Free chapter ยท Read without an account
24
by Hauwa A Usman ยท KโADDARA TAH
'''K'ADDARA TAH!!!'''
๐น
๐น๐น
๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น
๐น๐น๐น๐น๐น
~NAH~
*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_
*๐KAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโ๐ป*
_(DASHEN ALLAH)_
_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_
*EDITING BY MOMYN ZARAH*
24
A k'ofar gidan su Fauziyyah adai-daita sahu ya ajiye Fa'iza, da sallamarta ta shiga gidan, Mama ta iske a tsakar gida tana wanke-wanke, har k'asa Fa'iza ta durk'usa ta gaida, Mama,cikin fara'a Mama ta amsa mata, tace mata " shiga ciki mutuniyar taki tana d'aki bata jin dad'i ne, zazzab'i da ciwon kai ke damunta, " to Mama zan shiga tana maganar tana cire hijab d'in jikinta, " Mama tashi na k'arasa wanke-wanken, "a'a Fa'iza ki bari na ida karki b'ata jikinki, "lah bakomai Mama idan bamu taimaki iyayen mu ba meye amfanin mu, sosai Mama taji dad'in maganar ta, murmushi tayi ta d'auraye hannunta, Fa'iza ta zauna ta k'arasa wanke-wanken, tana yi suna hira da Mama, ta share gidan tas ta gyara ko ina.
Fai'za na shiga d'akin ta iske ta akan sallaya tana karatun Qur'an tana kuka, da sauri Fa'iza ta k'ara wajenta da alamar tashin hankali a fuskarta, tace " lafiya dai k'awata mai yake damunki haka, kai Fauziyyah ta d'ago ta kalle ta, cikin sanyi murya tace " bakomai, ina kika shige ni, inata nemanki na rasa ki, a hankali Fa'iza ta zauna a gefenta, tace" wallahi laifi nayi shine baban mu ya kwace wayata kuma ya hana ni fita ko k'ofar gida, shine kika jini shiru kwana biyu, kema kin san lafiya bazaki ji ni shiru ba, siririn hawayen dake zubo mata ta goge, kafad'arta Fa'iza ta dafa cikin alamun tausayi, tace" wai k'awata mai ke faruwa dake ne, naga duk kin fita hayyacinki, kin birkice, cikin kukan da take k'ok'arin dannewa ya kufce mata, kyale ta tayi tayi mai isarta sannan ta lallashe ta.
Babu yadda Fai'za tayi da Fauziyyah akan ta fad'a mata abinda ke damunta ba, amma tak'i fad'a mata, tayi bugun cikin harta gaji, ta kyale ta, tsakar gida ta fito da Fauziyyah, Mama tayi mamakin fitowar Fauziyyah saboda tunda abin ya faru bata fitowa ko k'ofar d'aki, kullum tana cikin d'aki tana kuka, zaunar da ita tayi ta tsefe mata kanta ta dafa mata ruwan wanka ta kai mata band'aki, tace " Fauziyyah tashi kije kiyi wanka ki wanke kanki san nayi miki tsoki, to Fauziyyah tace, ta mik'e ta shiga wankan, sosai Mama take mamaki, amma bata tace musu komai ba, ido kawai ta zuba musu.
Wanka tayi ta wanke kanta ta shafa mai ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa, da yake Fauziyyah doguwa siririya ce, marar tumbi, sai faffad'an k'ugu, ga d'uwawu, da hips tana da nonowa a tsaitsaye kamar tasa, irin su Fauziyyah ake kira da coka cola shape, sai cikin dake jikin ya lafe bai fito ba, farar hoda kawai ta shafa sai lip gloss, abinka da farar mace aiko aiko sai cikin ya kara mata haske ta zama kamar zabiya dan har wani jaja yalo yalo takeyi, ita kanta Fa'iza kamar yau ta fara ganinta ta k'ura mata ido, tace " kai k'awata Allah yayi halitta anan ke kinganki kuwa kamar Aishwairiyya rai, kai wallahi kamar ku d'aya sak, ashe da 'yan makarantar mu ke fad'a ba k'arya sukayi ba, musammman ma idonku da tsayin,da gashin kan, a biyu kawai zaki fita daga nono, sai hips, dariya Fauziyyah tayi har sai da hak'oranta suka fito tace "hmmmm k'awata kenan, " eh mana ai kema kin san kuna kama sosai.
Shiru Fauziyyah tayi a ranta take magana ita kad'ai, ita kanta tasan suna kama sosai dan ita kanta wani lokacin har mamakin kamar ta tayi da Ashwariyya Rai, 'yan gidan TV sun sha zuwa suce zasuyi hira da ita, ita ke k'in yarda, Fa'iza ce ta katse mata tunanin ta, ta hanyar cewa " ke ni zauna inyi miki kitsonki, zama tayi ba musu, duk iya kitson Fa'iza da kyar ta iya yiwa Fauziyyah shoku, saboda tsantsi, tana yi yana warwarewa.
Bayan ta gama mata kitson ne Fa'iza tacewa Fauziyyah " k'awata muyi girki ko? " eh kawai tace, Fa'iza da kanta ta tambayi Mama abinda za'a d'ora Mamance tace " su d'ora komai suke so, bayan kamar 2hrs suka gama dafadikan shinka suka saka mata isassun kayan lambu, zubo musu tayi suka zauna suna ci, da gudu ko sallama babu Aisha ta shigo, band'aki ta wuce, sai bayan ta fito hankalinta ya dawo jikinta k'amewa tayi tana kallon Fauziyyah ta kasa magana sai data gaji dan kanta sannan tace " Aunty kin daina kukan da rashin lafiyar? cikin sanyi Fauziyyah tace " eh na daina in sha Allah, aiko da gudu ta fad'a jikin Fauziyyah tana cewa "yawwa Aunty ko ke fa, har na dad'i da gidan yayi shiru ba dad'i, sai kuma idan ta ya kai kan shinkafa wani wawan tsalle tayi gami da sakin ihu tace " yeeeeee jollop rice with vegetables, yau zanci dad'i.
Sosai Mama take jin dad'in sakewar Fauziyyah yau, gashi har gidan ya fara dawowa normal, tana zaune tana kallan su sai murmushi take, bayan sun kammala komai ne Fai'za ta kalli Mama tace " zan tafi ko zamu je da Fauziyyah na d'an zazzagaya da ita naga kwana biyu bata fita ba, d'an shiru Mama tayi sannan tace " Allah ya kiyaye hanya amma karku dad'e, "to Fa'iza tace, a ranta kuwa kamar ta daka tsalle dan murna.
Suna fita Fauziyyah ta kalle ta tace " ina zamu? "gidan Aunty na, bamu tab'a zuwa da ke ba, shiru tayi ba tare data k'ara cewa komai ba, har suka isa k'ofar gidan, da sallama Fa'iza ta shiga gidan tana gaba Fauziyyah na biye da ita a baya, har suka k'arasa cikin gidan a wani madaidaicin falo Fa'iza tace" zauna bari na shiga ciki nayi mata magana, "to kawai tace cikin sanyin jiki.
Ba'afi 10mnts da shigar Fa'iza cikin gidan ba, Fauziyyah taga ta fita daga ita sai pant da bra, tana busa karan sigari, d'aya hannun tana rik'e da zundumemiyar kwalbar giya, bayan ta wasu k'attin maza su biyar suna biye da ita, dukkan su ba mai kayan arziki a jikin sa, zumbur Fauziyyah ta mik'e tsaya tana binta da kallan mamaki, wata irin dariya Fa'iza ta saki irin ta 'yan maye, cikin mayen tace "zauna mana Kawata karki damu magana zamuyi, k'in zama Fauziyyah tayi sai da Fa'iza ta daka mata wata gigitacciyar tsawa, aiko a tsorace ta zauna, jikinta sai rawa yake, Fa'iza ta fara magana " ni dai da farko cikekkeyar 'yar iska ce 'Yar bari, karuwa 'yar maye dan duk kayan mayen dake duniya babu wanda ban tab'a sha ba, 'yar kwangilar Fa'iz ce dan shine ya turo ni wajenki, ta kwashe labarin komai tun daga farko har k'arshe bata rage komai ba ta fad'a mata, sannan ta d'ora da cewa, "wannan video ma ni na d'auke ku, kuma ni na turawa Director, kuka sosai Fauziya take yi, ta zube a k'asa tana kuka kamar ranta zai fita tace " mai nayi miki a rayuwarki, kike bina da wannan sharri, dariya Fa'iza tayi tace "ai ban gama fad'a miki ba, jiya wad'an nan suka zo min da bukarki, nan ma ta kwashe komai ta sanar da ita, sanann tace " ni baki min komai ba Fauziyyah gabar dake tsakanina da Fa'iz ita ta ja miki, sannan abu na biyu saboda ke Fa'iz ya ci min mutunci, nan ma ta sanar da ita komai akan zuwa gidan su dayayi dan ta tura video.
Taci gaba da cewa " ni bani da burin komai a yanzu da ya wuce naga Fa'iz ya wulak'anta ya tozarta, rayuwarsa ta d'aid'aita ya shiga garari, cikin kuka Fauziyyah tace " Allah ya isa tsakanina daku in sha Allah sai kun shiga cikin garari, da wulak'antar rayuwa, tunda ni banga abinda nayi muku ba, babu wani abu daya tab'a shiga tsakanina daku, ya Allah ka isar min akan wad'an nan bayi naka, Allah ka saka min, ya Ubangiji kai kace baka barin zalunci da azzalumai kai kace kana karb'ar addu'ar wanda aka zalunta ya Allah kai kace ka hana zalunci akan kan ma, ya Allah ka sani an zalunce ni, wata irin dariya suka saki gaba d'ayan su suka yo kanta kamar mayunwatan zakuna sunga nama.
Mik'ewa tayi tsaye, ta saki wata irin k'ara da duk gidan sai da ya amsa, su kansu sai da suka tsorata suka ja ba, tace " wallahi Allah ina raye babu wani d'an iska, basik'i daya isa ya k'ara keta min haddi sai dai ina na mutu na bar duniya kuyi da gawa ta a lokacin bana numfashi, aiko suka kama kokawa haik'an, tun suna k'ok'arin jan ta dak'i har suka fara dukan ta, wani daga cikin su ya jefa ta kan center table kanta ya bugu ya fashe shima center table d'in ya fashe, garin ta fisge hannunta ta kara fad'awa kan dianing table, shima ya fashe, jikin ta duk jini ke fita, duk wani kayan glass sai da aka fasa shi, aka hargitsa falon, sosai suke dambe da ita dan zuciyarta ta riga ta kawo wuya ta gwammaci mutuwarta akan su cimma burin su akan.
Su kansu sunyi mamakin k'arfinta da dakewar zuciyarta, d'aya daga cikin su ne ya zuciya ganin k'aramar yarinyar na neman b'ata musu lokaci ya fisgo ya dalla mata wasu gigitattun marika ya wurga ta kan kujera cikin rashin sa'a sai kanta ya bugi bango cikinta kuma ya daki, kujerar , aiko ta tafi luuuuu jini yayi tsartuwa daga kanta, ta fad'a kan wani d'an glass dake gefen kujerar jini ya b'alle mata ta k'asanta.
Ganin ta fad'i bata motsi, ba alamar rai, d'ayan yace " ka kashe ta, da sauri ya nufi firji ya d'auko ruwan sanyi ya b'alle bakin robar ya tuttule mata amma a banza babu ko alamar motsi, jijjigata suka shiga amma bata ko motsa ba, dukkan su hankalin su yayi masifar tashi, ganin ta mutu, zama sukayi suka ji jigum-jigum kowa yayi tagumi d'ayan ya yunk'ura zai gudu suka rik'e shi, suka ce ai ba maganar guduwa dan munyi kisan kai, mafita kawai zamu nema, ita ko Fa'iza ta kasa magana saboda tsabar tsorata, d'ayan yace " shawara d'aya ce ku tashi mu gudu, gaba d'ayan su suka yunk'ura mai gidan yace " tab!! wato ni a kamo ni, kubar gawar a gidammu ko, wallahi wannan shawarar batayi ba a sake wata, wani kuma yace " gaskiya dai, amma ni ina ganin mu barta sai dare yayi mu d'auke ta musa ta a buhu mu d'aure mu kai ta kududdufi mu jefe, gaba d'ayan su suka yarda da wannan shawarar kowa ya amince...........
*Alhamdulillah*
*MOMYN ZARAH*
~Please comment~๐๐ป
~Please comment~ ๐๐ป
~Please comment~ ๐๐ป
'''YAWAN COMMENT D'INKU YAWAN POSTING D'INA'''
_ONE LOVE, LUV U SO MUCH MY FANS_
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
BYE