Free chapter · Read without an account
...09...
by Sadiya Auwal · SANADIN CACA
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:***
________________________________
*Book 1*
Chp[09]
Runtse idona nayi,bana ma son naga mai zai kasance.
Buɗe ƙyauren ɗakin yayi ya shigo,da farko bai kulada ni ba sai daya waiwayo tukunna muka haɗa ido.
Kallon mamaki yake bina dashi,nasan bazai wuce nazari yake ba akan mai yakawoni cikin ɗakinnasa..
"Keeee"
Ya faɗa cikin shaƙyƙyƙyiyar murya,wacce take ɗauke da gajiya da kuma takaici.
Shuru nayi ban amsa ba,dan banida wannan ƙarfin halin.
"Wai ba magana nake miki ba,ko ke kurmiya ce bakya magana?"
"Uh.....uhm... Iyee na'am"
"Me ya kawoki cikin ɗakina,duk filin dayake cikin gidannan ki rasa inda zakiyi burki sai cikin ɗakina,mai kike nufi wai anan zaki zauna"
"Ahah dama inna....."
"Mtsww tashi ki fita ki bani waje,idan kuma kika sake na ƙara ganin ƙafafunki a kusada sansani na......saina karya dukkan ƙasusuwan jikinki na babbakeki na ciyar da su durwa"
Me wai ni irin wannnan kashedin haka..
Miƙewa nayi daga kan katifar ƙafafuna suna rawa,haka na jasu zuwa bakin ƙofar,ina jin idanuwansa akan ƙeyata kaman zasu bula su shige,ban waiwaya ba harna fita daga cikin ɗakin.
Tafiya nake kaman ina kan glass har na isa bakin ɗakin inna Mairo. Ƙwanƙwasa mata nake a hankali harna fara da ƙarfi ganin bata buɗe ba.
Cikin muryar bacci tabude kofar tana kallona,nima kallonnata nake har sannan hankalina bai gama kwanciya ba.
"Sumaimah lafiya kuma na ganki anan,gojen bai dawo bane koh......"
"Yadawo koroni yayi,yace idan na sake zuwa kusada ɗakinsa sai ya kasheni"
"Me kisa kuma wacce iri?"
"Dan Allah inna karki sake cewa ba koma,idan kika maidani zai kasheni nikam....."
"Kinga kwantar da hankalinki,shigo nan mu kwanta,idan gari ya waye saina ɗauko miki kayanki a ƙofarsa,sanda komai ya daidai ta in yaso saiki koma"
Jinta kawai nake lokacin dana afka cikin ɗakinnata,dan dama abinda nakeso kenan nakuwa samu,zama da ita daram ba ruwana da wani ɗakin goje,haka kawai ana miji miji ya kasheka a banza..
Gado biyu ne a ɗakinnata,mai rumfa da kuma ƙarami na ƙarfe,shima akwai katifa akai saidai ƙarama,tsayawa nayi inna kallon ɗakin na jiyo muryar innan.
"Ga nan gado saiki kwanta,da su Atika ne suka kwana a kai,to yanzu sun koma wajen uwarsu tunda suka dawo. Sai ki dunga kwanciya anan kafin komai ya daidai..
Ɗaga mata kai kawai nayi banyi magana ba,ina jin haƙarƙarina akan katifa na saki ajiyar zuciyah,koba komai iya yau kam ai na tsira.
[Goje a Mahangar Gani]
Dawowa ta kenan garin cikin darennan,kwana guda da yini bana nan ina can sansanin ƙungiya BC sun gayyaceni na zama ɗaya daga cikin ƙungiyarsu. Tun wancan satin suka turomin takardar gayyata,sannan basu yarda naje da kowa ba idan zanje wajensu,saboda tsaro.
Fitinanniyar ƙungiya ce data addabi manyan ƙasa dama cibiyar binccike,saboda ƙungiyar tayi ƙaurin suna wajen fashin manyan bankuna da kuma gidajen ƙusosin ƙasa..
Kowa yasan labarinta da kuma irin aika aikarta,saidai babu wsnda yasan sunzo sun buya a wannan ƙungurumin daji.
Abune mai wahala su ɗauki wani yazama ɗaya daga cikinsu,saidai idan sun bincika sunga ehh ya cancanta.
Kamanni da labarin salona ya isa garesu,banida wani sha'awar shiga ƙungiyar,amma kuma ban sani Meyasa wani abu na cikin kaina yake kwaɗaita min shiga ɗin,koba komai baifi ƙara kwarewa ba,kuma dama irin wannan farmaki mai aji nakeson naga inayi..
A bakin jejin su na tsaya jiya,daidai inda suka kwatantamin,saida nayi kaman sa'a guda a wajen kafin naga wasu majaze da baƙaƙen kaya sun nufo inda nake..
Wani baƙin ƙyalle suka yafamin a kaina,kana suka riƙe hannu na muna tafiya.
Cikin duhuwa muke shiga har muka zo daidai wani bakin wani kogon ɗutsi mai masifar girma.
Wasu dakaru ne a wajen a tsaye da manyan manyan bindigogi a hannunsu..
Shigewa mukayi cikin kogon mai lunguna da saƙo kala kala.
Wani sansani muka zo mai matsakaicin fili da mutanen da zasu kai shida a wajen,dukkansu baƙaƙen kaya ne a jikinsu,saidai akwai guda ɗaya wanda shi nasa kayan ja ne.
"Barka da zuwa wannan ƙungiya Goje,mun samu labaranka da yanda ka kawar da yaronmu na garinku,da farko munso yin maganinka,sai kuma mukaga hakan dakayi ma daidai ne,dan kafishi jarumta da kuma kwarjini.
Munyi farinciki daka karbi gayyatar mu kakuma yarda cewar zaka........"
"Dakata a takardar ba'a nuna karbi aikinku ba,kawai takardar amsa gayyata ce,ko banyi daidai ba"
Nafaɗa ina kallon cikin idonsa,dan haka kawai naji banji tsoronsa ba,duk kuwa da yanda suffarsa ta zama abar tsoron..
Tsuke fuska yayi,lokaci ɗaya kuma yasake ta tareda yin shu'umin murmushi.
"Ehh kuma hakane ka faɗi gaskiya,rashin tsoronka ya burgeni. Kaman yanda kake gani nan shine sansanin BC,kuma basai nayi bayani ba kasan menene aikinmu tuntuni. Nine mai faɗa a ji na huɗu,akwai sauran mutane uku a sama na. Shugaba da kuma mataimakansa. Babu wanda yasan wanene shugaban wannan ƙungiyar,shugaba na biyu kuma ni kaɗaine na sanshi sai Shugaba na uku zamu haɗaka dashi idan ka amince da zama ɗayan Mutane biyu da suke kulada reshe biyu na wannan ƙungiyar,Idan ka amince da wannan aiki nan gaba zamu iya baka damar riƙe sansaninka na garinku. Wanda kana da wannan damar idan ka nuna mana waye kai,saika haɗu da shugaba na uku. Abinda kuma shine muhimmi bamu yadda wani yasan da wannan maganar ba"
"Harshe zaku yankemin in wani yasani? Da kunsan inada wannan inaga bazamu zo nan daku ba. Ni zan tafi in kun gama faɗin abinda kuke ganin yakamata na sani"
"Uhm ba matsala zaka iyah tafiyah,kanada damar yin tunani har nan da kwana uku,zuwa sannan zakaga ɗan aikenmu izuwa gareka"
Daga haka nayi sallama dasu muka fito daga wajen nida wanda suka rakoni.
Ajiyeni kenan da sukayi yanzu a ƙofar gida suka tafi. Garin yayi tsitt bakajin komai sai ihun mutanennamu wato karnuka,da alama dare yayi kenan.
Cikin gidan ma shuru yayi kaman babu kowa a ciki,duk wannan hayaniya ta gaji da ƴaƴan ta yanzu shuru kaman basa nan.
Ƙofata na nufah kaina tsaye,mamaki abin ya bani dana ga ƙofar ɗakina a buɗe,ban kawo komai ba dan nayi tunanin ko inna ce tayi min shara,saboda dama takanyi min idan na ɗau lokaci. Aikuwa indai hakane nasan saita zubarmin wasu abubuwan,na tsani a tabamin shirgina..
Toh ikon Allah,dana shiga warin wannan tsinken da take sakamin naji( turaren tsinke).
Takalmin kafata na cire na wurgashi wajen danake ajiyesu,gobe sai nayi gyara kenan,don duk ta ɗebi shirigina ta rufesu a gefe..
Waiwayo wa nayi wajen shimfiɗi na zan kwanta,da mutum nayi arba a zaune akan katifar,nidai nasan babu wanda muke irin wannan wasan dashi,da har zaizo kan katifata ya zauna,ba kuma barawo bane,inda shine bazai zauna shuru kaman ya mutu ba.
Lura danayi kaman macece tunda harda lullubi akan ta yasa na tunada wancan auren. Kutt amma wannan cin fuskar yayi wa,nace su kawota ta dunga aiki basai an ɗaura mata aure ba,masu kwainanen gari sunce ba haka ba,yanzun kuma na yarda da hakan bai ishesu ba sai an kawo ta cikin ɗakina.
Cikeda hassala nayi mata magana,danaji taƙi amzawa nayi zaton rai ni ne,sai kuma naga jikinta yafara rawa,wato tsorone yasakata kasa magana,hmmm mata dai,shiyasa fah a rayuwata na tsani sabgar dazata haɗani dasu,sunada wuyar sha'ani sosai..
Bayan tafita daga ɗakin ajiyar zuciya nasake,gajiyar dana ɗebo ce ta dawo cikin kaina,ga kuma nauyi da kaina yake..
Ohh no bai kamata naji wannan muryar ba yau.. Na faɗa cikin gajiyawa ina dafe kaina wanda nake jin jijiyoyin sa suna rirriƙewa.
Jujjyawa kan nake ina duban ɗakin,yanzu taya zan fara neman abinda zan busa a ɗakin,nasan babu makawa inna ta zubar da waɗanda na ajiye.
Faɗawa kan gadon nayi ina kallon silin ɗin dana haɗa da jarida da kuma lilo.
Dummm komai naji ya ɗaukemin,vanda juyawa babu abinda duniyar tawa takeyi,a haka na kasance har bacci ya ɗaukeni.
[Sumaimah a mahangar gani]
Hannu naji yana bubbagani,can kuma sai naji murya ƙasa ƙasa tana min magana..
Saida baccin ya dan bar idona kafin na naji ashe inna ce take tashina.
"Ƴar nan tashi kiyi sallah anyi assalatu,ko bakyayine"
Tasake maimaitawa a sanyaye.
Juyi nayi kafin na tashi zaune,ohh ban taba tunanin kwana na nafarko a gidan zanyi bacci hadda juyi ba kamar haka.
Kallonta nayi da farin hijabi a jikinta,hannunta riƙeda carbi tana kan sallaya.
Na lura da hakanne saboda hasken ɗan Club da ake haɗawa ya haska ɗakin..haka kawai naji ta burgeni,indai bawai mantawa nayi ba,tunda nake babu wanda ya taba tashina sallahr asuba a gidan mu.
Saƙƙowa nayi daga kan gadon wanda yanxu yazama nawa.
Inda buta take ajiye na nufa na ɗauka domin zuwa banɗaki.
Bayan na idar da sallah gaisheta nayi ta amsa cikin sakin fuska,har zuwa lokacin lazimi takeyi,nima danaga haka ban koma baccin ba saina fara nawa.
Muryar ta can sama sama naji tanamin magana,firgit na kalleta,kenan bacci na cigaba dayi a zaune.
"Sumaimah ki koma ki kwanta mana,ke ba kaman mu ba da baccin mu yanzu yayi ƙaranci,bare kuma kunsha hidimar biki,ki koma kiyi baccin ki kinji"
Ɗaga mata kai nayi,dan dama hakan nakeso.
Muryar inna naji tana magana da wasu yara,hakanne yasa na buɗe idona,lokacin rana ta fito tangargar.
Fitowa nayi daga ɗakin na zauna a tabarmar da take zaune..
"Kin tashi kenan,ga abin karyawa toh.."
"Ɗumamen tuwo ne sai kuma wani ɗan kwano da awara a cikin kaman guda bakwai,sai kuma kofin kokoh"
"Hmm kiyi haƙuri fah ƴar nan,amarya da aka sani da cin kaji a ranar farko kega abinda kika samu,wlh banda kuɗine,awarar ma a wajen gaji na karbo nace ta bawa baƙuwa"
Allah sarki tausayinta ne yakamani,hmm batasan a hakan kayan daɗi tabani ba akan abinda nake ci a gidan.
"Lahh inna karki damu,shimfiɗar fuska ma da kika bani tafimin komai da kike tunani,fatana Allah bamu ikon zama cikin aminci"
"Ameen ƴar nan,gaskiya ko kusa baki dace da wancan huhun ba,kawai dai ƙaddara ce da idan tazo baza'a tsallake ba. Sannan dan Allah kiyi haƙuri da son kaina,dan lokacin da naji wannan batun nayi niyyar na hanashi,amma kuma sai nayi tunanin wataƙila sanadin shiryuwarsa ne aurennaki. Yanzu dana ganki ma na ƙara tabbatar da hakan,dan inaga sai an zage garinnan kafin a samu mace irinki,kiyi haƙuri kiyi haƙuri kinji"
"Inna kidaina bani haƙuri,nima lokacin da Naji labarin kwana nayi ina Addu'a akan Allah kar ya hadani dashi,amma dana ga an ɗaura aurena dashi jiya sai nayi tunanin inaga shine mafi alkhairin dana daɗe ina roƙon Allah yabani,dan haka ki daina wannan bada haƙurin ba laifinki bane,fatana Allah yabani ikon jure duk abinda zaije yazo."
"Ameen kiyi ta haƙuri da sannu zakiga mafita"
Zancen duk ya isheni,tunda gani nazo gidan to kuma banason tuna wai dama ban xo ba,dan haka nayi ƙokarin kawar da zancen..
"Uhm inna wanne aikin za'ayi ne a gidan?"
"Ehh toh banice yanzu da tuwo ba gaji ce take saita bani,wanke wanke kuma atika ce take,idan bata nan kuma ninayi in su farida suna nan su jijjiƙa"
"Toh bari naje na gaishe ta ma,sainaji wanne aiki zan kama mata"
"Ahah kijidai ku gaisa,amma batun aiki ko zakiyi ma ai sai kinyi kaman sati ko sati biyu,dan haka kada ki damu kanki atika ai tana nan zata zo tayi wanke wanken"
To nacewa inna tareda kallon inda uban tulin wanke wanken yake,wasu manyan tukwane na abincin siyarwa da kuma su kansu kwanikan abincin siyarwar sun cika wajen famm,ƙudaje sai bin miyar data bushe suke,kaman dai na gidanmu haka yake..
Sallama nayi a bakin ƙofar,babu wanda ya amsa,sai hayani ya suke,inaga ma basuji shigowa ta ba.
Ban dai yi ƙasa a gwiwa ba na ƙarisa wajen da suke zaunen.
Gaji ce suke ta musu itada wata matashiyar budurwa,wacce ta juya bayan ta can.
"Haba gaji,idan baki yarda dani ba wazai yarda da nine,nace miki ban ɗau kuɗinki ba,yakikeso nayi ne wai?"
"Atika nafasan halinki,kwanannan na kula bakida kuɗi,koya nayi wasafai dana wa ɗebewa zakiyi,ya za'ayi ace har dubu biyu ta b'ata a cikin cinikin"
"To shikenan ai gani ki cazeni mana,kokuma ka jaka ta nan"
"Ohh shasha zaki mayarni ma,na caje........"
"Salamu alaikum"
Nasake sallama dan su san ina wajen..
A tare suka juyo inda na ɗora idona akan Budurwar..
"Atika??"
"Na faɗa cikeda mamaki"
Wani kallon juya ido tayimin tareda cewa cikin muryar duniyanci..
"To ya ranki,kinyi mamakin gani nane komai?"
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
***
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
***
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
***
Share please