Free chapter · Read without an account
3
*RAGAMAR DAMISA*
```FreeBook.```
*©️Halimahz*
*SADAUKARWA GA:-*
Muhammad Kareem(MK)
_for your business advert DM ***._
*(3)*
baƙar mota ƙirar ferrari, tayoyinta manne suke akan titin zuwa unguwar malali, daga cikin motar sanyin Ac ne ke hurawa wanda ya haɗe da daddaɗan ƙamshi na turaren mota, banda fitar numfashi da kuma waƙar barmana joge da ke tashi ƙasa-ƙasa ba abinda kake ji, dattijuwar da ke zaune a mazaunin driver tuƙin motar take yi shi ba da sauri ba kuma ba da gudu ba, jikinta sanye yake da shadda gezna milk colour tasha azababben ɗinki, yayinda idauwanta ke manne da siririn baƙin medical glass, ita ba zaka kirata fara ba haka ba zaka ce mata baƙa ba, kalar fatarta dai mai kyau kamar balarabiya ba.
ta ɗauke idonta daga barin kallon titi ta juya ta kalli kujerar me zaman banza, kallon da take yi masa har ya kusa mantar da ita cewa fa tuƙi take yi, wanda ba don Allah ya taƙaita babu motaci akan titin ba da zata iya bugar wata motar, shi dai kansa na kishingiɗe ne da jikin kujera idanuwansa a lumshe tamkar me bacci, wucewar sakanni ashirin da biyar tana kallonsa kafin ta ɗauke idonta akansa ta mayar kan titi.
ta sauke gajeren numfashi sannan tace,"ya batun masters ɗin naka?".
yana jin haka ya buɗe idanuwansa, fuskarsa ta ɗan ɓaci a dalilin maganar mahaifiyar tasa, ba zai amsa mata ba balle taja maganar da tsayi, hakan yasa shi maida murfin idonsa ya rufe, maganarta kuma ta sake kutsawa cikin tunaninsa.
"ya batun masters ɗin naka?".
muryarsa na bayyana sautin ƙorafi yace,"oh my God Ammi...".
bata barsa ya ƙarasa ba ta katse shi,"ka gama service baka da sauran abinda ya rage, yanzu zaka ɗora or until you get job?".
"babu rana".
"abunda yake dole ai za'a iya saka masa rana".
"bai zamar min dole ba gaskiya tunda ba so nake ba balle har in saka shi cikin lissafina".
"duk da ni ina so?".
zamansa ya gyara akan kujera, ya zare earpice da ke rataye a kunnensa ya sake shi a jikinsa, sannan ya fuskanci mahaifiyar tasa yace,"Ammi tun yaushe nake yi miki abinda kike so ko da bana so?".
"tunda na haifeka AbdulRashid".
"to amma Ammi why a yanzu ba za kiyi min uzuri ba?, Ammi tunda har kika kalla ina jayayya da ke akan hakan wallahi bana so ɗin ne, ko da zanyi ɗin ba za'a samu yanda kike so ba".
bata ce da shi komai ba sai fuskarta da ta nuna alamu na rashin jin daɗi, ya tsaya yana kallonta wucewar tsawon daƙiƙa biyu tukunna yace,"let me drive".
ta girgiza masa kai ba tare da tace komai ba.
ya sake cewa,"please".
tace,"no need ɗan gidan Wakili, just rest and continue to rest, ai saboda ba zaka iya driving ɗin ba ka taso ni nazo na ɗauke ka".
fuskarsa ta washe da murmushi me bayyanar da haƙora tare da kai hannu ya shafo fuskarta, ita kuma ta doke hannun nasa, sautin dariyarsa ya fito yana mai juyar da kansa zuwa kujerar baya, ayaba ya ɗauko acikin wani medium size basket ya ɓare, bayan ya gutsira ya kai bakin Ammi, itama ta buɗe nata bakin ta gutsira kafin nan ya shiga bata labari.
"Ammi time ɗin da muna level 1, akwai Malamin AEE namu, mutumin ba shi da mutunci irin azzaluman malaman nanne, aiko wata rana ya shiga class zai yi unexpected test, ga shi da yawa ƴan class ba su je ba, yana faɗin wai test ɗin na a matsayin exams namu ne kiji wata mugunta, aiko in less minutes sai ga ƙofar hall ta cika, muka dinƙa roƙonsa akan ya barmu mu shiga amma sam yaƙi, aiko dama ni da Huzaifa mun siyo ayaba muna ci, don haka muka haɗa plan ɗin da muka dame shi da knocking har sai da yazo ya buɗe ƙofar, dama yana tahowa na durƙusa, yana buɗe ƙofar kuma na cilla ɓawon ayaba guda uku a daidai saitin da zai saka ƙafarsa ta inda sam ba zai ankare ba, wato ina kai ki Ammi mutumin nan ya gama ciccimana fuska har da su zagi, ya maida ƙofarsa ya rufe, wallahi kansa da ya ƙwalu a ƙasa ƙarar har waje, ƙarshe har mu kai exams baya zuwa saboda karayar da yay a ƙafa".
ya ƙarashe maganar yana dariya tare da sake faɗin,"kai ɓawon ayaba mugu ne wallahi".
"kuma ai kun iya muguntar, ba ku tunanin hakkinsa akan ku?".
"ba wani hakki Ammi, muma ai ya zalunce mu".
"to amma dai ya biku muku carry over ko?".
"ahh haba dai carry over, idan yafi ƙarfin mu ai bai fi ƙarfin Allah ba, tuni muka dinƙa maka shi a daily prayers Allah yay mana maganinsa na wuce da A me aji ma kuwa".
Ammi na girgiza kai tace,"Allah ya shirya ku".
ta numfasa kafin ta ɗora da cewa,"ba kai ɗaya ba ne a wurin mahaifinka, don haka tarin dukiyar da yake da ita ba zata zama taka ba kai ɗaya, kazalika ba kai ne magajinsa ba, thats why i am advising you da kayi karatu to further, so that duk wani challange na rayuwa zai zo maka da sauƙi, ka sami tarin ilimi a wannan rayuwar tamu ta yanzu shi ne zaka zama wani Rashid, in har da iliminka kafi ƙarfin wulaƙanta da tagayyara..."
ya katseta da faɗin,"to Degree ɗin da nayi banyi komai ba kenan Ammi?, shi ba karatu ba ne?".
sai kuma ya hau mitar faɗin,"kin fa san karatun nan can ba sonsa nake yi ba, kawai don babu yanda zan yi ne Allah ya wullo ni a cikin gidan ƴan boko, ya kuma haɗa ni da murɗaɗɗen uba, ace ga tarin kuɗi amma ba za'a barka kayi business ba sai dai a tusaka a ƙasan federal government, aikin da wasu shekaru na zuwa za'a fara kira maka retire, kamin a baka albashi sai an galabaitar da kai, kasuwanci kuwa sai randa Allah ya jarabceka da karayar arziƙi...Degree, Masters, Phd, haba dai kayi ta karatu kayi ta karatu kamar dama don shi aka halicce ka, ni gaskiya i want to enjoy my life, ba zan iya karatun mutuwar da Yayuna suka yi ba, tunda Allah yasa ma kina raye kawai kici gaba da ɗaga ƙasan kaya kina ɗauko certificate kina sakawa degree ɗin albarka kullum, very soon ma aure zan yi in samu freedom ɗin kaina, don na lura wannan Gwaskan idan kana ƙasansa a boko zaka mutu".
"to shikenan ya isa haka, Allah ya baka haƙuri, bance ka rufe ni da duka ba".
yay shiru yana shafo sumar kansa, ya sunkuyar da kai tare da faɗin,"Am sorry".
"sorry for your self Ɗan gidan wakili".
ta faɗi hakan sa'ilin da take juya kan motar tana shiga wani layi, cikin su babu wanda ya ƙara magana har suka ƙaraso gida, sau ɗaya ta danna horn me gadi yazo ya buɗe, tare suka fito daga cikin motar bayan ta isa ga parking lot inda motoci suke danƙar a wurin kamar kamfanin sayar da motoci.
fitowar tasu tayi daidai da shigowar wata farar mota wacca aka je ɗauko me gidan a ciki, Ammi ta nufi motar da ɗan hanzarinta tattare da farin ciki, ɗan nata kuma ya sunkuyar da kai yana neman sa kai ya wuce ta dakatar da shi.
"wuce muje". Ammin ta faɗa sanda ta kamo hannunsa ta dawo da shi baya.
yasa hannu yana shafa sumar kansa, in seconds gaba ɗaya sai ya koma kalar mara gaskiya, yana ta yatsine fuska da cije haƙora, Ammi ta galla masa harara tana faɗin,"ni na hanaka sa hular".
hannunsa taja suka wuce wurin da motar Daddy tayi parking, lokacin kusan yaran gidan da matan duk sun fito tararsa, suka isa a lokacin da yake sauke waya daga kunnensa.
"sannu da dawowa, an dawo lafiya?, ya hanya?".
Ammi ta faɗa tana tsayuwa kusa da abokiyar zamanta.
kafin Daddy ya kai ga amsa mata Rashid yace,"Barka da Dawowa".
Daddy bai amsa masa ba yabi sa da wani irin kallo from up to down, shigar ƙananun kayan da yay kace irin arnan ƴaƴan ƙasar america.
"Daddy kawo jakar". ya faɗa tare da miƙa hannu zai karɓi jakar Daddy ya hana shi yana zabga masa harara, yay guntun tsaki yana ɗauke kai daga gare shi ya mayar kan Usama yace da shi,"fita waje ka amso min saƙo".
Usama ya bar wajen cikin sauri, Daddy ya bawa Hajiyarmu jakar sa'ilin da yake gyara zaman babbar rigarsa, Ammi da Umma ma suka bar wajen yayinda yaran ma suka mara musu baya.
"kai Rashid". Daddy ya kira sunan nasa cikin ɗagowar murya wanda hakan ya dakatar da Rashid daga tafiyar da yake yi, ya cije haƙora yana sosa ƙeya kansa a sunkuye.
"dan ubanka sau nawa zan faɗa maka ka daina yi min irin wannan shigar banzar acikin gidana?, duk kabi ka zama kamar ba ɗan musulmai ba, ji fa kalar ɗan iskan askin da ke kanka, uwarka kuma na ganin ka ta zuba maka ido, kai ko kunya ma baka ji kake yawo da yagaggun kaya?, da kimata da komai a garin nan salon ka zubar min da mutunci a idon jama'a, irin shigar da ka ga sauran ƴan'uwanka nayi kenan?, shashashan banza kawai me koyi da yahudawa, zaka lalata tarbiyarka ne idan baka yi wasa ba, kama jini da kyau duk namiji me irin wannan shigar ba'a ganinsa da mutunci, kuma baya zuwa neman aure a ba shi...kana bin abokan banza zasu lalata maka tarbiya, za su rabaka da ɗan guntun addinin da ka samu...kaf cikin ku kai ɗaya nake dana sanin fita da shi abroad, banda ma ƙarfin adu'a irin tawa da tsayin daka ban san me zaka zama ba".
sai kuma yay shiru lokacin da idonsa ya kai kan Anas da Umar suna shigowa, yasa hannu ya yafito su, suka ƙaraso gabansa su na rissinawa tare da faɗin,"Daddy sannu da dawowa".
bai saurare su ba yaci gaba da faɗa yana cewa,"kalli ƴan uwanka gwanin sha'awa, ana ganinsu anga masu mutunci masu tarbiya masu kirki, amma kai dubeka don Allah, ji wani aski akanka mara ma'ana".
yasa hannu ya ɗale wuyan Rashid da duka yana ƙara faɗin,"ina ka kalli ƴan'uwanka kana ƙara sadda kai ƙasa".
babu shiri zafin dukan yasa shi ɗago da kai yana kallon su yana ƙara ɓata fuska, duk ɗin su shigar manyan kaya ne a jikin su ɗinkin tazarce, ga hula sun ɗora akan askin da suka sha, sai kace wasu magidanta, shi kam baya jin zai iya jurewa.
bai yi aune ba Daddy ya kawo masa duka yana faɗin,"Rashid zan ci ubanka idan baka bar tsayuwa kana faman rangaji irin haka ba kamar ɗan shaye-shaye, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wai ɗabi'ar ƴaƴan arna a cikin gidana?, me na aikata ni kam a rayuwata".
sai ya fusata ya tattare babbar rigar ya ɗaga ƙafa zai yi ball da shi yana sake cewa,"ina magana kana ƙara kama hantsar wando wato ka ƙara shaida min lallai ka zama tantiri ko, zaka ɗauke hannunka a wajen ko sai na karya ƙashin hannun naka".
duk wannan faman tunzura da Daddy ke yi bai sa Rashid ya ɗaga ido ya kalle shi yace ƙala ba, sai da Hajiyarmu tace da shi,"ka bashi haƙuri Rashid".
Daddy yay karaf yace,"ya bani haƙuri kuwa yana ganinsa kanmu ɗaya, ai jinsa yake daidai da ni, gani yake kamar shi ya haife ni...banda ma dai kar nayi masa baki ya lalace gaba ɗaya kina gani faɗan nake masa amma sake wasu abubuwan yake yi, shi ne kama hantsar wando shi ne ɗora hannu akan ƙirji shi ne rangaji da kai, kai ba abokai ba balle ince huɗubarsu kake bi, to koma dai ka fara shaye-shaye ne banda masaniya Rashid?".
Rashid yasa hannu a sumar kansa yana shafawa murya a kumbure yace,"ni babu abinda nake sha Daddy, ai nasan haramun ne, zamanina ne kawai yazo da hakan, kuma Daddy hakan bafa yana nufin na lalace ba ne, its just gayu, gayu ne fa kawai Daddy, wallahi Daddy if na saka irin wannan kayan da kake ɗinka mana duk takura min suke yi, ga duk su saka inta yin zufa, hular ma sai yake hana iska shiga cikin brain ena tana functioning very well, buh i always feel comfortable a ƙananun kaya, and its even fits me more than waɗancan, kyawuna yafi fitowa, amma Allah idan na saka manyan kaya na fita daga gidan nan sai kaga ana min kallon nine Baban su Iftihal, wasu ma suke yi min kallon na aje mata biyu zuwa uku, duk fa Daddy sai inbi in wani tsufa, wa'annan masu karɓar sadaqar suke zaton ko kaine, amma irin waɗannan kayan nafi shan iska da su, nafi jin daɗin su, su fito min da samartakata, kuma Allah Daddy ba wai don mutum na saka ƙananu kaya shi ne yake ɗan iska ko kuma yana koyi da arna ba, Daddy kaima da kake riƙaƙƙen ɗan boko ai ya kamat....".
bai ida faɗin abinda zai ce ba Daddy ya cire takalminsa ya ruruma ya wurga masa a jiki,"wato nima ya kamata in yi koyi da kai ko, ko kuma in barka kayi duk kalar abunda ka ga dama ba zan kwaɓeka ba, in zuba maka ido ka zama yaron banza saboda naci boko na ƙoshi har na ture...to ni daka ganni ba ɗan banza ba ne kuma ba zan zama mutumin banza ba, ehh riƙaƙƙen ɗan boko ne ni amma ban yarda da koyi da ɗabi'ar ƴaƴan arna ba, yanda banyi ba haka ɗan dana haifa bai isa yayi ba kuma bai isa ya juyani na bar shi yay abinda ransa yake so ba...wuce muje ciki".
Rashid yasa kai zai yi gaba Daddy ya buga masa tsawar,"ubanka zan taka in tafi?".
Rashid yaji kamar ya kurma ihu, gaba ɗaya bai gane manufar Daddy ɗin ba sai da Umar yace da shi,"takalminsa da yake hannunka".
tukunna ya ankare yaje ya durƙusa ya ajiyewa Daddy takalmin nasa yana faɗin,"Sorry Daddy".
tsabagen takaici Daddy kamar zai tashi sama haka ya nufi part ɗin Ammi, yana shiga ya shiga ƙwala kiran,"Asma'u!Asma'u! Asma'u". kira kamar na mafarauta.
duk amsawar da Ammi ke yi baima san tana yi ba, haka ta sakko cikin sauri daga saman bene kamar zata gangaro, yaranta ma duk sai gasu sun bayyana a parlo kowa yana wurƙi-wurƙi da idanuwa suna kallon Daddy, kafin su mayar da kallon su kan Rashid da yake shigowa daga baya yana tafiyar ƙwambo kamar ba shi aka gamawa faɗa yanzu ba.
"Daddy lafiya?". cewar Ammi a hargitse lokacin da take isowa gabansa.
"ina kuwa lafiya wannan yaron yana neman ja min masifa, ƴaƴa goma sha biyar kaf ciki babu ɗan iska sai shi ɗaya, banbancin tarbiya na basu da shi ya fita daban?, ko kuwa su sauran Uwayen ƙwarai suka samu shi tasa uwar ce dai sai adu'a?, to wannan iskancin banzan ba'a gidana ba wallahi, ban amince ba kuma ba zan lamunta ba, magana ɗaya ce nake ta maimaitawa ba tun yau ba, amma saboda ke da ƴaƴanki ba ganina kuke yi da mutunci ba shiyasa kuke ƙetareta, to bari kiji in faɗa miki, yanda sauran matan da ƴaƴansu ke bin umarnina haka kema ya zamar miki tilas dole, ba yanda za'ai na bar wani yafi ƙarfina a cikin iyalina, ba kuma za'a yi shi ba".
yay shiru yana juyawa bayansa da Rashid ke raɓe, ya kamo kunnensa ya murɗe sannan ya dawo da shi gaban uwarsa still yana riƙe da kunnensa yace,"yaje ya aske wannan uwar sumar da ya tara kamar mahaukaci, yay aski irin na musulmai ƴaƴan mutunci, sannan ya tattaro min duk irin wannan kayan banzan da kike siya masa ya kawo min ɗakina...".
Ammi ta katse shi da cewa,"Daddy wallahi ni bani ke siya masa ba, da kuɗinsa yake siya".
"kuɗinsa ko kuɗina?, aikin uwar me yake yi dama?, ba saina bayar ba yake samu ba?, to sai dai idan wani uban zai yi ya dinƙa ba shi amma ni dai ƙwandalata Rashid ya daina ci muddin bai koma yanda nake sonsa ba irin yanda sauran ƴan'uwansa suka tsaya akai...kuma ina maimaita miki yaje ya aske wannan uban gashin kafin magriba, failure to do so ranki in yayi dubu sai ya ɓaci".
Ammi ta sauke numfashi tare da bashi haƙuri, yasa kai ya fice daga part ɗin nata cikin tsananin ɓacin rai.
Rashida ta zauna kan kujera tana harɗe ƙafafa fuska a ɓace tace,"wai Yaya R kai ta jawowa Daddy yana yiwa Ammi faɗa yana gaya mata magana...".
bata ida zancen ba yay kanta tayi saurin tashi da gudu ta faɗa kitchen ta kullo ƙofa.
"zan kamaki ne zaki faɗa min idan ni sa'anki ne, idona idonki sai na fasa miki baki".
dawowa yayi ya zauna a kujera kusa da Ammi, bata yi masa magana ba shima ɗin bai yi mata ba, sai can tai nisa ta kalli Suhaila tace da ita,"ɗauko masa abincinsa tun breakfast bai ƙara cin komai ba".
ta tashi tana kumbure-kumbure, dining taje ta ɗauko flask da plate tazo ta janyo center table gaban Rashid ta ɗora akai, sannan ta koma ta ɗauko jug ɗin lemu da cups ta dawo ta ajiye, ta juya zata koma ta zauna ya dakatar da ita.
"ɗauki ki mayar da su".
"kana ji fa Ammi tace in ɗauko maka".
ya sakar mata uwar tsawa,"kin ɗauka kin mayar ko sai na miƙe kinga ainihin tsayina".
muryar Ammi a ƙasa tace da shi,"ka dinƙa safafawa yaran nan Rashid, yanzu mene laifinta anan?".
"Ammi baki kalla yanda take faman cin magani ba ne saboda kince ta kawo min abinci tsabar rashin kunya, tana zuɓuro baki gaba ko ni tsaranta ne?".
"to kayi haƙuri, ai kasan basa yi maka hakan, ɓacin ran da suke yi ba akanka ba ne ai akan faɗan da Daddy yay ne".
"ni da akayiwa faɗan ban ɓata rai ba sai su, ko kuma ni ba uwata ya faɗawa magana ba?".
Ammi tace,"ya dai isa haka ci abincinka".
bai tanka ba ya naɗe ƙafafunsa ya kwanta kan kujerar tare da ɗauke kai.
"Rashid ulcer ɗinka fa, tun breakfast ɗin safe fa, so kake kaja min kwanan zaune yau?".
"indai wannan abincin ne bana ci".
"to wanne zaka ci?, girki ɗaya muka yi yau".
"indai ba zata ɗauka ta mayar da shi inda yake ba to ba zanci ba, zan zauna da yunwar, idan ciwon nawa ya tashi kiyi baccinki kawai, idan na mutu lokacina ne yayi".
Ammi ta sauke numfashi ta yunƙura ta miƙe zata kwashi kayan abincin, yay saurin cafko hannunta ya mayar da ita ta zauna, ya miƙe ya zare belt ya isa kujerar da Suhaila ke zaune tana danna waya ya shiga lafta mata, dukan farko ya haɗe da ƙwalla ƙararta da kuma maganar Ammi da ke cewa.
"Rashid! Rashid ka bari".
bai ko saurareta ba yaci gaba da dukan Suhaila wacce ke kururuwa tana faɗin,"Ammi zai kashe ni, wayyo Ammi kizo ki ceceni na shiga uku, wayyo Ammina wayyo Daddyna, Daddy ya fasa min bayana na mutu na lalace, Yaya kaima kazo don Allah".
Ammi dai na daga inda take, tasan ko ta tashi a banza, don bata yanda zata iya ƙwatarta a hannunsa, kuma duk maganar ma da zata yi masa baji zai yi ba, idan kuma tayi kukan da baya so yazo yana shiga damuwa ita kuma kona misƙala zarra bata son damuwarsa.
sai da ya zane Suhaila duk yay mata shati ruɗu-ruɗu ajiki ya fasa mata baki tukunna ya ƙyaleta yana faman huci.
"tashi ki ɗauka ki maida inda kika ɗauko".
"Yaya ba zan iya ba ka karya min ƙafata".
ya ɗaga belt ɗin zai ƙara mata tayi saurin miƙewa tana barin gabansa.
kwashe kwanukan abincin tayi ta mayar da su kan dining, da ƙyar take iya taka ƙafa, jikinta duk yay tsami.
"na maida". ta faɗa tana sosa bayanta, shi kuma ya wuce ya zuba abincin ya fara ci.
yana jin Suhaila na faɗin,"Ammi kinga ya fasa min wayata". ta faɗa tana kuka sosai, ita kuma Ammi na bata haƙuri da lallashi.
bayan rabin awa Suhail yay sallama a parlon, dama tunda ya sanyo ƙafarsa a corridor ya jiyo shashsheƙar kuka, kujera ya nema ya zauna idanuwansa na mannewa akan Rashida wacca Ammi ke yiwa tsifa, sannan ya mayar da idonsa kan Suhaila wacca ta dunƙule akan kujera a kusa da Ammi.
duk da cewar baya gidan kuma bai san me aka yi ba, amma hakan bai hana shi fahimtar abinda ka iya faruwar ba, laɓɓansa suka tale bakinsa na furta,"me ya haɗa ki da shi?".
taja majina da ƙyar tace,"ni bai ce min in ɗauke flask ba kawai sai ya kama dukana da belt, kuma Ammi tana tayi...".
Ammi ta katseta da faɗin,"to uwar zance tambayarki kawai akayi me ya haɗaku ba dogon jawabi aka ce kiyi ba".
Suhail ya ɓata rai yana faɗin,"ki barta ta ƙarasa maganarta mana".
Ammi tayi masa wani kallo tare da cewa,"ba zan barta ba ɗin...da ka dawo wa kaiwa sannu da gida?, kai gaka ɗan jarida uban san jin bayani da ɗaukan rahoto".
ya miƙe ya bar wajen yana mita, ya shiga kitchen ya ɗauko maltina da cup ya dawo, sai yanzu ya lura da Rashid da ke zaune kan kujerar dining yana danna waya, ya watsa masa wani kallo tare da faɗin,"kai wa me yasa baka da tausayi?, sai shegen zafin zuciya kamar damisa, haka kawai ka kama ka yiwa yarinya wannan dukan na mahaukata saboda kaga babu me hanaka, kana yawan dukan na su kake so suke baka girma?, to wallahi Allah zai saka mata kuma sai dai in banje gaban Daddy ba".
Rashid ya ɗago ido ya kalle shi yace,"da ka shigi ban kulaka ba, ka fita a sabgata bana son shishshigi, kuma karka ƙara alaƙanta ni da mahaukaci if not...".
"an faɗa ɗin mahaukaci, ina kaga hankalin da za'a kiraka da me hankali".
Rashid ya dangwarar da wayarsa a ƙasa ya taso a ƙufule yayo kan Yayan nasa, dakar ƙirjinsa yay tare da shaƙar kwalar rigarsa yana ƙoƙarin kai shi bango, da yake shima Suhail ɗin ba ƙyalen ba ne ya biye masa suka kacame da kokawa ana ƴar naushe-naushe, suka shiga faɗa sosai a ƙoƙarin kowanne ya kayar da ɗan uwansa ƙasa.
Rashida ta ruɗe tana faɗin,"Ammi ki raba su fa kin san halin su".
"bar su, su kashe kansu".
"Ammi to ki kira Daddy ki faɗa masa".
"Rashida bana son magana, idan kuma so kike su rabu da juna su dawo kanki tou sai inji".
ɗiff tayi shiru tana rarraba ido, saboda ita Allah yayita da tsoro, musamman ma akan faɗan Yayyenta, suna da baƙar zuciyata, tashin hankalinta ɗaya karsu kai ga fusata su ɗau makami, don ko cikakken wata biyu ba'ai ba faɗan da suka yi last Suhail ya bugawa Rashid kwalban malt aka, har sai da yay zaman jinya a asibiti.
"mu dai mun shiga uku, ace a side ɗinmu kawai Yaya da Ƙane ke faɗa da junansu".
Ammi ta ɓalla mata harara tace,"lokacin da za'ai acan zuwa za'ai a faɗa miki uwar iya magana uwar kinibibi".
ta rausayar da kai tace,"kai Ammi ni bada wani abun na faɗa ba".
Suhaila tace,"Allah yasa Yaya ya ƙara bugawa wancan mugun kwalba".
Rashida ta miƙe cikin tsoro da fargaban abinda ka iya faruwa ta ɗauke duk abunda yake kan dining ta kai kitchen, ta dawo ta tsaya a gefensu tana aikin basu haƙuri, su kuwa banda numfarfashi babu abinda suke aikin saukewa, duk sun shaƙe wuyan juna sunƙi saki.
tana kuka ta shiga roƙon su,"Yaya don Allah kuyi haƙuri, Yaya R kuyi haƙuri don girman Allah".
ba tayi aune ba Suhail ya kai mata mari a fuska ba shiri taja baya, Suhaila ta kama yi mata dariya, Ammi tace da ita,"zo ki kwashi kayan tsifarki sai kije kici gaba da rabon faɗan".
ta faɗa tana miƙewa ta kalli inda Suhail da Rashid ke faman tumurmusar juna a ƙasa tace da su,"tunda ƴan boxing na haifa idan kun gama ku gyara min waje, duk wani abu da ku ka san kun cillo shi ƙasa ku mayar da shi muhallinsa, manyan banza kawai, an girma ba'a san an girma ba".
ta faɗa tana barin wajen ta shige bedroom ɗinta dake downstairs.
#MssAnyway
#Gamjiwriters
#Repost
#wattpad:-mssanyway
#arewabooks:-mssanyway