Free chapter · Read without an account

23/24

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · KADDARATA CE



___________________


Hafiz da ke kwance cikin mawuyacin hali fuskarsa har ta kumbura, ga targaɗe da akayi masa a hannu, tunda aka hankaɗashi cikin cell ɗin, yake jin zarni da warin gardawa na tashi, tsabar wahala ko kuka ya kasa yi.


D.o.p ne ya shigo, "morning sir" waɗanda suke da morning duties suka yi salute (sarawa) ga ogansu, shiga office ɗinsa yayi, files ɗin daren jiya aka kawo masa ya duba, ganin babban case ne ya sa ya fito, dan ganin Hafiz.



A cikin kwana ɗaya gaba ɗaya kamanninsa sun sauya, jini ya taru a cikin idonsa na dama,kamar ba shi ba.


Kamar Baffa zai faɗi haka yake tafiya, faɗowa station ɗin suka yi da Inna da Isma'il har da su Malam Gaddafi, tare shi M. Gaddafi yayi ya na riƙo ci dan ya kusa tintsirawa, yi masa sannu yayi, "sannunku da aiki dan Allah ko nan aka kawo Hafizu Aminu daren jiya?" 

sajen Atiku wanda case ɗin ke hannunsa ya ce " eh wanda yayi wa wata yarinya fyaɗe a daren jiya ko?" Inna ta ce "a'a ba shi ba ne,babu wani wanda aka kama jiya a unguwar zage da kuka je?"

Atiku ya ce" shi ɗin ne dai" 

"innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun" kalmar da dukkan ninsu suke maimaitawa kenan, daɓar Baffa ya zauna a ƙasa,Inna da Isma'il sai kuka sukeyi tana faɗin "wallahi yallaɓai ko kaffara babu ba shi ba ne, ni nawa Hafizun ba zai taɓa aikata wannan aikin da kuka ce ba, wallahi, billahi,tallahi sharri akayi masa"

D.o.p ne ya ce" ya isa haka, yanzu dai ba mu da  ta cewa akan hakan dan duk wasu evidence da zai nuna shi yayi akwai su, yanzu Baba nan da kwana uku idan munga yanda jikin Yarinyar yake zamu tura case ɗin kotu"


Malam Hamza ya ce " ofisa a daren jiya har ƙarfe goma muna tare da shi, ni nasan ba shi ba ne wallahi"  

"ku je waje dan Allah"

Wani daga cikin ƴan sandan ya faɗa, dan sun dame su da ihu.

Malam Lawan da yasan sanadin zuwa duba shi wannan ƙaddarar ta faɗawa Hafiz hawaye yake kawai, dubu uku ya ɗauko ya miƙawa ɗansanda ya ce "a siya masa abinci da ruwa"

Inna ta ce, ni babu inda zanje sai na ganshi na sani ma ko ba shi ba ne, dan nawa ɗan baya irin wannan abu wallahi" cikin kuka take wannan maganar, d.o.p ne ya ce "Constable Faruk ciro shi ta ganshi" yes sir, Faruk ya amsa tare da soluted ga shugaba ya shiga ciki.



Hafiz da ke zaune jikin bango ya haɗa kai da guiwa ba sallah asuba ga tangaren da yayi a yatsansa na hannun sai ciwo yake masa,constable ya shigo ya na faɗin Hafiz Aminu fito nan" ya buɗe lock ɗin, cikin tsamin jiki Hafiz ya tashi suka fito, gaba ɗaya hankalinsu Baffa tashi yayi ganin kwana ɗaya kacal an raunata shi. Inna ta ce "Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun Hafizu me ya kaika nan wajen,ba karatu kawai ka ce zaka je ba?" Hafiz ya ce " wallahi Inna bansan komai akan abun ba, nima wucewa zanyi naji kamar nishin mutum naje taimako ne wallahi Baffa ba ni ba ne" ya fashe matsanancin kuka mai cin rai, Isma'il ne ya kula da hannun Hafiz ya kumbura, ya ce hannunka ya karye yaya" Gaddafi ne ya kula da targaɗen, ce wa yayi "dan Allah ofisa zan gyara masa hannunsa" tausayi suka ba su hakan ya sa ɗansandan amincewa, zagayawa Gaddafi yayi ya kama hannun Hafiz ya na ce wa " malam Hafiz kayi haƙuri indai kana da gaskiya na tabbata zaka fita daga wannna halin" 

Murmushi mai ciwo Hafiz yayi ya na gyaɗa kansa alamar tabbatarwa, gyara masa Gaddafi yayi, su Lawan ne suka fita kowa zuciyarsa ba daɗi.



Mai da Hafiz ciki akayi, aka siyo masa abinci da ruwa ruwan kawai ya fasa yayi alwala ya yi sallah, ya daɗe yana addu'ar Allah ya fitar da shi.


Da ƙyar Inna da Baffa suka bar station ɗin,cikin tashin hankali mai tsanani, hawaye kawai suke su Malam Hamza suna kwantar musu da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya....







Sai da Zainab ta farfaɗo likita ya ce ba wani abu ba ne shock ne ya sa ta suma, aka ba ta magani, ɗaya saura suka dawo gida, Inna da take ta fatan Allah ya sa Jawahir ta na gida, ta na ta kallon wayoyinsu ko Jawahir ɗin zata kira su,amma shiru har suka dawo Zainab kuka take,Alhaji Usman ya dawo da su.


A haka suka kwana, da asuba Umma ta kira Baba ta sanar masa halin da ake ciki, na ɓatan Jawahir, nan hankalinsa ya tashi ya nufi tasha ya hau mota dan dawowa gida, ƴan uwa ana ta jajanta masa, da fatan jin alkhairi Shamsiyya ma da sassafe ta zo gidan dan Zainab ta sanar mata ita ma da kuka ta shigo gidan Mijinta ya kawota, maƙota sai shigowa ake jajantawa, Hajiya Hadiza wacce take bayan layinsu ce ta shigo, ba ta daɗe da zama ba ɗanta ya kirata ya sanar da ita ya ji labari anyiwa wata Yarinya fyaɗe jiya da daddare ta sanar da su Umma aje asibiti a duba ko wacce ake nema ce, nan Hajiya Hadiza ta hau salati gaba ɗaya hankali ya dawo kanta ta ce " yanzu ake sanar da ni jiya anyiwa wata yarinya fyaɗe ƴansanda sun kaita asibiti" nan kowa ya fara faɗan albarkacin bakinsa wasu suna aje a gano, wasu suna anya kuwa, ba Jawahir ba ce wata ce can daban. 



Da gudu yara suka shigo suna faɗin ga ƴansanda nan sun zo tare da Jawahir, mummunar faɗuwar gaba Umma taji, da gudu Zainab tayi waje, ganin Jawahir na kuka wata ƴar sanda na riƙe da ita ta je ta rungumeta gaba ɗaya sai kuka sukeyi.



Kafin wani lokaci unguwarta cika da ƴan kallo, zancen ya bazu a ko ina, shigowa sukayi ƴan sanda suka hau bincike nan aka fara da tambayar Umma, cikin kuka take amsawa, ga mutane cike da gida.



Baba ya zo, ya samu wannan mummunan labari, ƴan sanda suka ce suna son ganinsa a station domin binciken akan abinda ya faru ga ƴarsa.


Ganin yanda ake ta kuka kamar mutuwa ya sa ƴarsanda Sara ta ce "ku kwantar da hankalinku an kama yaron a halin yanzu haka yana hannun hukuma, za'a ƙwatar mata hakkinta ku kwantar da hankalinku, doctors sunyi buncike babu wata matsala, zuwa anjima za'a je a karɓo result ɗin.

Sannan nan da sati biyu za'a mai da ita dan ƙara duba mahaifarta".


Cikin kuka Umma ta ce " cuta dai yaron ya riga ya cucemu Allah ya isa mun barshi da Allah" 

Haka aka lallaɓa akai ta ba su baki, Jawahir kuwa sai kuka ta ke Zainab da Shamsiyya ma haka.


Wata sarƙa Sargent Sar ta miƙawa Shamsiyya ta ce " ga sarƙarta da likita ta bayar,Allah ya kiyaye gaba".



Cikin jakarta kawai ta wulla sarƙar ta ci gaba da kukanta,dan ba ta jin komai sai ƙunci a ranta.


Ƴan Unguwa suka samu abin yi wato gulma.

Ko ina ya ɗauka zancen fyaɗen akeyi manya da yara.




Baffa da Umma da su ka koma gida nan suka gayawa su Zakiyya, suma sai kuka suke yi nan ma zancen an kama Hafiz da laifin yin fyaɗe.

Nan fa zancen ya ba za ko ina, wasu suna tunanin sharri akayi masa wasu suna cewa daman ai munafiki ne ba wani malami Allah ya tona masa asiri.Sumi-sumin da yake duk na iskanci ne.



Bayan kwana biyu da faruwar lamarin ƴan sanda su ka tura case ɗin Court, lawyer aka ce su ɗauka dan Hafiz ya dage akan ba shi ba ne, ƴan sanda da mutanen da suka kama Hafiz sun dage akan shi Yarinyarta nuna,kuma shi aka tarar a kanta rigarsa a yage duk jini.



Labarin cin zarafin da akayiwa Jawahir ya ba za gari, Hafiz da ake zargi ma ya dage akan ba shi ba ne kuma bazai amsa laifin da yasan ba shi ne ya aikata ba...



*********





Yusuf da ke kwance a parlour ya ga Rahma ta fito da sauri tana nunawa Mommynsu abinda ya faru ta ce "mommy!mommy kinga wata shari'a da za'ayi an kama wannan da laifin yin fyaɗe ya ce ba shi ba ne, hakama ƴan sanda sun tabbatar da shine, kuma ba su da kuɗin da za su iya ɗaukan lawyer Mommy a taimaka wa yarinyar nan dan Allah"


Hon.Murtala da ke karanta magazine ya ce " nonsense wana irin shari'a kuma za'ayi ba kince an kama yaron ba, me ne na shari'a bari in kira barrister Ammar Nura yanzu, wannan station ne da case ɗin?" 

Bansaniba Daddy" Rahma ta faɗa.

Ta na zama dan ganin hoton Hafiz da Jawahir wanda fuskarta a rufe take.



Yusuf da ke jin su ya ce " mtsww wai ke ina ruwanki ba dama ku ji abu sai kun shiga ciki, Dad ka daina shiga irin wannan case ɗin k.... Dalla yi min shiru hmmm yaro yaro ne" Hon.G.G ya gyara zama ya ce " da irin wannan taimakon zan siye zuciyar talakawa idan na tsaya takarar gwamna ba zansha wahalar samun zuciyarsu ba" wani makirin murmushi Mommy ta yi ta ce " hakane Alhaji nima zan ziyarci kotun dan talakawa su saki jiki da mu hahhhh" ta ƙarasa da fara'a.



Muhsin ne ya shigo ganinsu duk kansu a parlour ya sa ya zauna yana yi musu sannu da gida, Daddy ya kira barrister dan zuwa ya tattauna da Jawahir da kuma iyayenta kuma ya sanar musu da cewa Honorable Murtala Garba Gabasawa ne ya turo su domin su tsaya musu dan a kwato musu haƙƙinsu.




Baba na shirin zuwa station ya sanar da cewa shi ba shi da ƙarfin da zai iya ɗaukar lawyer, sun bar Hafiz da Allah,ya ji ana sallama a ƙofar gida.

Fita yayi ya ga wani kyakkyawan matsayi da fara'a suka gaisa nan yake sanar da Babba ce wa "suna na barrister Ammar Nura ni lawyer ne na gwamnati Hon.Murtala G.G ne ya turo ni dan in tsaya muku a koto har sai an ƙwato muku hakkinku na zalincin da akayi muku" 


Murna, farinciki gami da jindaɗi ne suka rufe Baba, "Alhamdulillah Allah mungode maka, sannu da zuwa barista bismillah shigo mana" 


Baba ya fara shiga dan sanarwa da Umma sun sami mai tsaya musu akan case ɗin, barrister ne ya shigo a tsakar gida ya zauna dan jin ta bakin Jawahir, bayan sun gaisa ne ya nemi ganin Jawahir. Tana ɗaki kamar kullum tana kuka Zainab ma tayi jigum Umma ta shigo ta kira su.

Hijab su ka sa suka fito barrister ya ce " wace ce abin ya faru da ita?"Baba ya nuna Jawahir ya ce "gata nan" 

Barrister ya girgiza kai cikin tausayawa ya ce " zo nan ƙanwata" 

A hankali Jawahir ta matsa ta na durƙusawa hawaye na bin kuncinta, barrister ya kwantar mata da hankali tare da alƙawarin ƙwatar mata hakkinta.


Wasu tambayoyi yayi mata dan sanin ta inda zai fara bincike.

Bata ɓoye masa komai ba sai dai ta ce "ba ta ga fuskar waɗanda sukayi mata ba" barrister ya ce " kenan ba mutum ɗaya ba ne?" kai ta ɗaga.


Barrister ya ce "amma ya kayi aka kama mutum ɗaya" Jawahir ta ce " shi ƴansanda suka tarar ɗayan ya gudu" kai barrister ya girgiza kawai ya tashi ya yi musu sallama, daga nan ya nufi station dan tattaunawa da Hafiz,samu yayi an kai Hafiz prinson dan an shigar da case ɗin koto...........







Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.