Free chapter · Read without an account
Chapter 8
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 15-16
Dagowa Abdallah ya yi da sauri ya kalli Abba, saidai gani yayi kamar bashine ya kira sunan nashi ba, dan haka gabanshi ya cigaba da faduwa, zuwa can ya dake cikin sunkuyar da kai ya ce, "Abba lafiya kuwa?" Fuskar Abba daure tamau ya dago ya kalli Abdullah sannan ya ce, "Na ji wani mummunan al'amari da ga gareka Abdallah, banso ace na yi maka magana yanzubaz saidai hankalina yaki kwanciya, nakasa zuba ido koda na kwana biyu ne, idan abin da naji gaskene zan gwammaci matuwa da ganin irin wannan al'amarin"
"Ni Kuma Abba?" Abdallah ya fada tare da tattara hankalin sa akan Abba gabanshi na faduwa sosai.
"Kai fa Abdallah, ina son in san menene alakanka da Sumayya? bana son zagaye-zagaye, abu daya na tambaye ka, dan haka amsan na ke bukata, ina son in san ta in da ka kulla alaka da matar aure dahar, karkamin karya" Zufa ne ke kara yanko wa Abdallah, tare da nemo kalmomin da zai kare kansa da su wurin Abba, gefe guda na zuwaciyarshi kuwa na kara zuzuta mishi kiyayyar Nur, tare da rayawa azuciyarshi dole ne ya kirkiro sanadin da zatabar gidan.
"Da kai nake magana" Abba ya sake fada wannan karon a hasale ya ke.
Cikin tashin hankali Abdallah ya sunkuyar da kanshi batare da ya shirya ba, jin sunan Sumayya a bakin Abba, daker ya iya daurewa ya ce, "Abba waye ya fada maka?"
"Abdallah amsan kawai nake son ka bani, aina naji ko waye ya gaya min wannan ba matsalarka bace"
"Abba bani da wani alaka da ita" Cikin Ido Abba ya ke kallon Abdallah gani yayi zufa sai gangaro masa ya ke dan haka ya ce, "Hakika zan ji mamaki kwarai idan na tabbatar da ka na aikata irin wannan abubuwan, domin ko kadan be yi kama da ɗabi'un ka dana sani ba, kana da ilimin ka daidai gwargwado, sannan ka mallaki hankalin kanka, kasan cewa kebewan da macen da ba muharamarka ba haramun ne, bare Kuma matar aure, Babana me ya kaika wannan danyen aikin?"
"Abba ni ban aikata hakanba Sam, yadda dani da kuke yi yasa ake son a bata ni a gurin ku, kuma nasan cewa ba kowa bane zai yi irin wannan maganar sai Nur, dan yariyar nan yanzu..."
Katseshi Abba yayi da cewa, "Me yasa zaka ce Nur ce ta fada?"
"Abba baka sani bane, yariyar nan ta dade tana son taga bayana, kwanaki Nur ta hadani Mamy akan maganar Sumayya, bansan da ga Ina aka turota ta batani a wurin ku ba, taje ta ce ma Mamy wai ina neman Sumayya, haka ran Mamy ya faci kiris ya rage ta tsine min, na yi kokarin wanke kaina awurin amma Mamy taki bani dama, kuma har yanzu ta na akan haka, sabo da kawai Nur ta fada mata, kenan ita Nur bata karya nine makaryaci, aranar raina ya baci har na daki Nur, ganin haka ciwon Mamy ya tashi, bansan me na tarewa Nur ba acikin gidan nan Abba, idan baka manta ba kwanaki a gabanka ta jefeni da babban kufin kwalba batare da na mata wani abu ba, ko na mata wani abu ma ai be dace tamin haka ba, yanzun kuma wurinka take son batani, me na tare mata Abba" Karake maganar yayi kamar zai fashi da kuka; dan haka Abba ya ce' "Babu abin da ka tare mata, wata kila gaya mata ake waje, amman akwai wadda taci min adakin Auwal ta ganku tare da idonta ba gaya mata aka yi ba"
"Abba to ta kawo wadda ya fada mata, idan ma ita ta ganni ta kawo shaida, ni zan iya kiran su Auwal su zamar min shaida, waya yake kokarin dagawa Abba ya ce "Dakata Babana, duk ba wannan bane mafita, ko ka aikata ko baka aikata ba Ina baka sharawa kaji tsoron Allah a dukkan lamuranka, sannan abu na gaba shi ne, maganar aure. Ina son ka yi aure nan kusa, dan banga abin da kake jira ba."
Jikin Abdallah da sanyi sosai ya ce, "Abba ka manta da mgnr karutu da zan tafi nan da wata biyu masu zuwa, kuma zai iya daukana tsayon shekara daya kafin na dawo"
Kara daure fuska Abba ya yi tare da fadin, "Toh yanzun Yaya ka ke nufi?"
"Idan na kammala zan yi Abba."
"Babana bani da wani buri ayanxun illa inga ka yi aure, Kuma nan kusa nake so, idan tafiyan ta tashi saika wuce da matar ka.
Shiru Abdallah yayi tsayon lokaci, zuwa can ya ce "Shikenan Abba, zan yi in sha Allah"
Yauwa zan yi tsananin farin ciki da hakan, nasan a kodayaushe kai me bin umarnina ne, ina son akan auren ka burgeni kazo min da labarin nan kusa"
Godiya yawa Abba, sannan ya tashi ya fice jikin sa a sanyaye. Kai tsaye dakin sa ya wuce cike da haushin Nur dankare a zuciyar shi, tunanin ya shiga mai zurfi akan shakkun da Nur tasa azuciyar Abba da Mamy game dashi, mafita ya shiga nema idonsa jawur akarshi hankalinsa ya tsaya akan cewa yayi auren kawai domin shine zaisa Nur ta fita hanyarsa.
Bayan sati daya Nur ce kwance tsakiyar gado bayan ta dawo Islamiyya, har yanzun tunanin Abdallah da tagani tare da Sumayya take, sosai abin ke daure kanta, tana cikin wannan Yana yin ta ji muryan Helen dan haka ta tashi zaune a daidai lokacin da Helen din ta shigo dakin, yadda taga fuskan Helen ya sa hankalita tashi sosai tare da fadin lafiya?
Nur ni da Mamma ne, na zo in gaya miki ne zamu tafi, idan mama ta ji sauki kila mu dawo... Katse Nur ta yi tare da cewa "Karatun ki fa?"
"Ban sani ba Nur, ni dai kawai nasan Mama bata da lafiya shine abin da ya dame ni yanzu, nina ce mata ta zo muje mu nemi lafiyarta"
"Babu Inda zakuje Helen, ki shigo da Mamma nan gidan barin je inyiwa Abbanmu magana.
Jimmm Helen ta yi tana kallon Nur tare da mamakin Kaunar da take nunawa a garesu batare da ta damu da banbancin addinin dake tsakanin su ba, bayan Nur ta fita dakin tabi da kallo komai tsaf, duk da cewa gidan Poul keraren gidane amma sai ya fiye mata can ban sha'awa, haka nan taji kaunar gidan na ratsa sassan jikinta, dan haka ta saki ajiyan zuciya mai cike da kwanciyar hankali.
****
Nur zaune gaban Abba, bayan ya sallami wani dake zaune daf dashi ya ce, "Nur! Cikin wasa da hannun Nur ta dago kanta, Cike da fara'a Abban ya ce, har yanzun baki bar damuwan bane? "
"Na bari Abba"
"Yauwa ki kwantar da hankalin ki, komai zaizo karshe, na yi magana dashi sosai, a yanzun haka maganar da nake miki aure zai yi, bayan na yi magana dashi da kwana biyu yayi min bayani akan iyayen yariyar da yake so, mun kuma je mun nema masa kuma sun bamu, a yanzun haka su muke jira su tsayar mana da rana."
Cike da fara'a Nur ta ce "Abba yaushe za'ayi bikin?" Kara fadada fara'a Abba yayi sannan ya ce, mu a shirye muke su muke jira"
"Abba!"
"Na'am Nur, na lura akwai abin da kike so ko?"
"Eh Abba"
"Toh inajin ki"
"Abba kawata dinan Helen, itace Mamman su bata da lafiya wai zasu koma kauyensu da zama"
Cikin rashin fahimta Abba ya ce "An nema maganin ne anan ba'a dace ba?"
"A'a Abba, kudin maganin ne babu ko abincin da zasuci basa samu agidan, kuma idan helen ta tafi shikenan ba lallai azana jabawar karshe da ita ba"
Shiru Abba ya yi tsawon lokaci zuwa can ya ce "Mai kike so ne yazon?"
"Abba Helen na cikin gidan nan yanzun haka, dama ka barsu su zauna anan"
Shiru Abba yayi zuwa can ya ce, "Wannan ba mai yiyuwa bane Nur, idan d'anta ya kasa riketa kamata ya yi ta koma gida kamar yadda zasu yi yanzun, shi taimako wani lokacin yana da wuya musamman kinga su ba musulmai bane, duk da cewa sum dade acikinmu, yanzu Ina ga abin da za'ayi zan bada kudi a kaita asibiti sannan zan musu sayayyar kayan abinci ta koma gida suci gaba da hakuri."
"Amman Abba bata da lafiya yanzu, Kuma ta riga tayi fushi da gidan, dan Allah Abba kadan barsu ko kwana biyu su yi a nan dan Allah, da mamaki Abba yabi Nur da kallo tare da ganin tana dauko ma kanta damuwan da yafi karfinta, jimmm Abba yayi tsawon lokaci zuwa can ya ce, "Shikenan"
Cike da farin ciki Nur ta shigo da su cikin gidan, ganin yanayin jikin Mamma Abba ya bawa Bashir izanin akaita asibiti, Mamy ce dauka zaninta na atamfa ta daurawa Mamma akan siket dinta dabe karasa guiwa ba, sannan ta daura mata dankwalin atamfar a kanta, bayan motar ta zauna saidai har yanzun rawan dari take dan haka Mamy ta kwalawa Nur kira bayan ta amsa ta ce ta kawo mata hijjabi, cikin gudu gudu Nur ta kawo hijjabin kasancewa Mamy na gaban motar bayan ta kawo Mamy ta ce tasawa Mamma, wannan karon cike da mamaki Nur ta nufa Mamma Helen dake zaune kawai tana rawar dari, cikin sauri ta zura mata, yadda Mama ta cure acikin hijjabin tamkar ba ita ba, sai da motar ta fice a gidan sannan Nur ta koma cikin gida, sai yamma su Mamy suka dawo, wannan lokacin babu wani rawan sanyi da take abinci taci sannan Tasha magani tai bacci.
Bayan kwana su uku sosai Mamma ta murje ta yi jawur da ita tamkar ba ita bace tazo da masassara, har yanzun ta na sanye da hijjabi tare da zannuwan da Mamy ta bata, ga abinci me kau har sai sunci sun barshi, komai da suka basu Mamy ta hada guri daya domin yaune Abba yayi Umarni su koma gida, misalin karfe uku na rana Mamy ta raka Mama gurin Abba domin su gaisa Kuma ta yi godiya, cikin Sakin fuska su ka gaisa da Abba, sosai ya nuna jin dadinshi ganin ta samu lafiya, nan ya bata kauta kudi bayan kayan abinci daya haka hada mu su, kuka ta fara tare da fadin, "Tun da nake a duniya ban taba tsintan kaina cikin nishadi da farin ciki kamar na yau ba, na sha wahala tun ina da cikin poul, mijjna ya mutu tun suna kanana nakiyin aure, duk domin ingina rayuwar Poul da kanwarshi, ba irin wahalan da basha ba wurin biya bishi kudin makaranta, da hidimar rayuwar sa, har ya zama abin da ya zama yanzu, amma daidai da rana daya betaba faranta min kamar haka ba, yata min alkarin zanji dadi amma Yana yin aure komai ya canza, dakatawa ta yi da maganar ta share hawaye sannan ta ci gaba da cewa, "Da Poul kadai nake takama, akanshi duk na aje burina, na dauki tallar ruwa akaina na biya mishi kudin makaranta amman yaki kulawa dani alokacin da karfina ya ke shirin karewa, sai gashi ku da bantaba tunanin zaku taimakeniba ku ne ku ka taimakeni, acikin kwana uku da na yi da ku naji ina kaunar ku, ina jin kewan rabuwa da ku, Alhaji ni da Helen zamu musulunta" Cikin zare ido Abba ya kalleta sannan ya juya ya kalli Mamy da fuskarta ya cika da mamaki, koda wasa Bata tsammaci jin irin wannan kalamin ba, cikin daburcewa Abba ya ce, "Kina nufin zaki zama musulma?
"Eh ta bawa Abba amsa cike da karfin guiwa, cike da sanyin jiki Abba ya ce, "Ikon Allah, mikewa yayi ya dauke hularshi ya sanya sannan ya Kira Mamy su ka fita, bayan tsayon lokaci Mamy ta dawo daf da Mama ta zauna tare da cewa Maman Helen kin yi shawara da yaranki kuwa?, Musamman shi babban kar abin ya kawo mu ku matsala."
"Karki da mu da shi Hajiya, bazai da mu ba, na yi magana da Helen mun yanke wanan shawaran Poul ba ma gabanshi, zai yi rayuwarsa ne mu yi ta mu"
Jimmm Mamy ta yi tsayon lokaci zuwa can ta sake cewa ba kuma fushin abin da yaron ki ya miki bane ya sa zaki musulunta? Ina nufin yanzu in da a ce zai bar abin da ya ke yi za yi zamanki a addinin ki? Cikin sauri Mama ta girgiza kai tare da fadin, nutsuwa da kwanciyar hankali da na gani a tattare da ku ya jawo hankalina, kana uku da na yi a gidan ku na fahimci wasu abubuwa da dama a tare da ku da kuma yaran ku, sannan kuma bana iya tuna rabon da na samu kwanciyar hankali da nutsuwa irin wadda na samu cikin kwana ukun da na yi a gidan nan.
Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta fita, zuwa can su ka sake shigowa tare da Abba, zama ya yi sannan ya ce, "Yanzun abin da za a yi ki je gida ki kara nutsuwa tare da zurfafa tunani, ki yi shawara da yaran ki, zuwa gobe ko jibi sai kizo...." Katse Abba Maman Helen da ta yi da fadin, "Ni fa na riga na gama yanke shawara, yau nake son nabar addinin can" Murmushi Abba yayi jin furucinta saidai ya na dan bargaba akan labarin nata, dalilin tuna waye danta, tun da ya mallaki gida a unguwar ta su baya mu'amala da kowa, ko daga hannu baya yi, dan haka ba kowa ne ya san fuskarsa ba, da wuya kasamu mutumin da zaice ya sanshi a fuska, saidai ana iya shaida duk motocin da yake hawa, ajiyan zuciya Abba ya yi sannan ya ce, "Shikenan tashi muje wajen Malam Zubairu. Mikewa suka yi fuka fito, yayin da Mamy ta kwalawa Helen Kira bayan ta fito suka shiga motar suka tafi.
Ganin fitan su Nur tace Mamy naso na rakasu har gida, ba gida zasu ba, Mamy ta fada tana gyara zamanta sosai nan ta kwashe komai ta bawa anuty da Nur labari, sosai Nur ta shiga farin ciki hakama aunty Saratu, bayan kusan awa biyu su Abba suka dawo, wannan karon Helen sanye take da hijjabi, ganin haka kwallar farinci ya cika idon Helen rungume juna suka yi ita da Helen tsayon lokaci. Abba ne ya Umarci Nur da tazo ta raka su gida, fitowa suka yi har da Abba, sabo da kayan abincin da ya hada musu ya sa ya kaisu har kofar gida sannan suka dawo gida, sai dai har yanzun a cikin zuciyar Abba be gama gamsuwa da Helen da Mahaifiyarta ba, dan haka ya ke dan rage fara'arsa, wani abu da yafi daga hankalinshi shi tunda suka fara ganarwa komawa Musulunci gabanshi ya fara haduwa kuma har yanzun daya sauke su ya dawo gida faduwam gaban nasa gaba yake ba baya ba, aduk lokacin da gabanshi ya fadi fuskar Poul ce ke fado masa arai dan haka ya shiga karato addu'oi
*****
"Duk in da nake tunanin zasu je naje basa nan, na gaji sosai, Ina son in ganta tukuna in je wurin aikina, komai nawa ya tsaya, babu Mamma babu Helen, anan babu Mamma a can gida babu Mamma" Ajiyan zuciya matar dake tsaye a gabanshi ta yi sannan cikin hausarta da bata fita sosai ta ce, "Wai dama ba kai ka sauke su ba, ai sun shigo dazon da kaya mai yawa"
"Mamma? sun dawo?" Tabe baki Matar ta yi sannan ta ce sun dawo, amman fa akwai matsala kamar dai almajirai haka suka dawo, kuma sun saka hijabi ajikinsu.
Hijjabi? Poul ya fada cikin daga murya sannan ya nufa hanyar da zata sadashi da dakin dasu Helen suke yana tafe kamar mai shirin tashi sama.