Free chapter · Read without an account

Page 15

by Jamila Abubakar Bello · NIDA UWAR MIJINA

*⚜️NIDA UWAR MIJINA⚜️*


      _By_


*'Yar mutan kankia ❣️*


_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via ***_ 




*🆓🅿️1️⃣5️⃣*





Tunda aka fito da Zainaba take aikin kuka, dan kuka take sosai kamar ranta zai fita. 

A cikin motar Yaya Annas aka dauketa, dan shi yace da kanshi zai kai kanwar tashi har gidan mijinta. 

Tun Sa'adatu na lailashinta har takai da ta sa mata ido, haka dai har suka iso gidan Kamal, duk da unguwarsu ɗaya amman ba round ɗinsu ɗaya ba. 

Annas da kanshi ya kama hannunta ya fito da ita daga cikin mota, sannan yayi part din da yake mallakin Zainaba a cikin gidan, sai da ya kanta har bedroom dinta, sannan ya zauna yayi mata wa'azi mai shiga jiki sosai, yayi mata fatan alkairi, ya tafi, bayan tafiyarshi duk suka zo, da marece yayi Hajiya Aisha tasa Zainaba tayi wanka, aka sake shirya mata, sannan suka tafi da ita part din Momy dan bata amanar Zainaba. 

Tafiya suka danyi ba wata mai nisa bace, sannan suka iso apartment din Momy, tunda suka shigo suka fara haduwa da Hajiya Jalila, wani irin malalacin kallo tayi masu, sannan tace.


"to dangin asiri, har anshigo kenan? Anzo asirce mana Yaya ko."!? 


Tunda tace dangin asiri, jikin su Hajiya Aisha yayi sanyi sosai, dan tun daga nan suka gane Zainaba zata samu matsala da dangin mijinta, haka dai suka ɗaure basu ce mata komai ba, suka tsaya suna kallon ta, Hajiya Ummaa ce ta fito ta gansu, tazo da sauri tana masu lale da zuwa, hannu biyu ta anshe su, sannan tayi masu jagoranci har room din da Momy take zaune da ƙawayenta, fuskar kunshe da farinciki, duk da tasan Momyn Kamal bata san auren, amman ba yanda za'ayi dole dai Kamal yayi aure, tunda yana bukatar haka, (Hajiya Umma, itace matar Alhaji Bala). 

Tunda ta shigo da su Momy bata sake dariya ba, ji take kamar ta tashi ta kama Zainaba tai ta bugu, daurewa tayi nan suka shigo da Zainaba aka samu waje aka zaunar da ita, kallon arziki Zainaba bata samu ba wajen Momy, sai ma ƙawayenta da suka tarbesu, duka wanda suka rako Zainaba wajen sirukarta sai jikinsu yayi sosai, sai murnarsu ta koma ciki, sun san Zainaba zata fuskanci matsala tunda Uwarmiji bata sonta. 

Haka dai suka bada Amanar Amarya sannan suka fito, dan ko dan tukauci basu samu ba, daga wajen mahaifiyar Kamal, duk abunda ya faru Zainaba taji kuma ta gani, dan ko lokacin da aka ce ta bude fuskar ta Mamar Kamal ta gani koda ta bude taga irin kallon tsanar da take jafarta da shi, dan take tsoro ya kamata, haka suka maidota, Hajiya Aisha tace su bar mata room din zatayi magana da Zainaba. 

Bayan sun fita ta fara yi magana kamar haka.



"Zainaba ban san kisa damuwa cikin ranki, har ya hadda sa maki wani abu."

Cigaba da cewa tayi."Zainaba akwai aiki babba a gareki, kina da aiki, dan alamu sun nuna mahaifiyar Kamal bata sonki, bata so kika aure ɗanta ba, to taya zaki zauna da ita? Shine abun dubawa Zainaba, kuma ni yanzun zan gaya maki yanda zaki zauna da uwarmijinki Zainaba."

numfashi ta sauke ta cigaba da cewa."kina jina dai ko Zainaba."!? 

Ƙarma kawai take, dan a tsorace take sosai, kallon Hajiya Aisha tayi idonta tab da hawaye sannan ta ɗaga mata kai, dan ko bata iya magana, fahimtar da Hajiya Aisha tayi Zainaba bata iya magana, take tausayin Zainaba ya mamaye zuciyarta, cewa tayi."Allah yayi maki albarka Zainaba, yasa albarka a cikin auren nan naki."

Cigaba da cewa tayi."Zainaba karki kuskura kice zaki kawo ma Kamal ƙarar mahaifiyarsa akan tayi maki wani abu, dan idan kika ce zakiyi haka, duk yanda yake sonki watarana sai ya bi bayan mahaifiyarshi, dan Uwa daban take Zainaba."

"Sannan kuma kiyi hakurin zama da ita, karki kuskura ki gaya ma Anninki irin zaman da kike da ita, sai kinga abun ya wuce misali sannan, ba itama zaki gaya ma ni kizo ki gayaman, idan kika gaya mata, to hankalinta ba zai sake kwanciya ba Zainaba."

Numfasawa tayi sannnan tace."wallahi Zainaba duk mai hakuri yana tare da riba, dan haka sai kinyi hakuri, sannan kina mata biyaiya tabbas koda ita fir'unnace dole ta sauko ku zauna lafiya."

"Daga karshe kuma Zainaba, komai kika dafa ki kai mata, ki ringa yi ma ƙannenshi kyauta, kina janyo su a jiki, ki nuna baki so kayanki, duk dan asamu dai a zauna lafiya, daga nan zance Allah yayi maki albarka Zainaba, dole sai ansa hakuri dai a zaman aure."

Murmushi tayi sannan tace."nagode Mama, kuma insha Allah zanyi duk abunda kika gaya man, a gaidaman dasu Anani ."

Cikin jindadi Hajiya Aisha tace."in sha Allah, zasu ji, mu mun tafi, kuma bance kiyi mana kuka ba."

Murmushin karfin hali kawai tayi, ta dukar da kanta kasa, tana hawayenta, tana ji suka tafi sukma barta ita ɗaya, da yake upstairs suka shiga da ita, tana kallonsu ta window suka tafi aiko nan ta fara aikin kuka dan gani take ta tazo karshe. 

Shiko Kamal yana cikin gida aka kawo mashi Masoyiyar tashi, ba abunda yake sai farinciki, duk da friends din shi suna tsokanar shi, Amman haka bai sa ya biye masu ba, dan shi gani yake yau yafi kowa farinciki, da Allah ya bashi masoyiyar shi ta zama matarshi ta suna. 

Sai da suka dawo sallahr isha'i sannan Sadiq ya bashi kaza da komai dai da ake bukata sannan suka tafi, dan su group din su na abokansu, basu raka ango sai dai su bashi kudi ya ba Amarya suyi mashi fatan Alkairi su tafiyarsu. 


Tunda suka tafi ya nufa apartment din shi, parlourn kasa bai tadda kowa ba, upstairs ya hau, tunda ya taho sama yake jin kukan Zainaba da sauri ya shiga ya tadda tana kuka, take ta bashi tausayi dan yasan dole tayi kuka, anrabata da Anani an kawo ta gidan miji. 

Shiga ya ida yi, ji tayi an rungumota, a tsorace ta juyo aiko suka hada ido da Kamal, kauda kanta tayi tana kokarin fita daga jikinshi, tana mai cigaba da kukanta, hanata fita yayi, yana girgiza mata kai, yana goge mata hawaye, koda yaga taki daina kukan fara lashe hawayen yayi yana girgiza mata kai, tunda ya fara lashe mata hawaye tayi shiru tana tureshi, ɗaga ta sama tayi yana juyi da ita, tun tana nuna bata so, har ta fara dariya, sauke ta yayi yace."Haba One love, sai kace ba gidan Masoyinki aka kawo ki ba, kike wanann kukan har haka."

Rufe idonta tayi da tafin hannunta tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace."to tashi muje muyi wanka sai muyi sallah."

Kallonshi tayi sai ta tashi ta haye gado, biyota yayi ya kwanta bisa cinyarta sannan yace."wankane baki yi One love."? 

Ce mashi tayi."zanyi mana, amman sai ka fara shiga ka fito sanann ni zan shiga."

Ƙara hawowa yayi kan gadon yana cewa."wallahi baki isa ba one love, ai bama ki isa ba, ina bama zata yuyuba."ya faɗa yana daukarta sama bai ajiye ta ko ina ba, sai toilet cikin bahon wanka, cire mata kayan jikinta yayi sannan ya cire nashi shima ya shiga ciki, tunda ya cire mata kaya ta rufe idonta, bata kalleshi tana ji yana jagwalgwala mata jiki, amman ba yanda zatayi da shi, sai da ya gama wankesu tas, sannan ya naɗota a shawal bai direta ko ina ba sai bisa gado, da kanshi ya dauko wata figigiyar riga ya samata, shima ya shirya ya daura mata zane ya bata hijab tasa sukayi sallah, tambayoyi yayi mata, sannan suka fara cin kaza, ita Zainaba da cewa tayi ita bataci, ce mata Yayi idan bata ci ba zai mata dure haka ta ci yana bata a biki har suka koshi, daukar komai Yayi ya maida kitchen, sannan ya dawo yayi sama da ita yana juyi da ita. 



     Tunda Momy taga Sadiq yana ba Kamal wani abu a hannu bayan sun fito daga massallaci, ta kasa tsaye ta kasa zaune, tunani take mai dan'iskan yaron nan ya ba Kamal, dan daman tuni ta gane komai Kamal yake Sadiq ke zuga shi yana daura shi hanyar banza har Yayi aure ba tare da ya nemi izinin ta ba. 

Husna ce ta shigo taga Momynta cikin wani hali, dan ta kasa zaune sai zagaye take ita daya cikin room, dafa Momyn tayi sannan tace."Momy haka zaki zuba ido, yanzun Yaya Kamal ya fita daga hannunmu ya zama na wata? Wanda ba ita ta haifa maki shi ba, ta samaishi a banza."!? 

Kallonta Momy tayi sannan tace."ina ai ba zata yuyu ba, bari ma ki gani."

Rike hannunnta Lamrat tayi tana girgiza kai sannan tace."aa Momy mun raga mata ranar yau ko, suci amarcins... Tas Momy ta wanke Lamrat da mari sannan tace."na fahimci baki damu da damuwa taba, tuni na gane farinciki kike da auren nan, sai kace ni Saude bani na ba Lamrat nona tasha ba, dan haka daga yau ki fidda hannunki kuma wallahi mudun kika ce kina bayan wannan tsinarniyar yarinyar da Kamal ya kwaso mana, to kisani Lamrat daga ranar ni Saude zan yaye ki daga cikin layin yarana, shasha kawai, wanda bata kishin uwarta."

Momy na gama fadin haka tayi haryar apartment din Kamal sai huci take, dan da taga taki isa sai ta sa gudu, Kamal ya manta bai kulle kofar ba daya shigo shiyasa Momy bata wahalar buguwa ba, tura kofar tayi ta shiga tayi upstairs dan tasan suna can, sauri sauri gudu gudu take dan so take taje taga abunda suke shukawa... 




My Guys yanzun fa aka fara wasan, wannan shine ake kira da wasa farin girki 😂🙆‍♀️




*Anan na kawo karshen free page ,idan kina son jin cigaban yanda wannan rigima da chakwakiya na cikin labarin nida uwarmijina zai kasance sae ki garzayo danyi payment yanda zakiyi payment dinki👇*




 _It's 500 Via account number 0777512438 Jamila Abubakar Bello Access bank evidence ta wannan number *** ,idan kati zaki turo please bansan VTU_



Share domin Allah

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.