Free chapter · Read without an account
Page 1
WATA ZUCIYAR
Lamarin ta sai Allah.
Ibrahim Aliyu Yakubu
A firgice ya tashi daga nannauyan baccin da ya dauke shi a
safiyar wannan rana, wanda shi a ka'idar sa da zarar ya tashi
sallar asuba to ko weekend ne baya kara komawa bacci sai
fah idan dare yayi ko kuma da rana, amma yau cikin ikon Allah
yana kammala zikirin safiya da maraicen da yake yi yaji wani
mahaukacin bacci ya hauro kansa wanda da kyar ya samu
damar tashi ya haura zuwa kan gadonsa tare da kwantawa, baccin kuma bai raga masaba kakkautawa. Wani mafarki yayi wanda yayi matuƙar ba shi mamaki da ban
al'ajabi sai dai yana yana farkawa daga wannan bacci yaji ya
manta duk abin da ya wakana a cikin mafarkin nasa abu ɗaya
da yake iya tunowa shine wata yarinya wacca baya iya tuna
fuskanta, mahaifinsa kwance bisa ga wani gado baya ko iya
motsawa, sai fah kuma maminsu. Take ya ji kansa ya harba, wani ciwon kai mai tsanani ya
sauko masa, ji ya ke yi kamar kansa zai fashe bisa dole ya rike
kansa, da tafin hannayensa. Take zuciyarsa ta harba masa wani tunani wanda hakan ya sa
cikin sauri ya fara neman wayarsa, ba komai ne wannan
tunani ba kuwa sai cewa " anya kuwa ba wani baƙon al'amari
ba ne ya faru da mahaifinsa, domin kuwa daga cikin abinda ya
ke iya tunawa da akwai mahaifinsa kwance baya iya motsa ko
da yatsan ƙafarsa, bisa ga wannan dalili ya yanke shawarar
kiran gida da gaggawa domin ya ji menene abin da ya ke
faruwa. Can ya hango wayarsa,a saman wani ƙaramin teburi inda yake
aje wayoyinsa da kuma system ɗinsa, anan yake aiki da ita
kuma mafi yawanci anan zaka samesu da wuri ya gyara
tsayuwar sa sosai tare da ziro ƙafafuwan sa bisa ƙasa, ya
girgiza kansa ko zai samu sauƙin ciwon kai, da kuma baccin
da bai ƙarass sakinsa ba. Daga kan gadon ya miƙa hannun sa kan teburin tare da ɗaukoɗaya daga cikin wayoyin nasa. Yana ɗaukar wayar, cikin ikon Allah sai ga kira ya shigo, inda
sunan My dear bro ya bayyana baro-baro akan screen ɗin
wayar, zuciyarsa ce ta fara bugawa da karfi, yayinda ciwon
kansa wanda ya dade da mantawa da shi ya dawo masa, wanda ya sanya shi rintse idan sa, ba don komai ba sai don
tunanin abinda zai iya ji daga bakin kanin nasa. Ƙasa ɗagawa yayi har zuwa lokacin da kiran ya katse kuma
wayar tana hannunsa, kira aka kara yi a karo na biyu, itama sai
da ta kusa yanke wa sannan Allah ya bashi ikon ɗagawa. Ƙara wayar yayi a kunnensa yayinda zuciyarsa ta cigaba da
bugawa kuma ya kasa cewa ko uffan yana mai jiran abinda zai
jiwo daga ɗan uwansa. Ko sallama ba'a yi ba daga can ɓangaren aka kira sunansa, inda ya amsa da " na'am me ya faru." Jan ajiyar zuciya aka yi daga can ɓangaren sannan yace " ka
zo gida, da akwai abin da yake faruwa."
" Me ya faru da Abba, faɗa mini ko na bata maka rai duk
lokacin da muka haɗu." Cikin daga murya yayi wannan
maganar kamar ace wancan mai magana yana gabansa, ne. Magana aka yi daga can ɓangaren wacca ta sanya shi rintse
ido, yayinda wasu hawaye Masu dumi suka biyo zirin idanunsa
har zuwa kan kuncinsa, wata ajiyar zuciya yai wacca idan har
kana kusa zaka jiyo ta, shiru ya ratsa tsakanin su na wani danlokaci wanda yake nuni da cewa shima na dayan kukan ya ke
yi.
A hankali ya fara takawa zuwa hanyar ficewa daga ɗakin, yayinda cikin wata , sassanyar murya ya ce " ka tabbata ba'a yi
komai ba har nazo. "
Yana zuwa nan ya katse wayar tare da ajiye ta akan daya daga
cikin cupboard da ke bakin kofar fita daga ɗakin. Cikin sauri ya fara rufe duk wani daki dake cikin gidan, da taga
inda a cikin ƙanƙanin lokaci ya gama, kai tsaye komawa yayi
zuwa ga ɗakin da ya fito. Yana shiga wasu jakunkuna guda biyu kaɗai ya ɗauka sai
kuma wayoyinsa da system ɗinsa waccan ya sanya ta a
jakarta tare da sanya ta a ɗaya daga cikin jakankunan, inda
lokaci zuwa lokaci ya kan yi ajiyar zuciya, fuskarsa kuwa da
ma ga duk wanda ya san shi m, shi ba ma'abocin sakakkiyar
fuska ba ne, da yawan magana to haka ma wannan lokaci
fuskar a turbune take tamkar bai taɓa yin dariya ba. A daidai wannan lokaci ne wasu ma'aikata biyu turawa suka
shigo cikin gida, da sauri suka ƙara so gareshi suna masu
kiran good morning Sir. Ko kallonsu bai yi ba ya cillawa dayansu kiya-kiyan gidan, sannan ya kama hanyar fita. Cikin sauri suka ƙara so gareshi suna masu karbar
jakunkunan dake hannunsa, kowannen su ya ɗauki daya, ba musu kuwa ya sakar musu, su ka yi saurin wucewa gaba yana
bin su a baya, har ya zuwa a wata mota dake fake a harabar
gidan, sanya kayan suka yi a Boot sannan suka tsaya suna
masu jiran umarninsa. Ana karasowa ya shiga bayan motar yayinda hakan ya yi ta
tabbatar musu da a wannan lokaci, dayansu ne zai tuka shi
zuwa duk inda za shi, wanda hakan bai taɓa faruwa ba tunda
suka fara aiki a karkashin sa wato tsawon zamansa a kasar ta
America cikin birnin Los Angeles. Da sauri kuwa ɗaya a cikinsu ya shiga motar, daga inda ya ke
zaune ta jigina bayansa akan kujerar motar ya jefa masa
nakulli, ya tada motar tare da ficewa daga cikin gidan. Sai a wannan lokaci ya tuna da cewa bai ma binciki jirgin da
zai tafi Nigeria ba a wannan lokaci, ko hanyar da zata isar da
shi zuwa Nigeria. Cikin Sa'a ya samu Qatar Airways wanda zai ta shi a wannan
lokaci zuwa Abuja, don haka a wannan lokaci ya yanki online
ticket kafin karasawar su airport wanda tun farkon tasowarsu
ya sanar da drivern cewa airport za shi, don haka "Ok sir" kawai ya ce sannan ya cigaba da tuƙinsa,Yana karasawa kuwa
bai yi zaman awa daya ba jirgin ya ta shi, a daidai 1:30 na
agogon Los Angeles wanda suke da banbancin awa uku da
agogon Nigeria, inda ya sanar da dan uwansa Ahmad
tasowarsa a daidai wannan lokaci domin ya shirya zuwa
daukarsa.Tafiyar awa goma sha biyar da wadansu mintoci ne ya kawo
su Nigeria, a cikin tsakiyar dare, yayinda suka sauka a Abuja
airport ɗin Nmadi Azikiwe don haka yana sauka ya fara zuba
ido domin hango ɗan uwansa. A cikin abinda bai wuce minti ɗaya ba kuwa idonsa ya hango
masa shi, tsaye jingine da motarsa,shima fuskar nan tasa
ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, mafi yawancin mutane suna
duba yan uwansu tunda jirgi ya sauka tare da rungume
junansu saboda murnar haduwa, amma shi ko motsi bai yi ba
daga tsayuwarsa, har ya zuwa lokacin da Khalil ɗin ya nufi
wurinsa kai tsaye, yana mai murnushi da halayen kanin nasa
wanda basu da maraba da halayensa, da kuma marigayiya
mahaifiyarsu wacca ta rasu tun bayan haihuwar Ahmad ɗin da
ƙananan kwanaki. Yana karasawa wurin motar, Ahmad ya bude masa mota ya
shiga shine ya dauki kayan nasa wanda suma sai da ya kawo
su wurin daa kansa bai yi yunkurin taimakonsa ba ya sanya su
a Boot. Da sauri ya shiga motar bayan sanya kayan tare da yi mata
key ya fice daga harabar airport da wani masifaffen gudu inda
sai a wannan lokaci ne ya jefowa Khalil ɗin sallama yana mai
cewa "babban yaya kazo lafiya."
" Lafiya qalau" kawai ya ce sannan yayi shiru na wani dan
lokaci kafin ya ce " menene ya faru ma'ana menene dalilin
mutuwar ta shi, yaya bayanin gawar.
Murmushi yayi sannan ya ce " wannan ni kaina ban sani ba" gawa kuma har an riga an gama shiryata, kai kaɗai ake jira
kawai gobe da safe a sallace ta akai ta makwancinta." Hawaye ya ƙara biyo zirin idanunsa har zuwa kuncinsa a karo
na biyu tun jin labarin abinda ya wakana, " su mai unguwa fah
da sauran mutanen kauyen sun iso ne."
"Eh sun iso ni ina kyautata zaton ma don su ne kawai aka
dakatar da kai gawar yau, ba don kai ba, don ni dai na yi iya
bakin ƙoƙarin dakatar da su daga ko taɓa gawar ne, amma
hakan ya ci tura, kuma matsalar ma shine mami ma tun da taji
labarin mutuwar ga hankalin ta ya tashi har ta faɗi ba ma ta
san inda take ba, yanzu ma haka tana Asibiti." Rintse idonsa yayi, tare da jan dogon numfashi, sai yanzu ya
tuna ma gaba ɗaya a tsawon ranar ba su yi waya ba " ya jikin
nata yanzu." Ya ƙara jefawa Ahmad ɗin wannan tambayar. Hadiye yawun da ya makale a nakogaransa Ahmad yayi
sannan yace " yanzu jikin da sauki sosai har ma na sanya ayi
mata allurar bacci domin ta samu wadataccen hutu, kuma
hankalin ta ya dawo jikinta."
" Fadil fah fatan ka sanar da shi". Murmushi Ahmad yayi tare da rintse ido, yana mai girgiza kai, tare da kallon Khalil ɗin ta gefen ido, saboda sanin cewa yayi
laifi, shi kuwa harararsa kawai yayi ya kauda kansa gefe, yayinda ya lula zuwa Duniyar tunani.
****
WASHEGARI. Harabar gidan ya cika makil da motocin manyan mutane, waɗanda suka haɗa da manyan yan siyasa attajirai, har ma da
baƙi daga mabanbanta kasashe waɗanda suka zo kawai don
halartar jana'izar Mahmud sadauki wanda mutuwarsa ta ratsa
lungu da saƙo na kasar, kasancewar sa shaharan attajiri, babba mai faɗa aji a ƙasar. Tun da safe Khalil da sauran yan uwa da abokan arzika da
suka kwana a gidan suka tashi, yana tashi wanka ya fara
gabatarwa, tare da sauya kayan dake jikinsa, zuwa wata
danyar shadda ruwan madara wacca ta ƙara fito da ainahin
surarsa ta ɗa namiji, yayinda tun daga nesa mutum zai iya
fara jiyon kamshin turarensa wanda ya kama lungu da sako na
ɗakin da kuma duka kayan sawarsa. Zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun dake falon dakin
ɓangarensa wanda aka ƙawata shi ainun kwarai da gaske da
ado mai kayatarwa. Duk da kasancewar ya dauki tsawon lokaci baya kasar amma
ɓangaren nasa a share yake fes tamkar ba'a taɓa daina
rayuwa a cikin sa na tsawon sati ba, hakan kuwa ba komai ba
ne sai don jajircewar Mani wajen ganin cewa an share taremopping din lungu da sako a kowacce rana ko duk bayan
kwana biyu. Hannunsa riƙe da mug din coffee yana sha a hankali yayinda
idan ka duba shi zaka ga ya ƙurawa makekiyar TVn dake
makale a jikin ɗakin ido ne amma ba haka lamarin yake ba
face yayi nisa wajen dogon tunanin da shi kansa bai san me
yake tunawa ba, har ya zuwa wannan lokaci kwakwalwar sa
bata huta da tunani ba. Sallama aka yi a kofar nasa har fiye da sau uku, amma yayi
nisa a tunaninsa hakan yasa bai ko jiyo sallamar ba, Ahmad
ne ya ke sallamar, knocking yayi duk da kuwa ya hane su da
hakan, kullum yakan cewa idan mutum ba zai yi sallama to ya
juya, don nan gidan musulmai ne ba za'a mayar da su
waɗanda ba su san abinda suke ba. Knocking uku yayi amma har a wannan lokaci bai ji an bashi
iznin shiga ba, kuma dai yana jiyo ƙarar TV wanda hakan yake
nuna tabbas Khalil ɗin ya tashi, don haka kai tsaye ya tura
Kofar falon yana mai ƙara yin sallamar a karo na biyu. Yana shiga kuwa idanunsa akan sa suka fara sauka, ya yi
matuƙar kyau a cikin shigar tasa, ga matuƙar kwarjini ga
ma'abocin kallonsa, ƙasumba tare dan karamin gemunsa da
suka sha gyara sun yi matukar ƙara fito da kyansa, sai dai
kuma yaga alamun tunani yana lalata musu baban yayan nasu, domin kuwa tun kafin faruwar wannan lamari hakan kamar
wata halayyar sa ce, a ko da yaushe abinda kawai Ahmad
yake tunanin jawo masa wannan matsalar shine rashin mahaifiyarsu, yanzu kuma ga shi sun rasa mahaifinsu
al'amarin zai ƙara tsamarin fiye da da. Batare da ya lura ba yaji hawaye ya fara kwaranya daga
idanunsa, cikin sauri ya share da farin handkerchief dake
hannunsa, sannan ya karasa yana mai dafa kafadar Khalil
wanda ya dawo hayyacin sa a daidai wannan lokaci. Cikin raha da wasa yace " babban yaya abar wannan tunanin
mana ka da da fah ya lalata mana kai, ka yi wa antin mu ta
gobe Asara." Murmushi kawai yayi batare da yayi magana ba, yayinda
hakan ya faranta ran Ahmad ɗin sosai don ko ba komai hakan
zai rage masa wani radadin a cikin ransa. Yana shirin kara kai mug ɗin coffee din cikin bakinsa Ahmad
ya fara magana bayan cin serious da yayi wacca ta dakatar da
shi daga kai mug ɗin bakin nasa yana mai cewa "ga fa mutane
har sun fara halatta kai kaɗai kawai ake jira, shi yasa ma na zo
domin na yi maka magana, ya kuma kamata ka hanzarta, gashi su kawu da mai unguwa tun dazu suke tambaya ta kana
ina, nace musu kawai kana daki ya kamata su Barka domin
samun wadataccen hutu, ko dan doguwar tafiyar da ka sha. Batare da yace uffan ya tashi tsaye daga daga kan kujerar
yana mai cigaba da shan coffee din a hankali, sannan ya fara
takawa har zuwa bakin window ɗin falon wacca zata isar da
idanun mutum har ya zuwa harabar gidan, slide din tagar yayi
waccan ita ce ta yiwa kunnen sa katanga daga jiyo hayaniyar mutane, da shigowar su gidan. Kallon mutanen yayi na wani ɗan lokaci tare da yin nazarin su
a cikin ƙanƙanin lokaci inda idanuwansa ya kai masa zuwa ga
wata yarinya wacca ta rufe fuskanta da facemask tana
shigewa cikin gidan ta wata ƙofa dake can gefe inda ba bu
wulƙawar mutane, kuma alamu sun nuna ta a fito ne daga
daya daga motocin da ke fake a gidan, ko dai wanda ta shigo
motar ya sani ko bai sani ba, amma dai tana alamu da na
marasa gaskiya. Kansa ne ya buga masa sakamakon wani abu da yake don
tunawa amma ya kasa, dafe kansa yayi sai kuma ya juya daga
kallon tagar da yake yi bayan bacewar yarinya daga idanunsa
yana mai ajiye mug ɗin coffee akan table ɗin dake falon. Nunawa Ahmad hanya yayi wanda ya tsaya yana mai binsa da
kallo duk inda ya motsa, yana mai yi masa alamar ya fita. Murmushin gefen baki Ahmad ɗin yayi kawai sannan ya sa kai
shi kuma ya bisa a baya suka tunkari hanyar sauka zuwa ƙasa. Bayan sun sauka Ahmad ya juyo yana mai ce masa bari naje
na yiwa su mai unguwa magana in ya so sai mu haɗu duka a
wajen. Girgiza masa kai kawai yayi yayinda ya wuce kai tsaye zuwa
ga hanyar fita shi kuma Ahmad ya a bi hanyar da aka saukar
da su wanda yake anan sashen kasa. Yana tafiya ne sai ya ji kamar an ja rigarsa, hakan kuwa ya faru ne a daidai wani lungu wanda zai iya fitar da mutum zuwa
can bayan gidan wajen garden idan ka mike tsayinsa. Tsayawa yayi na ɗan wani lokaci yana mai ayyanawa a
zuciyarsa waye zai iya yi masa haka don kuwa ya tabbatar
mutum ne ya taba shi, amma bai iya gano kowa ba. Da sauri ya juyo yana mai shigewa cikin lungun kai tsaye, inda
yayi arba da wannan yarinyar har yanzu sanye take da
facemask sai kuma Wani katon hijabi har kasa, yayinda daga
inda yake yana hango yadda kirjinta yake bugawa da karfi
saboda tsorata da shigowar sa. Sannan bayan haka duk da rufe fuskanta da tayi yana iya
ayyana ta a zuciyarsa tabbas ta yi kama da waccan za'a sanya
ta cikin kyawawa ajin farko, ko dan tsayinta madaidaici da
madaidaitan hanci da idanunta waɗanda facemask din bai
samu nasarar dakatar da idonsa daga isa garesu ba. Duk Wadannan nazariruka yayi su ne a cikin ƴan dakiku, kafin
ya fara takawa a hankali zuwa ga inda take, yayinda jikinta ya
fara rawa don ganin yana matsowa gareta kamar waccan aka
sanyawa shocking. Bai dakata ba har sai da ta matse da bango sosai ya zamana
tazarar dake tsakanin su ba ta da wani yawa, ta rintse
idanunta kamar mai jiran afkuwar wani lamari. Shi kuwa Khalil cikin wata ƙaramar murya waccan sai mai
tsananin ji ne zai iya jinta komai kuwa kusancin da ke tsakanin
su da shi yayi magana yana mai cewa " wacece ke?, Sanan meya kawo ki wannan gida?, Ko kinzo cutar da mu ne.?
Buɗe idonta tayi a hankali ta kalli fuskarsa tare da kawar da
kanta sannan ta fara magana cikin rawar murya tana mai
cewa " waɗannan amsoshi naka ba su ne suka kawo ni ba, amsa ɗaya zan iya baka, wato me ya kawo ki, ni ba kowa ba
ce face ƴar aike daga wani bawan Allah, sako na kuwa shine
ka binciki gawar mahaifinka kafin a kaisa makwancinsa, domin tabbatar da mutuwarsa da kuma dalilin mutuwar ta shi
idan ya mutu ɗin, sannan kuma sai ku kula da kai da duka yan
uwanka domin kuwa alamu sun nuna zaku fara fuskantar
wata jarabawa mai wahalar wucewa saifa ga mai tsoron Allah
da tsananin tawakkali, don kuwa kuna zagaye da mutane
masu WATA ZUCIYA da lamarin ta sai dai a bar wa Allah, tabbas na san kana da tambayoyi masu yawa game da
wannan saƙo nawa, amma sai dai ina mai baka haƙurin cewa
ban san komai ba game da amsohin tambayoyin ka. Tana zuwa nan a zancenta buge shi ta yi kawai ta fara tafiya
da matuƙar sauri zuwa ga tsayin wannan lungu, yayinda shi
kuma ya tsinci kansa a wani dogon tunani, bai ma san da wucewar ta ba kansa ya fara yi
masa ciwon da bai taɓa jinsa ba a tsawon rayuwarsa, shi
kansa bai san a wacca duniyar ma ya ke ba a daidai wannan
lokaci. Jingina yayi da jikin gini har na wani dogon lokaci kafin a
hankali ya ji juyawar da kansa ya keyi tayi sauki, bai san me
yake damunsa ba amma dai tabbas shima ya fahimci cewa
daga jiya rayuwa ta fara canza masa.
Tom anan zan dakata da page na ɗaya sai ku jiráye ni a feji na gaba Allah ya ba da iko Amin thumma amin.
Allah ya taimake mu ya bamu ikon rubuta duk abinda yake daidai ya kuma hane mu da rubuta abinda yake kuskure, makaranta kuma ya basu ikon amfani da duk faɗakarwar da take cikin wannan littafi, ya kuma hane su da ɗaukar duk abu mara kyau da ke cikinsa Amin.
Ibrahim Aliyu Yakubu