Free chapter · Read without an account

Episode 19

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · AZIZAN BABA

_________A guje ta nufi ɗakin BABA tana jin tsantsan farinciki, kwanon da yake ajiye wayarsa ta buɗe ta fito tana faɗin " ga ta, BABA" ta miƙa masa wayar, " yo ni na iya dubawa ne, lalubo mana shi mu ji"AZIZA ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "kai BABA wai babba da kai ba ka iya karatu ba tab" ta na nemowa ta na mamakin wannan lamari.


Kira ta danna, take kuwa ta fara ringing, ya na zaune a back sit ya ga kiran, fuskarsa ce ta yalwata da farinciki.


Amsawa yayi da sallama" Assalamu alaikum" daga can BABA ya amsa "wa'alekumussalam Aminu" 

"Na'am BABA kuna lafiya" Daddy ya faɗa, BABA ya ce " lafiya amma ba lau ba".

Subhanallahi me ya faru BABA" Daddy ya faɗa cikin razani, BABA ya ce " AZIZA ta ce dole a koma birni a yau, do Allah ka ba ta haƙuri zuwa wani satin ai zai fi ko?"

Daddy ya saki ajiyar zuciya ya ce " to BABA ba ni ita, daman zanje Osun State a satin nan, ranar Lahadi sai in zo kenan" BABA ya ce " to Ubangiji ya tsare, ga AZIZA" ya miƙawa AZIZA" a hankali ta ce "Baban birni dan Allah ka zo mu tafi, ni bazan zauna a garin nan ba" Daddy ya ce" ki yi haƙuri my daugter kinga zanyi tafiya, da zarar na dawo zan zo kinji" AZIZA sai hawaye ta ce " to shikenan, kuma za mu je Makka ma ai ko" Daddy ya ce "in sha Allahu, ki shirya tsaf daga Kano sai Makka" ta sa dariya sai kuma ta ce" hmmm ai wallahi za ta san da ni take zancen, tunda suka tafi sunan nan ba ni" Daddy da bai gane zancen ba, ya ce" ki gaishe da su Inna da Baba Tabawa" ta ce "Baban birni na gaishe ku" BABA ya ga ta warware, hankalinsa ya kwanta.


BABA ya ce" to ba ni muyi sallama" ba shi tayi, Daddy ya kuma ce masa "ku kintsa ina nan tafe in sha Allahu, nagode" BABA ya ce " to a gaishe da iyalin" ya kashe wayar.


Inna Gaji ta ce" oh ni Shatuwa wannan ƴa sai fatan shiriya" AZIZA ta ce "BABA mu shirya ya ce zai zo, kwana haka zamu ƙara kenan ko(ta faɗa ta na dunƙule yatsunta da ɗora biyu akai) BABA ya ce " eh, yanzu ina fita sallar la'asar zan sanar, hakama idan naje fadar maigari, kuma ku fara sallama da maƙota tun yanzu" 

Inna Gaji ta ce" za muje ko ina, gobe zanje gidan Baba Ilu in sanar masa, daga nan sai in biya gidan Ceɗiya muyi bankwana(family house) ɗin su Inna iyayen duk sun mutu, sai ƴaƴa da jikokinsu.



Baba Tabawa ta najin duk abinda suke faɗa, sanin dole a koma Kano da ita, ya sa tayi musu shiru,dan ita yau ɗin nan zata fara shirinta. Bayan la'asar Baba ya yi wa Liman magana kamar abun arziki ya ce"akarama kallahu ina son zanyi sanarwa do Allah"Malam Liman ya ce"to Baba" sannan ya ɗaga murya ya ce" jama'a ku ba mu hankalinku akwai wata muhimmiyar sanarwa" kowa ya ba da hankali, matsawa BABA yayi ya juyo ga mutane, ya ce" assalamu alaikum kamar yanda kuka sani, ni haifaffen garin na nan, to Allah da ikonsa sati mai zuwa zan yi ƙaura daga wannan gari, ɗa na Aminu ya na son mai da ni kusa da shi, saboda sukorito kun san dai Allah yayi masa arziki ko ba hakaba" jama'a suka ce"gaskiya ne BABA, hakan kuwa yayi kyau" BABA ya ce"yauwa bi sa hali na rayuwa ina neman afuwa ga dukan wanda nayi wa ba dai-dai ba, do Allah ayi min afuwa"kowa ya hau faɗin "ba abinda kayi mana BABA, amma ba mu so zaka bar garin nan ba,mun saba munaganinka tamkar uba agare mu"BABA ya ce " ai ba wai na tafi kenan ba zan dawo wani lokaci wannan tafiyar ma saboda AZIZAN BABA zanyi ta, amma ba wai don Aminu ba" sai aka hau kallon-kallo a masallacin.


Malam Isa ne ya ce "yanzu BABA akan AZIZA za ka bar mahaifarka ba wai dan Alhaji ya ji daɗi ba?" BABA yace " alagafarta Malam Liman a sanar da shi mahimmmancin kyautatawa maraya,da alama Isa bai sani ba"

Malam Liman ya ce"ai ba a yi haka ba BABA muna maka fatan alheri Allah ya sa a koma a sa'a" addu'a aka yi masa da fatan komawa cikin nasara.


Inna Gaji da AZIZA suka nufi gidan Ceɗiya,guri-guri ta shiga ta na sanar da su za su koma Kano, murna ake tayi mata ana mata son barka, AZIZA kuwa sai ta ƙara da ce wa" ai kuma har Makka zanje, zan siyo muku kallo-kallo da kuma  Kazar gwangwani da Raƙumin gwangwani, har da ma ƴar tsana mai magana" haka take ta faman yi wa mutane alƙawari manya da yara.


Baba Salame ce ta ce"dan Allah Inna Gaji ɗan tsumman kayan AZIZA a ragewa Kyauta ko kala biyu ne" kafin ta rufe baki Inna Gaji tace" sai kuma aka ce miki tsirara zamu tafi, wai meyasa ba ku da godiyar Allah ne" Baba Salame ta ce" a'a ba da wata manufa na faɗa ba, gani nayi zata zama ƴar birni me zatayi da kayan saƙi, da jar atamfa" 

AZIZAN BABA ta ce" zan kawo mata idan naje Makka irin wanda Baban birni ya siyo min da sallah" sai Baba Salame ta hau murna har da godiya ga AZIZA.


Inna Gaji ta bar cikin gidan ta shiga wani, haka tayi ta sallama har magriba sannan suka tafi.




Baba Tawaba kuwa sai da taga kowa ya tafi, ta shirya Baba na shigowa bayan la'asar ta ce "yauwa Malam zanje gida dan faɗa musu za mu koma Kano, wani satin" BABA ya ce" haba Tabawa idan mun koma gaba ɗaya kuma waza'a barwa gidan iye, ko kuwa so kike ya zama kango?"

Cikin mamaki ta ce"me kake nufi, ni zan zauna ko me?"BABA ya ce" to ai dai kinsan ba'a bar gida ba kowa ba, sannan ga su Aliya da Maimuna da jikokinmu duk anan, ina kike so su dinga zuwa saboda Allah" Baba Tabawa ta tasa dariya har da shewa, ta na yi wa BABA kallon sannu da ƙoƙari, ta ce "ahayye nanaye tabdijan wallahi Malam ba zan zauna ba, duk inda ka sa ƙafarka nan zan mai da tawa ƙafar, yo ni da ba ni da amfani, ban haihu ba sai na zauna saboda jikokin wasu, ai mai gindin haihuwa ya kamata ta zauna ta kula da ƴaƴa da jikoki amma ba Maryama ba" BABA ya ce "au yau kuma ni zaki ma ɗiban albarka Tabawa?" ta ce" kaga Malam babu yanda za'ayi ina gani zan bari a shiga haƙƙi na wallahi sai dai ginan nan ya ruɓe amma ba zan zauna ba" ta ja ƙofarta gararam ta rufe ta fice ta bar BABA tsaye yana mamakin wannan fitsara da Tabawa ta gama yi masa.



Sai da ta siyi tsaraba sannan ta je gidansu, iyayenta duk sun tsufa, Babanta ba ya ma iya tashi, ƙaninta Mu'awiya da iyalansa ne a gidan.


Tana shiga ƴaƴan gidan suka taro ta da murna,suna oyoyo Baba, Matarsa Marawiyya wacce take da tsohon ciki haihuwa ta tara zatayi ta washe baki, ganin Yayar mijin nata ta zo, da fara'a Baba Tabawa ta amsa, ta shiga ɗakin Iya(mahaifiyarta) ta na zaune tana jan carbi tsohuwa ce sosai ta ɗago ta kalli Tabawa, ta na murmushi, duk cikin ƴaƴanta tafi son Tabawa saboda ita ce Aƙima(mara haihuwa)ta ce" ke ce tafe uwata sannu da zuwa" Tabawa ta zauna kusa da tsohuwar ta ce "sannu iya ya gida ya girma?" Iya ta ce " da dama ya gidan fatan duk su na lafiya,ina AZIZAN BABA?" Baba Tabawa ta ce "lafiya lau ya jiki Baba" Iya ta ce" dq sauƙi" Tabawa ta ce "bari mu gaisa in dawo" ta shiga ɗakin Babanta, tsohon babu inda Baba Tabawa ta baro Malam Musa mahaifinta komai shi ta biyo, daga kwancen da yake ya sakar mata murmushi yana ɗaga mata hannu, da sallama ta shiga ta zauna kusa da shi, akan shimfiɗarsa ta ce "sannu Baba ya ƙarfin jiki" a hankali ya amsa ya na tambayarta gida da abokiyar zamanta, ta amsa da lafiya,lau sannan ta ce" daman za mu koma Kano da zama ne dake Aminu da AZIZA sun matsa, shi ne ya ce mu je muyi sallama" Babanta ya ce" ma sha Allah, ki ce za ki koma kusa da Zakariyya" Baba Tabawa ta ce " a Kano yake daman, na zaci a Kaduna yake ai" Baba ya ce "a'a yana nan a Kano cikin unguwar Ƴankaba, idan kinje  ki neme shi, banson ki zauna babu wani naki a kusa" murmushi Baba Tabawa tayi sanin Mahaifinta ya na kulawa da ita, dan yakan sa ƴaƴan ƙannenta su je su gano ta, da har kwana sunayi a gidan, to ana yawan faɗa akan AZIZAN BABA da yaran, shiyasa BABA ya hana zuwan masa gida.


Tabawa ta ce"in sha Allahu kuwa zan nemi gidansa" a hankali ya dinga yi mata nasiha da kuma mahimmancin haƙuri a rayuwa, ta na jinsa ta san akan ba ta taɓa haihuwa ba ne Babanta ya ke  mata wannan nasihar, ƙarshe sai ta fashe da kuka dan ita kaɗai ta san haƙurin da take da Inna Gaji, sama da shekara ashirin da aurenta.


Iya ce ta shigo ganin ta jima ba ta dawo ba, tarar da ita tayi ta kifa kanta ƙafaɗar tsohonta tana kuka tana tuno abinda Baba ya gama ce mata a gida kafin ta fito.

Iya ta ce "kai wai wannan ƴar ba za ki girmaba ne, ba daman ayi miki nasiha sai kuka haba" Tabawa ta ce" Allah Iya ina haƙuri a gidan nan, ba za ku gane ba ne" Baba ya ce "nasani ai rayuwa sai an ɗaure" nan ta ke sanarwa da iya zancen komawa Kanon da za suyi.


Daga nan ta koma ɗakin Iya,matar ƙaninta ta shigo sukayi ta hira, nan take jin za su bar gari, Marawiyya ta ce" ba dan maigidan bai son yara ba da kin tafi da Ummita can Yaya" Baba Tabawa ta ce"hmmm sai ka ce ba ni za ku iya yi"cikin fara'a Marawiyya ta ce "alkur'an da gaske nake miki" Baba Tabawa ta ce tunda bayaso ni nagode, Allah ya raya zuri'a ya yi musu albarka"amin suka amsa.


Yaran suna ta shan raken tsaraba, manyan kuwa duk suna waje ba ta same su ba, hakama ƙaninta Mu'awiya, daga nan ta je gidan ɗayan ƙanin nata, Ibrahim dan gidansa ba nisa da nan gidan, nan mata sami matansa Jummai da sadiya sukai ta hira, aka kawo mata tuwo dan magriba ta kusa, kaɗan ta ci, ta sanar da su za su koma Kano, suka ce za su sanarwa da Ibrahim, dan su san sai yaje har gidanta akwai ƙauna sosai tsakaninta da ƙannenta.

Sallama tayi musu ta tafi.


Inna Gaji na shiga ta sami BABA yana ta mita akan Tabawa, ta tambayi dalili ya faɗa mata abinda ya faru.


Inna Gaji ta ce" au dan ka ce ta zauna shi ne ta ce min haka lallaima matar nan" 

Sallama Tabawa tayi tana ajiye gyalenta kan igiya, Inna Gaji ta ce" Allah nagode maka, na haifa har ana cin arzikin ɗana, kuma jikoki tubarkallah maye ya ci kansa da kansa" AZIZAN BABA da take cin kantu ta ga yanda Inna Gaji take sai ta ji Baba Tabawa ta ba ta tausayi.

Ba ta yi magana ba ta tashi ta tura ɗakin Baba Tabawa ta shiga ta zauna sai ta sa kuka duk da bata gane abinda suke wa faɗa.....





 KANO 


"A'a a kwance na tafi, ƴan iskan yara sai shegen sa idon tsiya, za ku fita ko kuwa sai na ci ubanku" ta faɗa da tsawa, a tsorace suka bar ɗakin, pretty ta fashe da kuka, sanin tana cikin ɓacin rai Siyama ta ja ta tana faɗin "sorry stop crying,may be tana bad mood ne, mu bari anjima mu ƙara tambayanta" suka koma ɗaki, sallah sukayi suka yi jigum-jigum.



 Abdul ne ya shigo gidan, ganin babu kowa a parlour gidan shiru, ya nufi sama ɗakin Mami ya fara zuwa, ta yi wanka ta shirya, ta idar da sallar magriba kenan, ya shigo.

Sallama yayi yana zama, ta gama addu'arta ta ce"my son an dawo?" Abdul-azeez ya ce " eh Hajiya na gaishe ki, Mami gaskiya a san abinyi akan aunty Kausar" Mami ta ce "meyasa mi Kausar ɗin?" ya ce " ba wani abu ba ne kawai dai a yi ƙoƙari a cire mata wannan cikin yayi girma".Mami ta yi murmushi duk da agajiye take amma son da take wa Abdul ba zai misultuba ta ce" nima nayi wannan tunanin amma zuwa gobe za mu koma wajen doctor asan abinyi" ya tashi ya na faɗin "gaskiya ya dai kamata, bari in yi refresh kaina" ya bar ɗakin dan da yunwa ya dawo.


Sai da Mami ta sauko, sannan ta kira Munnir ta ce"kira min su pretty" da sauri ya koma, tare suka sauko,pretty ta koma ta raɓe jikin Siyama.Mami ta saki murmushi tana faɗin, common my pretty zo nan kinji"da sauri ta je tana jindaɗi ta rungumeta.


Sai ta saki jiki, suka hau hira da yaran kafin Daddy ya dawo,Abdul ne ya sauko cikin shigar crezy jeans da t-shirt mai matsewa, ya zauna dan jiran Daddy ya dawo, wannan sabon da ya riga yayi musu ne, babu mai yin dinner sai ya dawo.


Bakwai da kwata ya dawo, cikin farinciki ya shigo gidan, dan dawowar BABA kamar wani abu ne wanda ya fitar da rai lokaci ɗaya ya samu abun nan.


Taro shi pretty tayi hakama Munnir, sannu da zuwa Daddy suka faɗa a tare, ya amsa yana shafa kan pretty ya kamo hannun Munnir suka zauna.

Mami ta ce " yau ka jima Allah ya sa dai lafiya" Daddy ya yi murmushi ya ce" lafiya ƙalau wani ɗan abu ne ya tsaida ni, ya gidan" ta ce "normal" ya ce " okay let me fresh-up" ya wuce sama,Mami ta ɗauki briefcase ɗin da ya shigo da ita ta bi shi.

Sai daɗi take ji, za'a kama mata shi a hannu, tare suka sauko ya sanya doguwar jallabiyya maroon colour,mai gajeran hannu.

Dinning duk suka nufa, zama sukayi,Mami ta shiga serving kowa.


Babu abinda ke tashi sai ƙarar spoons, Daddy ya ce " yau ina cikin farinciki" Abdul ya ce "wow Daddy me yakawo hakan" ya faɗa yana gyara zama dan jin abinda zai ce.

Mami ta saki shu'umin murmushi tana alfahari da Mijinta dan shi ɗin mai nasara ne, duk abinda ya sa a gaba, in sha Allahu sai ya cimma burinsa.


Daddy ya ce " BABA dai ya amince za su dawo nan kusa da mu?".

Abdul-azeez ne ya ƙware, Mami kuwa a razane ta miƙe ta na faɗin" what?

 Daddy ya saki fara'a ya na jinjina kai, alamar tabbatarwa, da sauri Siyama ta miƙawa Abdul-azeez ruwa, da sauri ya karɓa ya sha.

Mami kuwa sai ta wayance ta wangale baki ta zauna ta na faɗin " BABAn ne ya sanar maka zai dawo?" Daddy ya ce " tabbas amma fa sanadin AZIZAN BABA"

Abdul-azeez da idanunsa har sun ji jar saboda ƙwarewar da yayi ya ɗago da sauri yana faɗin " it means har ita za'a dawo nan ɗin Daddy?" Daddy ya ce " ƙwarai kuwa" innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun" ya furta a hankali ya tashi ya bar area'n.


Mami da tuna da layar da boka gobe da nisa ya bata, ta ce "ina zuwa" ta bar dinning ɗin.

"Wallahi ƙarya ne ba su isa ba sunyi kaɗan"ta ɗauko laya ta sa a bakinta ta, zuciyarta nayi mata zafi.

Ta dawo da murmushi ta zauna ta kalli Daddy ta ce " ni kuwa Alhaji mai zai hana kabar su a can tunda naga wai kamar sunfi dacewa da zaman can ɗin ko?" 


Daddy ya ce " a'a Hadiza, su suka so dawowa yanzu kuma nima zanfi jindaɗi ina ganinsu kusa da mu" Mami ta kuma tauna layarta ta ce " gaskiya Alhaji ban amince ba,dan haka kabarsu a can da ya fi dacewa da su, banda ma rigima me za suyi a Kano saboda Allah" 

Wani abu ne ya ke ratsa zuciyar Daddy ya kalleta cikin sanyi ya ce..........





Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.