwaro na talatin da ke ƙauye ne sai ta tara kayan dayawa a gabanta ita da su Fadila su ka sha, duk ta raba musu. 

Ƙanƙarar ta ɗauki biyu ta bar musu uku su raba.

ana komawa class AZIZA ta fara wani irin tari.



Gida BABA ya koma ya dinga sirfa bala'i Inna sai haƙuri ta ke bayarwa jin wai AZIZA makaranta ta tafi ba ta ci komai ba, hakan ya sa duk suka kasa nutsuwa, Inna Gaji ta dafa shinkafar da AZIZA take so, ko tsayawa ta karya bata yi ba, shago ta je ta siyo kwai guda uku, dan nasu ya ƙare kuma BABA bai sanarwa da Aminu ba.

Dafa shi tayi ta zuba a kwano ta nufi makarantar su AZIZA, sun koma kenan ta isa.


Babu mai gadi a school ɗin kai kawai Inna ta sa, da Malama ta haɗu,suka gaisa nan take ce mata, ta zo wajen AZIZA ne, malamar ta ce" AZIZA ABDUL-AZEEZ?" Inna ta ce "eh ita fa" ajin ta nuna mata ta yi gaba.


AZIZA na ta faman tari, Inna ta shiga ajin, da sauri ta nufeta ta na riƙeta, "sannu kinji, yunwa ce ta kamaki, ga shinkafar zo ki ci" 

AZIZA ta girgiza kai, alamar a'a.

Tarin ne ya taso mata, sai amai.


Inna duk ta ruɗe, sai nadamar dukanta da tayi take, ba'a tashi ba ta ɗauki AZIZA su ka tafi, sai ce wa take "kiyi haƙuri tsautsayi ne ya sa na dake ki, ga shi na janyo miki rashin lafiya" 


Tun daga nesa suka hango, mota a ƙofar gidansu da alamar baƙi sukayi.

AZIZA ta ce "yeeee Baban burni ya zo, wallahi Inna bazan zauna a nan gidan ba, tunda kika dake ni.............





Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.