Free chapter · Read without an account

10

by Hauwa A Usman · RABO AJALI..

_*RABO AJALI...!*_



*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_



'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''



_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_



*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*


_DEDICATED TO_ 

*AISHA ALIYU GARKUWA*



1⃣0⃣



Dai-dai lokacin da aka shafa fatihar D'AURIN AUREN NEEHAL DA NEELAH, 

Najwah ta farka a firgice daga bacci had'i da kurma uban ihuuuu, 

cikin tsantsar tashin hankali ta duro daga kan tamfatsetsen gadon da take kwance, 

ta zube k'asa batare data kula da fad'uwar datayi ba ta mik'e zambur, 

ta nufi k'ofar fita daga bedroom d'inta while tana cigaba da ihuuuun cike da tsoro jikinta nata kerrrrrma yana b'ari, 

kacib'us sukayi da Mamah (mahaifiyarta) wacce ta nufo d'akin jikinta na rawa sakamakon jin ihuuuun Najwah!, 

ganin Najwah bata kula da ita ba tana k'ok'arin fita yasata saurin rik'ota, 

had'i da cewa " ke lafiyarki kuwa....!? 


Bakin Najwah na rawa ta fara k'ok'arin yin magana had'i da yin nuni da hannunta zuwa saman bed, 

kallan gadon Mamah tayi taga bakomai kana ta mayar da kallanta ga Najwah, 

ta kuma tambayarta a karo na biyu, 

" lafiya! meke faruwa dake....!? 


Cikin kerrrrrma Najwah tace " Mamah Nee....Nee.... ha...l, tayi maganar a rarrabe, 

ido Mamah ta zaro waje cikin rashin hankali tace " meya same shi, wani abun ne ya same shi....!? 


Ta jerawa Najwah tambayar a lokaci d'aya, cike da tsoro, 

still kasa magana Najwah tayi, illa Neehal!.... Neehal...! datake ta faman fad'a, 

gumi ya jik'ata sharkaf duk da sanyin AC dake d'akin,

ganin yanayin da Najwah ke ciki yasa gaban Mamah ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku, 

dan a zatonta wani mugun abun ne ya samu Neehal, 

cikin tsawa Mamah tace " wai dan ubanki bazaki fad'a min abinda ya samu Neehal d'in ba...!? 


Bakin Najwah na rawa tace " ma.. far.... ki na... yi..., 

tsoki Mamah taja had'i da cewa " aikin banza kawai, 

tayi maganar tana k'ok'arin fita da sauri Najwah ta rik'eta gami da sanya kuka, 

tana cewa " wallahi Mamah mummunan mafarki nayi akanshi,

kuma kinga tunda ya tafi fa bai kira ni ko sau d'aya ba, 

k'uluwa Mamah tayi sosai dan kwata-kwata ta tsani halayen Najwah, 

" dalla can ni gafara ki bani waje, mara kunya kawai, dan mijinki ya tafi kwana d'aya bai kira ki ba shine kike wannan abun...!? 


"Banza sakarya mara wayo, kwana d'aya kawai da tafiyar miji, shine kike hauka....!? 


Tayi maganar a zafafe, jin abinda Mamah tace yasa Najwah k'ara marairaicewa tare da k'ara sautin kukanta sosai, 

ta kuma rik'e Mamah gam "please Mamah ki fahimce ni mana, ba yadda za'ayi Neehal yana lafiya, 

ya tafi harya kwana wani daren ya k'ara yi batare daya kira ni koya kira wani ba, 

yadda Najwah tayi maganar yasa jikin Mamah yin sanyi ta d'an yi shiru tana tunani, 

Najwah ta cigaba da magana " kuma haka nan naji gaba na na fad'uwa, jiki na yana bani tabbacin wani mummunan abu yana shirin faruwa dani koma ya faru, 

jiki na yana bani kamar yana tare da wata mace, tayi maganar cikin sanyi tana kallan tails while bata bar kukan ba, 

d'a da mahaifi sai Allah, take Mamah taji tausayin Najwah ya kamata, a hankali ta d'ora hannunta saman kafad'arta, 

kana ta soma magana cikin sanyi, 

" kiyi addu'a dan itace maganin komai da duk wata masifar dake tunkaro mutum, 

walau ya sani walau bai sani ba, ki kuma kasance mai kyautatawa mijinki zato a koda yaushe, 

Najwah zatayi magana Mamah tayi sauri cewa " no! jeki yi alwala kiyi sallah ki sanar da mahaliccinki, majib'ancin lamuran mu, mai yaye mana k'unci da damuwarmu matsalarki, 

cikin sanyin jiki Najwah ta d'aga kai, Mamah ta shafa kanta had'i dayi mata murmushi tace " good girl, kana ta fita, 

maimakon Najwah ta shiga bathroom tayi alwala kamar yadda mahaifiyarta ta sanya ta, 

sai ta koma saman bed ta zauna tana sharar hawaye had'i da sak'a da warwara.


******************


A b'angaren Neehal kuwa ana shafa fatihar d'auren auren shi da yarinyar da ko sunanta bai sani ba, 

saboda tsabar tashin hankali ko da aka ambaci sunnanta yayinda ake d'aura auren rud'ani bai barshi yaji sunan ba balle ya fahimta, 

a hankali ya lumshe idanshi hawaye na gangarowa daga idanshi, wanda shi kanshi bazai iya tantance dalilin zubarsu ba,

shin hawayen farin cikin ya tsira da rayuwarshi ne, 

kona bak'in cikin auren daya k'ara bayan yayiwa annurin ranshi alk'awarin bazai tab'a yi mata kishiya ba, yafi a irga, 

ko kuma hawayen tausayin Najwah ne ....!? 


Ya tambayi kanshi cikin ranshi, 

Malam Liman ya kalli Neehal dake faman zubar hawaye kamar mace, 

cike da tausayin kanshi, dana tilon 'yarshi dana kuma Neehal, 

wanda ya tabbatar auren dole akayi mishi, dan yasan idan da abinda Neehal yafi tsana a rayuwarshi bai wuce wannan auren ba, 

ya tabbatar ba k'aramin abu ne zai sanya namiji kamar Neehal mai kafaffiya zuciya da taurin kai kuka ba, 

duk da ya hango k'uruciya k'arara cikin kwayar idonshi, 

ajiyar zuciya Malam Liman yayi a fili tare da d'ora hannunshi saman na Neehal, 

a hankali ya bud'e idanshi gami da d'ago kanshi ya kalli Malam Liman , 

Malam Liman yace " tashi muje, ba musu Neehal ya mik'e suka bar wajen still hannunshi cikin na Malam Liman, 

har sunyi nesa Malam Liman ya kwalawa wasu matasan masari su uku kira, 

suna tafe samarin na bin su a baya babu wanda yace k'ala,  

har suka isa bakin bukkar da mai gari ya bawa Neehal kana ya kalli matasan yace " wannan bukkar tayi mishi k'ank'anta kasancewar yana da kaya da yawa, 

dan haka kuyi mishi wata babba mai fad'i sosai, 

cikin girmamawa suka amsa da to, 

bayan Malam Liman ya gama da samarin ya juya ya kalli Neehal, 

ya zuba mishi ido batare daya ce komai ba, ganin haka yasa Neehal cewa " ina san shiga ban d'aki, 

cikin rashin fahimta Malam Liman yace " meye kuma ban d'aki....!? 


Shiru Neehal yayi batare daya san abinda zaice mishi ba, 

kana yace " ina san zan d'an zaga ne, 

still Malam Liman bai fahimci Neehal ba, 

Neehal yace " ina san na kewaye, ina nufin makewayi, inda zan tsuguna, 

" au! to! to! ai ban fahimta bane, kasan Hausar ba isar mu tayi ba, 

sunkuyar da kai Neehal yayi batare daya ce komai ba, d'aya daga cikin samarin Malam Liman ya kira, 

yace " raka shi inda zai tsugunna, "to! , saurayin yace kana ya kalli Neehal yace " muje ko!, 

batare da yayi magana ba yabi bayan saurayin, Malam Liman yabi bayan shi da kallo, 

zagayawa sukayi bayan bukka saurayin yace " tsugunna nan, 

ko muyi gaba....!? 


Filin Allah fetal Neehal ya kalla, ya kalli saurayin yana zaro ido yace " anan zan tsugunna!? 


"Eh!, 

Neehal yace " kaga fa fili ne cikin gonaki babu abinda zai tare ni koya kare ni, babu abin sakayawa a haka kake nufin na tsugunna!? 


Saurayin yayi murmushi yace " ai haka muke yi, idan mutum zayyi kashi ko fitsari cikin gona muke yi, 

idan kuma wanka ne sai mu tafi rafi, mu bamu da ban d'aki kamar ku birni mu ko'ina tsugunnawa muke yi mu biya buk'atar mu, 

a fili Neehal ya sauke numfashi gami da cewa " gaskiya bazan iya ba, 

saurayin zayyi magana Neehal ya juya ya koma inda Malam Liman ke zaune, 

saurayin na biye dashi, Malam Liman yace " kun dawo....!? 


Neehal yayi shiru kanshi k'asa, saurayin yayiwa Malam Liman bayanin yadda sukayi da Neehal, 

d'an shiru Malam Liman yayi kana yace " idan a matse kake kaje kayi kafin nasan abin yi, 

" a'a ba damuwa, Neehal yace, 

shiru Malam Liman ya kuma yi kafin ya kalli saurayin nan yace " wacce bukkar dana ce muku tayi mishi k'ank'anta, 

ku bar mishi ita mazaunin makewayin, 

idan kun tashi yi mishi babbar sai kuyi mishi ita gaf da k'aramar, 

kusa da kusa yadda ko cikin dare yake da lalura zai iya shiga, 

da taimakon Malam Liman akayiwa Neehal bukka mai kyau wacce kota mai garin bata kaita kyauta ba, mai girma sosai da yalwa, 

cikin samarin wani ya koya musu yadda ake yin masan tsugunno akayi mishi,

cikin ban d'akin kana suka taya shi ya shinfid'a carpet ya sanka babbar katifarshi ciki,, 

suka shirya kayan tsaf bukkar tayi kyau sosai abin sha'awa,  

tayi kamar d'aki kasancewar akwai kome da kome, dayake bukkar nada girma sosai a cikinta daga gefe yayi kitchen, 

ya shirya kayan abinci dana girki a gefe d'aya, d'ayan gefen kuma ya shirya kayanshi, 

it look like bedroom & kitchen, sai da aka gama shirya komai kana ya kalli Malam Liman yace " ina ake d'ebo ruwa ina san nayi wanka...!?


"A rafi muke wanka amma bari nasa aje gida a d'auko maka jarka sai a d'ebo maka ruwa ciki in yaso sai kayi wankan, 

Neehal yace " ai ina da botiki bari na d'auko sai su raka ni na d'ebo ruwan, 

" a'a kabar botikinka sai ka rink'a zuba ruwan sha, jarkar kuma sai ka barta a ban d'akin, 

" nagode...! Neehal yace a tak'aice, Malam Liman bai kula da godiyar da Neehal keyi mishi ba, 

ya mayar da hankalinshi ga samarin yana basu umarnin suje gidanshi su d'auki jarkoki biyu, 

suje rafi su ciko da ruwa kana su kawo, 

bayan samarin sun bar wajen Malam Liman ya mayar da hankalinshi ga Neehal,

yace " ni zan koma gida saboda shirye-shiryen kawo maka matarka, 

kayi wankan sai ka huta zuwa dare za'a kawo maka matarka, 

" to nagode sosai, Neehal ya fad'a kanshi k'asa, batare da Malam Liman yayi magana ba yabar wajen, 

Neehal ya koma cikin bukkarshi ya zauna gefen katifa yana tunaninnika kala-kala, 

samarin basu jima ba suka dawo kowannen su d'auke da jarkar ruwa guda, 

cikin bukkar dake mazaunin ban d'aki suka aje kana suka sanar da Neehal sun kawo ruwan, 

cikin sanyin jiki da murya Neehal yayi musu godiya sosai, 

kana ya d'ibi kayan da zai saka ya shiga yayi wanka had'i da d'auro alwala, 

jallabiya da gajeren wando kawai ya zura ya gabatar da salla, ya jima kan sallaya yana kuka tare da jera addu'a, 

kan auren da yayi da Najwah yana kan sallayar ya fara jiyo gud'a tana nufo bukkarshi,

hakan ne ya tabbatar nishi da 'yan kawo amarya ne suka iso, 

sosai gaban shi ya tsananta fad'uwa, cikin nutsuwa ya mik'e gami da ninke sallayar ya aje gefe, 

ya koma gefen shima daga k'asan carpet ya zauna, 

daga bakin k'ofa ya jiyo sallamar 'yan kawo amarya wanda ya saka gabanshi gigitaccen fad'uwa, 

k'irjinshi yayi mahaukaciyar bugawa da tsananin k'arfin gaske, 

bakinshi na rawa ya amsa musu had'i da basu izinin shiga, 

matan da suka zo kawo Neelah bazasu wuce goma ba, dukkansu suka shiga cikin bukkar, 

dan ganewa idansu abinda matasan samarin nan suke fad'a, 

dan tuni suka kai labarin had'uwa da tsuruwar bukkar dan tunda suke basu tab'a ganin wasu abubuwan ba, 

sai a wajen Neehal, k'asan carpet suka zauna tare da zaunar da Neelah itama, 

matan suka shiga kalle-kalle suna al'ajabi, 

har suka manta da abinda ya kawo su, suka shiga magana k'asa-k'asa, 

baki ya tab'e yana binsu da kallo ganin yadda suka shagala suna kallan bukkar, 

da ganinsu ba sai ka tambaya ba kasan topical k'auyewa ne na bugawa a jarida, 

ganin yadda suka cika mishi d'aki ga wani bashi-bashin wari na tashi, 

tunda ba turare suka sani ba, yasa shi yin gyaran murya cike da kyama yana binsu da kallo, 

tamkar yaga kashi,

gyaran muryar da yayi ne ya dawo da hankalin wasu daga cikin su gare shi, 

wata mace daga cikin matan tayi murmushin yak'e had'i da cewa " ga yar mu nan mun baka ita amana, 

ka dubi Allah da manzonshi ka rik'e mana ita bisa gaskiya da amana dan Allah, 

kana ta juya ga Neelah dake tsugunne kanta rufe da mayafi, 

tace " nasan halinki sarai Neelah da rashin ji da rashin kunya da fitsara, 

ki sani wannan ba namiji bane kamar kowa, ba namiji bane kamar kowanne namiji ba, 

wannan namijin a hannunshi rayuwarki ta duniya da lahira take, 

dan haka kema ina rok'anki da kiji tsoran Allah kiyi mishi biyayya, 

kai Neelah ta d'aga batare da tayi magana ba, wata mata daga cikinsu kuma ta cafke ta d'ora daga inda d'ayar ta tsaya, 

sosai akayi musu nasiha duk da ba wani ilimin addini ne da mutanan k'auyen ba, 

d'an shiru kowa yayi d'akin yayi tsit kowa yayi jugum suna ta kalle-kalle, 

gyaran muryar Neehal ya kuma yi a karo na biyu dan ya fahimci basu da niyyar tafiya, 

da sauri suka mik'e had'i dayi musu sallama suka fita, 

suna fita yaja uban tsoki had'i da cewa " useless villagers, 

kana ya juya da niyyar kwanciyya, daga bakin k'ofar ya kuma jin anyi sallama, 

jin muryar Malam Liman yasa shi saurin mik'ewa gami da amsa sallamar, 

an d'an jima kafin Malam Liman ya shigo hannunshi rik'e da tray,

Cikin nutsuwa Malam Liman ya zauna daga gefen Neelah a k'asan carpet, 

tare da tankwashe k'afafunshi, ya aje tray d'in a gefe, 

cikin girmamawa Neehal ya gaida Malam Liman, 

ya amsa a mutunce, d'an shiru ne ya biyo baya na wucin gadi, 

kafin Malam Liman yayi gyaran muryar cike da kamala ya soma magana, 

" bawan Allah kaji tsoran Allah, ka tuna akwai mutuwa, kwanciyar kabari da tsayyuwa gaban Allah, 

komai zakayi ka tuna akwai Allah akwai kuma hisabi, haka mutuwa gaskiya ce, 

batare dana sanka ba, kona san daga inda ka fito ba, batare dana san asalinka, 

tushenka da nasabarka ba, asali ma ban san waye kai ba, ban san daga inda ka fito ba, 

bani da sani akan ka, halaye da d'abi'unka, ban san k'abilarka da yarenka ba, 

ban san takamaiman daga inda ka fito ba, ban san su waye iyayenka, danginka da 'yan uwanka ba, 

babu abinda na sani daga gare ka ko naka, amma na d'auki auren tilon 'yata wacce nafi so, 

fiye da komai da kowa na baka, bani da kowa a duniya face ita da mahaifiyarta, 

haka zalika suma basu da kowa face ni, ka tuna da alkhairi na, 

ka tuna da alkhairin danayi maka na ceton ranka da rayuwarka da nayi, 

ka tuna na ceci rayuwarka a sa'in da kake gaf da mutuwa, 

ka tuna dukkan mutanen garin nan kowa k'in baka 'yarshi yayi, 

amma ni na d'auka na baka, dan haka ina had'aka da girman Allah, 

da girman wanda akayi duniya da lahira dominshi, ka dubi darajar mahaliccinka ka RIK'E MIN NEELAH AMANA, 

babu abinda nake nema ko buk'ata daga gare face ka rik'e min amanar NEELAH!!!, 

idan har ka rik'e min ita amana, ka biya ni, ka kula da ita da rayuwarta, ka bata kulawa dai-dai gwargwadon iyakar iyawarka, 

ka kula da addini da tarbiyyarta, ka bata ilimi dan girma Ubangijin sammai da k'assai, 

kayi min alk'awarin zaka kular min da Neelah, kayi min alk'awarin bazaka tab'a cutar da ita ba, 

tsit..! d'akin yayi babu wanda yace k'ala, idan Malam Liman kan Neehal ya kafe shi da ido yana karantar shi, 

ganin tsayin lokacin Neehal bece komai ba, bashi kuma da niyyar cewa koman, 

yasa Malam Liman sauke numfashi gami da cewa " Allah ya sani ni dai alkhairi nayi maka, 

bana kuma tunanin zaka saka min da sharri dan da gani baka yi kama da mutanen dake saka sharri da alkhairi ba, 

ni bana buk'atar komai daga gare ka, bana san komai sai kayi min alk'awarin zaka kular min da Neelah, 

dan Allah kayi min wannan alk'awarin ko hankali da zuciya ta zasu kwanta,! 

nutsuwa ta ta dai-daita, 

a hankali Neehal ya sauke ajiyar zuciya gami da d'ago kanshi ya kalli Malam Liman, 

da sauri ya mayar da kanshi k'asa saboda had'a idon da sukayi da Malam Liman, 

yaga idanshi yayi jajir kamar gauta kwallar kuka ta cika mishi ido tana neman zubowa, 

cikin sanyin jiki gaban Neehal na fad'uwa yace " in sha Allah zanyi iya bak'in k'ok'ari na akanta, 

murmushi Malam Liman yayi kwallar data cika masa ido ta gangaro zuwa kumatunshi, 

ya sanya hannu ya goge yana murmushi yace " nagode! nagode sosai Muhammad Allah ya saka maka da alkhairi, 

kana ya juya ga Neelah dake zaune kanta k'asa, yace " nasan halinki da tsiwa da rashin kunya Neelah,

wannan da kike gani ba mutum ne kamar kowa ba, shi daban yake a rayuwarki, 

yana da matuk'ar mahimmanci fiye da kowa, kada ki sake naji ance kinyi mishi tsiwa ko rashin kunya, 

duk abinda ya saki kiyi mishi babu musu, kada ki sake kiyi mishi gardama kinji ko!? 


" To!, Neelah tace cikin sanyin murya, kallanshi ya mayar ga Neehal yace " ga abinci nan na kawo muku da fura, 

Allah ya bamu alkhairi, Ubangiji ya tashe mu lafiya, 

" amin! Neehal yace yana mik'ewa da nufin ya raka Malam, 

" kayi zamanka karka damu kaji, bayyi magana ba sai da ya raka Malam bakin k'ofa suka k'ara yin sallama, 

kana ya dawo ya zube saman foam mattress yayi rigingine idanshi na kallan sama, 

a hankali ya lumshe idonshi ya shiga tunanin duniya da rayuwa, 

yana mamaki da al'ajabin yau wai shine cikin d'akin d'aya da mace, 

kuma a matsayin matarshi ta sunna wacce ba Najwah ba, 

kanshi girgiza gami da gyara kwanciyar shi yace " lalle Allah shine ke tsarawa kowanne bawa rayuwarshi, 

babu wanda ya isa yasan gobe, balle jibi, 

babu wanda yasan k'addararshi ko abinda zai faru dashi, 

ya tuno haukan da Najwah keyi idan mace ta kalle shi kawai, 

ya tuno yadda yayi mata alk'awarin bazai tab'a yi mata kishiya ba sau da dama, 

ya tuno maganar da Nauman ya fad'a mishi, ya tuno irin shawarar da Mamynshi ke bawa Najwah, 

"Ikon Allah sai kallo, yace a fili yana fitar da numfashi, 

cikinshi daya karta k'irjinshi ya soma suya ne ya tuna mishi rabonshi da abinci tun kan ya shigo k'auyen Sunkhanni, 

a hankali ya bud'e idonshi yana tunanin abinda zaici, ya jima a haka kafin ya tuno da abincin da Malam Liman ya aje wanda ko kallan inda ya aje bayyi ba, 

kanshi ya d'ago ya kalli tray d'in, a ranshi yace " Allah dai yasa ba wannan shegen bak'in tuwon bane, 

kamar bazai tashi ba, sai kuma ya mik'e ya taka inda tray d'in yake, 

ya sanya hannu ya bud'e kwanikan, gasheshshan naman rago, 

da had'add'iyar damammiyar fura da nono ya gani, 

kama da wane bata wane, wani kayan sai amale, ganin yadda furar ta damu likui, 

taji nonon saniya ga man shanu nan kwance a sama, yayinda gashashshen naman ragon ke tururi yasa yawon Neehal tsinkewa, 

amma saboda tsabar muskilanci da bak'in hali irin na Neehal yasa shi jan tsoki, 

had'i da komawa ya kwanta, 

wai shi karya bada kanshi. 


**********************


Tun daga k'ofar d'aki Malam Liman ya soma jiyo sautin kukan mahaifiyyar Neelah, 

da sauri ya k'arasa shiga d'akin, dan dama tun lokacin dayace ya bawa Neehal auren Neelah, 

ya lura ta shiga damuwa, ta danne damuwarta ne kawai gudun b'acin ranshi,

kasancewar ta mace mai tsananin biyayyar aure da matsanancin hak'uri kamar damo, 

dan duk duniya bata da abokin musu balle musiyar yawo ko fad'a, 

ta kasance mace mai tsananin hak'uri, kara da kawaici, tunda sukayi aure da Malam Liman, 

babu wanda zaice ya tab'a ganin ko musu tayi mishi, ko tangard'ar harshe bata tab'a yi mishi ba, 

bama shi ba haka take da gaba d'ayan mutanan k'auyen dan ta samu shaida wajen kowa, 

jin shigowar Malam yasata saurin goge hawayenta, had'i da mik'ewa tana yi mishi sannu da zuwa, 

" lafiya! meke damunki....!? 


Cikin sanyin murya tace " bakomai, 

" a'a ina fa bakomai, bayan na shigo na ganki kina kuka,

" bakomai, ta kuma cewa tana k'ok'arin fita daga d'akin,  

" dan Allah kar muyi haka dake ki daure ki sanar dani damuwarki, 

sosai Malam ya rok'eta kafin tace " Malam ni dai hankali na bai kwanta da auren Neelah da wannan bak'on ba,

kwata-kwata na kasa samun nutsuwa, zuciyata tak'i hutawa,  

" ashsha! subhanallahi haba ya kike irin haka....!? 


"Dan Allah karki k'ara furta irin haka, kamata yayi mu bisu da kyakkyawan fata da kuma addu'a, 

sosai Malam ya kwantar mata da hankali had'i da yi mata nasiha mai ratsa jiki. 


*********************** 


Jin yunwa na neman kashe shi yasa shi mik'ewa jikinshi na rawa da kerrrrrma, 

idonshi yana ganin bibbiyu ya isa gaban tray d'in yayi zaman dirshen, 

ya soma cin nama yana shan furar hannu baka hannu kwarya, 

Neelah na zaune inda aka ajiye ta, har zuwa lokacin bata motsa ba, 

bata kuma yi magana ba, har ya gama cin abincin ya k'oshi, 

a fili yayi hamdala gami da mik'ewa ya fita, ganin ya fita yasa Neelah bud'e rufin kanta, 

dan innarta (k'anwar mahaifiyarta) ta gargad'eta kan karta sake ta bud'e mayafinta, 

a hankali ta shiga bin bukkar da kallo tana mamaki dan bata tab'a ganin bukka irinta ba, 

kallanta takai ga fridge & generator k'atuwar da katifar dake aje, 

kana ta kuma kallan bargo da pillows da gidan sauro net, 

ta sanya hannunta tana shafa k'asan carpet tana mamaki bakinta bud'e, 

ta jima tana kallan bukkar tana mamaki kafin ta mik'e a hankali, 

ta nufi inda abincin yake ta zauna tana ci, 

kasancewar itama tana jin yunwar sosai, tana ci Neehal ya shigo, bai ko kalli inda take ba, 

ya wuce kan foam mattress ya kwanta, 

bayan ta gama cin abincin ta mik'e ta fita ta wanke hannunta, 

kana ta dawo ta taje gabanshi ta tsaya a hankali tace " bacci nake ji! ina zan kwanta....!? 


Jin muryarta ya sashi saurin d'ogowa a kid'ime ya kalle ta, 

ganinta da yayi yasa shi mik'ewa tsaye zumbur cikin tashin hankali, 

had'i da nuna ta da hannunshi yace " wannan halittar aka aura min.....!? 


"Kina nufin kece matar da aka aura min......!? 


Yayi maganar bakinshi na rawa............! 




Bana sai da novels d'ina but bance bazan saida ba, anytime anyday kuna iya jin nace muku na mayar dashi na kud'i, 

saboda b'ata garin da aka samu wad'anda suke amfani da basirarmu, wahalar da hikimarmu, suna amfana da ita, 

suna siyarwa a WhatsApp groups, suna d'orawa a YouTube etc, 

wai har _*RASHIN SANI...!*_ ake siyar da document d'inshi 200,

har a Okada app ake d'ora mana novels ana siyarwa 300 ko 500, nayi magana har na gaji, 

dan haka daga yau duk wanda yace ku bada kud'i ya baku novels d'ina, 

bani bace babu kuma ruwa na, idan zan sayar da novels d'ina kai tsaye zan siyar, 

kunje kuna biyan kud'i ana baku novel wanda an riga an gama shi, inda maruciya ce tace ta mayar da littafinta na kud'i da sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, 

amma gashi can kuna bawa wasu k'attin banza wad'anda bama su san lokacin da muke shan bak'ar wahalar rubutawa ba. 


Gare ku masu siyar mana da novels, nayi Allah ya isa, nayi magana har na gaji, an I will say it again duk wanda ya k'ara siyar min da novels, Allah ya isa, ko yayi min amfani dashi ban yafewa, tunda wahalata ce ko fad'a muku akayi ni ban san kud'i...!? 

dan haka duk wanda ya k'ara saida man da littafi Allah ya isa.




Please duk wanda yayi min magana banti reply ba yayi hak'uri network problem ne





MOMYN ZARAH    'YARBAIWA

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.