Free chapter · Read without an account
30
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
3⃣0⃣
"What! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
badai kwantar da ita zakuyi ba?
Fuskar Doctor d'in d'auke da tausayawa,
yace " eh! dan gaskiya koda zamu sallame ta sai ya kai zuwa gobe,
" meke damunta?
Zazzab'i ne da ciwon kai, kuma dole sai anyi mata k'arin ruwa da allurai,
"tana ina?
Sir Moli yace a tak'aice,
" muje Doctor ya fad'a yana fita daga office d'in,
a baya Sir Moli ya bishi har zuwa d'akin da aka kwantar da Sanah,
hannunta d'auke da drip,
bakin gadon yaje ya tsaya had'i da k'ura mata ido,
Doctor yace " anyi mata allurar bacci ne,
dan ta samu hutu, dan ta jigata sosai,
ajiyar zuciya Sir Moli ya sauke had'i da yiwa Doctor godiya sosai,
sallama Doctor yayi mishi kana ya fita,
a hankali Sir Moli ya zauna a bakin gadon had'i da k'ura mata ido,
sai lokacin ya hango 'yar ramar da tayi,
fuskarta tayi firit, ga haske data k'ara,
cikin nutsuwa ya kai hannunta saman goshinta ya shafa,
a hankali ya rink'a shafa saman goshinta zuwa kanta,
cikin bacci Sanah ta saki ajaiyar zuciya,
had'i da motsawa ta kamo hannunta Sir Moli ta rungume a k'irjinta,
cikin sand'a Sir Moli ya fara k'ok'arin zame hannunsa daga jikinta,
idanta rufe still tana baccin, ta turo baki,
had'i da k'ara k'ank'ame hannun a k'irjinta,
kana ta k'ara gyara kwanciyarta,
murmushi yayi kana ya zame hannunsa,
baki Sanah ta kuma turawa had'i kwab'e fuska kamar zatayi kuka cikin shagwab'a,
ita a dole anyi mata ba dai-dai ba,
a hankali ya mik'e daga bakin gadon,
kan sofa ya koma yana tunanin abinyi,
ya sandai bai kamata ace ta kwana hospital ba tare da sanin Family'nta ba,
so dole ya sanar da su,
to amma ta yaya?
Ya tambayi kanta, shiru yayi na tsayin lokaci yana tunanin abinyi,
wayarta daya bari cikin mota ya tuno,
a hankali ya mik'e yaje bakin gadon,
ya ja mata blanket sama ya rufe ta,
kana ya juya zai fita, caraf yaji ta rik'o hannunshi cikin nata,
a hankali ya juya had'i da zuba mata ido,
still dai baccinta take yi,
cikin bacci Sanah ta k'ara rik'e hannunshi gam cikin nata,
tace " please karki tafi ka barni,
fa fad'a tana yamutsa fuska alamun shagwab'a,
murmushi yayi had'i da cire hannunta,
ya shafa kanta had'i dayi mata light kiss a goshi kana fita,
tun daga nesa yayi using remote ya unlocking motar,
yana daga waje ta b'angaren zamansa ya zura kansa da jikinta ya d'auko wayar,
kana ya rufe mota ya koma cikin hospital d'in,
gudun kar ya shiga cikin d'akin yayi waya ta tashe ta,
yasa shi tsayawa daga k'ofar d'akin ya kunna wayar,
luckily babu pin a wayar yayi mamakin ganin wayar babu pin dan wancan karon ma haka ya gani,
wayar ya shiga juyawa a hannunsa yana kallanta,
had'i da tunani,
dan yasan is so hardly kaga wayar 'yan mata da samari a wannan zamanin babu password,
a ransa yace " ta yarda da kanta kenan,
ya fad'a yana dialing number Abbu,
daya gani a jeren missed call,
tana soma ringing Abbu yayi picking,
cikin girmamawa Sir Moli yace " Assalamu Alaikum,
d'an shiru Abbu yayi jin muryar namiji,
sai da Sir Moli ya sake maimaita sallamar kana Abbu ya amsa,
gaidashi Sir Moli yayi Abbu ya amsa cikin sanyin jiki,
a nutse Sir Moli yayi mishi bayanin shi Malamin su Sanah ne,
kuma yanzu haka suna asibiti bata da lafiya har an kwantar da ita,
cikin tension Abbu yace " subhanallahi a wanne hospital aka kwantar da ita?
Cikin nutsuwa Sir Moli yayi masu bayani,
sosai Abbu yayiwa Sir Moli godiya kamar me,
kana Abbun yace gasu nan yanzu,
bayan Abbu ya kashe wayar ya kalli Mamu yace " dama Sanah bata lafiya kika barta ta tafi makaranta?
Mamu tace " wallahi ban sani ba meke faruwa?
Abbu yace " lecturer sune ya kira ni yanzu yake shaida man an kwantar da ita a asibiti,
a kid'ime Mamu ta mik'e tana salati tace " a wanne asibitin! meke damunta?
Abbu yace " kwantar da hankali yace man zazzab'i ne kawai,
yanzu zanyiwa Didi waya yaje,
Mamu ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,
Abbu yayi dialing number Didi,
bayan sun gaida Abbu yace " 'yarka ce ba lafiya, an kwantar da ita a hospital,
" subhanallah a wanne asibitin?
Didi ya fad'a cikin tension,
Abbu yayi masa bayani,
kana ya kashe wayar,
da sauri Didi ya mik'e yayi parlor wajen Juju,
a gaggauce yayi mata bayani kana yace ta shirya abinci yanzu,
itama da sauri ta mik'e ta shirya suka fita,
a compound Didi ya had'u da Ziyad da Zafran ganin yadda suke sauri yasa su nufarsu,
suna tambayarsu lafiya,
a gaggauce Didi yayi musu bayani,
kana ya shiga mota suka tafi,
Ziyad yacewa Zafran" jeka shirya kazo mu tafi,
Zafran ya amsa da " OK,
koda suka shiga su Halan cewa sukayi sai sun bisu,
haka rungud'uma suka tafi gaba d'ayansu,
Sir Moli yana gama wayar ya koma cikin d'akin ya zauna akan sofa,
ba'afi 20 minutes ba su Didi suka k'araso,
number Sanah Didi ya kira Sir Moli yayi picking Didi yace " gamu mun k'araso,
Sir Moli ya fita ya shigo dasu,
su Juju basu jima da zuwa ba su Ziyad suka k'araso,
gaba d'ayansu hankalinsu a matuk'ar tashe yake,
jikinsu sai kerrma yake, duk sukayi cirko-cirko a bakin gadon da Sanah ke kwanciya,
Halan sai shafa kanta take,
yau kam Sir Moli yaga yadda Sanah keda gata,
ake kuma mugun santa a cikin Family'nsu,
dan kowa ka gani a cikinsu yadda kasan zai d'ora hannu aka ya kurma ihuu,
ganin dangin Sanah sunzo yasa Sir Moli yi musu sallama,
sosai su Didi, Ziyad, Zafran da Juju sukayi mishi godiya kamar me,
sai lokacin hankalin Halan ya kai kansa,
tayi mamakin ganinsa sosai,
har k'asa Halan ta durk'usa ta gaida Sir Moli cikin girmamawa,
shima ya amsa cikin mutuntatawa,
har bakin motarsa Ziyad da Zafran suka raka,
kana suka kuma yin musabaha had'i da sallama ya tafi,
bayan ya basu wayar Sanah.
Tunda Khulud ta shiga mota ta zauna take ta faman kuka kamar ranta zai fita,
abu ya had'u yayi mata yauwa ga mari ga tsinka jaka,
shiru Hanash yayi baice komai ba,
motar tayi tsit babu abinda ke tashi sai sautin kukan Khulud,
a harabar gidan yayi parking ya fito da sauri ya zagaya b'angaren Khulud jikinsa na rawa ya sunkuya da niyyar d'aukarta,
duka hannayenta biyu Khulud ta sanya ta tura shi baya,
cikin masifa tace " don't dare you touch me again,
ta fad'a tana fitowa daga motar idanta tarr cikin nashi,
sororo Hanash yayi yana kallanta,
kasancewar shi ba mutum bane mai san hayaniya da fad'a yasa shi tsayawa yana kallanta,
yama rasa abinyi har ta shige cikin gidan ta barshi,
bayanta yabi da kallo yana matuk'ar mamakinta,
dan da fad'a mishi akayi Khulud tana da wannan zafin ran bai tab'a yarda,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kana ya taka yabi bayanta,
koda ya shiga cikin gidan iskewa yayi harta shige bedroom d'inta ta rufe k'ofar,
bedroom d'insa ya wuce yayi wanka,
ya zura kaya marasa nauyi kana ya fito,
yadda ya bar k'ofar haka ya dawo ya iske ta,
bai wani tsaya yi mata magana ba yayi ficewarsa,
bai dawo ba sai dare wajen k'arfe 9:00pm،
rik'e da ledoji dan yasan ba lalle idan tayi girki ba,
kamar yadda yayi tsammani haka ya tarar,
yadda ya fita yabar k'ofar haka ya dawo ya iske ta rufe,
bakin k'ofar yaje ya tsaya yana tunanin abinyi,
daga bakin k'ofar ya rink'a jiyo sautin kukanta,
ba k'aramin mamaki Hanash yayi ba,
ganin har lokacin Khulud na, kuka,
cikin mutuwar jiki yayi knocking k'ofar,
amma shiru, daga wajen yace " dan girman Allah kiyi hak'uri ki bud'e man,
still banza Khulud tayi dashi bata ce mishi komai ba,
Hanash ya kai wajen 20 minutes tsaye bakin door yana ta faman bata hak'uri,
had'i da rok'onta kan ta bud'e masa k'ofar,
amma bata amsa masa koda sau d'aya bane,
ganin haka yasashi komawa kan sofa ya zauna had'i da ciro wayarsa cikin aljihu,
yayi dialing number Mimmee bugu d'aya Mimmee tayi picking,
cikin sanyin murya ya gaida ita,
ta amsa masa, yanayin yadda taji muryarsa yasa ta cewa " lafiya dai Son!?
" Muryarsa na rawa yace " please Mimmee ki kira Khulud kice ta bud'e man k'ofa,
cike da mamaki Mimmee tace " kamar ya?
Yace " ni dai please Mimmee kawai kice mata ta bud'e man k'ofar,
Mimmee tace " fad'a kukayi?
Shiru yayi baice komai ba,
a d'an hasale Mimmee tace " uban me kayi mata?
Yace " banyi mata komai ba,
nima yanzu na dawo gidan na iske ta shiga d'aki ta rufe k'ofa tana ta faman kuka,
Mimmee tace " subhanallah bari na kira ta,
kashe wayar Mimmee tayi kana tayi dialing number Khulud,
sai da wayar ta kusa tsinkewa kana Khulud tayi picking,
cikin muryarta da bata fita sosai,
ta gaida Mimmee, Mimmee ta amsa cikin fad'uwar gaba dan ta fahimci akwai matsala,
Mimmee tace " Khulud lafiyarki?
Khulud tayi shiru bata yi magana ba,
Mimmee tace " Khulud meke faruwa tsakaninki da mijin naki?
Khulud tace " bakomai Mimmee,
babu yadda Mimmee batayi kan Khulud ta sanar mata abinda ke faruwa tsakaninta da Hanash ba,
amma Khulud tak'i, tace babu komai,
ajiyar zuciya Mimmee ta sake cikin ranta kuma tana jin dad'i dan ta fahimci Khulud macece mai matuk'ar sirri,
da alama bazata tab'a fallasa tsakaninta da mijinta ba,
bazata tona sirrinsu ba,
Mimmee tace " to koma miye kiyi hak'uri,
saboda ita rayuwar aure ta gaji haka,
duk macen da kika gani gidan mijinta zaman hak'uri takeyi,
sosai Mimmee tayiwa Khulud fad'a da nasiha masu ratsa jiki da zuciya,
ta nusashsheta abubuwa da dama kan zamantakewar aure,
daga k'arshe Mimmee ta k'ara da bata hak'uri sosai,
kana tace " ki daina yawan kuka gaban miji indai bana shagwab'a,
ko na kissa bane, dan yawan kuka yana kawo raini tsakaninku,
sannan yana sa namiji k'osawa dake,
ko ya daina tsoro da shayin yi maki laifi,
Khulud ta amsa da " to,
kana ta umarce ta kan taje tayi wanka taje wajen mijinta,
cikin sanyin jiki Khulud tace " to Mimmee in sha Allah zanyi duk yadda kikace,
murmushin jin dad'i Mimmee tayi kana tace " yauwa 'yata nagode sosai kinji,
Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a ta gari,
kasa amsawa Khulud tayi saboda kunya,
kana sukayi sallama Mimmee ta kashe wayarta,
Mimmee na kashe wayar Khulud ta mik'e cikin sanyin jiki,
ta shiga wanka, dan nasihar Mimmee tayi masifar shiga jikinta,
bata dad'e ba ta fito, ta shirya,
dayake tayi sallah ، tana gama shiryawa ta bud'e k'ofar ta fita parlor.
zaune ta iske shi kan sofa, yana ganinta ya mik'e da sauri jikinsa yana rawa ya nufeta,
ya shiga k'ara bata hak'uri,
ta d'an saki ranta ba yabo ba fallasa,
dakyar Khulud ta d'anci abinci,
a hankali Hanash ya rungumo ta jikinsa ya kwantar da ita saman k'irjinsa,
yana shafa kanta, yana cigaba da bata hak'uri.
K'arfe 11:30pm na dare Sanah ta fara motsi,
a hankali ta sanya hannunta wanda ke sanye da cannular ta dafe kanta,
had'i da bud'e idanta a hankali a hankali,
bakinta d'auke da salati,
da sauri Halan ta mik'e taje kusa da Sanah,
ganinta ta farka yasa Ziyad fita da sauri ya tafi kiran Doctor,
tare Doctor da Ziyad suka shigo tare,
duddubata Doctor ya kumayi kana ya bada umarnin a bata abinci taci,
cikin lallab'awa Halan ta kama Sanah ta zaunar da ita,
muryar Sanah na rawa tace " sallah zanyi,
batare da b'ata lokaci ba, Halan ta kama ta ta kaita har cikin toilet kana ta fito had'i da rufe mata k'ofar,
kafin Sanah ta idar da sallah Juju ta had'a mata tea da abinci,
ruwan tea Sanah ta fara sha kana daga baya Juju ta matsa mata taci farfesun kaji,
kana tasha magani,
sosai Sanah taji dad'in jikinta,
ta wartsake, ta shiga hira da su Juju kamar ba itace patient d'in ba,
sai dare su Halan suka koma gida suka bar Juju ta kwana tare da Sanah,
duk da Halan taso kwana Didi ya kad'a su suka koma gida,
washe gari da safe su Halan suka dawo,
suka iske Sanah ta warke garau,
bayan tayi breakfast Doctor yazo ya k'ara dubata kana ya sallame ta,
duk abin nan da ake hankalin Sanah yana kan Sir Moli,
badan komai ba sai dan ciwon dake hannunsa,
k'arfe 12:00 na rana suka isa gida,
Halan da Juju suka raka Sanah part d'in Mamu har cikin bedroom d'inta.
Kasancewar ranar Friday aka sallamo Sanah yasa ta samu ishashshen lokacin hutu,
dan Saturday and Sunday babu makaranta,
tun da Sanah ta dawo gida ta shiga tunanin ko ya Sir Moli yake?
ko ya jikin nasa yake?
ga bata da number shi balle ta kira shi,
cikin ranta tace " Allah sarki duk sanda nake cikin wani hali ko matsala sai Allah ya kawo man shi ya taimake ni,
ganin tunanin ba kai mata zayyi ba yasa ta mik'ewa ta shiga bathroom ta watsa had'i dayin alwala tayi sallah kana ta kwanta.
Ranar Monday da wuri Sanah ta shirya ta tafi makaranta,
office d'insa tayi niyyar fara shiga tayi masa godiya amma ta fasa,
dan ganin baifi 10 minutes left a shigo masu lectures ba,
tana shiga class Rose ta taso da sauri ta tare,
had'i da rik'e hannun Sanah taja ta waje,
can gefe Rose taja Sanah inda babu kowa,
Rose ta kalli Sanah tace " ina kika shige ne ina ta nemanki?
Sanah tace " rashin lafiya nayi shiyasa kikaga kwana biyu ban shigo ba,
Rose tace " ayya sorry dear,
Sanah tace " thank you,
Rose tace " kin tuna maganar da mukayi dake kwanaki akan Muslims?
Sanah tace " eh!
Rose tace " maganganun da kika fad'a a wannan lokacin sunyi tasiri a zuciya ta,
sun kashe min jiki sosai, dan haka naje nayi tunani sosai,
daga k'arshe nayi bincike mai zurfi akan addininku na muslunci,
so in fact I want converted to Islam,
cikin matsananciyar murna da farin ciki Sanah ta rungume Rose,
yayinda hawayen farin ciki suka shigo zubowa Sanah,
na tayi sanadiyyar musluntar da wani,
da sauri Sanah taja hannunta zuwa office d'in Sir Moli,
saboda tsabar murna da farin ciki Sanah bata tsaya neman izinin shiga ba,
ta danna kai cikin office d'in kanta tsaye,
zaune suka iske shi akan kujera yana aiki a system,
fuska ya tsuke kana yace " ubanwa ya baki izinin shigo man office kai tsaye?
Bata kula da maganarsa ba tace " Sir wajenka muka zo,
a tsawace yace " get out!,
ya fad'a yana nuna mata k'ofa,
a d'an tsorace Sanah taja baya kana tace " Sir Rose ce take san musulunta,
jikin Sir Moli yayi sanyi,
a hankali ya mayar da kallansa ga Rose yace " are you sure you want converted to Islam?
"Yes Sir Rose tace tana murmushi,
" Alhamdulillah Sir Moli yace,
a nutse Sir Moli yayi hanyar fita had'i da cewa " ina zuwa,
Sir Moli bai jima ba, ya dawo da manyan malaman addinin mulunci dake BKU,
had'i da shuwagabanin makarantar,
kowa fuskarsa d'auke da murmushi,
d'aya daga cikin Malaman ya kalli Rose yace " kin tabbatar musulunta zakiyi da zuciya d'aya?
" Eh Rose tace,
Malamin ya kuma cewa " me yaja ra'ayinki zuwa ga musulunci?
Rose ta basu labarin abinda ya faru tsakaninta da Sanah,
da yadda tayi ta bincike da neman k'aramin bayani akan musulunci,
gaba d'aya malaman sun jinjinawa basira da hikimar Sanah,
anan cikin office d'in Sir Moli aka musuluntar da Rose,
Sanah nata hawayen farin ciki,
yayinda itama Rose d'in hawayen farin cikin takeyi,
Malamin ya bata zab'in d'aya daga cikin sunan musulunci,
Rose ta zab'i sunan Fatima,
cikin Malaman wani yace " Alhamdulillah Fatima yanzu kin zama cikekkiyar musulma,
wanka kad'ai ya rage miki,
then what about your family issue?
Rose wacce ta koma Fatima tayi murmushi tace " family na basu da matsala dan Brother na ne ya fara musulunta last year,
bai kuma fuskanci matsalar komai ba,
kuma sai da na sanar da parents d'ina,
su suka amince min kamar yadda suka amincewa Yaya na,
Alhamdulillah Malaman sukace,
kana ya sanar da ita zasu sakata a d'aya daga cikin islamiyoyinsu ta rink'a zuwa karatu,
dan ta san abubuwa cikin addinita,
Fatima ta amsa da to,
bayan Sanah ta koma gida cikin murna da d'oki ta sanar da 'yan gidan su labarin musuluntar Fatima,
sosai 'yan gidansu Sanah sukayi murna,
Abbu yace ta kawo mishi ita zayyi mata kyauta.
A b'angaren su Khulud sun dai-daita sosai,
dan Hanash hak'uri yayi ta bata,
yana rarrashinta,
had'i da kwantar mata da hankali yana fad'a mata dad'ad'an kalamai masu kwanatar da zuciya,
yayinda da kullum Khulud da Sanah sai sun nemi juna a waya amma basu samun juna sai dai suyi magana ta WhatsApp,
hakan yasa kullum kuma koyaushe suna cikin chart da juna,
dan dukkan su babu wanda yayi wani tunanin.
Ranar Friday bayan an tashi daga lectures,
around 4:30pm na yamma Sir Moli zaune cikin motarsa ya kishingid'a had'i da lumshe idanshi,
jin zuciyarshi na bugawa da tsananin k'arfi yasa shi bud'e idanshi a hankali,
yana bud'e idan ya hangota tana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,
da ganinta kasan babu abinda ke damunta cikin rayuwarta,
ido ya k'ura mata sosai, tun daga nesa har ta wuce shi,
ido ya sake lumshewa ya bud'e had'i da sauke ajiyar zuciya,
kana yayiwa motar key,
gabanta ya tsaya batare dayayi mata magana ko ya bud'e motar ba,
tsayawa tayi ta kama k'ugunta,
tare da yin rolling sexy eyes d'inta,
a nutse Sanah ta taka ta bud'e motar ta shiga,
daga shi har ita babu wanda yayiwa wani magana,
sai da akaui d'an lokaci kafin Sanah tace " ina wuni?
Banza yayi da ita bai amsa ba,
murmushi Sanah tayi tace " dama ni kake jira ko?
Jin abinda tace yasa shi juyowa a hankali ya kalli cikin kwayar idanta,
na seconds kana ya mayar da kallansa ga tuk'in da yake yi,
rolling sexy eyes d'inta ta kuma yi, kana tace " deaf!
kallanta ya kuma yi batare da yayi maganar ba,
Sanah tace " ah yau inaga ciwon baki da azumin magana yake yi,
" talkative! yace batare daya kalle ta ba,
murmushi tayi tace " ashe dai yana magana!
fuska ya tsuke yadda kasan anyi mishi sammacin mutuwa,
had'i da kauda kansa gefe,
ganin ba hanyar gidansu ya d'auka ba yasata kallanshi da niyyar yin magana,
ganin kwata-kwata babu fuska dan ya had'e fuskarsa yasha mur sosai yasa ta yin shiru dole,
A harabar wani k'ayataccen park mai shegen kyau yayi parking,
wajen ya k'ayatu sosai kamar a k'asar waje,
bayan yayi parking a wajen ya bud'e motar ya fito batare daya ko kalli inda take ba bare yayi mata magana,
baki ta zumb'uro had'i da bin bayansa da harara,
kana ta bud'e motar ta fito tabi bayansa,
wata hanya taga yabi tayi saurin bin bayansa sai da sukayi 'yar tafiya kana suka b'ulle,
tsayawa Sanah tayi cak had'i da furta " wow! masha Allah,
ganinta a tsakiyar lambu wanda ya gaji da had'uwa,
daga hannun dama kwantaccen ruwan ne kwance a k'asa,
daga b'angaren hagu kuma table ne guda d'aya tak d'auke da kuje biyu,
a saman table d'in babbar kwalbar lemon mai kama da giya,
sai glass cups guda biyu a gaban kowacce kujera,
hannu Sanah ta d'aga sama had'i lumshe idanta,
ta d'aga kanta sama tana juyi a wajen had'i da shak'ar dadd'an k'amshen furannin dake zagaye da wajen,
yayinda sassanya iska mai sanyin dad'i ke kad'awa,
hannu Sir Moli ya hard'e a k'irjinsa had'i da zuba mata ido,
fuskar Sanah d'auke da murmushi ta bud'e idanta ta sauke su akan Sir Moli tace " wow! wajen ya burge ni sosai,
ta fad'a cikin kwanciyar hankali,
bayyi mata magana ba ya k'arasa inda kujerun suke ya zauna akan d'aya daga ciki,
cikin nutsuwa itama ta taka ta zauna tana cigaba da sauraren dadd'an kukan tsuntsayen dake tashi cikin lumbum,
ga sautin ruwa mai dad'in sauraro,
idanshi na kanta ya kafe ta da shu'uman idanuwansa,
bai ko k'iftawa,
ta wata k'ofa wani matashin sauri ya fito a hankali yazo ya bud's drinks ya zuba cikin cups d'in,
kana ya d'an rusuna yabar wajen,
cikin k'asaita Sir Moli ya d'auki cup d'in gabansa yakai baki,
ya d'an kurba kana ya aje,
itama d'aukar cup d'in tayi takai bakinta ta kurb'i lemun ciki,
Sir Moli yace " it's bar!
cikin tsoro da firgici Sanah ta zaro idonta waje,
tace " what! mekace?
Kamar bazayyi magana ba,
sai kuma yace " yes! ai nasan kinji ,
a kid'ime Sanah ta mik'e tsaye cikin tashin hankali ta d'auki kwalbar tana dubawa,
nannauyan ajiyar zuciya ta sauke ganin tacaccen ruwan inibi ne,
had'i da komawa ta zauna akan kujerar,
har lokacin idashi na kanta bai ko k'iftawa,
idanta ta jefa cikin nashi tace " meyasa!?
Sai da ya d'auki lokaci kana yace " nace miki ki sha ne?
Idanta cikin nashi ta girgiza mishi kanta had'i cewa " a'a,
yace " to akan me zaki sha?
kanta ta kunyar k'asa batare datace mishi komai ba,
yace " wata rana idan kina irin haka sai kin sha wani mugun abun,
cikin shagwab'a Sanah ta turo baki had'i da cewa " to ai naga kasha ne,
bayyi mata magana ba bai kuma d'auke idanshi daga kanta ba,
jin notification yasa ta bud'e hand bag d'inta ta d'auko wayarta dan tasan Khulud ce,
video taga Khulud d'in ta turo mata dan haka tayi saurin yin playing,
short comedyn film d'in na mamajo na marigayi Rabilu Musa Ibro (Allah yayi masa rahama),
ta gani, tun kafin ta gama gani ta sanya dariya sosai kamar me had'i da sanya hannunta saman bakinta ta rufe bakin tana cigaba da yin dariya,
Ido Sir Moli ya k'urawa Sanah yana kallan yadda take yin dariya sosai yayi,
a bazata tammakar saukar aradu Sanah taji muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " *I LOVE YOU SANAH!!!*
MOMYN ZARAH