Free chapter · Read without an account
Page 001
CIKI DA WAJE
IBRAHIM ALIYU YAKUBU
001.
Note;
Tun farko a gabatarwar wannan labari nace hatta garuruwa wanda ya zo ƙwaƙwalwa ta kawai nake sawa, saboda haka ko sunan wani gari ne da ka sani kada ma ka yi zaton da garin nake, don idan har na san sunan gari ma a tsawon rayuwa ta ba za ka ji shi cikin wannan labari, haka zalika character, da duk wani abu da ke cikin sa.
CHAPTER 01
ALMAWA STATE.
Almawa state na daga cikin manyan jihohin Nigeria da ke arewa maso yammacin ƙasar, haka zalika garin na almawa shine dai a matsayin baban birnin jihar inda anan ne state secretariat take.
Almawa state tana da girman ƙasar da za'a iya sanya ta daga cikin jihohi mafi girman ƙasa a Nigeria domin kuwa idan bata kasance na ɗaya ba, to ba zata wuce na biyu ba ko na uku.
Bayan haka jihar tana da yawan mutane, duk da dai inda gari ya mamaye a jihar bai kai kaso ashirin cikin ɗari na girman murabba'in ƙasar ba, hakan ne ya sa mutanen birnin suka dogara da noma, ainun wajen samarwa da kansu hanyoyin shigowar kuɗaɗe.
Dajin SALMARAN GAME RESERVE na ɗaya daga cikin dazukan da suka shahara a ɗaukacin Nigeria wanda ake lissafa shi a matsayin mallaki jihar ta almawa duk da kuwa ya ratsa ta cikin da yawa daga cikin jihohin dake maƙobtaka da jihar, shima yana taimakawa ƙwarai da gaske ainun ga mazauna yankin dake kusa da shi wajen samar musu da hanyoyin samun kuɗin shiga duk da sai sun bi ta hanyar karya doka sukan samu damar hakan, amma mafi yawanci dokar ta fi aiki akan talakawan dake zaune a yankin masu shiga cikin dajin domin yin itace sannan su samu damar ciyar da iyalansu da ɗan abinda suka samo wanda da zarar jami'an tsaron da ake kira gandun daji sun kama su zasu ƙwace itace, da Gatari wani zubin harda abin hawa walau keke ko mota su kora su.
Amma abin mamaki sai ka ga kawai waɗanda ake kira ƴan mandarin sun shiga cikin tsakiyar dajin, suna sare bishiyoyi tare da samar da katako kuma batare da an dasa Wasu bishiyu a wurin ba, ko kuma masu samar da gawayi da zasu babbakawa bishiya guda wuta har sai ta ƙonw ƙurmus w wanda hakan a ƙaida shine zai iya zama laifi ba kamar waɗanda iya busashen suke ɗiba, amma da yake su waɗancan sukan haɗa ma'aikatan da ɗan wani kuɗi da bai taka kara ya karya ba sai su bar su su yi ta aikata wannan ɓarna.
Bayan haka idan ka yi dubi da ɓangaren rafuka da akwai manyan rafuka da suka wuce lissafi a ɓangare da dama na jihar, wanda shi ma yana samar musu da ayyukan yi na sun kifi, da ya yawaita a ɓangarorin jihar, BALMARI DAM shi ma ba laifi yana ɗaya daga cikin rafuka mafi girma a jihar, duk dai girmansa bai kai a lissafa shi cikin dama-daman Nigeria ba amma yana da tsayi da faɗi, an kuma samar da shi ne tun farkon kafuwar jihar a matsayin jihar guda, inda tun a wannan lokaci gwamnan ya samar da hanyoyin ruwa channel wanda suka shiga ɓangarori mafi kusa da dam ɗin, duk inda suka shiga kuwa ana lissafa shi a matsayin wuri Mafi samar da da yawa daga cikin abin da ake nomawa a jihar.
Idan ka dubi ɓangaren al'adu da addini a jihar ta almawa zaka samu cewa da akwai al'adu daban-daban, yayinda idan ka dubi fuskar addini kuma zaka iya cewa musulmai da kiristoci yawansu zai iya zama ɗaya sai dai kuma a zance mafi tabbas musulmai sun fi yawa, saboda haka jihar ƙasa ce ta al'adu.
Kamar yadda yake a mafi yawan jihohi dake da gamayyar mabiya addinan biyu har ya zamana yawansu ya kusa zama ɗaya akan samu yawan faɗace-faɗace to haka ma jihar almawa wannan matsala tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da rashin zaman lafiya a wasu lokutan cikin jihar.
A daidai wannan lokaci kamar yadda mafi yawa daga cikin jihohin arewa ke fuskantar rashin tsaro maganar gaskiya za'a iya lissafa jihar almawa a matsayin jihar da matsalar ta ta'azzara, har ta so wuce makaɗi da rawa, domin kuwa da akwai lokacin da har cikin birnin almawan suka shiga suka aiwatar da ta'addancinsu abin dai ba daɗin faɗa.
A ƴan wannan lokuta jama'a an shiga mawuyacin hali na rashin tabbas ɗin rayuwa, ga kayan masarufi yayi tsada wanda hakan ta wani ɓangaren za'a iya lissafa shi da laifin shugabanni amma kuma da laifin ƴan kasuwa da ba sa sassauta wa kansu su ma, har ya kan zamana wasu daga talakawa kan rasa abin kaiwa bakin salati a wasu ranaku.
Matasa rashin aikin yi ya zama ruwan dare wanda hakan ya tilasta su shiga cikin abubuwan da zasu taɓarɓarar da rayuwar su na ta'addanci, sace-sace, ƙwace, shaye-shaye da abinda ake kira dabar siyasa, kai harma da duk wani nau'in abin ƙi da wasu ɓata garin kan iya shiga.
Matsalolin jihar ta almawa a wannan lokaci ta wuce ƙiyasin masu ƙiyasi, domin harkar lafiya, da ilmi sun yi taɓarɓarewar da ba a bada labari, ga harkar tsaro da hanyoyin sufuri na tituna da suka lalace a mafi yawan ɓangarorin jihar har ma da cikin birnin.
Gwamnan da ke mulkin birnin a wannan lokaci shine A.S.A SARAKI, dattijo ne da bai haura shekara arba'in da biyar ba a duniya, saboda yanayin jikinsa ma ba kai tsaye zaka yi tunanin ya ma kai waɗannan shekarun ba.
Kafin zamowarsa gwamna a kakan zaɓen da ta gabata wanda gashi a wannan lokaci har wani zaben ya ƙara gabatowa gadan-gadan domin har wasu jam'iyyun sun fara fitar da ƴan takarkarun gwamna, amma dai jam'iyyar su har yanzu ana dai jita-jitar tsayarwa duk dai abin da ya shahara a bakunan talakawa shine A.S.A ba zai koma ba, saboda bai yi abin kirki ba ko ɗaya da za'a kalla a yaba, su kansu manyan masu faɗa aji na jam'iyyar sun tabbatar da cewa komawarsa daidai yake da suɓucewar mulki daga hannunsu, wanda kuma hakan babbar barazana ce gare su. duk da kuwa kafin zamowarsa gwamna ya kasance daga dangi ko kuma ma ace ɗa ɗaya tilo ga Alhaji amadu saraki wanda ya shahara a bakunan al'umma saboda yawan dukiyarsa a shekarun baya, wanda bayan mutuwarsa A.S.A SARAKI ya cigaba da jan ragamar dukiyar ta sa, inda cikin ƙanƙanin lokaci ya shahara ba don komai ba sai don taimakon da yake yi da dukiyar ta hanyar samar wa da matasa aiki, da gina masallatai, da samar da jari ga manoma, wani kuma abu da ya ƙara sanya sunan sa gaba-gaba a bakunan talakawa shine nusar da gwamnati ga duk wani kuskure da ya ga ta yi, da ba da shawara da ya san zata taimaka wajen kawo cigaban jihar.
Kwatsam! Kuma kakar zaɓen da ta gabata sai ga jam'iyya mai ci ta dira a kansa bayan manyan cikinta sun kira shi taron gaggawa na buƙatar sa da ya zama ɗan takarar gwamna a wannan shekarar.
Da farko abin ɗaure masa kai yayi, ya kuma nuna bai yi maraba da hakan ba, amma yadda suka cika shi da daɗin baki, da nuna masa cewa su fah suna bashi dama ne da zai gyara kura-kuran da ya daɗe yana nusar da su akan su gyara amma har rana mai kamar ta yau ba su kawo karshen da yawa daga cikin matsalolin da ya lissafo ba.
Duk da haka bai karɓi tayin su ba, sai a karo na biyu bayan sun zanta da abokansa waɗanda suka dinga bashi shawara a ƙarshe dole ya amince ba don ransa ya so ba.
Batare da ɓata lokaci suka tsayar da shi a matsayin ɗan takarar su, wanda Allah ne kaɗai ya san manufar su ta aiwatar da wannan lamari, cikin ikon Allah kuwa kiristoci da musulmai saboda kyautata masa zato da suke yi suka yi masa ruwan ƙuri'u, duk da dai wasu kiristocin kan zaɓi wanda ya fito wata jam'iyar saboda ra'ayin su na addini, haka ma a wasu musulman, a ƙarshe dai shine ya ci zaɓe da yawan ƙuri'un da ya wuce na biyun sa da fikon kashi talatin cikin ɗari, talakawa kuwa sun yi matuƙar murna saboda matuƙar kyautata masa zato da suke yi.
Sai dai kash! Lamarin sai ya canza salo bayan shekara ɗaya da fara gwamnatin sa, a shekarar farko dai ba laifi ya yi ayyuka da suka haɗa da fara gyara wasu titunan jiha, gina Almawa state University, Almawa state Library, samar da vocational activities ga samari masu zaman banza, har mutane suna zaton ba makawa a shekara huɗun ne duk wasu matsalolin su sai sun kau, amma a cikin ƙanƙanin lokaci komai ya rikice, wasu daga cikin titunan da aka haƙe da niyyar gyarawa ma ayyukan suka tsaya sai ya zama na cewa maimakon gyara, ɓarna ma aka yi tun da har kawo yanzu ba'a ƙara waiwaye aikin ba, rashin sakin albashi da zabtare wani kaso idan an saki, haka dai ya zamana cewa matsaloli sai tasowa suke yi a gwamnatin A.S.A SARAKI ƊIN.
Eh ba makawa a farkon hawansa yayi manyan ayyukan da bazu mantu ba a tarihin jihar, amma kawo zuwa wannan lokaci babu wani ɗan siyasa da aka fi tsana a jihar kamar sa, saboda tsanani da ya kawo a jihar, lalacewar harkar ilmi shine abinda ya sanya tsanarsa a zuciyoyin samari da suka zama ƙashin bayan al'umma a kullum kuma daga jam'iyyar adawa ba su da abin da suke yi face sukar sa a gidajen rediyo, talabijin, da kuma kafafen sada zumunta na zamani, duka yana gani amma bai taɓa fitowa ya kare kansa ba, sai dai daga masoyan sa a cikin jam'iyyar kan yi haka, yayinda duk da haka a cikin jam'iyyar ma da akwai maƙiyansa ta wani ɓangare har ma su suka fi yawa.
Ya kan yi murmushi ya kuma ɗauki lokaci yana tunani, tabbas bai taɓa tunanin shine zai zama jagoran al'umma kuma a samu wannan taɓarɓarewar da ta wuce misali a jihar sa ba, yayi da na sani mara yanke wa, ya gama fahimtar manyan jam'iyyar suna kan shirin samar da wani ɗan takarar ba shi ba, da zai fito a jam'iyyar, abu ɗaya da basu sani ba shi tun shekarun baya ya cire rai da cigaban mulkin jihar ta almawa a zango na biyu.
Idan ya daɗe yana tunani ya kan ce siyasa mugun was, na wajen ta bai san na cikin ta ba, saboda haka CIKI DA WAJEN siyasa da banbanci, saboda na wajen bai san menene ke cikinta ba.
Ya yi matuƙar da na sanin karɓar tayin su tun a shekarun baya, yana matuƙar samun kansa a matuƙar damuwa idan ya tuna matsaloli da yawa da ya kasa magance wa a matsayin shugaba, wani lokacin har ya kan ji ya matsu yau ya ga ya miƙa mulkin jihar a hannun wani shima ya ɗan huta.
A mafi yawan lokuta ya kan ji kuma tamkar ya nemi wucewa zango na gaba, saboda a yanzu ya tsara hanyoyin da zasu samar da mataki zuwa ga ƙarshen duk matsaltsalun da suka addabi jihar, amma kuma idan ya tuna cewa bai da tabbacin samun nasarar cika burinsa sai duka sa ran da yake game da cikar burinsa ya yanke, ya ƙara tabbatarwa da kansa cewa mafi alheri shine kawai ya sauka ya bawa wani ya jarraba.
Shi kansa ya sani ba komai ba ne ya jawo masa wadannan matsaloli sai rashin sanin abubuwa da yawa, da ya kamata ya sani kafin zamansa gwamna, kasancewarsa baƙo a siyasa da kuma tsananin sanyin da yake da shi, wanda hakan ya jawo masa raini a wurin muƙarrabansa har suke aiwatar da abin da suka ga dama batare da shayin komai ba, shi kuma ya gagara kawo ƙarshen hakan.
Tabbas da ace ya san CIKIN siyasa, wacca take da banbanci da wajen ta, da ba makawa za'a samu nasara fiye da waccan aka samu a wannan karon ma, amma dai abin yanzu gaba ɗaya sai a hankali.
Wannan shine taƙaitaccen bayani game da jihar almawa, yanayin al'umma da yanayin rayuwar mutanen cikinta, har ma da ɗan kaɗan akan gwamnati, saboda haka ku biyo mu a cigaban littafin CIKI DA WAJE domin jin me yake wakana a wannan jihar? Na san dai za ku so ku ji shin ko yana fitowa a matsayin ɗan takara, idan ya fito kuma ko zai iya lashe zaɓen? Har ma ya cika burinsa?
Duka zaku samu amsohin tambayoyin ku a shafukan da zasu zo nan gaba na littafin CIKI DA WAJE.
..
A matsayina na wanda ya fara rubutun kwanakin baya kaɗan a taimaka da comments wanda hakan zai taimaka wajen nusar da Ni da akwai masu bibiya ta, har na samu na dinga kawo muku cigaban labarin akan lokaci.
..
..
IBRAHIM ALIYU YAKUBU