Free chapter · Read without an account
Episode 14
________________Kashe gari Daddy da BABA suka kai ziyara wajen Malam Yusuf mai almajirai, yana zaune cikin ɗalibansa ga su nan manya da yaro, ƙolo, da gwani, ƙangaren, da kuma ƴan ƙananan yara Maza da Mata. Ya na gano BABA ya tashi da sauri dan taro shi, Malam Yusuf Babban Malami ne a garin Mazoji.
Zama sukayi su ka hau gaisawa, BABA ya ce" Malam kamar yanda aka saba, ga Aminu nan ya zo, ayi masa sauka, sannan akwai jikata AZIZAN BABA,Malam baki yayi mata yawa ga miyagu suna so su cinye ta, ita ma ayi mata wani abu na taimako"
Malam Yusuf yayi dariya ya ce"to BABA za'ayi in Allah ya yarda,Alhaji barka da zuwa" Daddy ya ƙara ba shi hannu suka ƙara gaisawa, ya ba da kuɗin saukar da ake masa duk lokacin da ya zo garin, Daddy ya ce "mu zamu koma Malam" ya tashi don da wuri yake so ya koma Kano.
BABA ya ce " yauwa Malam shiga ka kawo taimakon na kai wa AZIZA" Malam Yusuf ya ce " anjima a aiko a karɓa mata" BABA ya ce"a'a ni kam bazan ɗara ko ina daga nan ba sai ka ba ni, haka kawai a illata min ita,kasan yanda maƙiya suka baibayeta kuwa, kai bancire maka kowa ba har a cikin zuri'ata akwai so maƙil"
Malam Yusuf yayi murmushi ya san halin BABA da rigima ya ce" to bari a kawo ruwa ayi mata tofi yanzu sai akai mata"
Kai Kamilu shiga ciki ka ɗauko min ruwa" yaron ya ajiye allonsa ya shiga cikin gidan Malam.
BABA ya washe wawulonsa ya na godiya, a kofin silver aka kawo ruwan na borehole, ya karɓa ya yayi addu'o'i a ciki ya bawa BABA ya na faɗin, a turo akarɓa mata rubutu"
BABA ya ce " to shi Aminun ai komawa zai yi ya za'ayi da shi?" Malam ya ce" babu komai za mu sa ka shi cikin addu'a" BABA ya ce "to,to madallah, angode Malam" sannan ya tashi Daddy ya ce"kawo na riƙe maka" BABA ya kau da hannu yana janye kofin ya ce"bar shi zan iya da kaina, abun tsautsayi haka kawai ka zubar min da shi" Daddy ya janye hannunsa suka tafi.
Munnir da Siyama da Pretty duk sun ƙagu Daddy ya dawo su wuce, AZIZAN BABA da ta koma gefe ta zauna gami da zabga tagumi, ta na son faɗar abinda ke zuciyarta na son zuwa birni, tana tsoron Baba Tabawa tayi kyauta da ƴaƴanta.
Inna Gaji ta kallesu duk suna tsaye ga trolley a hannu, ta ce" ai kwa jira uban naku ya dawo ko?" Siyama ta ce"ai jira muke yi, ta kalli agogon da ke jikin wayarta, sha biyu har da ashirin bayan Daddy ya ce a gida za su yi azahar in sha Allah.
Tsaki ta ja tana mai buga ƙafa, Inna Gaji ta juyo da sauri ta ce"kar ki ƙara yi mana wannan shashancin banzan anan, yara duk sai fitsara da rashin kunya" Baba Tabawa ta ce" sai haƙuri ai yaran zamani sai addu'a"
Siyama ta taɓe baki ta koma ɗaki ta zauna ganin har yanzu ba su dawo ba.
Abdul-AZEEZ da bai sami bacci ba daboda ɓacin ran da ya shiga akan AZIZA yanda BABA ya ci masa mutunci kuma Daddy na gani bai iya ce wa komai ba, ya ƙara sa shi ɗaukan zafi.
A hotel ɗin ne ma ya samu yayi waya da Mami, in da ya sanar da ita ko Daddy ya yarda ko kar ya yarda gobe dole ya bar garin.
Kallon bf ɗinsa yayi a system ɗinsa har dare ya raba bai sani ba, yana kallo yana istimna'i sai da ya gama jagula jikinsa sansan ya yi wanka ya kwanta bacci.
Da safe ya kira uwarsa ta na ɗakinta dan ko saukowa bata yi ba, tunani take akan zuwa wajen malam, ta ga kiran ɗan nata.
My boy antashi lafiya, Abdul-AZEEZ ya ce'lafiya ƙalau Mommy anjima zan tawo yanzu zanje can gidan in musu sallama"
Mommy ta ce"wace sallama kawai ka tawo, ni zanji da mahaifinku, ba faɗa kake tsoro ba to ba zai maka ba" Abdul-AZEEZ ya ce"ba za ki gane ba Mommy banaso su dinga zargin Daddy hakan ma ba tsira yayi ba, wannan tsoron nake ji Mommy"
"hahhh au hakan da kake ne zai sa su bar shi, kai bakasan halin waɗannan tsofaffin ba duk abinda zai musu ba burgesu yake ba,ba dan iyaye iyaye ne ba wallahi ko hummm ka dai tawowarka kawai"
Abdul-AZEEZ ya yi murmushi ya ce " naga da alama mommy har kin fi ni ƙin ƙauye"
kai ya isa hakanan, ka shirya ina jiranka, sai ka dawo" ta kashe wayar.
Shiryawa yayi cikin ƙanana kaya, red trouser da t-shirt black sai black half shoe, kasancewarsa fari sai ya fito tamkar Bature.
Key ɗin room ɗin da ya sauka ya bayar ya saɓa jakarsa ya nufi mota, gidan ya koma dan yasan Daddy na jiransa tunda ya kira shi da daddare ya sanar masa ya fito da wuri.
Baba Gaji da ta manta da abinda akayi jiya, ta ce "AZIZA zo ki kai min wannan niƙan injin Iliya" AZIZA da take jiran ganin shigowar Daddy da BABA ta ce"a'a Baba idan na tafi nasan kafin na dawo sun tafi, kuma ni...kuma ni... Ta kasa faɗa, Inna ta ce " ke me ne faɗi mana"
Sallamar su BABA ce ta dakatar da su daga zancen da sukeyi.
"Yauwa yaki nan AZIZAN BABA, ga taimako na karɓo miki" BABA ya faɗa ya na nufar wajen AZIZA.
AZIZA sai ta sa kuka ta na kallon Daddy dan bataso su tafi su barta zamansu a gidan duk da ba wani wasa suke da pretty ba ta ji daɗi, yanda suka ƙaru, da zarar sun tafi shikenan sai su kaɗai.
BABA ya ruɗe yana faɗi "wane ɗan kusun uwar ne ya taɓa ki iye"AZIZA sai kuka take, Inna Gaji ta riƙe baki tana salati ta ce" yanzu fa ake mata magana ta kai niƙa, ta tsaya za tayi mata rashin ɗa'a wai idan ta je su Siyama tafiya za suyi"
Daddy ya je ya kamota ya na faɗin " in bar miki so anan?".AZIZA ta kalli Baba Tabawa sai ta kuma sa kuka, ganin haka Inna Gaji ta zargi wani abu.
Ai kuwa ta ce " ke AZIZA me tayi miki?"AZIZA ta riƙe baki ta na matsar ƙwallah,Baba Tabawa ta ce " ki faɗa mana me ne ne"
Ta ce" in faɗa Baba Tabawa?" ta faɗa ta na kallon Baba Tabawa, aikuwa ta ce" eh ki faɗa AZIZA"
Ta ce " ni zan bi Baban birni" gaban BABA ya yanke ya faɗi, ya ce " ita ce ta ce ki bi shi,dan tagaji da yi miki hidima?" Baba Tabawa da ta ga BABA ya fassara hakan a bai-bai ta ce" a'a fa Malam, ce wa tayi zata bi su, ni kuma sanin son da kake mata ya sa nace kar ta faɗa dan nasan ba iya rabuwa da ita za kayi ba"
Rufe min baki, watukun bakison ganinta a tare da ni, to ƙafata ƙafar AZIZA, ya kalli Daddy ya ce "Aminu idan na kintsa zan sanar da kai ka zo ka ɗauke mu za mu koma marayar ni da AZIZA" Inna ta ce" aikuwa bazan zauna anan ba binku zanyi ita da ta kitsa abun sai dai ta zauna ita kaɗai a gidan"
Daddy da ya ji abun kamar a mafarki, shekara da shekaru ya na son BABA ya amince da komawa Kano yaƙi, AZIZA yau da ta faɗa ya amince.
Ya ce "da gaske kake BABA za ka koma Kano da zama?"BABA ya ce "muddin AZIZAN BABA ta na so, nima ina so Aminu zamu koma" AZIZAN BABA sai ta hau dariya ta na rungume BABA ta na tsalle, ta ce"Inna a bani kayana BABA ka tashi mu tafi" BABA ya ce "haba tafi so tafi sauran mata kinga ban kintsa yanzu ba, ki bari su tafi mu daga baya idan mun gama sallama da kowa sai ya zo mu tafi ko kuwa?" AZIZA ta ce " to ka faɗawa Baba kar ta bayar min da ƴaƴana" Baba Tabawa ta ce" ni Maryama ba wanda zan bawa AZIZA, aikin gama ai ya gama"
Siyama ta ce "wai BABA da gaske kake zaku koma can da zama?" BABA ya ce "ƙwarai kuwa Maryamu"
Ta jinjina kai tana hasaso yanda Mami za tayi idan ta ji wannan mummunan labari.
Abdul-AZEEZ ne yayi sallama ya na mai nufar inda ya gansu kowa a tsaye BABA da AZIZA ne a zaune, ɗan duƙawa yayi ya gaishe su, ƙannensa suka gaishe shi, AZIZA da tayi kamar ba ta san da zuwansa ba, Baba Tabawa ta ce "ba ki gaishe da yayan ku ba AZIZA"
Murguɗa baki tayi ta ce" Allah ya kiyaye in gaishe da shi, ai malamin mu ya ce, idan ana girmama iyayenka kai ma ka girmama mutum, to kuma wanda ba ya girmama iyayenka fa me za'ayi masa, kinga sai aƙi girmama shi, ta hura hanci tana shan ƙamshi.
Abdul-AZEEZ da zuciya kusa ya ja tsaki ya ce" dan Allah Baba ku daina biyewa mai matsalar ƙwaƙwalwa, Allah Daddy sycartory ya kamata akaita"
BABA ya ce"Aminu ja ƴaƴanka ku tafi, tunda wannan jemamman ya zo, kar raina ya ɓaci"
AZIZA ta dinga maimaita kalmar sycartory, sycartory duk son turancinta da kuma bakin malamansu ba ta taɓa ji ba, tuno yau Alhamis har yanzu ba'a ta shi ba, ta ta shi ta fita a guje, ta na faɗin Baban birni ka tsaya yanzu zan dawo"
Abdul-AZEEZ ya bi ta da kallo ya na ƙara tabbatar da haukanta, BABA ya ce "ko ina zata je Aminu ka jira kaɗan nasan wani abun za ta kawo muku" Inna Gaji ta ce"aikuwa dai ko me zata kawo oho"
Siyama ta ce" dan Allah Daddy mu tafi kawai"
Daddy ya ce"a jira ta dawo"
A guje ta shiga makarantar tasu, ana ta karatu ta hango malam Yahaya ta ce" Malam, Malam,dan Allah me ne ne sycartory?"
Tana nishi ta na haki, Malam Yahaya ya ce "why are u absent today?"
Sauri nake yi kayiwa Allah ka faɗa min"ganin ta damu ya ce" kamar a ce masu matsalar ƙwaƙwalwa/mahaukaci dai haka".
Kutmar burar uban nan ni ce mahaukaciya" sai ta juya a guje, gonar Mato ta biya ta na kuka ta sa leda ta ɗebo karara ta nufi gida hawaye wani na bin wani, ta na shiga gida ta nufi Abdul-AZEEZbta kama rigarsa ta baya ta ce "meyasa ka kira ni da mahaukaciya, ashe wannan karara take shafa masa.
Ya juyo face-face ya ce" to da me ce,sai ta kama hannunsa da sauri ya ƙwace ya na toshe hanci, kamar wari take, Daddy da BABA babu wanda yayi magana sai ta fashe da kuka, bayan ta gama aikinta.
BABA ya ce"Aminu ku tafi, zamuyi magana ta sailula Allah ya tsare hanya" jiki a sanyaye Daddy ya ce to sai na zo ɗaukar naku BABA,AZIZA ki yi shiru ke ba mahaukaciya ba ce, murmushi tayi ta ce "Allah ya kaiku lafiya"ta ce "aunty Siyama ku gaida gida" Abdul-AZEEZ da ya yi waje da sauri dan jin kamar ƙaiƙayi a bayansa ya fita ya fara sosawa a mota, driver ya na kallonsa ya ce "lafiya kuwa?"
Abdul-AZEEZ ya ce" bansani ba!" cikin tsawa, duk da Mudan ya girme shi, shiru yayi ya juya, Abdul-AZEEZ yayi fuska sai ya ji hannu ya fara, nan ma ya sosa, sai kuma ya ji ciki ya fara, nan ma ya sosa.
Daddy suka shiga mota da tsarabar man shanu, barkono, su kuka,kuɓewa daddawa Fura da nono da sauran kayan ƙauye.
BABA da su inna suna tayi musu a sauka lafiya suka ɗauki hanya, Abdul-AZEEZ dai ba dai-dai yake ba, tun yana mazewa har ya hau neman cire riga yana faɗin " Daddy, Daddy.......
Zinariya ce✍🏻