Free chapter · Read without an account

19

by Hauwa A Usman · RABO AJALI..

_*RABO AJALI...!*_



*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_



'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''



*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*


*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*


_Ina masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek'e masge kwarkwatar idanunsu wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik'a, fasihiyar marubuciyar nan da kuka sani, kuka dad'e kuna jiran sabon littafinta_ *AISHA ALIYU GARKUWA,* 

_ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k'unshe da abubuwan mamaki, al'ajabi, kala-kala, wanda zai nishad'antar daku, ya d'ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa,_ *HUKUNCIN ALLAH....!* _shine sunan littafin wanda zai zo muku nan bada jimawa ba, *HUKUNCIN ALLAH....! duk masu buk'atar wannan shahararran labarin ya tura naira 200 kacal, ta wannan account number 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA ko ta WhatsApp number da za a turo katin mtn ****_


'''DEDICATED TO'''

*BATUL ADAM JATTKO*



1⃣9⃣




A matuk'ar razane cikin matsanancin tashin hankali Neehal ya sungumi Najwah,

yayi waje da ita da gudu yana kwalawa driver kira da iya k'arfinshi,

jikin driver na b'ari ya nufi Neehal ganin halin da Najwah ke ciki,

yasa shi bud'ewa Neehal motar ya shiga, shima ya zagaya ya shiga had'i da jan motar,

har suka k'arasa asibiti Neehal yana jijjiga Najwah tare da kiran sunanta,

" Najwah! please karki yi min haka, dan Allah karki mutu ki barni,

tun kafin motar ta k'arasa yin parking a harabar asibitin ya fito yayi cikin asibitin a kid'ime,

yana kwalawa Nauman kira, " Nauman...! Nauman...!!,

Nauman na duba marasa lafiya Neehal ya shigo d'auke da Najwah,

gaba d'aya ya firgice ya fita fit daga hayyacinshi, " lafiya meke damunta....!?


Cewar Nauman a rud'e yana k'arasawa wajen Neehal, " please ka taimake ni Aboki ka ceci rayuwar Najwah,

muddin kana san cigaba da gani na a raye cikin k'oshin lafiya ka cece ta dan Allah,

Neehal yayi maganar cikin kuka, batare da Nauman yayi magana ba, 

ya fita ya kira nurses guda biyu tare da gadon tura marasa lafiya,

jikin Neehal na kerrrrma ya kwantar da Najwah saman gadon, 

nurses d'in na k'ok'arin fita da ita, tayi saurin rik'e hannun Neehal,

fuskarta d'auke da wahalallan murmushi a matuk'ar galabaice tace " dan Allah ina neman alfarmar kona mutu karka k'ara aure,

ina rok'onka da girman Allah ko bayan rai na karkayi min kishiya please,

cikin mutuwar jiki Neehal yace bazaki mutu ba, tare dake zamu rayu za mu mutu,

hannunshi dake cikin nata ta k'ara damk'ewa sosai kana tace " ni dai kayi min alk'awarin bazaka k'ara aure ba koda a bayan rai na ne,

dan Allah kona mutu cikin salama, cikin sanyin jiki ya d'aga mata kanshi,

tayi murmushi had'i da cewa " ka tabbata.....!?


"Eh..! yace yana shafa kanta, " in sha Allah mu biyu kawai zamuyi rayuwa a duniyarmu, 

" kayi alk'awari....!?


Ta kuma tambayarshi a galabaice, daga Nauman har nurses d'in sororo sukayi suna kallan ikon Allah,

cike da tsantsar mamakin bak'in kishin Najwah, a fili Nauman ya sauke ajiyar zuciya,

had'i da kallan nurses d'in yace " please ku tura ta zuwa emergency,

yayi maganar a kufule, batare da b'ata lokaci ba suka tura ta, suka fita daga office d'in Nauman,

yabi bayansu, yana jin Neehal nayi mishi magiyar yayi k'ok'arin ceto rayuwar Najwah,

amma yayi banza dashi, ko juya bayyi ba balle ya bashi amsa,

treatment hannun akayi mata had'i da yi mata allurar bacci, aka kaita rest room,

fuskar Nauman a had'e ya fito, tsaye ya iske Neehal bakin k'ofa, yana safa da marwa,

ya kasa zaune ko tsaye, ya had'a uban gumi yana ganin Nauman ya nufe shi da sauri,

" Aboki ya take....!?


Banza yayi dashi ya nufi office d'inshi, Neehal yayi saurin bin bayanshi,

yana cigaba da tambayarshi, " please Aboki ka fad'a min ya jikin My heartbeat....!?


" She is okey, Nauman yace a tak'aice yana zama kan kujera,

Neehal yace " kai karkayi min iskancin banza mana, ina tambayarka halin da matata take ciki kana neman raina min wayo,

me kake nufi....!?


Still banza Nauman yayi dashi yana rubuce-rubuce, biron hannunshi Neehal ya warce, 

tare da cewa " dakai fa nake Malam ko baka jina ne...!?


Cikin nutsuwa Nauman ya d'ago kanshi ya kalli Neehal, " uhummm ina jinka me kace...!?


"Kan uba..! Nauman ni zaka rainawa wayo...!?


" Wai kana nufin ma baka ji abinda nake ce maka ba ko me..!?


"In da naji zan tambaye ka ne...!?


Nauman yayi maganar idonshi kan Neehal, k'asa Neehal yayi da murya yace " please mana Aboki,

ajiyar zuciya Nauman ya sauke had'i da cewa " tana lafiya, babu wata matsala yanzu,

she is out of danger so thank God,

a fili Neehal ya sauke nannauyan numfashi,

had'i da dafe k'irjinshi yace " Alhamdulillah..! Alhamdulillah..! ya Rabbi na gode maka,

Nauman ya cigaba da cewa " ka godewa Allah ka kawo ta akan lokaci da komai yana iya faruwa, wata k'ila ma da tuni an saka ka a turu,

" turu kuma....!?


Cewar Neehal cikin rashin fahimta, Nauman yace " eh..! turu mana dan na lura kad'an ya rage a kad'a maka gangi,

" yanzu dai ina matata...!?


"Oho ban sani ba, " kamar ya oho, ban gane baka sani ba....!?


"Ka bani ajiyarta ne....!?


Cewar Nauman batare daya kalli Neehal ba,

marairaice murya Neehal yayi yace " dan Allah tana ina, Allah ina san ganinta please....!?


"Tana bacci bazata farka ba sai nan da 4 to 5hrs, karka je ka tashe ta, 

" ka tabbatar dai babu wata matsala ko....!?


"K'aryar dana saba yi maka yau ma ita na zabga maka, Neehal yayi murmushi batare dayace komai ba,

shiru sukayi na d'an lokaci kana Neehal yace " kasan meya faru kuwa...!?


"Hummm zai wuce kan banzan kishin haukanta ne, 

" wallahi kamar ka sani ......! daga nan Neehal ya fad'a mishi duk abinda ya faru,

Nauman ya sauke numfashi tare da zubawa Neehal ido,

" lafiya...!?


Cewar Neehal, Nauman yace " ka k'ara aure Neehal dan shi kad'ai zayyi maganin Najwah,

dan harga Allah na fara tsoron kar wata rana ta lahanta ka,

tun tana lahanta kanta tazo ta illata ka, so kawai kayi aure idan tana sanka dole zata hak'ura ta zauna dakai haka,

shiru Neehal yayi ya fad'a duniyar tunani, babu abinda yake tunani sai k'auyen Sunkhanni,

ganin Neehal yayi shiru yasa Nauman zaton ko zai d'auki shawararshi ne,

dan haka ya gyara zama tare da cigaba da kwad'aita mishi k'arin auren, da k'ok'arin sanya mishi sha'awar mata biyu,

Neehal ko baima san abinda Nauman ke cewa ba, dan gaba d'aya tunaninshi ya tafi wajen Abpa,

ganin kwata-kwata hankalin Neehal baya jikinshi ya sanya shi cewa " kana ji na kuwa...!?


Neehal bai ji abinda Nauman yace ba balle ya bashi amsa, k'ara maimaita mishi tambayar yayi amma bai ji ba,

tab'a shi Nauman yayi had'i da kiran sunanshi " Neehal..!,

firgigit yayi tare da cewa " Abpa...!,

"Abpa..! Nauman ya maimaita kana yace " waye kuma Abpa...!?


Cikin alamun rashin gaskiya Neehal yace " um...um..ummm ba..ko...mai,  

" bakomai kace fa....!?


Eh..! Neehal yace yana mik'ewa, yace " bari naje na dubo Najwah, 

yayi maganar yana barin office d'in da sauri, Nauman yabi bayanshi da kallo,

gefenta ya zauna had'i da shafa kanta yayi mata light kiss a goshi,

gami da rik'e hannunta yana shafawa a hankali, Najwah bata farka ba sai bayan sallar ishaa,

da sunan Neehal ta fara farkawa maimakon ambaton sunan Allah,

cikin rawar jiki ya d'ago ta ya d'ora saman k'irjinshi, yana shafa kanta,

tare da sauke ajiyar zuciya, cikin rawar murya Najwah tace " am so sorry dear na d'aga maka hankali na saka ka cikin damuwa sosai ko....!?


"Karki damu babu komai, ni dai buri na ki samu lafiya ki kuma rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali mara yankewa,

" kayi hak'ur....! baibarta ta k'arasa ba, ya d'ora hannunshi saman lips d'inta,

tare da cewa " shhhhhhh, bata kuma magana ba ta k'ara shegewa cikin jikinshi,

sai da Najwah tayi kwana uku hospital sannan aka sallameta suka koma gida.


***********************************


K'auyan Sunkhanni


Neelah zaune jikin bishiyar mangoro suna wasa da wani yaro,

suna wasan k'asa Neelah na tuk'a tuwon k'asa, a zafafe Bintalo uwar yaron ta k'araso wajen,

ta gyara d'aurin k'irjinta, had'i da rankwashin Neelah tana cewa " shegiya jarababbiya manya,

bana hanaki wasa da d'ana ba...!?


Kanta ta dafe tana shafawa, tace " yo ai bani zaka hana wasa da d'anki ba,

shi d'an naki zaki hana wasa da ni, tayi maganar cikin tsiwa, " ni kike wa rashin albarka dan gidanku....!?


Bintalo tayi maganar tana k'ok'arin kaiwa Neelah duka,

da sauri Neelah ta goce tana turo baki tare da cewa " rashin kunya ko gaskiya, 

kuma wallahi karki k'ara duka na, rik'e hannun yaron,

Bintolo tayi tana cewa " bari naje wajen uwarki itace sa'ar yi na bake ba,

Dada na tsunne tana wanke k'orai (kwarya), Bintalo ta tsaya kanta,

tana jijjiga k'ugu tace " ke kika cewa fitsararriyar 'yarki ta zage ni....!?


" Kin tab'a ganin uwa mahaifiya ta arziki ta koyawa 'ya'yanta fitsara....!?


Cewar Dada tana kallan Bintalo, " haka ma zaki ce kema...!?


Bata bari Dada tayi magana ba ta d'ora da cewa " to wallahi bamu yarda muna ji muna gani,

Neelah ta lalata mana tarbiyyar yara , tunda ita yanzu ba yarinya bace,

tunda tasan D'A NAMIJI, ta kuma san DAD'IN NAMIJI, 

damu da ita duk d'aya ne, ke kanki uwarta d'aya kuke,

dan abinda ake yi miki itama ta d'and'ana taji,

dan haka bazamu bari ta koyawa yaranmu iskanci ba, 

sai dai kuma idan so kike ta mayar mana yara irinta,

Dada batayi magana ba saboda bak'in cikin maganganun Bintalo,

Neelah tace " ni ba 'yar iska bace kiga d'an iska ganin idonki,

Bintalo ta tafa hannu tare da cewa " eh! haka ne, dan kinyi wannan ai ba abin mamaki bane,

yarinyar dana san namiji, ta d'and'ani maza, Dada ta zubawa Neelah harara tare da cewa " wuce ki bani wuri,

Neelah tayi hanyar bukka tana zabgawa Bintalo harara,

tare dayin k'unk'uni k'asa-k'asa, Dada tace " wai bazaki wuce bane...!?


Sai da ta k'ara watsawa Bintalo harara kana ta shige bukkar,

Dada ta mik'e ta shige bukka tabar Bintalo nan tsaye tana ruwan bala'i.


Bayan wata uku


"Wai ni aboki na yaushe ne tafiyarku Dubai....!?


Cewar Nauman yana kai glass cup bakinshi, 


" Next week ne fa, Nauman ya zaro ido a d'an zabure yace " kace har abun ya matso kusa gaf....!?


"Wallahi kuwa, cewar Neehal, " wanne course Najwa zatayi....!?


Sai da ya d'an yamutsa fuska kana yace " Accounting, yayi maganar so calm,

Nauman ya lura kamar akwai abinda Neehal ke b'oye mishi,

dan kallo d'aya zakayi mishi ka fuskanci yana cikin 'yar damuwa,

a hankali Nauman ya d'ora hannunshi saman na Neehal tare da cewa " aboki na meke damunka....!?


"Meka gani...!?


Neehal yace a tak'aice, " wallahi Neehal akwai abinda ke damunka, na sanka fa farin sani,

sai dai na fad'awa wani waye kai, na san akwai abinda ke cikin ranka,

please ka fad'a min damuwarka, idan kuma ban isa sanin damuwarka bane shikenan,

ido Neehal ya k'urawa Nauman na d'an lokaci kana ya bud'e baki da niyyar sanar dashi maganar Neelah,

da k'arfi gabanshi yayi muguwar fad'uwa, take zuciyarshi ta shiga gargad'inshi,

kan karya sake yayi kuskuran sanar da kowa yabar maganar a matsayin sirrin ranshi shi kad'ai,

dan haka yayi murmushin yak'e tare da cewa " babu abinda ke damuna,

kawai ina tunanin tafiyarmu Dubai karatu ne, duk da ni masters zanyi, 

ina jin kewarka ne Aboki na, Neehal ya fad'a cikin tsokana yana san wagarar da waccan maganar,

Nauman yayi murmushi danya fahimci manufar Neehal ta san banzatar da maganar da suke yi,

bai damu da dole sayya san matsalar Neehal ba, dan haka shima yabar maganar,

har suka gama hirarsu suka bar wajen Nauman bai kuma tambayar Neehal abinda ke damunshi ba,

bayan kwana biyar ana saura kwana biyu tafiyar Najwah da Neehal k'asar Dubai k'arin karatu suna zaune gaba d'ayansu a parlour gidansu Mamy,

su Suhaima na zagaye dashi,  while Najwah na zaune kusa dashi,

wayar Neehal ta soma rori, ganin sunan Nauman yasa shi saurin yin picking tare da karawa a kunne,

" ina gidan su Mamy, Neehal yace a tak'aice, d'an shiru yayi da alama magana Nauman yake yi,

kana Neehal yace " ok to saika zo, yayi maganar yana dropping wayar,

ba'afi 10 minutes ba, wayar Neehal ta soma ruri a karo na biyu, ganin sunan Nauman ne yasa shi mik'ewa ya fita,

batare da yayi picking call d'in ba, " dan iskanci shine zaka tsaya nan ka wani kira ni baka shiga ka gaida su Mamy.....!?


"A'a ba haka bane, karka had'a ni da Mamy, kawai ban san shiga ne,

zama saman motar Neehal yayi kusa da Nauman, yana cewa " kamar bakinka da magana ko...!?


"Wallahi kamar ka sani aboki na, " to bani nasha meke tafe dakai,

" wata yarinya na gano maka, yarinya k'arama kyakkyawa ajin farko,

Neehal yace " ji wani rainin hankali kai da baka da mata ai ka ya kamata ka shiga wajen bani ba,

" baka san me mata d'aya yana iya yin ta biyu saurayi bayyi ko d'aya ba....!?


"Dan haka nake san ka k'ara ta biyu, " hummm ta biyu kuma sai dai kar a k'ara sai dai ta uku kuma,

Neehal yayi maganar cikin ranshi, a hankali Nauman yace " ban gane abinda kake nufi ba....!?


Cikin tashin hankali Neehal ya kalli Nauman dan bai san maganar da yayi ta fito fili har Nauman ya ji ba,

kanshi ya shafa yana kame-kame " uhnnnn dama.....! Najwah mana,

yayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana, ido Nauman ya kafe shi dashi kamar me san gano wani abun,

Neehal ya kuma yin murmushin yak'e had'i da d'age gira d'aya yace " lafiya dai samari....!?


"Bakomai...! cewar Nauman yana sauke ajiyar zuciya a hankali,

dan Neehal ya kawar da tunanin Nauman yace " kawai ka fad'a min ka samu matar aure,

" a'a wannan zubinka ce, cikin rashin fahimta Neehal yace " zubina kamar yaya...!?


"BAFULATA...! ce na lura kamar kana san matan Fulani, Nauman ya fad'a yana dariya,

danya san babu abinda Neehal yafi tsana a rayuwarshi a halin yanzu kamar Fuld'e,

duka Neehal ya kaiwa Nauman dan ya lura tsokanar shi yake yi,

Nauman ya goce yana dariya gami da cewa " yauwa aboki na bani labarin abinda 'yar k'auyen nan sukayi maka,

da suka saka ka tsani Fulani haka, dan nasan ruwa baya tab'a tsami banza,

shiru Neehal yayi had'i da k'urawa k'asa ido yana kallo, 

ganin yadda ya zubawa gefe ido yasa Nauman tab'a shi had'i da kiran sunanshi,

batare daya kalli Nauman ba ya sauke ajiyar zuciya, fuskarshi d'auke da murmushin yak'e,

cikin sanyin murya Nauman yace " wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, 

akwai abinda ke damunka, kawai dai kana b'oye min ne, amma na tabbatar akwai wani sirrin da kake k'ok'arin b'oye min,

which is ni babu abinda nake b'oye maka Neehal, wallahi Allah ko kisan kai nayi you're the first person da zan fara sanarwa,

but kai gashi nan kana b'oye min wani abu, 

wanda ni ban tab'a tsammanin hakan daga gare ka ba, ban tab'a tsammanin har akwai sirrin da zaka kasa sanar da ni ba,

shiru Neehal yati yana tunani harga Allah yana san fad'awa Nauman gaskiyar al'amarin daya faru dashi a k'auyen Sunkhanni,

yana san sanar dashi labarin Neelah da maganar auren shi na biyu,

amma duk sanda yayi k'ok'arin sanar dashi sai tsoro da fargaba su hanashi,

zuciyarshi ta shiga gargad'inshi kan karya sake ya fad'awa kowa sirrin ruhinshi,

murmushi Neehal yayi tare da furta *ASIRIN CIKI SAI HANJI*,

(saban littafin *BATUL ADAM JATTKO*)

Nauman zayyi magana Suhaima ta fito daga cikin gidan " ku zo mu ci abinci inji Mamy,

saurin dirowa daga kan motar Neehal yayi dama jira yake,

gudun kar Nauman ya tsare shi da tambaya harya kuma kofsawa,

Nauman yabi bayanshi da kallo yana murmushi, kana ya bi bayanshi, 

gaba d'ayansu zaune kan kujerun dinning table har da Naufal da Umairah,

ana ci abinci, Naufal ya kalli Neehal yace " jibi k'arfe nawa jirginku zai tashi....!?


"4:30am na tsakar dare, 

" tab kace daga nan zamu yi sallama, 

" wallahi kuwa, sai idan kun kawo mana ziyara ko mu mun zo hutu,

Mamy tace " Allah sarki Nauman zakayi rashin abokinka, 

ni kai nafi tausayawa ma, Nauman yayi murmushi had'i da marairaicewa,

yace " bari kawai Mamay ji nake kamar nayi hauka, ko na had'a kaya na nabi shi kawai,

" uhmmm kaji shi kamar gaske, cewar Neehal yana dariya, 

" kaima kasan ai dole zanyi kewarka, ni babban matsalarma da bani da wani abokin wallahi,

amma bari zan nemo wani cikin tsofaffin abokai na da, nayi swapping, 

gaba d'aya aka saka dariya, Daddy ya mayar da kallanshi ga Umairah yace " Daughter this month wanne k'auyen za'aje ne....!?


" Jahar Taraba zamu b'ulla wannan karon dan bamu tab'a zuwa can yankin ba,

naji ance akwai k'anan k'auyuka acan,

Daddy yayi murmushi tare da cewa " masha Allah wanne b'angaren a Taraba....!?


" Hard'o-koa'la....! ta bashi amsa cikin girmamawa, dai-dai lokacin Neehal yakai abinci bakinshi,

ba zato yaji maganar Umairah ta daki dodan kunnenshi,

hakan ya haifar mashi da muguwar kwarewa, ya soma tari haik'an,

hawaye ya soma gangaro mishi, kan kace me gumi ya jik'a shi sharkaf,

Mamy da Najwah sukayi saurin mik'ewa mishi cup, jikinshi na rawa ya amshi na Mamy,

ya sha, Nauman ya soma bubbuga mishi bayanshi yana yi mishi sannu,

sai da ya d'an d'auki lokaci kafin ya dawo cikin nutsuwarshi,

tarin ya lafa, ido Nauman ya kafe Neehal dashi, yana jifanshi da wani irin kallo mai wuyar fassara,

while deep down yana mamakin wannan abu na Neehal kawai daga fad'ar Hard'o-koa'la,

sai tari da kwarewa, hakan ne ya k'ara tabbatar mishi akwai wani abu,

Daddy ya kalli Umairah had'i da cewa " sai ki nemi k'arin bayani wajen Oga Neehal,

tunda naji kamar can yankin yayi service, Umairah ta kalli Neehal tana dariya ta bud'e baki zatayi magana,

yayi saurin mik'ewa yabar wajen, gudun kar Nauman ya gano wani abu,

danya lura da irin kallan tuhumar da Nauman ke jifanshi dashi,

washe gari Najwah gidan su ta yini, sai dare Neehal yaje d'aukar ta,

a daren suka had'a kayan tafiyarsu, k'arfe 3:50am na dare suna Airport, 

jirginsu bai tashi ba sai gaf da asuba, a Adis Ababa Ethiopia jirginsu yayi landing,

daga can ne jirgin zasu hau jirgin Dubai, basu jima a Adis Ababa ba suka d'aga zuwa Dubai.


************************************


A k'auyan Sunkhanni kuwa sosai al'amari ya tsananta ga Neelah dasu Abpa,

gaba d'aya yaran karkarar aka hana su wasa da Neelah,

cewar iyayen su Neelah tasan namiji karta lalata musu yara,

kuma tana da farar k'afa, da bak'in k'ashi, sosai aka dami Dada da habaice-habaice irin nasu na mutanen k'auye,

ba hali ta shiga taro ko kicin jama'a, sai ayi ta yadda mata magana,

haka ma Abpa ko masallaci sallah daina zuwa yayi saboda maganun mutane,

k'iri-k'iri za'a kalle shi ace kwad'ayin abun duniya ne yasa shi d'aukar Neelah ya bawa Neehal,

haka aka sako su gaba da k'ananan maganganu marasa dad'in ji,

dole tasa suka koma zaman bukka, duk da kasancewar Neelah yarinya hakan bai hana ta,

fahimtar halin da suke ciki ba, dan sosai mutanen k'auyen ke k'yamarta,

duk inda ta shiga sai ayi ta hantarar ta cike da kyama, data fita sai yara su biyota,

suna yi mata ihuuu suna tsokanarta,

hakan yasa Neelah komawa zaman bukka,

kullum tana cikin matsanancin kuka sosai ta shiga damuwa ta rame ta k'ek'ashe sosai,

gidan su ya zama kamar gidan makoki babu mai walwala,

dole Dada da Abpa ke k'ok'arin danne damuwarsu saboda Neelah,

amma ina ko filin waje bata fitowa ta koma zaman bukka gaba d'aya,

sosai rayuwar Neelah tayi bala'in k'untata, ta shiga cikin k'unci.


Motar Lagosa Helper tayi parking a k'ofar gidan chairman na Hard'o-koa'la, 

bayan anyiwa su Umairah iso, suka shiga, suka sanar da Chairman d'in abinda ke tafe su,

suka kuma buk'aci daya fad'a musu k'auyukan dake k'ark'ashin shi,

batare da b'ata lokaci ba Chairman ya shiga lissafa musu,

bayan ya gama lissafa musu Umairah ta kalle shi a nutse tace " a cikin wad'annan k'auyukan wad'annene suka fi buk'atar taimako kusa-kusa.....!?


D'an jimmm yayi kafin yace " eh to gaskiya gaba d'ayansu suna buk'tar taimako,

amma K'AUYAN SUNKHANNI gaskiya duk yafi su buk'atar taimako, " ok dan Allah idan ba damuwa ko za'a raka mu k'auyan....!?


"Ashsha damuwar me kuma...!?


" Ai babu wata damuwa ko yanzu kike so sai a raka ku, " ah to mu je , tayi maganar tana mik'ewa, 

chairman ya mik'e shima, tare da mutane uku daga cikin jama'arshi,

suka shiga cikin babbar Bus d'in dasu Umaira suka zo da ita,

wacce harda tv, ac, toilet da fridge cikinta, driver yaja, d'aya daga cikin mutanen yace " anko yi sa'a yanzu ba damuna bane lokacin rani ne,

" idan damuna ne akwai matsala ne...!?


Umairah ta tambaya, " sosai ma, dan kwata-kwata garin bai shigowa da damuna,

har suka k'arasa suna bata labarin k'auyan Sunkhanni,

direct wajen mai gari aka kaisu, bayan an gaisa Umaira ta soma magana,

" mu daga birni muke muna d'iban 'ya'yanku ne muna kai su birni suyi karatun boko dana addini,

muna tsaya musu suyi karatu boko har sai sun gaji, duk da irin kallan da mutanen k'auyen keyi mata,

baisa tayi shiru ba sai da ta dasa aya,

gaba d'aya mutanen k'auyen suka fara maganganu k'asa-k'asa,

suna rad'e-rad'e cikin alamun rashin yarda, me gari ya kalli su Umairah yace " ku d'an bamu waje muyi shawara, ba musu su Umairah da jama'arta suka koma gefe,

duk garin kowa yayi tsalle ya dire kan bai bayar da 'ya'yanshi,

me gari yace " o'o dama nima ban yarda da wannan tsarin nasu ba,

kiran su Umairah me garin yayi, kana yayi musu bayanin kowa yace bazai bada 'ya'yanshi ba,

Umairah ta shiga yi musu bayani tana k'ok'arin wayar musu dakai,

amma ko gezau babu wanda yayi, juyin duniya, da rarrashi da bada baki amma sukayi tsalle suka dire,

suka ce bazasu bayar da yaran su ba, daga k'arshe ma watsewa jama'ar sukayi, kowa ya kama gabanshi, suka bar su Umairah nan tsaye,

cikin sanyin jiki Abpa ya mik'e ya tafi bukkarshi,

zai shige bukka Dada tace " Malam lafiya dai naji ana shela...!?


"Eh..! lafiya lau, wasu bak'i ne suka zo daga birni, wai suna san a basu yara su kaisu birni karatu.....!,

daga nan Abpa yayiwa Dada bayanin komai, Dada ta sauke numfashi tare da cewa " Allah ya kyauta,

Neelah na d'aki kwance, jin maganar Abpa yasata fitowa da gudu,

tace " Abpa ina bak'in birnin sun tafi....!?


"A'a suna nan Mamana, " karatu zasu kai mutum birni yayi....!?


"Eh..! cewar Abpa yana kallanta, " suna ina yanzu....!?


"Suna wajen me gari na baro su, amma tafiya zasu yi....!, ai tun kafin Abpa ya gama rufe bakinshi Neelah ta kwasa da gudu tayi waje,

Abpa ya kalli Dada itama ta kalle shi, cike da mamaki, Dada zatayi magana Abpa yayi saurin bin bayan Neelah,

Dada ma tabi bayansu, 

lokacin da Neelah taje har su Umairah sun shiga mota sun soma tafiya,

da gudu tabi motar tana d'aga musu hannu tana cewa " ku tsaya...! ku tsaya...,

ta fad'a da k'arfi, ta window Umairah ta hango Neelah da sauri ta dakatar da driver, 

Neelah ta k'araso tana haki Umairah ta fito daga cikin motar,

cikin haki Neelah tace " da gaske zaku kai mutum birni yayi karatun boko dana addini har ya gaji......!?


Da sauri Umairah tace " eh sosai ma, karatu saima kin zab'i wanda zakiyi,

Neelah na haki tace " ZANI....!, ZAN BIKI BIRNI KI SAKA NI A MAKARANTA......!, dai-dai lokacin Abpa da Dada suka k'araso wajen....................!





*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*




MOMYN ZARAH   'YARBAIWA

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.