Free chapter · Read without an account

BABI NA HUDU

by Rukayyaharun · Kawaye ne guda biyu masu so da kaunar juna kwatsam sai wani babban al'amari ya gibta a tsakaninsu, a bangaren guda cin Amana, yaudara, son Kai da Kuma hakuri, ku biyoni danjin yadda zata kaya

_*YAN UWAN JUNA*_

   _(zumincin mu a yau)_



               *NA*


*_RUKAYYA HARUNA(MAMAN NOUR)_*

       



*_✍️ HAZAKA WTITERS ASSOCIATION_*


Assalamu alaikum masoya barka da yammaci ya hakuri dani, to Alhamdulillah nagode da addu'o'i Allah ya saka da alheri, yanzu kam naji sauki sosai.


_*Sakon godiya*: Tabbas masoya kune farin cikina, hakika nayi farin ciki matuka, Allah ya saka da alheri ya kuma kara budi *Samira Usman Zamfara*_



*Page 4*


Idan mai karatu bai mantaba mun tsaya ne a gurin da Karima ta bawa Aziza shawarar suje gurin mai ruhanai. To anan muka tsaya yanzu ko zamu daura.



"Aziza wallahi tun farko ke kika yi sake, ace miji ya yita juyaki kamar masar da kulli ya yi ruwa. Hmmm ki tashi tsaye wallahi, karki bari wankin hula ya kaiki dare..."


Hannu Aziza ta daga mata tare da ce "Dan Allah ki kyaleni da wannan farsafar taki, ni kawai mafita nake nema."


Cigaba suka yi da tsula gudu a kan titi kamar zasu tashi sama, har suka isa kauyen Doka dake garin Zaria, babu mai cewa kowa ta tafas sauke. A bakin wani gida suka tsaya, kofar gidan cike da mata da maza, yawancin mutanen gurin manyan mutanene yan siyasa da manyan alhazawa, matan dake gurin kuwa yawanci matan manyane da yan duniya.


"Hajjajuna fito mu karasa kinga akwai layi sosai a gabanmu." Bata ko kalli inda karima take ba ta amsa da "Ok"


Bude murfin motar ta yi sannan ta zuro siraran kafofinta waje, Aziza kyakkyawace ajin farko. Duk Wanda ya ganta zai ce bata fi asirin da dauriya ba, amma shekarune da ita tsababa, tsabar kyan jiki ne kawai dan yanzu takai talatin da takwas. A yatsine ta fito ta tura murfin motar ta cigaba da tafiya, wani mugun kallo Karima ta bita da shi tare da cewa. "Hmmm yaro man zaka, wai har ni kikewa tsawa. Wallahi sai na zamar miki kadangaren bakin tulu." Kusan awansu uku sannan layi yazo kansu, tare suka shiga Karima ta wassafawa mai ruhanai komai, take ya tabbar mata tunda tazo gurin shi kukanta ya kare. Sunan mijin ta fada tare dana mahaifiyarshi, garin magani ya hadota da shi tare dayi mata bayanai akan kowanne. Sosai ta yi mishi godiya tare da cika shi da ruwan kudi. Bayan ya sallame su sun fito Karima ta zaro idanu tare da cewa 

  "Na shiga uku na manta banyi masa bayani akan jarabawar da zamu zana ba, dan Allah jirani a mota."

  Tsaki Aziza taja sannan ta yi gurin data ajiye motarta, shiga ta yi sannan ta kunna Ac tare da kure wakar Chass ta ado gwanja, ba a dauki lokaci ba sai ga Karima rike da wata leda sai fara'a take. Tana shiga suka figi mota sai garin kaduna. Horn biyu ta yi mai gadi ya fito da gudu tare da wangale mata kofa, a shkwane ta hankada hancin motarta ciki tare da yin nannauyan ajiyar zuciya. Ba kuwa komai ne ya sakata ajiyar zuciya ba, illa motar Dr Imran da ta gani a wannan lokacin. Sosai ta shiga tashin hankali, domin yaja mata kunne akan fita batare da izinin shi ba, amma ita a kullum bata jin magana abubu kullum kara tabarbare mata suke.       "Karima basai kin shigo ba kinga gobe mayi magana, yanzu zanje ciki nasan abunda zan fada mishi."


A nan suka rabu Karima ta tafi gida Aziza ta shigo zuciyarta fal tsoro, Dan ta tabbatar yau sai sun samu matsala da Dr. Turus ta yi a tsakiyar parlour dan jiyo muryar da bata yi tsammani ba. "Baba" ta fada a zuciyarta tare da cigaba da tafiya zuciyar ta kamar zata bullo waje dan zulumi, da kyar ta daga kafarta ta karasa inda zuke a zaune, yaran na ganinta suka taho da gudu suna. "Aunty oyoyo." Da ta ware hannu domin yaran su shiga jikinta sai ta tuna da hudubar da Karima ta yi mata a kwanakin baya. "Koda tsautsayi yasa ya dauko yaran sunzo karki sake musu sam, babu ke babu yi musu dariya wallahi, domin idan kika yi musu fuskar shanu dole da kansu zasu nemi komawa gurin kakarsu."


Take ta hade rai tare da komawa gefe, saura kiris karamar ta fadi baban ya yi saurin tarota, Allah ya rufa asiri ta fada akan hannunshi da ba karamin faduwa za ta yi ba.

  "Haba Aziza wani irin mugunta ne wannan, wai ke meyasa kullum ba za a zauna...."


"Ah ah Imrana ba ta yi zaton zasu fadi ba, kuma baka ga wasa sukeyi ba na tsakanin Yaya da Uwarsu bane, um um banaso."

  Maganar mahaifiyar shi yasa ya nemi guri ya zauna yana ajiye numfashi, hakika babu macen da zata wulakanta mishi yara, amma ba bu komai a juri zuwa rafi. Kan kujera aziza ta zauna sannan ta ce. "Baba ya hanya ince kunzo lafiya." Baba ta yi murmushin manya kana tace. "Lafiya kalau alhamdulillah." Daga nan ba bu wanda ya kuma cewa kala, kusan mintuna sha biyar dukkansu suna zaune, sannan Dr yace

  "Aziza dan zo mana." Yana fada ya shiga kitchen, ba bu jimawa ta biyo shi tana yamutsa fuska. "Haba Aziza ai ko wani daban na kawo gidan nan Kya bashi ruwa da abinci balle mahaifiyata." Dan murguda baki ta yi sannan ta ce

  "Kajimin bawan Allah, nikan Dr wani hali kake so ka saka ni a ciki? Toma banda abinka yau ka fadamin babarka tana hanya? To ni banyi girki ba."


 Bai jira ta karasa magana ba ya fice daga gidan gaba daya.




Wannan gida😳



***

Maman Nour taku ce

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.