Free chapter · Read without an account

Page 9&10

by Jamila Abubakar Bello · NIDA UWAR MIJINA

*⚜️NIDA UWAR MIJINA⚜️*


_By_


*'Yar mutan kankia ❣️*



*MANAZARTA WRITERS ASSOC*



***



_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via ***_



🆓🅿️0️⃣9️⃣▶️1️⃣0️⃣




Tunda Kamal ya tafi office yake cikin farinciki,yasan shi yau baida wata damuwa,duk da idan ya tuna Momy bata san da maganar auren nan nashi ba sai yaji jikinshi yayi sanyi sai yaga kamar bai kyauta mata ba a matsayinta na mahaifiyarshi mai kaunar duk wani cigabanshi,Amman ba yanda zaiyi dan idan baiyi aure ba da matsala kuma shi maganar gaskiya hakurinshi ya kai geji.

Alhaji Bala yana gama duk abunda yake ya hau motarshi sai garin Abuja,yanda Usman ya turo mashi addresses haka yabi har yaje gidan su Maryam,bayan yayi parking a cikin compound din gidan su,yasa gate man yayi mashi sallama da Babanta,daman sun san da zuwan nashi an shirya mashi tarba ta musamman,bayan angama kawo mashi Kayan lashe baki da makulashe,abunka da anzo gidan da naira ke kuka,ruwa kawai da lemu yasha sannan yace shiko Alhamdullilah ba zai ci abinci ba,ba yanda ba'ayi dashi ba,amman yace hakan ma ya godiya kuma ya yaba da tarbiyar gidan,hakan yayi mashi dadi sosai.

Bayan sun gama gaisuwa da mutanen gidan yake gaya masu abunda ya kawoshi,duk da sun san abunda ya kawo su Amman ya sake maimaitawa saboda nema ma Usman mutunci a cikin idon surukanshi.

Suma sunji dadi sosai,kuma sun na'am da tarbiyar da Usman ya samu a wajen iyayenshi,ko da Alhaji Bala ya gaya masu mahaifin yaron ya rasu,shine yanzun ya rage masu basu da kowa sai shi da mahaifiyarsu,bayan sun gama suka tsada ranar aure nan da wata biyu,sannan ya taso ya taho kuma yaji dadin tarbar mutuncin da surukan Usman suka yi mashi.




Tunda ta gaya ma Anani iyayen Kamal sunce zasuzo yau,ta shirya ta wucewarta wajen aiki,bayan ta gama abunda take ta wuce gidan su Sa'adatu close friend dinta ce sosai,kuma unguwarsu da'ya bayan ta yi parking din motarta ta shiga cikin da gida da Umminsu ta fara gaisawa sannan ta wuce room din Sa'adatu,kwance ta tadda tana hutawa dan itama dawowarta kenan daga wajen aiki take hutawa.

Sallama tayi sannan ta kadamata bugu tana cewa."halan tun dazun kike kwance ko."!?

Cewa tayi."wash Allah,Besty wallahi na tsorata sosai,ga kuma wannan uban bugun da nasha duk ni da'ya."....ta fada tana sosa wajen da Zainaba ta bugeta tana shagwaba fuska.

Tsayawa Zainaba tayi kallona dan ba abun mamaki bane dan Sa'adatu tayi haka cewa tayi."gaskiyane Auta lokacin kine,dole kiyi abunda kike so gida daga ke sai Ummi baki aikin komai daga zuwa office sai kwanciya kiji dadinki."

Murmushi itama sannan tace."ai kema kina jin dadi ta biyun Autar Anani ,harma kin fini,yanzun na dawo wallahi duk na gaji kinsan aikinmu na kananun yara dole ake gajiya ba irin naku ba na manya,zama kawai kuke kuna yin sing kinga ai da banbanci ko."!?

"Ba wani banbanci Besty kedai Allah yasa mudace,Amman wannan zamanin ba abunda zamu iya cewa sai Allah yatsare mu kawai."

"Amin ya Allah,ya Anani dasu ango Autan Anni."!?

Hhhhhhhhh!"wai Besty kinji labarin Auta shima aure zaiyi kenan."!?

"Naji mana Besty,da yake kinsan Muhisin ba kunya ne dashi ba sosai,jiya ba na kiraki waya ba nace kizo ki rakani saloon ba kikace man baki samun damar fita kanki na ciwo."!?

"Eh hakane anyi haka,wani abu ya faru kenan."!?

"Aa ba abunda ya faru sai abun dariya,bayan na fito da motata ina shirin yin reverse kenan sai ga Muhisin shima ya kunno hancin motarshi muka tsaya zamu gaisa nan yake ceman tunda muki yin aure shi ya shirya dan ankusa yin bikin shi ya zama Dady shima Kamar yanda su Yaya Anna's suka zama."

"Ikon Allah,wallahi ko Besty ban taba ganin marar kunya ba Kamar Auta,nima yau da safe yace man karna sake cemai Auta,Idan ban iya kiranshi da Muhusin to ya hutar dani kiran sunanshi na dunga cewa wane,dan ba yanda za'ayi yana shirin zama Dady ina kiranshi da suna Auta."

Uhmmmuhmmmuhmmm!"ai naga sai rawar kai yake,Allah dai ya tabbatar da Alkhari."

"Amin,Besty nima fa yau za'azo a tsada rana,daman Dady yace rana daya zaiyi mana aure nida Auta."

"Woow,Besty naji dadin wannan labarin ko,ina fatan dai da Kamal za'ayi."!?

"Wallahi ko Besty dashi za'ayi,yanzun mai kike ganin za'ayi a bikin."!?

"Kawai ayi kamu da wa'azi Kamar zaifi dan kinsan idan aka cika yin program a biki a wannan zamanin da muke cikin akwai problem kinga kawai gwara ayi kamu,shima kamu karda su Adije suce ba'ayi ba kinsan su da son harka sosai."

"To shikenan hakan ma yayi Besty,bari na shiga wanka sannan na tafi gida nasan har iyayen sun zo yanzun ko ya kika gani."!?

"To shiga,bari na dauko mana abinci sai muci kafin su tafin."

"Ok."





Shiryawa Alhaji Bala yayi ya kama hanyar gidan su Zainaba daman ya gaya ma Dadyn Zainaba yau zai shigo ,duk anshirya mashi tarba da mutunci,dan Dady yaji dadi sosai da yaji Kamal ďan kanin Alhaji Bala hakan yayi mai dadi sosai,bayan sun gama shirya komai suka jira isowar shi.

Tunda ya shigo yake murmushi dan sun dan Jima basu hadu ba ,huging din juna suka yi sannan Dady yace."Sannu da zuwa abokina ya hanya."!?

Cikin murmushi da jindadi Alhaji Bala yace."lafiya lau Abokina ,Fatan na samaiku cikin koshin lafiya."

"Alhamdullilah wallahi,muna lafiya kaima ya kabaro gida."!?

"Lafiya lau Alhamdullilah."

Nan suka shiga part din baki inda aka fara tule mashi abinci kala kala ,tun yana mamaki har yazo da ya daina,dan abun ma har mamaki yake bashi kallar wannan tarba haka sai kace wani bako?

Bayan duk angama Jere mashi abinci ,akazo aka zuba mashi nan ya zauna yaci,ji yayi da kunya yace ya koshi,duk abun abinci nan dan shi daya akayi shi ai babu batun cewa ya koshi,haka yaci ba laifi yasa ruwa da lemo,sannan su Annas suka zo suka gaidashi,bayan sun gama gaisheshi Dady ya shigo suka fara maganar abunda ya kawo su,sunyi magana ta fahimta sannan aka tsada ranar auren Kamal da Zainaba nan da wata Kamar yanda aka tsada na Usman kuma rana daya za'ayi da na Muhisin shima.

Sun kara gaisawa sannan yace shiko ya wuce gida sai kuma sun sake haduwa,daga gidan su Zainaba Alhaji Bala gidan su Kamal ya wuce.



Bayan ya dawo daga wurin aiki gida ya wuto,sai da ya fara yin wanka sannan ya wuce apartment din Momy zaune ya tadda ta tana kallo hankalinta kwance,duk da taso ta dan shiga cikin damuwa da Usman yace mata zaiyi aure,su Husna suka bata hakuri gami da kwantar mata da hankali,shiyasa ta sauko dan ko da ko abinci kasa ci tayi sai da suka hada da lailashi gami da ban baki sannan suka shawo kanta.


(😂😂😂Niko nace baki shiga tashin hankali ba Momy tunda baki san aika aikar da Kamal yake kullawa ba,amman fa Fans ina tausayin Zainaba sosai fa😭).


Zaunawa yayi kusa da ita yace."Momyna sannu da hutu.".....kallon shi tayi gami da yin murmushi tana shafar kanshi tace."yauwa yaron albarka ya aikin."!?

"Aiki Alhamdullilah Momy,Yaya Usman bai dawo ba kenan."!?

Hmmmm!!!"taya zai dawo bayan yana wajen Wanda na haifamawa?tun yanzun ya fara fifitata akanmu ina da yayi auren."!?

"Momy please wallahi babu dadi idan kina irin kallar wannan maganar,nasan wani abune mai mahimmaci ya hana Yaya Usman dawowa da wuri fa Momy."

Hmmmm!"kamal kenan bakajin abunda nike ji shiyasa zakace haka,kuma kai yarone shiyasa bakasan komai ba,mu zuba ido ai muna jiran dawowarshi tunda wani abu ya tsadashi."

"Yauwa sweet Momy haka nike son naji kince ai."

Kallonshi tayi sannan tace."ai kaji nace Kamal ,maza tashi kaje kaci abinci karka tsaya jiran gawon Shanu."

"Ok Momy."

Nan Kamal ya tashi yaje ya zuba abinci yana ci yana kallon Momy dan yana tunanin yanda zasu kwashe da Momy idan taji ansa mashi biki yau,dan Zainaba tayi mashi text tace Baba Bala yazo harma ya tafi.

*Niko nace Kamal baka san gidan ku yayi ma tsinke ba😜.*

Yana cikin cin abinci Usman ya shigo da alamu daga part dinsu yake dan har kaya ya chanza gaida Momy yayi sannan ya wuce dining shima ya zuba abinci ya fara ci suna cikin cin abinci suka ji sallamar Baba Bala...




*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*

*MTN* . *Airtel*

1GB = ₦300. 1GB = ₦300

2GB = ₦600. 2GB = ₦600

3GB = ₦900. 3GB = ₦900

4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200

5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500


*GLO* . *9MOBILE*

1GB = ₦350. 500Mb ₦500

2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100

3GB = ₦1050. 2GB ₦1600

4GB = ₦1400. 3GB ₦2000

5GB = ₦1750. 4GB ₦2500


*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*

For cable subscription or sell recharge card

Call this numbe r or whatsapp

👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

*🪀****



*Muje zuwa..🖤*



*Yar'Mutan kankia ce❣️*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.