Free chapter ยท Read without an account

31

by Hauwa A Usman ยท Kโ€™ADDARA TAH

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_




'''Congratulation kawata ina tayaki murnar kammala novel d'inki RANAR BAIKO NA Allah ya sanya alkhairi Ubangiji ya k'ara basira da bazaka Allah ya barmu tare my dear''' 



*(MRS MAKAMAโคโค)*



~ME & YOU ONE LOVE IYA WUYA ANA MUGUN TARE๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜~




*EDITING BY MOMYN ZARAH*



31



Batayi aune ba kawai sai ji tayi yana k'ok'arin shigar ta ,jin yana neman hanyar shigarta ne yasa ta sakin wani mahaukacin ihu wanda yasa shi muguwar firgita da sauri ya daga ta yana tambayar ta meye?




Yana daga ta ,ta hantsila baya ta ja bed sheet ta rufe jikin ta,jajayen idonta ta zuba mishi k'uri bata ce masa komai ba ,kunya ce ta kama shi ya sunkuyar da kansa k'asa a hankali ya maida kayansa cikin jin kunya ya debe kayan ta ya mik'a mata ,kansa a k'asa har a lokacin bata daina kallon sa ba ta kafe shi da ido shiko duk ya rasa abin yi sai kawai yayi kneeling down ya shiga bata hak'uri,cikin kuka tace " gaba d'ayan ku halin ku d'aya ne ,kad'an ne na Allah,dakun keb'e da mace burinku kawai ku kwanta da ita ,Farhan ka ban mamaki ka bata rawarka da tsalle ,wallahi da na dauka kai na daban ne acikin maza ganin tsayin lokacin da muka dauka baka taba kokarin koda rike man hannu bane ,ashe kaima irin su ne ,dama ce kawai baka samu ba,halin ku d'aya ne,ta kareshe maganar cikin matsanancin kuka ,cikin sanyin jiki yace " wallahi Fauza hakan ba halina bane yanzu ma tsautsayi ne da sharrin shaid'an ban tab'a attempting nayi even romance da wata mace ba ,balle har nayi kokarin sex da ita wallahi sai ke,please kiyi hak'uri nasan nayi laifi amma duk hukumcin da kika dauka na yarda na amince. 




"Ka amince? "eh dear ,hawayen face d'inta ta goge ta d'aga kanta sama tayi ajiyar zuciya ta maida kallonta kansa tace " please ka fita daga rayuwa ta ,ka shigo rayuwa ta gaba d'aya ka hanani sukuni ka hana min kwanciyar hankal........... "please my Fauza banda wannan bazan iya rayuwa babu ke ba please kiyi man adalci,laifi ne nasan nayi amma please kiyi man hak'uri wallahi idan kika ce na rabu dake a yanzu mutuwa zanyi dan nasan bazan taba iya rayuwa babu ke ba, please, ya ka rasa maganar kamar zaiyi kuka.




"Please ka fita daga rayuwa ta idan da gaske kana so na,idan kana san kasancewa ta cikin farin ciki da walwala,shiru yayi yana sharar hawaye yace "nayi kuskure but hukuncin nan yayi man tsauri, itama tace " please cikin matsanancin kuka zumbur ya mik'e yayi k'ofar fita sai kuma ya dawo ya kalle ta ya buga kansa da bango har jini na fita ganin jini yasa ta tsorata ta zazzaro ido yace " shikenan tunda haka kika zab'a zan barki amma nasan kwanan nan za'a ce maki na mutu in sha Allah zan fita daga rayuwarki cikin sanyin murya ya kalle ta yace " I love you Fauza!, I really love you!!, I love you with all my heart!!! ya fice daga d'akin,yana fita ta kifa kanta ta saki kuka mai ban tausayi.




Farhan na fita bai wuce ko ina ba sai Air port,yayi Nigeria sai da ya shiga jirgi ya zauna yayi wa escort d'inshi waya ya sanar da su yace su d'ebo mai kayan sa suma su taho,yana gama wayar ya shiga gallery yana kallon pictures d'in shi da Fauza yana zubar da wayen takaici, itama Fauza sai da taci kukanta ya ishe ta sannan ta mik'e ta saka kaya tayi sallah tana tunanin halin maza a fili tace " ashe ba Fa'iz bane kad'ai d'an iska ba ashe kusan duk maza haka suke ,da so suke yaudararmu su cimma burinsu akan mu, idan namiji nasan cutar ka ko yana yaudarar ka baka isa ka gane ba sai bayan ya samu biyan buk'atarsa ko in Allah ya tsare ka, ya Allah ya k'ara tsare mu daga sharrin maza da fad'awa tarkon su.




**************************************




Malam Muhammad yana can yana fama da yara 'yan islamiyya da kuma limancin masallaci har gemu ya tsayar ,kuma gemon sai ya karawa face dinsa kyau sosai ,sai ya k'ara fito masa da kyansa da yarintarsa, Fa'iz yayi matuk'ar shak'uwa da Aisha sosai harta kai Aisha ke yi masa wanki da sauran bukatun sa ,suna zama suyi hira sosai , duk abinda ke faruwa Mama na sane dan haka tace dole tayiwa Abba magana gudun kar shaidan ya shiga tsakani ,bayan Abba ya dawo yayi wanka yaci abinci ya nutsu Mama ta same shi a d'akinsa kusa dashi ta zauna d'aga kai yayi ya kalle ta yasan da magana a bakinta yace "Maman yara ya akayi ne? " murmushi tayi tace " akan yaran nan ne , " wanne yara kuma ? "naga soyayyar yaran nan tayi tsamari mai zai hana ayi musu aure? " wadan ne yara kenan? a hankali tace " Aisha da Malam Muhammad ,murmushi yayi yace " nima nayi wannan tunanin amma ina tsoran abinda zaije ya dawo.




Kallon sa tayi tace " me zaije ya dawon? "Saboda kinga yanzu ba'a cikin haiyacin sa yake ba ,bamu san asalin sa ba ,bamu san tushen sa ,iyayensa ,danginsa ba,shi kansa bamu san waye shi ba,bamu san daga inda ya fito ba ,bamu sani ba ko yana da mata harda yara ba bamu sani ba ko idan ya dawo haiyacinsa zai ci gaba da son ta ba, ko bayan mun yi auren ya dawo haiyacin sa yace baya son ta ba, ko iyayensa suk'i yarda ,tunda da ganin yaron kinsa d'an manyan mutane ne da gani iyayen sa masu hali ne,ina gudun kar muyi abinda zamu dawo muna danasani musa 'yar mu cikin bak'in ciki da takaicin rayuwa.




Shiru Mama tayi cikin sanyin jiki da fad'uwar gaba tace " haka ne ,Allah yayi mana zab'in alkhairi,murmushi Abba yayi yace "Amin.




Fa'iza ana can ana cin duniya da tsinke ana shanawa tun abinda sukayiwa Fa'iz suka ji dad'i sai suka fara fashi da makami suka zama gagaruman 'yan fashi ,in banda duniya babu abinda ke gaban su, burinsu kawai suji su da kudi suci su sha kuma suyi sex dan Fa'iza har groups sex take yi,ta zama cikekkiyar 'yar iska ta bugawa a jarida dan yanzu sunfi k'arfin zaman katsina tuni sun haura Abuja idan basa Abuja suna Lagos ,dan har kiddnaping mutane sukeyi , amma duk abinsu basa kisan kai,za dai su nadawa mutum mugun duka suyi gaba ,yanzu su Fa'iza an zama manyan yara masu kudi.




*BAYAN WATA D'AYA*




Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, lokaci baya jira sai dai kai ka jira shi ,sannu bata hana zuwa ,yau Allah yayi ranar dawowar Fauza Nigeria tun k'arfe 12:30pm Abba da Sadik suka tafi taryarta a Aminu kano international airport,babu yadda Sadik baiyi da Malam Muhammad akan yazo suje ba amma fir yak'i zuwa duk ya rasa abinda yake damun sa tun jiya da Aisha ta fad'a masa dawowar Fauziyyah yaji gaban sa na muguwar fad'uwa duk ya rasa sukuni da walwala,hankalinsa yak'i kwanciya ya rasa mai yasa a fili yace " ko meye dalili oho ,mai yasa na shiga tashin hankali ne, haka dai yayi ta magana shi kad'ai har bacci mai nauyi yayi gaba dashi, jirgin su Fauza na sauka a garin kano ta tsinci kanta da fad'uwar gaba da rashin nutsuwa ,a hankali ta fara karanto addu'o i , a hankali ta mik'e ta fito daga cikin jirgin sanye take da Arabian gown ja ta saka black shoe da black bag,tayi matuk'ar kyau duk wasu halittu na mace sun k'ara baiyana a jikin ta skin nata yayi mugun kyau da laushi ga santsi ,idan ka ganta sai rantse bata tab'a sanin Nigeria ba balle yaren hausa Fauziyyah mace mai matukar kyau na jiki dana fuska gata santaleliya doguwa siririya sai hips da cikar kirji (cokacola sharp) gata da jan aji shiyasa yawan cin mutane ke kiranta da mai girman kai ,kwata-kwata bata san yawan magana ,gaba daya Barrister Fauza ta canja idan ba mugun sani kayi mata ba bazaka iya gane ta ba, dan sai yanzu kamar ta da Ashwariyya Rai Bachan ta fito sosai,cikin takunta na isa take takuwa tana karewa kowa kallo ta cikin glass din dake face d'inta,wata muguwar fad'uwar gaba Sadik yaji a lokacin daya hangota dan yafi 15mts yana kallonta amma bai gane ta ba sai da ta matso ya kura mata ido.




A ransa yace " Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga Ubangijin sammai da k'assai godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin daya haliccin My Fauza ,tunda ta fito ya kura mata ido ya kasa d'auke idonsa daga kanta wani mugun yawo ya had'iya ,yana cikin wannan halin ta karaso da gudu ta fad'a jikin Abbanta dariya Abba yayi yace " masha Allah Fauziyyah ta andawo lafiya? " lafiya Abba ,yasu Mama da Umma da Bab......My dear baki ganni bane ya fad'a yana silent killer smile ,hankali ta juya tace " lahhh yaya na ganka murnar ganin Abba ce,gaba d'ayan su suka saka dariya ,a hanya a cikin mota sai hira suke har suka k'arasa gida a k'ofar gidan su Fauziyyah Sadik yayi parking a hankali ta bud'e motar ta fito tana fitowa gabanta yayi muguwar fad'uwa jikin ta ya d'auki rawa lokaci d'aya fargaba da tsoro suka dirar mata a hankali tace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.............!




*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*




~PLEASE CIMMENTS~๐Ÿ™๐Ÿป



'''A GAAKIYA KUNA MATUK'AR BURGENI JIDDARH NOVELS COMMENTS D'INKU YANA K'ARA MIN K'ARFIN GWIWA NAGODE SOSAI ALLAH YABAR K'AUNA DA ZUMUNCI'''

โคโคโค


~LUV U SO MUCH DEAR~

 ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹



_ANA MUGUN TARE NI DA KU_

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜




BYE

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.