Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Azizat Hamza · SAKATARIYA TA

Tana zaune a office Faruƙ ya kirata wai gashi a kamfanin su. Kwatancen office ɗin ta ta ma sa sannan ta ajiye wayar tana cigaba da aiki. Minti biyar kacal sai ga Yakubu da Faruƙ sun shigo.

"Farida haka yaron nan ya zama luƙeƙe. Kin san da farko ban ganeshi ba"

"Kai ma ka faɗa ai, wannan sai ya goyeni yai yawo da ni duk faɗin garin nan bai gaji ba"

"Haba Anty, ɗan ni ɗin nan" Faruƙ ya faɗi yana dariya

Yakubu ya fita ya basu wuri, dama wajen Anas zai je ya haɗu da Faruƙ ɗin.

'Yan uwan biyu su ka zauna su na taɗi, su na yi su na dariya.

Wayar Farida ya ƙarɓa ya na duba hotuna. Ko ba a gaya ma sa ba ganin hotunan selfie da Farida ta yi da wani saurayi ya tabbatar ma sa shine Rayyan.

"Sis, wannan shi ne sirikin na mu ?"

"Kai ba na son gulma"

"Wallahi ba ku da ce ba, wannan ai kin fi ƙarfinsa. Hmm ina tausaya ma sa wallahi, aka yi auren nan mijin ta ce zai koma dan ba zai iya da masifar ki ba"

"Buuuuyagi" wafce wayan ta yi tana faɗin " ka ji min rainin hankali, wato dai ni ka ke zagi ko" ta maki kafaɗar sa ta ce " Faruƙ yaushe ka raina ni haka?"

Yarfe hannu ta farayi shi kuma ya fara dariya. " jikin ka kamar wani katako, wai yaushe ka girma ne haka? Faruƙ"

"Serious Anty Farida ba ki dace da shi ba, kin ga lokacin Lukman..."

"Faruƙ!" Ta faɗa da ƙarfi.

Ya haɗa hannu ya ce "afuwan Anty na ta kai na"

Haɗe fiska ta yi ta tsume.

Faruƙ ya sa hannu ya fara tattaɓa kumatun ta yana tsokanarta kaman yadda yake yi lokacin suna yara.

"Anty kumatu, Anty Kumatuttu"

Ba ta san lokacin da dariya ya kuɓuce ma ta ba.

"Yaron nan ka mugun raina ni wallahi"

Yai dariya ya ce " na tuna da, lokacin idan na ce mi ki Anty Kumatu har maƙota sai anji faɗar mu"

Ta fara dariya sosai harda kama ciki.

Faruƙ ya cigaba " lokacin tunda na gano bakya son sunan sai na samu abun tsokala. Kin tuna lokacin da ki ka kwaɗa min tukunya har goshi na ya fashe?"

"Ai ranan Ummi ta zane ni kamar ba gobe" ta faɗa cikin dariya. Suna cikin dariyan kakkausan muryan Najeeb ya doki kunnen ta.

"Miss Salihu"

"Sir" ta faɗi tana miƙewa tsaye.

"To my office"

Ya jima tsaye yana kallon su tun daga lokacin da Faruƙ ya ke shafa mata kumatu. Zuciyar sa ta yi baƙi haka nan idon sa ya kaɗa yai ja, a take ƙwaƙwalwarsa ta tariyo ma sa sunan da ya gani ranan *My Ray*

Ta ya za ta kawo saurayinta har office tana iskancin da ta ga dama. Enough is enough dole ya taka ma ta birki. Abinda zuciyarsa ta tsayar kenan dai-dai lokacin da Faridan ta shigo.

"Ga ni Sir" ta faɗi a hankali

Da ƙarfi ya fara masifa "Miss Salihu yaushe ki ka maida office wajen soyayya da iskanci?. Listen young Lady, idan ba ki san yadda za ki kama kan ki ba go and get married. Ki dena mayar min da office wajen karuwanci. And i..."

"Sir Najeeb ba fa ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa. Daga ƙani na ya kawo min ziyara sai ka maidashi wani zancen banza wai karuwanci. Ba Karuwanci ba a'a Kwartonci"

Kalmar *ƙani na* da ya ji shi ya sanya duk wani masifar da ke cinsa ta washe, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kamar kiftawar ido, muryar sa da yanayin sa su ka chanja. Cikin sanyin murya ya ce "Miss Salihu, da ƙanin ki da saurayin ki, nan ba wajen ziyara ba ne"

Haushin sa da ta ji kaman ta makeshi takeji sai dai yanzu ba ta son samun matsala da shi dan ankusa biyan albashi, ƙaramin aikinsa ne ya cire mata wani kaso a ciki.

"Zan iya tafiya?"

Yai ma ta nuni da hannu. Sai da ta fita ya sauke numfashi. Cikin zuciyarsa yana cewa to ma miye ruwansa idan ma saurayinta ne?.


Tana zama ta yi tsaki " shi komai masifa, yai wa mutum kyakykyawar fahimta ba zai yi ba"

"Sis Ogan kin nan ya burgeni fa. Saurayi da shi amma ya mallaki babban kamfani kamar wannan, gaskiya na jinjina mi shi"

"Ko za ka je ya baka aiki ne. Nan za ka san wannan saurayin zuciyar dutse gareshi"

"Oh really"

"Hmm ai ni ma ba dan bana barin hau ta hauni ba da tuni an jima da fatattaka ni"

"Kai Masha Allah, wa su kam Allah ya basu duniya, ga shi handsome, ga kuɗi, ga class..."

"Zan make bakin ka Faruƙu"

Dariya yai ya ce " Jiya na yi mafarkin kin auri wani millionaire. Wai gamu a wani haɗaɗɗen mansion, wai nan ne gidan ki"

"To Sayyadi Sheikh Umar Faruƙ, ma su mafarkin waliyyai"

"Da gaske fa Anty Kumatu"

Ta ɗau wani littafi za ta buga ma sa ya kauce yana dariya...


...................

Wannan karan ba ta yi garajen barin wajen aiki ba dan ta san yana ɗaya daga cikin babban dalilin da ya sa Najeeb ya rage albashinta a watan farko da ta fara aiki. Ranan Laraba ta tambayeshi leave ɗin kwana biyu ya ce ya bata kwana ɗaya. As usual sai da ta yi ƙorafi amma bai kulata ba.

Wannan karan bayan Walima ba abinda za'ayi. Baffa yai iya ƙoƙarinsa wajen yiwa Maijiddah kaya, duk da bikinta ya zo ma sa cikin matsi.

Ranan Alhamis aka je yi ma ta jere, su Farida ne 'yan gaba-gaba wajen ganin komai ya tafi dai-dai. Gidan yana da kyau sosai, tana da ɗakuna biyu na ta sannan an ware ma ta kitchen daban sai dai store ne za su haɗa da Aneesa...

Gidan ya cika saboda gobe ne walima jibi Asabat kuma a ɗaura aure. Farida tun da su ka dawo daga wajen jere ba ta samu zama ba, shiga ta yi cikin ma su haɗa kayan waliman gobe ana aiki da ita.

Cikin ma su aikin cupcake ta ke ana yi ana hira. Chan wata 'yar uwar su wanda ita kan ta Faridan ba ta san takamaimai ta ina su ka haɗu ba ta ce " Ikon Allah, kaman ba yau aka yi hidiman bikin Farida ba, na tuna cake ɗin da aka yi ranan mai daɗi, su Talatun Haruna ne su ka yi cake ɗin nan ko?"

Farida ta fusata da wannan zance. Ta miƙe tsaye " Inna Tabawa ki ke ko wane. Wallahi ki riƙe girman ki, na ga take-taken ki tun awajen jere. Ba zan miki da daɗi ba"

"Daga magana. Ni na ce kiyi sosayya da ɗan shege" Taas Farida ta wanke ta da mari ai kuwa matan kowa ya tashi wasu su ka ja Farida gefe wasu kuma su ka tsaya da Inna Tabawa da ta ke ta zage-zage...

Kai tsaye falon Baffa Ummi ta shige da ita bayan an kawota wajen Ummin.

"Mi ye haka Aishah?, zafin kan ki har ya kai ki mari mace kamar Tabawa"

"Ummi so ta ke ta ci mutuncina cikin jama'a. Tun a wajen jere ta ke ta min habaici ina shareta. So ta ke wanda ma ba su san abinda ya faru ba su sani"

" shikenan?" Ummi ta faɗi ranta a ɓace

Farida ta kalli mahaifiyarta da mamaki ta ce "Ummi maganan Lukman fa"

" da ta yi maganan akwai abinda ya ragu ko ya ƙaru a jikin ki ne?"

Farida ta girgiza kai.

"To ni banga abin ɗaga hankali ba anan. Ƙaddarar ki ce ta zo da haka. Kuma Alhamdulillah Allah ya chanja mi ki da mafi alkhairi sai ki yi ta gode ma sa, ki share 'yan gulma da gulmar su"

"Amma Ummi..."

"Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta"...

Ɗakin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daɗin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba ɗaya zuciyarta na ma ta ɗaci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi baƙin ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita...

...................

Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.

"Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support ɗina Anty"

"Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi 'yan kallo. I dont want to ruin your day"

"Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina buƙatar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci"

Da ƙyar Farida ta haƙura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa'azi.

Washe gari Asabat ƙarfe shaɗaya aka ɗaura auren *Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako*

Ɗaurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta ɓangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab ɗin.

Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos...

Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.

Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.

Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko baƙin ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banɗaki.

Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana roƙo sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sauƙin wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ƙaruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaɗai sai ta ke jin cikin ta na ƙugi yana kuma murɗawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ƙarshen kunya aka shigo ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin yai daidai da kukan da cikinta yai "ƙululululu"

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya ɗaga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.

Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haɗawa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

"Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana"

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta ɓarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.

"Bari mu yi sallah sai mu ci abinci, na san baki ci wani abin kirki ba yau"

A karo na ba adadi cikinta ya sake yin ƙugi, wannan karan kam AbdulWahab ya ji.

"Sorry princess yunwa ko?"

Idan ta cigaba da shiru za ta cutu haka nan da kunya ace ta gaya ma sa matsalarta sai dai ya za ta yi.

"Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata" ya katse tunanin ta

Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.

Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banɗakin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.

Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce " gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?"

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali " I'm sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya"

Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce " There's nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama ɗaya ai"

Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce "kinsha magani?" Ta ɗaga ma sa kai.

"Barin haɗo mi ki tea sai ki fara sha"

Fita yai daga ɗakin wanda cikin minti shabiyar da ya ɗauka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banɗaki.

Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she's nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec  shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.

A yadda ya ganta she's already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.

Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haɗa ma ta da kaza.

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki"

Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.

"Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa"

Gaba ɗaya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buɗe closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta ɗaura hijab akai.

Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.

"Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi"

Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas ɗin ta.

"Ya cikin na ki?"

"Da sauƙi"

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji"

Ta gyaɗa kai.

"Now breath in and breath out"

Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.

Kafin ya shimfiɗa sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu'a ya kashe wutan ɗakin...

Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama ɗaya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.

Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce "inaa, Anty ni kam ai na sha kunya" a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi ta ma ta dariya.

Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.

Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.

Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan...


.........................

Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita " mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba"

Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office ɗin Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta ɗauka baya office ɗin dan ya fita ɗazu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.

Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.

Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi...

Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.

Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin "kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda"

Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta

"Miss Salihu"

Kaman ta nitse cikin office ɗin haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banɗakin ne ya shigo office ɗin.

"Miss Salihu whats the meaning of this?"

Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce

"Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni'ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi. Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni'ima. Abu ne ba babba ba yaro"

Ta ɗan haɗe rai ta ce " yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni'imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?"

The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce " Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banɗaki?"

"Saboda ya fi kusa da ni mana"

"This should be the last time da za ki yi haka"

"Ok Sir"

Har za ta wuce sai ta juyo ta ɗan yi gyaran murya ta ce " Sir ina da magana"

Ido ya ɗaga ma ta alamar miye.

"Sir, tsakani da Allah tusar da na yi ɗazu ka ji ta?"

Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.

"Get out of my offfice"...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.