Free chapter · Read without an account

57

by Hauwa A Usman · RASHIN SANI…

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




5⃣7⃣




Cikin kid'ima Sanah ke yiwa Khulud wani irin hargitsatsan kallo,

wanda ni kai na na kasa gane fanufarshi da ma'anarshi,

 gaba d'aya jinta da ganinta suka d'auke,

ta daina ganin komai sai duhu,

ta kuma daina jin komai sai shuuuuuuu,

komai nata ya tsaya cak ya daina aiki,

kwakwalwarta tayi hook ta daina fahimta da gane komai,

cikin matsanancin kuka Khulud tace " wallahi Allah ban san wannan maganar ba,

yama za'ayi hakan ta faru sai kace a cikin cartoons.....!?


"Sai dai kawai ida HANASH D'IN TAKE SO.....!,

ta fito ta fad'a ni kuma zan yarje mishi aurenta,

gaba d'aya parlor'n akayi shiru sai sautin kukan da Khulud keyi,

ido Sanah ta zubawa Khulud tana ji tana cewa " wallahi dama tunda Sanah ta dawo daga bautar k'asa,

na fahimci akwai matsala, dan gaba d'aya ta canja,

hakan yasa har na fara zargin kodai ta samu matsalar HAUKA NE,

ko kuma ta fara SHAYE-SHAYE ne,

 kowa yayi tsit yana sauraron yadda Khulud ke kuka da rantse-rantse,

hannu Abbu ya d'aga mata had'i da cewa " ya isa,

kana ya mayar da kallanshi ga Sanah dake kamar mutum mutumi,

da ido kawai take bin kowa dake cikin parlor'n,

batare da tana fahimtar abinda ke faruwa ba,

Abbu ya kira sunanta " Sanah....!

bata san ma yana yi ba balle ta d'ago kanta,

" kinji abinda Khulud ta fad'a.....!?


 Shiru tayi mishi,

Abbu yace " ke dake nake magana,

batayi magana ba balle ta kalle shi,

a fusace Abbu yace " wai baki ji na ne....!?


Still dai shirun ta kuma yi mishi,

a fusace Ziyad ya dalla mata gigitattun marika kyawawa guda biyu,

cikin masifa yace " baki ji ana yi miki magana.....!?


" Ko wani sabon islaci da rainin hankali ne haka.....!?


Hannu Dide ya d'aga mishi tare da cewa " ya isa,

kana ya mayar da kallanshi ga Sanah,

da har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,

yace " Sanah kiyi magana dan Allah kema,

yadda tayiwa Abbu shima haka tayi mishi,

ya kuma cewa " dan Allah meye gaskiyar wannan al'amarin.....!?


Shiru dai ta kuma yi bata ko motsa bakinta ba,

" Sanah baki jin ina miki magana ne....!?


Shirun ne dai ya kuma biyo baya,

saboda komai nata yayi kasancewar mugun shock d'in datayi،

ganin Sanah tayi tayi magana kota kawo hujjar da zata kare kanta ba,

yasa gaba d'ayansu suka yarda Khulud ke da gaskiya,

Halan ce kad'ai ta kasa yarda ta gaskata Khulud, taji tafi yarda da Sanah fiye da Khulud d'in,

a fusace cikin fad'a da masifa Abbu ya mik'e tsaye yana kallan Sanah,

yace " so kike ki raba zumuncin dake tsakanin ahalin mu....!?


"So kike ki gama sanadiyyar wargajewar iyayenmu wanda muma tare muka taso muka gansu....!?


" So kike ki tarwatsa mu.....!?


"Yanzu Sanah duk irin yardar dani yi dake amma da haka zaki saka min.....!?


" A 'yan shekarunki har kin san ki shirya wannan kitimurmurar.....!?


"Kin ban kunya Sanah, kinsa jiki da gwiwoyi na duk sunyi sanyi akanki,

kin saka ina jin kunyar dangi da 'yan uwa na,

to bari kiji idan ma dan baki san aure kika shirya wannan kitimurmurar da tuggun,

wallahi wallahi wallahi Allah yau baki kwana sai da aure bisa kanki,

yau da auren wani zaki kwana, kina matsayin matar shi,

kana ya mayar da kallanshi ga Aarib yana huci yace " kai ka fiddo wacce zaka aura ko kuwa.....!?


Kanshi k'asa dan shima harga Allah yafi yarda da Sanah akan Khulud,

saboda duk ranar da iyayensu sukayi musu maganar su fiddo masoyansu,

data fito gidan Khulud take tafiya,

muyarshi na rawa yace " Abbu ku dai tsaya ayi bincike a tabbabar da gaskiya al'amarin,

a fusace Abbu yace " kai ni zaka koyawa abinda ya kamata nayi.....!?


"A'a Abbu kawai dai naga ya kamata ayi bincike ne,

a bi komai a hankali kar a yanke hukunci cikin fushi....!

" shine nace abinda ya kamata zaka koya min.....!?


"A'a yace cike da girmamawa,

Abbu yace " wato so kake a barta tayi abinda take so ta kuma ga dama ko......!?


"A'a ya kuma cewa, kallanshi Abbu yayi from head to leg,

yace " kai dakata ma....!, kodai bakinku d'aya tare kuka shirya komai ne dan na lura kaima ba auren kake so ba....!?


Da sauri ya kuma cewa " a'a,

Abbu yace " tambayarka nayi kana da wacce kake so kuma zaka aura koko.....!?


"Bakinshi na rawa yace " dama dama so nake na......!

" dama dama me....!?


"Ok fine & good abu yazo da sauk'i,

Dide yace " Hamraz ya kira shi da ainahin sunanshi,

hakan yasa Abbu juyawa ya kalle shi,

Dide yace " please ka sausautata zuciyarka ka nutsu,

ka kuma kwantar da hankalinta ka bari muyi bincike,

kafin mu zartar da hukunci, ido Abbu ya k'ura mishi ya rasa abinyi,

saboda da ace ba Sanah bace ta sai yayi mishi magana,

juyawa yayi yana niyyar fita batare dayace mishi komai ba,

Abbu na k'ok'arin fita Halan tace " dan Allah Abbu a d'an dakata tukunna,

saboda wallahi Sanah bata cikin hayyaci da nutsuwarta idan ka lura,

 uwar harara Ziyad ya watsa mata wacce tasa ta sunkuyar da kanta k'asa,

" wallahi summa tallahi yau zan aurar da ita ga duk wanda yasa mijinta ne,

tunda iskanci take ji, kwanakin ma dana bata na janye su a yau-yau d'innan zan d'aura mata aure,

" Hamraz.....!, Danish mahaifin Dide ya kira sunnashi,

" dawo nan ka zauna, ya fad'a cikin dattako,

ba musu ya koma ya zauna a inda yake tun farko,

Danish na k'ok'arin yin magana Gahen mahaifin Abbu ya kalli mutanen dake falon yace,

Rawan da Hamraz su tsaya amma sauran gaba d'ayanku ku fita,

a hankali Halan ta tashi cikin sanyin jiki ta kama Sanah,

wacce ke bin gaba d'ayansu da ido,

batare data san komai ke faruwa ba,

duk suka mik'e suka fita amma banda Aarib,

Rawan ya kalle shi yace " kai kuma zaman me kake yi......!?


Cikin girmamawa yace " da maganar da zanyi daku ne nima,

bedroom d'inta Halan ta kaita ta zaunar da ita tare da zama kusa da ita,

tace " nasan yanzu ko nayi miki magana ba lalle ki fahimci abinda nake cewa ba,

amma ki huta zan dawo muyi magana kinji ko....!?


Batare datace mata komai ba,

ta bita da ido harta fita, Khulud dake lab'e tayi saurin shigowa,

tare da dannawa k'ofar key, kana ta tako zuwa gaban Sanah,

fuskarta d'auke da shu'umin murmushi,

tana taunar chewing gum k'ass k'ass k'ass,

tsaye tayi a gabanta tana kallanta,

while tana murmushi, a hankali ta sanya hannu ta d'an bubbuga kumatun Sanah,

gami da sunkuyo da fuskarta saitin fuskarta tana kiran sunanta,

ganin kwata-kwata bata cikin hankalinta,

yasa Khulud takawa ga fridge ta bud'e ta d'auko robar ruwan sanyi,

murfin ta b'alle had'i da tsayawa k'erere a gaban Sanah,

ta d'aga robar ruwan ta shiga tsiyayawa a tsakiyar kan Sanah,

cike da zallar mugunta while tana murmushin,

a razane Sanah ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tare da fashewa da rikitaccen kuka,

" wallahi Abbu da auran Hanash a kai na, dan Allah kar kayi min aure saman aure,

please my Khulud kiyi musu bayani,

baya Khulud ta d'anja had'i da hard'e hannuwanta a k'irji,

ta zura hannu d'aya ta rik'e hab'arta tana kallan Sanah,

had'i da yin sauti da harshen ta,

toussssss tousssssss toussssss,

kana tace " babu mai jinki bare ya gaskata ki,

jin muryarta yasa ta mik'ewa a sukwane,

had'i da mik'a hannu da niyyar rik'e Khulud,

da sauri Khulud taja baya tare da cewa " don't dare you touch me,

don't ever ......! 

" a matuk'ar rud'e Sanah ta kuma nufarta tana kuka tace " please my Khulud help me kar mu shiga wuta,

"baki ji abinda nace miki ba kenan.....!?


Khulud ta fad'a tana kuma ja baya,

" in taimake ki inyi miki me Sanah.....!?


" Do you think I love you....!?


Idon Sanah waje tace " what do you mean....!?


"I mean what you think an what you hear,

Khulud tace tana kallan Sanah,

marin kanta ta shiga yi tana cewa " this is not my real beloved Khulud,

this is not you Khulud, some bad evil enter you,

wallahi bake bace dan nasan baki tab'a yi min haka Khulud,

murmushi Khulud tayi gami da cewa " baki da wayou yarinyar,

kin tabbaka babban kuskure kinyi sake,

kina tunanin zan zab'i naji kunyar duniya ne......!?


" Ko a hauka irin naki kina zaton zanyi ganganci nayi saken rasa Sultan da Hanash......!?


"Wallahi zan iyayin komai a kansu,

Sanah kece kika jefa rayuwata cikin k'unci da musiba,

an you think I was still love you,

kanta ta shiga girgizawa tana ja baya gami da cewa " no...! no....! this is not my lovely Khulud she have mercy & beautiful heart,

wallahi an canja min ke Khulud wannan bake bace an canja ke,

ko kuma na tabbatar akwai wani abun a k'asa,

Murmushi Khulud tayi tare da rausayawa tace " makaho ba shi da ido,

amma ida ka kira shi da ainahin sunanshi na makaho bazai ji dad'i ba,

mugu idan ya cika mugu baya fito da suffarsa ta asali arar ta mutanan kirkiri yake yi dan ya amfana da ita....!,

a zahiri kin fini magana, fad'a da rashin hak'uri,

amma a bad'iri nice asalin shaid'aniyar kuma muguwar,

ke kina da zuciya, yafiya da saurin manta sharri,

amma duk zafin zuciyar da kike da ita NAFI KI ZAFIN ZUCIYA SANAH,

danni bana yafiya, bana saurin manta sharri amma ina da saurin manta alkhairi,

cikin matsanancin kuka Sanah tace " why why Khulud me nayi miki......!?


" Good Question,

da farko ke kika lalata min farin ciki na,

kika lalata min cikar burina kika yi min babban illar da har na mutu bazan manta ba,

kika lalata min mahifa, Na zama juya,

duk sanda Jaddah ta kira ni da juya,

ba ita nake jin haushi ba, ke nake jin Na tsana fiye da komai,

naji mugun zafi da rad'ad'i akanki,

 then....! Hanash,

kin tsane shi, ni kuma kanshi babu abinda ban iyawa,

wallahi Allah ina iya kashe mutum kan Hanash,

sannan kika AURE SHI, wannan ya tabbatar min dake maciya amana ce,

tunda har zaki iya auren miji na ki kuma had'a gado da jiki dashi,

kin san yadda nake ji duk lokacin danaga kin shiga bedroom d'inshi.....!?


" Kin san yadda nake jin ihuuunku na sex.....!?


"Wallahi nasha attempting kashe kai na, saboda tsabar bak'in ciki, 

akanki na k'auracewa mijina inaji ina gani,

akanki Hanash yake jifa na da maganganu kala-kala marasa dad'i,

 akanki babu irin kukan bak'in cikin da banyi ba,

akanki babu bala'in da ban gani ba,

idan har nayi sake Hanash ya gane kece ke faranta darenshi,

ki hasakaka rayuwarshi, ki fad'ad'a mafarkinshi,

ki yalwanta duniyarshi nasan bai tab'a iya rabuwa dake,

wanda hakan ni kuma dai-dai yake da tsinkewar numfashi na,

saboda BAK'IN KISHI da Allah yayi min,

wallahi Sanah in banda kece da tuni......!

sai kuma tayi shiru had'i da cije lips d'inta,

ina da bala'in kishi, ina matuk'ar so da k'aunar Hanash fiye da komai da kowa,

babu abinda ban iyawa kanshi,

ina kishinshi fiye da tuninki, Allah ya jarrabe ni da azabban kishi,

haka duk macen da tayi gangancin rab'a ko kusantarshi sai buzunta,

babu abinda na tsani koda jin sunanshi irin KISHIYA, 

amma sai gashi ke kin kasance KISHIYA TA, 

kin had'a gado da jiki dashi,

har yana fifita ki a kai na,

kika lalata min mahaifa, kika fito k'iriri kika nuna baki k'aunar Hanash,

Allah kad'ai yasan masifa da bala'in da nake idan kuka kasance tare,

then na fad'a miki hali na, ina da saurin manta alkhairi,

amma ina da rik'o da sharri,

har Khulud ta dasa idon Sanah ta kallanta cike da tsantsar mamaki.


While hawaye na zubo mata, ta kalli Khulud tace " nayi matuk'ar mamaki duk da kasancewarki mutum 'yar Adam,

wacce zaku iyayin fiye da abinda yafi haka ma,

but I still surprise an shock,

ke da kanki kika zo min da maganar auren Hanash ko kin manta....!?


"Ke kika matsa min kika kika rink'a rok'o na,

kika saka na lalata gaba d'aya rayuwata da farin cikin duniya ta,

kika wargaza min cikar buri da muradi na da komai nawa...!,

kika rink'a bina kika kuka kina rok'o na, 

Khulud idan baki manta ba, a ranar da kika fara min maganar auren Hanash har suma nayi,

kika sa na yaudari iyaye na, na ci amanar Sir Moli,

duk dan na faranta miki, na kuma sanya ki cikin farin ciki Khulud,

then ban tab'a k'in Hanash ba, 

mun dayyi 'yar tsama, amma ban tab'a tsanar shi ba saboda ke,

da kuma son da nake yi miki,

& maganar Sultan har abada ba'a tab'a canjawa tuwo suna har abada,

_(Niko nace k'arya ne Sanah dan da larabci ma sunanshi ASIDA)_ 

kuma komai daren da d'ewa dole sai gaskiya tayi halinta ta bayyana,

saboda baki tunda kike a duniya baki tab'a jin ance gaskiyar mutum ta k'are ba,

sai dai ace k'aryarka ta k'are,

kuma dama rayuwar duniya ta gaji haka wanda ka yarda shi,

kake so tsakani da Allah da zuciya d'aya yakan iya cutar dakai,

saboda fad'ar Annabi SAW ce ,

" kaso masoyinka saya-saya saboda wata rana yana iya komawa mak'iyinka,

haka kak'i mak'iyinka saya-saya saboda wata rana yana iya komawa masoyinka.


Murmushi Khulud tayi had'i da takawa gaf da Sanah tace " ki nisanci Hanash da Sultan,

nisa mai masifar tazara, dan kamar yadda kika ji nace zan iyayin komai akan su,

to ina nufin komai fa, 

harta juya ta nufi k'ofa, Sanah tace " ji mana....!

cak Khulud ta tsaya had'i da juyowa,

fuskar Sanah d'auke da murmushi tace " duk da cewa munanan abubuwa da zunubai,

sukanyi kerere suyi fad'i ki sani tubalinsu ba shi da kwari,

wata rana dole zai rufta kuma tare da ma'abota shiryasu,

 baki Khulud ta tab'e ta juya da niyyar fita,

sai kuma ta juyo ta dawo har zuwa gaf da Sanah tace " oopss karki manta da auren mu akanki fa,

karkije kina zance da neman maza da auren mu dan nasan Hanash bai tab'a yi miki k'arya,

danna lura ke ba k'aramar jarababbiya bace, baki gajiya da sex,

a fusace Sanah tace " idan ni mazinaciya kinfi kowa sanin hakan,

tunda a gabanki na kaiwa lusarin namijinki budurci na,

kin san me yake cewa duk lokacin daya kasance tare dani......!? 


"Hummmm cewa yake yi yana 3yrs da aure amma bai san dad'in sex,

da mace ba sai a kai na, 

a matuk'ar harzuk'e Khulud tayi yo kan Sanah da niyyar shak'eta,

ko me ta tuna sai kuma ta fasa,

ta juya d'an shiru Sanah tana kallanta,

kana tace " wait...! Khulud wai yama akayi Doctor, Driver & Papu suka mutu lokaci d'aya at the same time.....!?


Murmushi Khulud tayi idanta cikin na Sanah,

ta taka gabanta gaf da gaf ta yadda har suna iya jiyo numfashin juna,

tace " zan iyayen komai akan Hanash ya kufce min,

wallahi babu abinda bazan iya aikatawa ba,

muddin naga Hanash na neman sub'uce min,

ta fad'a had'i da cije lips d'inta da k'arfi idanuwanta duk waje sunyi jajir tamkar mahaukaciya,

ta juya zata fita Sanah tace " Khulud zafin rai mak'iyin meshi ne,

domin yakan saka ka aikata aikin nadama,

nasara tana tare da wanda ya nutsu yayi aiki cikin hankali da nutsunuwa,

murmushi Khulud tayi batare datace komai ba ta fita,

sakwaf Sanah tayi zaman dirshen a k'asa,

kwata-kwata ta rasa abinda keyi mata dad'i,

ga ta kasa yin kuka taji dad'i ko d'igon hawaye yak'i zubo mata,

gaba d'aya duniya da abinda ke cikinta suka taru suka fice mata fit a rai,

komai ta tuna kuma naga tayi zumbur ta mik'e ta fita a sukawa ne,

a parlor ta tarar da Mamu da su Ziyad zaune da sauri ta k'arasa gare su tana kuka tace " wallahi tallahi ina da aure,

babu wanda yako kalli inda take bare ya kula ta har ita kanta Mamu,

haka Sanah ta sanya su gaba tana kuka da rantsuwar tana da aure amma babu wanda ya kalle ta balle ya kula ta,

daga k'arshe Mamu tace " karki k'ara yi mana magana Sanah,

na kuma hana 'ya'ya na da gaba d'aya ahalin gidan yi miki magana har abada,

kanta ta dafe dan sai lokacin ta kula da gaba d'ayansu fishi suke yi da ita,

babu mai kula ta, sun taru sun had'e mata kai,

a hankali takai dubanta ga Khulud dake lab'e jikin k'ofa tana shan coffee cappuccino,

babu wanda ya kula da ita,

ido d'aya ta kashe mata had'i da d'age gira d'aya,

da ido tayi mata alamar you see,

fuskarta d'auke da shu'umin murmushi,

kawar da kanta tayi gefe tana jin k'ululun bak'in ciki,

da sauri Khulud ta k'arasa shigowa cikin parlor jikinta na rawa,

ta nufi Sanah tare da sanya hannu tana niyyar d'ago ta,

a fusace Mamu tace " karki soma tab'a ta,

banza marar zuciya kawai, duk abinda tayi miki amma har kike wani rawar jiki a kanta,

cikin yanayinta na yaudara tace " Mamu please, kana ta mayar da kallanta ga Sanah tace " tashi my Sanah,

" wallahi idan kika k'ara yi mata magana sai ranki yayi masifar b'aci Khulud,

kinji dai na gaya miki, da sauri Khulud ta saki had'i da nufar bedroom tana kukan makirci,

Sanah ta kalle ta tace " wallahi ko ban yi miki Allah ya isa ba,

sai Allah ya isar min dan Allah ba azzalumin sarki bane,

baya kuma yafe hak'k'in wani akan wani,

kuma........! tassssss tassssss Ziyad ya kifa mata mari,

" mu zakiyiwa iskanci da fitsara.....!?


Kuncinta ta dafe tare da mik'ewa ta kalle shi ido cikin ido،

 tace " na tabbatar akwai ranar da zata zo wacce zaku ji kunyar abinda kuka aikata,

domin gaba d'ayanku kuna bayan k'arya ne,

kun kuma san k'arya fure take bata 'ya'ya,

a zuciye Ziyad yayi kanta yana k'ok'arin jibgarta,

Zafran da Idrak sukayi saurin rik'e shi,

cikin masifa Zafran yace " baka da hankali ne.....!?


Cikin fad'a Mamu ta mik'e tace " kai baka jin abinda ta tsaya gaban mu tana cewa.....!?


" Kuma kawai sayya hau dukanta,

Mamu na shirin yin magana Aarib da Halan suka shigo,

su Abbu na shigowa suma,

da sauri Halan da Aarib suka nufi Sanah,

Aarib yace " lafiya meke faruwa kuma.....!?


Cikin b'acin rai Zafran yayi musu bayani,

Halan tace " dan Allah yanzu meye haka....!?


Akan yarinya k'arama kun tsaya kuna yin abu haka,

" ba ruwanki karki kuma yin magana ai dama bakin ku d'aya,

Ziyad ya fad'a yana huci,

Halan tace " wallahi komai zai faru sai dai ya faru amma banyin shiru ana neman takewa yarinya hak'k'in ta,

" ok bari na dake ta naga abinda zakiyi,

da sauri Zafran yace " wallahi ka dage ta saina rama mata,

Aarib yace " nima haka kana tab'a ta nima zan tab'a ka,

gadan-gadan Ziyad ya nufi Sanah,

Halan tayi saurin sanya ta bayanta ta tare gabanta,

Aarib da Zafran suka hau tattare hannun riga,

ganin hakan yasa Dide da Abbu dake tsaye suna kallan ikon Allah,

abinda bai tab'a faruwa cikin zuri'arsu ba,

dan ko musu ba'a yi cikin su, gyaran murya sukayi lokaci d'aya dayasa gaba d'ayansu nutsuwa,

Abbu na shirin yin magana Dide yace " no argument please,

cike da tsantsar bak'in ciki Abbu yayi shiru,

yana tunanin yanzu duk wannan tashin hankalin Sanah ce ta haifar dashi,

yau a cikin zuri'arsu ne har ake k'ok'arin yin dambe,

Dide ya kuma yin gyaran murya yace " an riga da an D'AURA AUREN SANAH,

kuma ku dukkanku kun san haka,

tunda a gabanku akayi, Mamu tace " da waye......!?


"Idan taje ta ga kowaye,

Mamu ta kuma cewa " yaushe aka d'aura.....!?


"Yanzu bayan mun idar da sallar Magrib a masjid agaban jama'a da gaba d'aya Hard'o family's,

hannu ta d'ora aka had'i da kurma gigitaccen ihuuuuu،

" wallahi ina da aure, dan Allah karku yi min aure akan aure,

wuta zani, kin cuce ni Khulud na yarda dake,

na so ki nayi miki alkhairi amma kika butulce min،

cikin sanyin murya Dide yace " idan kina da hujja da shaida ki fito da ita,

da gudu ta mik'e tayi bedroom،

ta shiga har gitsa kayanta tana neman passport da fuskar da akayi musu da voice maker,

amma sama k'osa ta rasa su,

" hummmm wanda ya riga ka bacci dole zai riga ka tashi 'yan mata,

ta jiyo muryar Khulud daga bayanta,

kana ta cigaba " ai saboda irin wannan bak'ar ranar na kwashe duk wasu evidence,

da zaki yi amfani dasu, na d'auke fuska, voice maker, da passport d'inki,

da gaba d'aya kayan sawar da muka siyo,

jikin Sanah na kerrrrma ta nufi parlor,

Khulud tace " me zakiyi.....!?


"Zan nuna musu mark d'in CS da akayi min,

murmushi Khulud ta k'ara yi kana tace ki fara dubawa ki gani,

sororo Sanah tayi a tsaye gabanta na dukan uku-uku, 

daga b'angare d'aya kuma ta fara tsoran Khulud,

gira d'aya Khulud ta d'age mata had'i da yi mata alamar duba mana,

da idonta, jikinta na tsuma ta d'age rigarta sama tare da dubawa,

wayam taga wajen babu komai,

da kid'ime ta shiga shafa wajen da duka hannayenta biyu,

" ki daina shan wahalar dubawa dan babu,

bakin Sanah na rawa tace " that's impossible but how...!?


Murmushi k'unshe a fuskarta tace " is not impossible is possible,

"how....!?


Sanah tace bakinta na rawa while idanta kan Khulud,

" kin mata takardar dana kawo miki hospital kika saka hannu......!?


D'an shiru Sanah tayi na wani lokaci kafin ta tuno tabbas,

Khulud ta kawo mata takarda ta sanya hannu akan za'a gyara mata CS d'inta bayan mutuwar Papu,

ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Khulud,

" masha Allah da kika tuna dama dad'i na dake akwai babban kai,

sai dai kina da zafin soyayya da saurin yarda da mutane,

to wannan takardar tana kawo miki kika saka hannu,

ta laser ce da za'ayi a goge miki tabon,

an kuma yi an goge dan gashi nan ma kin gani da idonki,

" har abada bazan tab'a bud'ar baki nayi miki Allah ya isa ba,

haka bazan tab'a bari ki wulak'anta ba, dan har yau har gobe alk'awarin dake tsakani na dake yana nan daga b'angare na,

ta kaiwa nan ta juya ta fice tabar Khulud,

Dide na ganinta yayi saurin mik'ewa had'i da cewa " kin samo....!?


Cikin sanyin jiki ta kalle shi had'i girgiza mishi kanta alamar a'a,

da k'arfi ya runtse idonshi kana ya koma ya zauna,

ya kalle ta cikin sanyin jiki yace " tashi kibi mijinki,

gaba d'aya zuciyar Sanah ta gama k'ek'ashewa ta bushe rak'a yau,

haka ma idonta ya bushe kwata-kwata babu alamar hawaye،

sai jikinta da yayi mugun yin sanyi,

tace waye.....!?


batare daya kalleta ba ya mayar da kallanshi ga Aarib yace " ku tafi,,

a hankali Aarib ya kalli Sanah yace " tashi muje, ba musu ta mik'e had'i da cewa " bari na kwaso kaya na,

ta fad'a tana barin wajen, shima barin wajen yayi yabi bayanta danya taimaka mata shirya kayan nata,

bata bar koda kwayar zarya cikin kayan ta ba, ta kwashe kaf,

ta loda a kwatuna Aarib ya fita dasu ya luda cikin mota,

ganin sun gama kwashe kayan suna niyyar fita,

yasa Halan saurin mik'ewa tabi bayansu,

Ziyad nayi mata magana bata ko juya ba,

" ku jira ni ina zuwa, ta fad'a had'i da wucewa part d'inta ta zura hijab,

kana ta dawo ta shiga motar suka tafi,

tunda suka bar harabar gidan ta kifa kanta, ba kuka take ba, 

haka bata san takamaiman abinda take yi ba,

bata d'ago kanta ba, har motar tayi parking,

a hankali ya bud'e ya fito ya d'an jima da fita kana ya dawo yace " Bismillah ku shigo,

" kiyi addu'a Halan tace mata,

batare data bata amsa ba, ta fita,

gani tayi kamar tasan gidan amma tashin hankalinta ya hana ta gane gidan,

a hankali suka taka zuwa main k'ofar gidan Aarib na gaba suna biye dashi a baya,

hannunta cikin na Halan,

" ki tsaya anan kiyi addu'a, sai da aka d'an d'auki lokaci kafin Sanah tace " na gama,

da sallama suka shiga cikin parlor'n gidan,

a zaune suka iske Aarib a saman d'aya daga cikin American sofa chairs d'in dake parlor'n,

a hankali Halan ta zaunar da ita itama ta zauna kusa da ita,

sihirtaccen k'amshin dataji ne yasata lumshe ido,

dan ya tuna mata da HUBBINTA, 

Aryan Moli, saboda irin k'amshen shi ne sak, 

" sannunku da zuwa ina yini.....!?


Taji shu'umammiyar muryarshi wacce ko a gigin mutuwa take bazata tab'a manta ta ba,

taji ta daki dodon kunnenta, take duk ilahirin jikinta ya d'auki rawa, tsuma da kerrrrma,

" kayi hak'uri anyi abun ne cikin gaggawa da k'ank'anin lokaci,

shiyasa duk bamu shirya ba, an kawo ta babu shiri,

Aarib ya fad'a,

k'ayataccen murmushinshi yayi mai matuk'ar tsada tare da cewa " bakomai hakan ma mun gode sosai,

da yanzu zanje d'aukarta saboda Abbu yace na tabbatar naje yau na d'auke ta,

sai kuma ga kiranka ya shigo kace kun taho,

ta kuma jin muryarshi mai eco ta daki dodon kunnenta, a karo na biyu,

"eh....! Dide ne ya matsa ai,

murmushi yayi gami da cewa " finally......!, Alhamdulillah the game is over,

na mallaki K'ALBI......!

a kid'ime ta zabura had'i da yaye rufin fuskar da Halan tayi mata,

danta tabbatarwa kanta abinda kunnowanta ke jiye mata,

ganinshi tayi a tsaye har lokacin bai zauna ba,

cike da zallar farin ciki da tsantsar annushuwa bakinshi kwata-kwata yak'i rufuwa,

cikin shiga ta alfarma yasha gayu wanda bata tab'a ganinshi da irin ba,

fuskarshi d'auke da yalwataccen k'ayataccen murmushi................!






MOMYN ZARAH  'YARBAIWA

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.