Free chapter · Read without an account

33

by Hauwa A Usman · RABO AJALI..

***


*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*



_*RABO AJALI...!*_



*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_



'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''



LITTATTAFAINA MASU ZUWA


_*RABO AJALI...!*_

_*SAKI RESHE...!*_

_*WATA SHARI'AR...!*_

_*DUK NISAN DARE...!*_

_*NISAN KWANA...!*_

_*NADIYA...!*_

_*ABU A HUDU...!*_

_*DA KAMAR WUYA...!*_

_*SAKI NA DAFE...!*_




3️⃣4️⃣




Ya dad'e kwance yana fitar da numfashi dakyar kafin ya mik'e yana jan k'afa, while yana dafe da k'irjinshi, 

Allah ya taimake shi bayyi tafiya mai nisa ba ya samu napep, dakyar ya fad'awa me napep d'in inda zai kaishi, 

sanin bashi da kud'i yasa shi cewa napep d'in ya jira shi a bakin get, 

yana dafe da k'irjinshi ya shiga get d'in gidan yana kwalawa Neelah kira, 

a kid'ime Neelah, Naufal da Umairah suka fito, jikinshi na rawa ya zube gaban Neelah, 

had'i da fasa mata kuka, ya kasa furta koda kalma d'aya, a hankali tari da hakkin da yake yi suka soma tsananta, 

kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin mawuyacin hali, ya jigata sosai, ko numfashi dakyar yake iyayi, 

yana dafe da k'irjinshi ya bud'e baki dakyar cikin muryarshi da bata fita sosai yace " nasan nayi miki kuskure but I'm sorry, kiyi hak'uri, 

ki yafe min, ki tuna muma masu laifi ne a wajen Ubangijinmu, muna yi mishi laifi yayafe mana, 

Allah mai yafiya ne, yana kuma san mutane masu yafiya, Ubangiji me tausayin bayinsa ne, haka yana san mutane masu tausayi, 

ki dubi girman Allah Neelah kiyi hak'uri ki yafe min wallahi Allah na tuba na canja hali,  

na kuma gane kuskure na, please, ya k'arasa maganar jini fitowa daga hanci da bakinshi, 

idanta kanshi tana k'ok'arin danne abubuwa da dama cikin ranta, tace " baka canja ba, inda ka canja bazaka rink'a tunanin kanka, 

da nemawa kanka mafita kai kad'ai ba, ko sau d'aya ka tab'a tunanin ni ina sanka ko bana sanka? 


"Ka tab'a tunanin halin da Nauman zai shiga? 


"Ina da tabbacin matuk'ar aka raba mu daga ni har shi sai mun shiga fiye da halin daka shiga, 

amma saboda tsabar san kanka dayayi maka yawa ta kanka kawai kake yi, 

kanshi ya shiga girgizawa yana cewa " nasan kina so na Neelah, ko shakka bana yi akan irin son da kike yi man, 

hakan ne yasa ban..... dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga mishi hannu tana kallan kwayar idanshi ta nuna kanta, 

had'i da cewa " wa! ni nake sanka? 


Da sauri ya d'aga kanshi tare da cewa " eh! I knew you really love me, 

murmushin gefen baki tayi tace " ashe abinda kake tsammani kenan? 


Bata bari yayi magana ba ta cigaba da cewa " to idan ma abinda kake tunani cikin ranka kenan, 

gwara tun wuri ka janye danni babu wannan shirmin cikin raina, ko an fad'a maka bani da hankali ne da ina ganin kashi da rana zan taka? 


"Bayan na san waye kai, nasan halaye da d'abi'unka, sannan zan so ka, 

" wallahi nasan kina so na Neelah, dan tun kafin kisan komai a duniya kika san so na, 

tun kafin kisan wacece ke kika kamu da soyayya ta, tun kafin kisan meye duniya, rayuwa da mutuwa, hankali da nutsuwa kika san son Neehal, 

baki san komai ba sai so na, baki san kowanne d'a namiji ba sai ni, da dakon soyayyata kike kwana kike tashi, duk wannan tsayin lokacin,

fashewa tayi da matsanancin kuka had'i da durk'ushewa k'asa, ta shiga girgiza kanta tana cewa " a'a k'arya kake ban sanka, bazan kuma tab'a sanka ba,

a hankali ya durk'usa a gabanta ya sanya hannunshi ya tallafo fuskarta, 

hawaye na gangarowa daga idonshi yace " idan bakya sona meyesa a wancan lokacin kike kishi na? 


"Idan baki so na meye a baya kike kallan fuskata idan ina bacci? 


"Meyesa baki ganin laifi na? 


Sautin kukanta ta k'ara had'i da runtse idonta da k'arfi ta kawar da kanta gefe, tana cewa " a'a ba haka bane, bana sanka, ban tab'a sanka ba, Nauman nake so, shi zan aura, 

karkato da fuskarta yayi suna kallan junansu yace " idan bakya so na meyasa ki kuka yanzu? 


Cak ta tsayar da kukanta tana kallan cikin kwayar idanshi, dan idan za'a kashe ta bata san dalilin kukan ba, ido kawai ta zuba mishi ta kasa cewa komai, 

kamar zan tsikareta ta mik'e zambur, tana goge hawayenta tace " duk mutum kirki an sanshi da tsaida magana d'aya, 

dan haka na riga na gama magana, 

kozan mutu bazan tab'a canja magana ta ba, Nauman nake so, shi zan aura, mik'ewar shima yayi tsaye, 

ya taka zai isa gare ta, tayi saurin ja da baya, ya kuma takawa ta kuma ja baya,  

wuf Neehal yayi ya rungume Neelah tsam a jikinshi, ya ruk'unk'umeta, yana ji tamkar ranshi zai fita, " please! please! ki ceci rayuwata karna mutu, 

ganin Neelah nata faman k'ok'arin kwacewa ta kasa yasa Naufal nufarsu, 

ya soma k'ok'arin kwatar Neelah, amma ya kasa, sosai Neelah ta jigata saboda yadda ake cali-cali da ita, 

dakyar da taimakon Umairah aka kwace Neelah, aiko bak'in ciki ya sanya Neehal kwad'awa Naufal mari, 

yana huci tamkar zaki yace " ina ruwanka, matata ce, dan haka ku bani matata, ya fad'a a haukace tamkar zararre, 

yana nufar inda Neelah take, saurin kare ta Naufal yayi cike da tausayin d'an uwannashi, 

yace " kayi hak'uri please ka nutsu, ka dawo hayyacinka, ihuuuu Neehal ya kwarara yace " bazan nutsun ba, nace maka ka bani matata ko? 


Yayi magana cikin hauka tuburan, while yana cigaba da ihuuuun, sosai matsanacin tsoro ya kama Naufal da Umairah da Neelah,

ganin yadda Neehal ya koma, ya zama cikekken mahaukaci, ya zage yana zuba hauka tuburan muraran, 

a haukace ya shak'i Naufal ya shiga dukanshi yana cewa ka bani matata,  

kai da ganin yadda yake dukan kasan baya cikin hayyacinshi, yayinda Naufal ya kasa ramawa saboda ganin halin da Neehal ke ciki, 

ya d'aga hannu zai kuma kaiwa Naufal naushi yajiyo muryar Neelah cikin kuka na cewa, 

" wallahi tallahi kona rasa mijin aure bazan tab'a aurenka ba, bana sanka, I hate you, 

cak ya tsayar da hannun a dai-dai fuskar Naufal, ya k'ame tsaye a wajen, da k'arfi zuciyarshi ta shiga bugawa, tari ya turnuk'eshi, kafin kace me tuni ya soma kwarara aman jini ta hanci ta baki, 

idanuwanshi suka kakkafe sukayi fari fat, numfashinshi ya d'auke, cikin tashin hankali Naufal ya nufe shi, yana kiran sunanshi, 

dai-dai lokacin Daddy ya shigo da motar asibiti (ambulance), 

kasancewar me gadin gidanshi ya sanar dashi yanayin da Neehal ke ciki, 

batare da b'ata lokaci ba nurses suka kimkime shi suka shigar dashi mota, 

Naufal, Daddy da Umairah suka bi bayansu, k'asa Neelah ta durk'ushe ta fasa kuka mai cin rai, 

sai da ta gaji da kanta sannan ta mik'e ta shiga kicin gidan tana shawarar barin garin gaba d'aya, 

a gaggace ta had'a kayanta cikin trolley ta zari key d'in motarta ta fita, 

bata zame ko'ina ba, sai gidan su Mamy nan ma tayi sa'a babu kowa sai Nail, Nailah da Neelam, 

da sauri ta shiga cikin bedrooms d'insu ta had'awa kowanne kaya a trolley taja hannunsu, 

duk ilahirin jikinta na tsuma gami da kerrrma, 

yaran na tambayarta ina zasu je amma bata bi ta kansu ba, ta dannasu cikin mota ta hau kwalta.


A b'angaren Neehal kam sai dai addu'a, a k'alla likitoci sun kai biyar da suka rufa a kanshi suna k'ok'arin ceton rayuwarshi, 

sun d'auki tsayin lokaci suna duba shi amma abun ya faskara ya wuce saninsu, 

sai k'arfe d'aya saura na dare suka samu nasarar ceto rayuwarshi dakyar, 

dan har sun tsunke da al'amarin, yayinda dasu Daddy keta faman sintiri a k'ofar emergency room d'in, duk sunyi jigum-jigum babu wanda yake magana, 

kowa na addu'ar Allah ya tashi kafad'un Neehal, fitowar da Doctors d'in sukayi ce ta sanya su nufarsu da sauri, 

Naufal na k'ok'arin yin magana aka turo gadon da Neehal ke kwance, yayi firit dashi kamar wanda ya shekara a kwance, 

yayi muguwar rama, 

kwat Naufal ya had'iye wayo tare da sauke ajiyar zuciya, yace " Doctor da sauk'i jikin nashi? 


A fili Doctor ya sauke ajiyar zuciya cike da jimami da jinjina abinda zai sanar musu, 

" lafiya!? 

"meke faruwa? 

"Kodai da wata matsalar ne? 


Naufal ya jerawa Doctor tambayoyin, numfashi ya fitar kana ya tattara gaba d'aya hankalinshi ga Daddy yace, 

" magana ta gaskiya akwai babbar matsala Alhaji, dam! gabansu yayi muguwar fad'uwa, dakyar Daddy yayi k'ok'arin saita kanshi murya na rawa yace " wacce iri? 


"Yakai matakinshi k'arshe wanda daga shi bamu da abinda zamu iya yi mishi,

zuciyarshi tayi rami daga ciki sosai, ga zuciya a kumbure take, a halin yanzu ma gaskiya bama tunanin magani zayyi mishi aiki, 

sai dai muyi addu'a dan komai yana iya faruwa, rayuwar shi na cikin had'ari, matuk'ar ana san ya cigaba da rayuwa dole a guje yawan b'ata mishi rai, ko fad'ar abinda zai tada mishi hankali, 

a bashi abinda yake so, in ko ba haka ba ana gaf da rasa shi.....! matsanancin kukan da Mamy ta saka ne yasanya Doctor yin shiru, 

cikin tashin hankali, kid'ima da firgici ta soma cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, 

na shiga uku ni Taheera zan rasa d'ana, dan girman Allah Alhaji ka taimaka min, karya mutu, 

idan baka yi wani abu ba zamu iya rasa shi please, ta fad'a tana rik'e gam da Daddy, 

Daddy da shima hankalinshi yakai k'ololuwar tashi, daurewa kawai yayi gudun kar ya d'agawa sauran mutane hankali, 

amma deep down ihuuuun zuci yake bama kukan zuci ba, sakin Daddy Mamy tayi, ta nufi hanyar fita tana cewa " tunda bazaka iyayin komai ba, 

na tafi nemarwa d'ana magani, zanje na durk'usa har k'asa na bawa Neelah hak'uri, 

na kuma rok'i Nauman ya barwa Neehal ita, kafin Daddy yayi wani yunk'uri ta fice.


Nauman ya dad'e zaune cikin mota yana mayar da numfashi kafin ya saita kanshi, a hankali yayiwa motar key yabar wajen, 

ikon Allah ne kad'ai yakai Nauman gida lafiya dan kwata-kwata bai san takamaiman inda yake cilla motar ba, 

direct gidanshi daya gina wanda ya shirya yin daddad'ar rayuwar aure mai cike da zallar farin ciki shida Parinshi ya wuce, 

yana yin parking a harabar gidan ya fito baiko tsaya rufe motar ba ya shige cikin gidan, 

tun a parlour na soma cin karo da maka-makan hotunan Neelah a kowanne jikin bango, 

bai tsaya a falon ba ya wuce bedroom ya zube saman bed had'i da fasa kukan bak'in ciki da takaicin, 

macen dayafi fiye da kowa a duniya ita d'an uwanshi, abokinshi kuma amininshi yake so, 

Allah ya sani yana matuk'ar so da k'aunar Neehal amma son da yake yiwa Neelah yafi gaban kwatance, 

dan bazai iya had'a soyayyarta data kowa ba, ji yake rabuwa da ita tamkar rabuwa da ruhinshi ne, 

yana jinta a ko'ina na jikinshi, tashi yayi zaune had'i da k'urawa hotanta dake gaban gadonshi ido, 

" no! wouldn't, bazan iya ba, bazan iya rabuwa dake ba, bazan iya sadaukarwa da kowa ke ba, 

koda kuwa hakan yana nufin mutuwar koma waye, kece rayuwa ta, kece duniya ta, kece hasken idaniya ta, 

ya fad'a yana girgiza kanshi hawaye na gangaro mishi, tun da Nauman ya shiga bedroom bai fito ba, 

sallah kad'ai ke tada shi daga gaban hotan Neelah, amma ko abinci bai ci, wannan kenan. 


Tunda aka kai Najwah gidan mahaukata babu wanda yaje, ko 'yan gidansu basu je ba, 

in banda ihuuu da hargowa gami da kururuwa babu abinda take yi, 

ita babbar damuwarta tasan Neehal nacan na tare da Neelah, take abubuwa da dama suka shiga yi mata yawo aka, 

ta shiga hango su suna sex, da romance, 

hakan ne ya k'ara gigita ta, ta kuma mahaukacewa da ihuuuu, tana danna musu ashar,

" wayyyo na shiga uku suna can suna shan soyayya, kuzo ku bud'e ni, suna can suna cin amana ta, 

wallahi sai na kashe su, nice ajalinsu, sai na zame musu bala'i da masifa a rayuwarsu, 

sai na zame musu gobara daga gogi, sai na k'ona su da ransu, ihuuuuuu wa'ehoho, sai ni Najwah, 

k'asa tayi da muryarta tare da fashewa da matsanancin kuka tana cewa " ka cuce ni Neehal, kaci amanata, ka yaudare ni ka ha'ince ni, 

akanka nayi sanadiyyar lalata mahaifata, ashe kai kana da yara har uku, ashe yaranka na raina ban sani ba? 


"Wallahi dukkanku, daga ku har yaranku saina kashe ku, shegu munafukai, 

yadda Neelah taga rana haka taga dare tana ruwan hauka da tijara iri-iri, ashar kam babu irin wacce batayi ba, 

sauran mahaukatan da suga ta hana su bacci sukayi mata rufdugu, suka rufar mata da duka, 

sukayi mata lilis tun tana kuka da ihuuu harta daina, me cizonta nayi, 

me yakushi nayi, me mari nayi, me ja mata gashi nayi, in banda Allah ya taimake ta, ma'aikatan gidan sun farga da wuri da sai sun kashe ta, 

dakyar aka kwace ta daga hannunsu, tayi kwance lamo tana fitar da nishin wahala,  

duk da haka bakinta bai mutu ba, ta cigaba da tsinewa Neehal da Neelah tana cewa itace ajalinsu, 

duk sanda ta hana mahaukatan bacci sai su taru akanta, suyi ta gana mata azaba iri-iri, 

su nad'a mata uban duka, 

kusan ko'ina na jikin Najwah a fashe yake saboda duka, mahaukata su nad'a ma'aikatan gidan su nad'a, dan suma tana hana su bacci, kanta kam harya gaji da fashewa, 

bakinta yayi sumtum, duk da irin wuyar da take sha saboda taurin kai bakinta bai mutu ba, bata daina ruwan tijara ba, haka zuciyarta bata samu salama ba, burinta kawai ta ganta a waje ta samu damar aiwatar da abunda ke ranta. 


A Airport Neelah tayi parking ta fito cikin rawar jiki, ta fito da yaran ta zagaya ta fito da kayansu, 

Nail yace " Taraba zamu je wajen Dada da Abpa Mom? 


"Eh! tace a tak'aice, tana jan hannayensu suka shige reception, tsallen murna suka fara yi, 

kasancewar sun saba dasu Abpa dan kusan duk hutun makarantar su acan suke yinshi, 

suna bala'in so suji ance zasuje Sunkhanni, rayuwar karkarar ba burgesu sosai, sukayi sa'a akwai jirgin Taraba a k'asa dan haka basu b'ata lokaci ba jirginsu ya d'aga zuwa Taraba State. 


Daga bakin get Mamy tayi parking bata shigar da motar harabar gidan ba, cikin girmamawa mai gadin gidan Neehal ya tare ta, 

yana niyyar zubewa gabanta ya gaida ita tayi saurin hana shi, suka gaisa sama-sama, tana k'ok'arin shigewa mai gadin yace " Hajiya gidan babu kowa fa, 

cikin rashin fahimta tace " Ba Neelah tana ciki ba? 


"A'a ta fita, cikin mamaki Mamy tace " yaushe? 


" Ta d'an jima da fita, da alama kuma tafiya tayi dan da akwati ta fita, saurin kallanshi Mamy tayi tace " da akwati fa kace? 


"Eh!, a kid'ime Mamy tayi baya ta fad'a mota, gidanta ta wuce, nan ma bata shigar da motar ba, ta shiga gidan jikinta na tsuma dan a zatonta Neelah na gidan, 

ta duba ko'ina amma babu Neelah, da sauri ta fito wajen me gadi, muryarta na sark'ewa, tace " ina su Nailah? 


"Neelah tazo ta d'eb'esu, a tsawace tace " ina ta kaisu!? 


Sosai me gadin ya tsorata dan tunda suke da Mamy babu wanda zaice ya tab'a ganin koda fushinta balle b'acin ranta, 

muryarshi na rawa yace " wallahi ban sani ba, naga dai ta shiga cikin gidan ta fito da yaran da akwatuna, 

" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Mamy tace, bata bi takan me gadin ba tayi waje, harta isa asibiti tana kiran wayar Neelah amma a kashe, hakan ne tabbatar mata guduwa Neelah tayi, 

cikin tashin hankali ta tura k'ofar d'akin da Neehal ke kwance, Daddy, Naufal da Umairah, 

sun zagaye gadon da yake kai, kuka Mamy ta fashe dashi, tana cewa " shikenan mun rasa shi Alhaji, 

ganin yanayin Mamy da kalaman bakinta ba k'ara min d'aga musu hankali yayi ba, 

da sauri Daddy ya tallafe Mamy dake k'ok'arin durk'ushewa k'asa, " lafiya Taheerah? 


Daddy ya fad'a out of control, "Alhaji mun rasa Neehal, shikenan nasan mutuwa zayyi, 

" meke faruwa Mamy?


"Neelah ta kwashe yaranta ta gudu, "what? 


Suka fad'a dukansu a tare, cikin matsanancin kuka ta kwashe komai ta fad'a musu, kafin wani yayi magana suka jiyo razananniyar k'arar da Neehal ya kurma, 

" wayyo na shiga uku, Neelah da yara na sun tafi sun barni, mutuwa zanyi, 

wayyo Allah na shiga uku, girman kai da fariya sun kai ni sun baro ni, najawa kai na, na cuci kai na da rayuwa, 

d'agawa da jijji da kai sun jawo min, na rasa matata da yara na, ya fad'a cikin matsanancin kuka kamar ranshi zai fita, 

" wayyo mutuwa kizo ki d'auke ni na huta da azaftuwar zuciya da ruhi na, wallahi na gwammaci mutuwa da wahalalliyar rayuwa da nake yi, Neelah ta tafi ta barni, kallanshi ya mayar ga Daddy da Mamy yace " please ku taimake ni, 

ku ceci rayuwata ku bawa Neelah hak'uri ta dawo gare ni, ku dawo min da matata da yara na, idan suka barni mutuwa zanyi, 

dan Allah ku bani matata da yara na, ku bani Neelah da yara na, wayyo zan mutu ya fad'a lokacin da yake faman kokowa da numfashin shi dake sark'ewa, 

tamkar me chronic asthma haka yake jan numfashi kwarrrrr-kwarrrrr hannunshi dafe da zuciyarshi, 

yana ta faman k'ok'arin magana amma ya kasa, 

illa nuna da yake yi musu da hannu had'i da motsa lips d'inshi yana kiran sunan Neelah, 

da gudu Daddy da Naufal suka fita kiran Doctor, yayinda da Mamy takai k'ololuwar rud'ewa ta fice daga hayyacinta, 

dan komai k'iyayyarka da Neehal kaga halin dayake ciki dole ka tausaya mishi, 

wata irin tsuma gaba d'aya jikinshi ya d'auka take idonshi ya kafe kumfa na zabowa daga barinshi, 

while jini na zuba ta hanci da baki, in banda sunan Neelah babu abinda yake kira, 

cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya kamanninshi suka canja, gumi ya jik'a shi sharkaf,  

da gudu Doctor ya k'araso bakin gadon, halin dayaga Neehal ba k'aramin tsorata shi yayi ba, 

innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai Doctor d'in yake maimaitawa yama rasa abinda zayyi, 

da gudu ya fita bai jima ba ya dawo tare da wasu Doctors d'in da nurses, gaba d'ayansu suka rufa kanshi, 

nurses suka fara k'ok'arin fitar dasu Mamy daga d'akin saboda kukan da suke yi, 

salati Neehal yayi had'i da satin hannunshi suka zube yaraf, jikinshi ya daina rawar da yake yi,  

hannu Mamy ta d'ora aka had'i da kurma gigitaccen ihuu, ta zabewa k'asa, 

Naufal ma zubewar yayi a sume, hakan ne ya k'ara d'agawa Daddy da Umairah hankali, 

suka gigice suka kid'ime, batare da b'ata lokaci ba nurses suka kwashe su, suma Doctors suka rufa kansu. 


Najwah na kwance a tantagaryar sumunti babu ko shinfid'ar taburma, jikinta sai kerrrrma yake yana b'ari, 

kanta da fuskarta sunyi sumtum kamar an d'ora mata dutse a nad'e da bandaji, 

hannunta da k'afarta d'aure cikin sark'a irin wacce ake sawa mutane a gidan mari, 

dakyar take iya jan numfashi, kallo d'aya zakayi mata ka kauda kanka saboda bala'in da take ciki, 

tayi wujiga-wujiga ta jigata sosai, tayi muguwar rama ta k'ek'ashi, idan ba mugun sani kayi mata ba, 

bazaka iya gane ta, duk rashin imani da tausayin mutum idan yaga mawuyacin halin da Najwah ke ciki sayya tausaya mata, 

babu girma kai da tak'amar nan, dan kullum babu bashi mahaukatan sai sun nad'a mata uban duka, 

sai da Najwah ta gwammaci mutuwa akan wahalar da mahaukatan ke bata, 

duk mahaukacin da aka daka akanta zai rama, haka duk wanda haukanshi ya motsa kan Najwah yake sauke shi, 

idan akayi musu allura ko aka basu magani akanta suke hucewa, 

sun mayar da ita tamkar jaka, sai tula sukeyi sabe da rana, ta kod'e ta jeme abin tausayi, tana kwance tana nishi cikin mayuwacin hali, ko idanta bata iya bud'ewa, ma'aikaciya ta shigo ganin halin da Najwah ke ciki ya tsorata, 

ta fita da sauri ta sanar da shugaban ma'aikatan dake gidan, tare suka dawo dashi da wasu ma'aikatan, 

suma sun tsorata da halin da take ciki, dan haka suka kira ambulance, babu b'ata lokaci aka kwashe ta zuwa asibiti. 


Tun daga ranar da Nauman ya shige gidanshi bai k'ara fitowa ba, ko abinci bai iya ci, sai yunwa ta dameshi yake iya shan fruits salad, 

ko fresh milk, ya rame sosai ya k'ek'ashe kallo d'aya zagayi mishi kasan yana cikin mawuyacin hali,

yana kwance sai juyi yake saman bed ya kasa bacci, tuni Nauman ya saba da rashin bacci, 

yama manta yaushe rabonshi da bacci, yana kwance wayarshi ta soma ringing, yayi banza da ita, harta tsinke bai d'aga ba, 

aka sake kira a karo na biyu bayyi picking ba, 

jin an sake kira a karo na uku ya sashi jan tsoki had'i da mik'a hannunshi ya d'auki wayar ya kara a kunne batare daya duba wanda ya kira ba, 

muryar Daddy yaji cikin kuka yana cewa " Nauman Allah yayiwa Neehal rasuwa, tashin hankali ne ya sanya Nauman sakin wayar ta sulale k'asa, 

jikinshi na rawa ya mik'e yana san tuna abinda Daddy ya sanar dashi, 

dan tashin hankali da kid'ima sun mantar dashi, kamar daga sama ya jiyo muryar Daddy na amsa kuwwa cikin kunnenshi,, 

Nauman Allah yayiwa Neehal rasuwa, 

razananniyar k'ara ya saki wacce gaba d'aya gidan saida ya amsa, had'i da fashewa da gigitaccen kuka, 

a rud'e ya shiga laluben wayar tamkar makaho ga wayar a gabanshi har tab'a ta hannunshi yayi amma saboda tsabar razane bai gane ba, 

ya dad'e yana neman wayar kafin ya gane wayar na hannunshi, cikin rawar jiki ya kira Daddy, bugu d'aya ya d'aga, yace " kuna ina? 


Muryar Nauman kad'ai ta isa ta shaidawa mutum tsantsar tashin hankalin dayake ciki, 

" asibitinku, Daddy ya fad'a a tak'aice, bai kuma magana ba yayi dropping call d'in, 

Nauman ya manta jikinshi babu kaya daga shi sai singlet da gajeren wando iya gwiwa, 

ya fad'a mota tare da figarta kamar zai tashi sama, ikon Allah ne yakaishi lafiya, wani irin parking yayi a harabar asibitin k'uuuuuu k'ura ta tashi, 

jikinshi na tsuma ya fito ya shiga cikin hospital d'in, 

tsugunne ya iske Daddy ya had'a kai da gwiwa yana kuka wiwi kamar k'aramin yaro, 

dan harga Allah duk cikin yaranshi yafi son Neehal, 

Daddy na ganin Nauman ya mik'e tsaye had'i da nufarshi, shiko ganin Daddy yasashi durk'ushewa k'asa, 

kwata-kwata ya kasa kuka sai mugun suya da rad'ad'i da zuciyarshi keyi mishi, 

ji yake tamkar ana babbaka mishi k'irjinshi, " Neehal ya mutu Nauman, 

Allah ya karb'i rayuwar Neehal, Daddy ya fad'a, karaf maganar, Daddy ta sauka a kunnen Najwah, 

dake kwance saman gadon marasa lafiya an fito da ita daga emergency room, 

wani irin wawan tsalle tayi ta duro k'asa bisa k'afafuwanta, take ta nemi duk wani ciwo da azabar da take ji a jikinta ta rasa, 

ihuuuu ta sanya had'i da nufar Daddy, " Daddy da gaske Neehal d'ina ya mutu? 


Sai a lokacin suka kula da Najwa, jikin Daddy a sanyaye yace " eh! Allahn daya bamu aronshi ya karb'i rayuwar abinshi.....!  

bata k'arasa jin abinda Daddy zai fad'a ba ta sulale k'asa a sume, itama nurses suka d'ebe ta, 

dafa kafad'ar Nauman Doctor AAY yayi, cike da tausayawa yace " congratulations abokinka bai mutu ba, 

zumbur Nauman da Daddy suka mik'e a tare, had'i da kafe AAY da ido, murmushi yayi musu had'i da jinjina musu kai yace " yes! he's alive, yana nan a raye, sai dai he's in coma, 

Nauman bai san sanda ya rungume Doctor yana sakin murmushi ba, yace " thank you for the good news, na gode sosai, 

Daddy kam zama yayi yana godiya ga Allah daya raya mishi Neehal, sakin Doctor AAY yayi ya isa gaban Daddy ya duk'a had'i da d'ora kanshi saman cinyar Daddy, 

yana sauke ajiyar zuciya ya kasa magana, a hankali Daddy ya d'ora hannunshi saman kan Nauman yana shafawa, 

Doctor AAY yace " to aje a saka kaya nuna k'irar ta isa haka, kallan jikinshi Nauman yayi da sauri dan baima san babu kaya jikinshi ba, 

Daddy da Doctor suka saka dariya, " ya jikin Mamy da Naufal da Najwah? 


"Lafiya lau, razane sukayi amma a kowanne lokaci suna iya farfad'owa....!, 

kafin Doctor ya gama rufe bakinshi suka jiyo mahaukacin ihuuuun Najwah, da sauri Daddy da Nauman suka shiga d'akin, 

" da gaske Nauman ya mutu Daddy? 


Najwah ta fad'a tana sakkowa daga gadon, mayar da ita saman gadon Daddy yayi yana murmushi, 

yace " Alhamdulillah Allah ya raye shi, yana raye bai mutu ba, saurin mik'ewa tayi, jikinta na rawa tace " please ku kaini na ganshi, 

babu musu Daddy da Naufal suka wuce gaba Najwah ta bisu, yana kwance lamo, hancinshi manne da oxygen, 

idonshi rufe da alama bacci yake yi, kuka Najwah ta sanya had'i da kawar da kanta gefe, 

ganin cikin 'yan kwanaki yadda Neehal d'inta ya jeme, ya k'ek'ashe, ya zama abin tausayi, duk rashin k'aunar da kakewa Neehal sai ka tausaya mishi,

a hankali ta isa bakin gadon ta zauna had'i shafa fuskarshi hawaye na gangarowa daga idonta, 

ganin haka yasa Daddy da Nauman fita suka shiga d'akin da aka kwantar da Mamy da Naufal, 

Umairah na zaune gefen su, tana zubar da hawaye, ganin su Daddy sun fita yasa Najwah kwanciya kusa dashi tana shafa kanshi, 

zuwa k'irjinshi, tace " I love you, zan iyayin komai akanka, a hankali ta d'ora hannunta saman k'irjinshi, 

saitin zuciyarshi tana murmushi tace " ni kad'ai ce anan ko? 


Ta fad'a tana yi mishi kiss a kumatu, kamar saukar aradu Najwah taji muryar Neehal na furta NEELAH!, 

kwata-kwata muryarshi bata fita, dakyar ya iya furta sunan, fuska Najwah ta tsuke had'i da mik'ewa zaune, 

ta kafe shi da ido, ganin idonshi rufe, ta kuma dad'e tana kallanshi bai motsa ba, bata kuma k'ara jin yayi magana ba, 

yasata yin murmushi ta kwantar da kanta saman k'irjinshi, 

tace " I know dan ni kad'ai zuciyarka ke bugawa, nasan ni kad'ai kake so, " Neelah kece rayuwa ta ki taimaka ki dawo gare ni, 

idan baki damuwa ba mutuwa zanyi, ciwon sanki ne zai zama ajali na, zambur Najwah tayi tamkar an caka mata mashi haka taji, 

ji tayi tamkar ta shak'e shi kowa ya huta, gudun kar zuciyarta ta saka ta aikata abinda zata dawo tana danasani yasata mik'ewa ta fita, 

d'akin dasu Mamy suke ta shiga ta zauna, Nauman yace " ya tashi? 


Dakyar tace " a'a, zayyi magana salatin Mamy ya katse shi, saurin k'arasawa yayi yana murmushi, 

yace " Mamy ki tashi our Neehal is alive, da sauri Mamy ta tashi zaune tana kallan Daddy dan ta k'ara tabbatar da maganar Nauman, 

murmushi yayi yana shafa kan Mamy yace " yes! he's alive, cikin zak'uwa tace " da gaske Alhaji? 


Murmushi yayi had'i da rik'o hannunta yace " muje ki gani da idonki, suna gaf da fita Naufal ya farfad'o, 

cikin d'oki Umairah ta sanar dashi Neehal yana raye, jikinshi na rawa ya mik'e yana fisge k'arin ruwan dake jikinshi yayi waje, 

batare daya jira su Mamy ba, murmushi suka yi kana suka bi bayanshi zuwa d'akin Neehal, 

tsaye suka iske Naufal yana bin d'akin da kallo, turus duk sukayi suna kallan gadon da Neehal ke kwance ganin babu kowa, 

jikin Najwah na rawa ta nufi band'aki da gudu ta bud'e nan ma wayam babu kowa, 

" ina Neehal? 


Nauman ya tambayi Najwah, " nan fa na barshi kwanci yana bacci, " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, 

ya tafi neman Neelah, cikin rashin fahimta Nauman yace " ina Neelahn? 


"Bata nan, ta kwashe yaranta ta tafi, tashin hankali ne ya sanya Nauman kifawa, Naufal yayi saurin tare shi, 

a rud'e ya cakumi wuyan Naufal yana huci, take kamanninshi suka sauya, idanuwanshi suka koma asalin jajaye, 

ya horance, ya fita daga hayyacinshi, idanuwanshi suka rufe, kunnuwanshi suka dod'e ya daina ji da ganin komai, 

" ina kai min matata? 


Nauman ya fad'a cikin matsananciyar tsawa da saida ko'ina ya amsa, wallahi tallahi akan Neelah ina iya rabuwa da kowa, 

ina kuma iyayin komai, idan ma b'oye ta kuka yi kuna shirin wani abu saboda Neehal gwara ma tun wuri ku fito min da ita, 

yayi maganar a haukace, hannunshi Daddy ya rik'o da had'i da cewa " yanzu ba lokacin wannan bane, jeka sako kayanka kazo muje mu nemusu in yaso sai asan abinyi daga baya, 

Nauman zayyi magana Daddy yace " amma dai kasan bana magana biyu ko? 


"Tunda nake dakai ka tab'a ji ko ganin nayi magana na canja, ko nayi alk'awari na sab'a? 


Kai Nauman , ya sunkuyar k'asa yace " I'm sorry Daddy ban iya controlling kai na ne akanta, 

" wallahi tallahi ka sawa ranka aure tsakaninka da Neelah babu matuk'ar ina raye, koda hakan zai zama sanadiyyar mutuwa Neehal, 

kai da Neehal duk d'aya ne a waje na, dani da mahaifinka uwarmu d'aya ubanmu d'aya, 

kamar Neehal da Naufal, dan haka duk abinda zanyiwa d'an cika na shi zanyi maka, dakai dasu babu banbanci, 

d'a da dukiya ba'ayi musu mugunta da bak'in ciki dan Allah kad'ai yasan me morarsu, 

ka sawa ranka idan kaga ba'ayi auranku ba, d'ayan biyu kodai kai kace baka so, ko kuma cikin mu uku ni, kai ko Neelah wani ya mutu, amma ko ita kanta Neelahn ce tace bata sanka wallahi sai na d'aura auranku, 

sai sai hukunci da nufin Ubangiji, 

dan komai a hannunshi yake, shike yin yadda yaso, akan wanda yake so, 

dan haka ka kwantar da hankali ka, yana kaiwa nan ya fice, ya nufi get yana sauri tamkar zai tashi, su Naufal na biye dashi, 

Nauman office d'inshi ya shiga ya zira jalliya a gaggauce, ya fito, a bakin get ya iske Daddy yana tambayar masu gadin asibitin, 

" eh! Alhaji munga wani ya fita jikinshi babu kaya daga shi sai 3 quarter, amma babu ko riga a jikinshi, 

yana tangad'i kamar mashayi, " what! amma shine kuka barshi ya fita? 


Nauman ya fad'a a hasale, " wallahi babu yadda bamuyi mu dakatar dashi ba, yak'i sauraronmu

dan ko magana baya iyayi sai hakki, babu wanda ya k'ara magana suka nufi inda motocinsu suke aje, 

Daddy ya bud'e mota zai shiga Naufal yace " ina zamu je Daddy? 


"Nemansu mana! Nauman ya fad'a " ta ina zamu fara!? 


Gaba d'ayansu suka yi shiru, sai can Umairah tace " Sunkhanni, na tabbatar Neelah can ta tafi dan nasan halinta ciki da waje, 

Nauman yace " nima na yarda da maganarki na kuma tabbatar shima Neehal can d'in ya nufa, 

" muje Mamy tace a k'agauce, Nauman ya kalli Naufal yace " kaja Umaira da Najwah a motarta, 

ni zan ta ja su Daddy a d'aya motar, babu musu Naufal ya karb'i key d'in, yaja zuwa airport.


A b'angaren Neehal ko dama idonshi biyu ba bacci yake yi ba, yana ganin Najwah ta fita, 

ya cire oxygen da cannular dake jikinshi, had'i da fisge na'urorin dake manne a k'irjinshi, 

daga shi sai 3 quarter ya fita babu ko takalmi balle riga, yana dafe da k'irjinshi, 

while yana ta faman haki da tari, gumi kam yadda kasan ruwa aka zuba mishi, da d'an sauri yana jan k'afarshi dakyar ya nufi get, 

babu yadda masu gadin basu yi su hana shi fita ba amma suka kasa, yasan babu inda Neelah zata tafi daya wuce Sunkhanni, 

dan haka ya yanke shawarar nufar can, ya dad'e bakin titi yana tsayar da masu napep suna k'in tsayawa dan a zatonsu mahaukaci ne, 

musamman yadda k'asumba tayi mishi buzu-buzu a fuska, gashi babu riga da takalmi, sai dakyar Allah ya taimake shi wani ya d'auke shi zuwa Airport, 

yasha wahala kafin a bashi ticket sai da yace musu ganin likita zashi kafin suka barshi ya shiga jirgi, ya d'aga zuwa Taraba babu riga balle takalmi, 

su Daddy ma Airport d'in suka je, babu b'ata lokaci suka shiga jirgi zuwa Taraba State. 


K'AUYEN SUNKHANNI, GARIN ASALIN FULANIN DAJI


Hummm such is life, rayuwa kenan, wata rana kayi dariya, wata kayi kuka, abinda ya baka dariya wata rana shi zai saka kuka, haka d'an hakin daka raina..! abi duniya a hankali, wallahi tallahi Allah baya bacci, abinda ka raina zai iya zame maka babbar matsala a rayuwa, abinda baka tab'a tunani ba zai iya addabar rayuwarka, abinda ya baka haushi zai baka mamaki, musamman masu wulak'anta mutane, mutum yana da daraja dan suk halittun duniya babu kamar d'an Adam, ya kamata asan daraja da k'imar D'an Adam, wulak'anci, fariya, girman kai, d'agawa ba'abun yi bane, dan babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah, duk wanda yake wulak'anta mutane sai yaga ikarshi a rayuwa so take note






STAY AT HOME, STAY SAFE PLEASE, PRAY & ASK ALLAH FORGIVENESS, PRAY FOR THE WHOLE WORLD PLEASE







MOMYN ZARAH

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.