Free chapter ยท Read without an account
23
by Hauwa A Usman ยท KโADDARA TAH
'''K'ADDARA TAH!!!'''
๐น
๐น๐น
๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น๐น
~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_
*๐KAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโ๐ป*
_(DASHEN ALLAH)_
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_
*EDITING BY MOMYN ZARAH*
23
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un abinda kowannen su yake dad'e kenan, jin jiri na d'ibarta ne yasa dole Mama ta zaune shiko Abba gumi ne kawai ke keto masa, shi kansa likitan ganin irin tashin hankalin da suka shiga ne yasa shi fuskantar lalle akwai wani abu a k'asa, kasa hak'uri yayi yace " lafiya kuwa naga duk kun shiga damuwa naga ai abin farin ciki ne, ina mijin ta?
Cikin k'arfin hali Mama tayi murmushi tace " tsabar farin ciki ne yasa mu shiga wannna halin daka gannu, mijinta ya mutu kuma bamuyi tsammanin an samu rabo, murmushi shima yayi yace " ikon Allah kenan, haka dama Allah yake ikon sa, shiru suka yi su duka babu wanda ya k'ara cewa k'ala, magaunguna ya rubuta musu yace" idan kun fita ku siya.
Suna komawa gida kowa yayi d'aki tana shiga d'aki ta fad'a gado ta saki kuka mai ban tausayi da k'ona zuciya, tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allah wannan wacce irin mummunar k'addara ce, Allah kai kace baka d'orawa bawanka abinda bazai iya, ya Allah ka bani ikon cinye jarabawar nan, ya Allah ya taimakamin ka d'auki rai.
K'ara fashewa tayi da wani kuka tana ta surutan ta ita kad'ai, Mama na shiga d'aki ta sami Abba zaune a k'asa ya had'a kai da gwiwa yayi tagumi sai zufa ke zubo masa kusa dashi Mama ta zauna ta dafa shi, sai kuma ta fashe da kuka mai k'ona rai.
A hankali ya d'aha kansa sama ya kalleta, ba kad'an yake jin zafin kukanta a ransa ba, yace " haba Maman yara ke kiyi kuka suma suyi kuka ya kike san nayi, idan suma yaran suka ga kukan ki ai sai ki karya musu zuciya, ki dubi girman Allah kiyi shiru, sautin kukan nata ta rage sai shashsheka dake fita a hankali, yaci gaba, ki yarda da K'ADDARA mai kyau ko marar kyau mana, Allah baya tab'a barin d'ayanmu ba tare daya jarrabe mu ba, mu irin tamu K'ADDARA kenan kin san ta wasu, kin san wace irin jarabaawa Ubangiji yayiwa wasu? kai ta girgiza alamar a'a, murmushin k'arfin hali yayi yaci gaba" to ki goge hawayenki, ki godewa Allah a bisa jarabawar da yayi mana, mu daure muci jarabaawar nan, ni yanzu zuciya ta tayi sanyi, saboda yawan kiran Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, da hasbunallahu wani'imal wakil, subhanallah Alhamdulilah Allahu Akbar, na yarda da K'ADDARA, duba da irin halin da Fauziyyah ta shiga, na yarda da jarabaawa ta Ubangiji, na d'auka, Allah ya bani ikon cinye ta, a hankali tace" Amin.
"Ni dai abu d'aya na sani idan duniya zata tashi baza'a tab'a zubar da cikin nan ba, wallahi Allah sai ta haife abinda ke cikin ta, wani irin mummunar fad'uwa gaban Mama yayi, a ranta tace " shikenan abinda nake gudu ya faru, yanzu sai munyi shege, jin shirun da tayi yasa Abba tab'a ta yace " ya akayi ne Maman yara? sanin halin Abba shiyasa ta b'oye halin da take ciki, dan yanzu itama sai ya shafe ta, murmushin k'arfin hali tayi tace " hakan yayi, "yawwa Maman mu, ya fad'a da alamun tsokana dariya tayi, sai da Abban ya kwantar mana da hankali sosai, sannan yace " maza jeki lallashi Fauziyyah dan nasan yanzu tana can tana sana'ar tata.
A hankali Mama ta shiga d'akin a kife ta samu Fauziyyah tana ta faman kuka tana ta sambatu, ita kanta bata san me take cewa ba, ba k'aramin tausawa 'yar tata tayi ba, a hankali ta zauna kusa da Fauziyyah ta dafa ta, a hankali ta d'ago kai, idonta duk ya kumbura ta zube a k'asa tana kuka tace " Mama na jawo muku magana na jawo muku kunyar duniya, dangin Abban mu sun samu abin fad'a burin su ya cika, dan Allah Mama ku yafe min ko naga haske a rayuwa ta ta gaba, Mama ki bawa Abban hak'uri, wallahi na gwammaci mutuwa ta da na saku cikin wannan mummunan halin, Mama na gwammaci ciwo mai tsanani ko hauka da ganin halin dana saku, Mama dan Allah ku rok'a min Allah ya d'au rai n.........
Da sauri Mama ta ta katse ta ta jawo ta jikinta ta rungume gaba d'ayan su suka saki kuka, abin ban tausayi, sun dad'e a haka sannan Mama tayi k'arfin halin yin magana ta daina kukan tace " bakomai Fauziyyah mu mun yarda da K'ADDARA, mun yarda da jarabaawar Ubangiji, dan kin shiga wannan halin bazamu tab'a kyamatarki ba, iya kaci dai mu nuna miki kuskuren ki, to Alhamdulilah mun nuna miki kuma ke da kanki kin gane hakan, haka dai mama taita fad'a mata kalamai masu dad'i har ta kwantar mata da hankali
*************************************
Tun abinda Fa'iz yayiwa Fa'iza tsanar shi ta k'ara k'aruwa a zuciyar ta, babu abinda ke yi mata yawo a zuciya sai wutar d'aukar fansa dake ruruwa a zuciyar ta, ta zama cikekkiyar 'yar maye kullum tana cikin shaye-shaye da maye saboda tsabar takaicin abinda Fa'iz yayi mata ta haukace saboda tsabar neman hanyar d'aukar fansa ta kasa samun sukuni da kwanciyar hankali burinta kawai ta d'au fansa a kansa, so take taga tayi masa abinda har ya mutu bazai manta ba, so take taga ya wulak'anta ya tozarta ya zama abin tausayi ko a wajen mak'iyin sa ma balle kuma masoyansa, wannan tunani ne yayi mata yawa ganin ta rasa mafita ne yasa ta yawan shan kayan maye.
Fa'iz ne zaune da Gan's d'insa yana basu labarin irin ni'imar daya kwasa a jikin Fauziyyah yace " wallahi tunda nake ban tab'a yin sex da mace kamar Fauziyyah ba, na dad'e ina mamakin irin ni'imar, da laushin fatar ta, fatar ta ga santsi, gaskiya yarinyar tayi har yanzu ban k'oshe da ita ba, ko yanzu idan na samu dama zan dama, tun ina 18yrs na fara sex, amma Allah har yau Allah bai had'ani da yarinya kamarta ba, nayi sex da turawa, indiya, larabawa,China, nan gida Africa kuwa ina tunanin babu da jinsin da banyi sex ba, amma wallahi yarinyar nan ta tsotse min ruwan kai na, naji mugun dad'in ta, wata irin shewa suka saki gaba d'ayan su, d'aya daga cikin su yace " to muma oga ka barmu mu dankwali arziki mana, wani ma yace " muma muji abinda kaji ba, dariya yayi yace "aini na gama nawa, is left 4 u, idan kuna ra'ayi zaku iya zuwa.
"Wani yace " to oga ta wacce hanya ina shawara, dariya yayi har sai da dimples d'insa ya lotsa, ya shafa sumar kansa yace " ta hanyar dana bi mana, "oga wacce hanya kenan? cikin kosawa da maganar dayake shima bamai yawan san magana bane yace " Fa'iza mana, kud'i kawai zaku sakar mata kuga aiki har gida zata kawo muku ita.
Dad'i suka ji sosai, wani yace " wani hanzari ba gudu ba, yanzu ina zamu nemo Fa'iza, tsaki yayi yace " oho muku, abin bai dame ku ba kenan tunda har kuke neman inda zaku nemo ta, tashi yayi yana tangad'i yabar wajen wani d'aki ya nufa inda kyawawan 'yan mata ke jiransa ya shiga, sai da ya gama masha'ar sa dasu sannan ya kwanta gefe yana mayar da numfashi, yana tunani ya rasa mai yanzu tunda yayi sex da Fauziyyah baya iya samun biyan bik'ata da kowacce mace, idan zai kwana yana abu d'aya baya samun gamsuwa, ya rasa dalili, wani lokacin ko tunanin movements d'in shi yayi da ita sai kaga sandar girma ta mik'e baya iya samun nutsuwa da kowacce mace, duk abin ya dame shi ya rasa ina zaisa kansa.
Kuma duk irin wulak'anci da yake yiwa mata a banza dan su ke binsa, ko dan Fa'iz cikekken namiji ne ga kyau na ajin farko dan duk inda namiji mai kyau yakai to Fa'iz yakai ko ince harma ya wuce, ga dogo, mai k'irar zaki, mai faffad'an k'irji, wanda gashi yayi kwance a k'irjin, gashi da kwantacciyar sumar kai kamar ta Renoldo ga saje wanda ya had'e a hab'arsa, yayi kamar askekken gemo, fari ne tas, sai godon hanci da lulu eyes, irin na salman khan, gashi da dimples wanda ko magana yake sai ya lotsa, ga kud'i ga hutu gashi d'an gata, gashi da aji, dan yana class akwai shi da yanga, shi magana ma ba damunsa tayi ba, balle yawan surutu, abin sai dai muce masha Allah.
Bayan abokanan Fa'iz sun sanarwa da Fa'iza buk'atar su akan Fauziyyah, sai tayi murmushin mugunta ta cije leb'e, a ranta tace " Alhamdulilah abin nema yazo ya same ni har inda nake ba tare dana sha wahala komai ba, jin tayi shiru tana ta murmushi ne yasa su yi mata magana " lafiya Fa'iza?, bakomai tace, " ni bana buk'atar komai daga hannunku, banasa kud'in ku, kyauta zan kawo muku ita, amma da sharad'i! had'ani baki suka yi gaba d'ayan su suka ce mata " sharad'in meye, "a'a bazan sanar daku ba sai hak'onku ya cimma ruwa, ganin duk sunyi jugum-jugum ne ya sata cewa " kar fa ku tada hankalinku ba wani abu bane mai wahala, abu ne na taimakon kai da kai, "ok badamuwa, yanzu yaushe zaki kawo mana ita? " da wanne lokaci kuke so, dan ni ko yaushe ina iya kawo muku ita, ko yanzu kuke so, "yawwa mu da zaki kawo mana itan ma yanzu ai da yafi.
"Ok ina zan kawo ta, " ki kawo mana ita gida na d'aya daga cikin su yayi managa, " to ku bani nan da 30mnts zaku gan mu, suka rabu a haka tashi tayi, tayi shigar mutunci hijab d'inta har k'asa, ta tare d'an adai-daita sahu ta nufi gidan su Fauziyyah.........
*Alhamdulilah*
*MOMMY ZARAH*
'''A gaskiya nayi matuk'ar jin dad'i da had'in kan da kuka bani, ina godiya sosai, Allah ya saka da Alkhairi, Ubangiji yabar zumunci da so da k'auna, kunyi comment sosai naji na gani Kuma na yaba'''.
'''One love daku iya wuya ana mugun tare, ina ji daku sosai mosoyana, luve you alot'''
~Please kuci gaba da comment yadda kukayi min juya~
~Please comment~๐๐ป
~Please comment~๐๐ป
~Please comment~ ๐๐ป
_Idan zaku rink'a yin comment zaku rink'a jina akai-akai_
Bye