Free chapter · Read without an account
Chapter 22
CIWON YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 42-43
Murmushi Nur ta yi batare da ta sani ba, duk da cewa ta juyawa Bilkisu baya amma ta gane Nur murmushi take, dan haka ta shiga tunanin yadda al'amuran zasu kasance domin da alama Nur tana son Poul Bata kula zuciyarta ne sabo da ganin bazai yuwuba. Zuwa can Bilkisu ta ji tsayuwan mota, dan haka ta kalli Nur adaidai lokacin da Nur take cewa "Aunty rufe Ido gashi nan" Batare Da Bilkisu tace komaiba ta rufe idonta, Waigowa Nur ta yi taga idon Bilkisu a rufe, dan haka tai saurin shigewa bayi, tana turo kofar r Abdallah na buga kofar tare da Sallama a bakinshi, buguwa yayi tayi har ya gaji ya wuce, sannan Nur ta fito ta nufa kofar afalo, samunshi ta yi zaune afalon suna gaisawa dasu Mamy, bayan sun gaisa tace "Yaya ina bayine" Cikin sakin fuska yace "Nayi tunanin ma bakwa dakinne, Ina Aunty tamu ta shirya dai ko?" Karyar da kai Nur ta yi sannan tace "Bata tashiba in je in tasota?, Cike da mamaki yace "Kar dai Abdallah be sanar mata da maganar zuwa asibitin ba"
"Ya gaya mata, harma tace zan rakata, in tasota ta yi wanka?" Agogon dake daure a kan hannunsa ya kalla, sannan yace "Yanzun har saina jirata ta yi wanka? Zanyi latti ai" Mikewa yayi tare da saka hannu cikin aljihu ya ciro kudi ya mikawa Nur tare da cewa "Ki tasheta, in kunshirya sai ku wuce, amma kuna isa kimin waya, zan hadaku da likitan dazai dubata."
Cike da gamsuwa Nur tace "To" Saida ya fice sannan ta koma daki, inda ta samu Bilkisu ta gama shiryawa, dole suka dan tsaya suka bata lokaci sannan suka fito suka wuce, kamar yadda Bashir ya ce haka suka yi, bayan an gama mata gwajegwajen da za'a mata aka sallame su, Har zasu fita Bilkisu tacewa likitan "Ba wani magani da zaka rubuta mini?" Dagowa yayi ya kalleta sannan yace "Bashir zai taho dashi" Cike da gamsuwa suka fice, sannan suka wuce asibitin da Poul ke kwance.
Duk su biyun sanye suke cikin babban hijjabi har kasa, saidai ita Bilkusu tasa jibgigiyar rigar sanyi ta ciki, dan haka tayi katuwa, number Zainab tasa a wayar Bilkisu ta kira, bayan ta dauka ta sanar da ita gata a sibitin, nan danan kuwa Zainab ta fito cike da fara'a, Hannun Nur ta rike yayin da Nur Kuma tai saurin roko hannun Bilkisu duk da cewa bata jin karfin jikinta a haka suka tafi, Mamma ce kadai a dakin, tana Zaune gefen Poul tana mishi fifita, ganin shigowan su Nur yasata dago tana musu sannu, Zainab ce tabawa Bilkisu kujerar da ta tashi, ita da Nur Kuma suka tsaya a tsaye, ciki da fara'a Zainab kecewa "Mamma ki gaya mishi ga Nur" kallon Mamma Nur ta yi, itama tana sanye da hijjabi ga carbi nade a hannunta, sunkuyar da kai tana mamakin ganin mamma cikin damuwa, kenan duk da Wulakancin da Poul din yake mata tana sonshi a haka yanzun, muryan Mamma taji tace "Poul!" Batare da ya bude baki ba ya amsa, dan haka ta sake cewa "Ga Nur tazo dubaka" Cikin Sauri ya bude idon tare da rarraba su, zuwa can idonshi ya sauka akanta, tana tsaye ta dafa kujeran da aunty ke Kai, gaidashi Bilikisu ta yi ya dago mata hannu, Daker Nur ta iya yi mishi ya jiki, sannan ta sunkuyar da kanta kasa, nan Mamma ta fara basu labarin ciwon sh,i inda ta alakanta abin da rashin cin abinci ne, shiko Poul tun daga lokacin be sake rufe Ido ba, lokaci bayan lokaci Yana kallon Inda Nur take dan haka ta kasa sakin jiki a wurin, domin gani take ya hanata sakat da kallonshi da baya karewa, Zainab na Murmushi tamai ta yin cin abinci yace a'a. Shiru wurin yayi zuwa can Zainab ta nufa kofar fita tare da Kiran Mamma suka fice tare, ganin haka Bilkisu ma ta mike tare da cewa Nur "In kin gama ina waje kiyi sauri Amma." Kamar Jira Poul yake Yana ganin fitan Blikisu yayi ajiyan zuciya tare da waigowa ya kalleta, har yanzun tana rike da saman kujeran da aunty ke kai. Hannun sa ya miko mata tare da cewa "Rike ni in tashi" Yadda take haka take har yanzu bata bata motsaba, dan haka ya kara miko hannun tare da cewa "Dan Allah fa!" Wannan karon dagowa ta yi ta kalleshi sannan ta sake sunkuyar da kanta kasa, ganin haka ya sa ya maida hannunshi tare da cewa "Washh" sannan ya dubeta yace "Haram ne ko? Babu kyau?" Batare da ta dagoba ta daga kanta alamar eh, dan haka yayi murmushi sannan yace "Tam idan Helen ta dawo zata dagani" Wannan karon yi tayi kamar batajiba, zuwa can taji ya sake cewa "Ita ta gaya miki banda lafiya?" Wannan karon ma dai kai ta daga, dan haka ya sake yin mirmushi sannan yace "Ta gaya min abin da yayanki yace, amman yanzun ansan kinzo?" Bata saba karyaba dan haka ta girgiza kai alamar a'a, ajiyan zuciya yayi sannan yace "Na gode" Shiru suka sake yi zuwa can yace "Anjima in zakiyi waya dani? in kira number gidanku da wayar Helen? Tunda ke nace ki kirani kin ki" Can kasa makoshi tace "Wacece Helen?" Lumshe Ido yayi duk da cewa can kasa tayi maganar amman ya ji me tace sabo da Yana kallon bakinta, dan haka yace "Na manta ta canza suna ko? meye sunan ma?" Wannan karon kawar da kai Nur ta yi sannan tace "Zainab" jinjina kai yayi sannan yace 'Baki amsa ba min tambayar da nayi mikiba, idan na Kira zakiyi magana dani?" Tsintan kanta ta yi da daga Kai, Dan haka ya lumshe Ido tare da cewa "Na gode, kuje tunda kince ba'asan kinzoba, waccen wacece kuke tare?" Kawar dakai Nur ta yi sannan tace "Matar Yaya na ne0"
"Bashir?" Ya sake jeho mata tambayan, kaita girgiza tare da mamaki ta Yaya aka yi yasan sunan Bashir, bata rufe bakiba yace "Wadda aka yi baki kwanaki Abdallah ko?" Kai ta daga har yanzun da mamaki akan fuskarta, ganin wurin ya sake yin shiru ta juya tare da cewa "Allah ya sauwake" Saidai harta fita bataji ya amasa.
Tare dasu Mamma ta samu aunty Bilkisu, sallama suka yi suka wuce, bayan sun dawo gidama Nur kadai taci abinci, Bilkisu ko kudundunewa tayi sabo da sanyin Dake damunta, Nur ko ta kasa cire fuskar Poul a zuciyarta, tun da ta dawo tunashi take a lokacin da yake miko mata hannu. Misalin 08:00pm Bashir yazo gidan, dan haka Nur tanajin sallaman sa ta fice, acikin dakin Mamy ta aameshi suna gaisawa da Mamy, zama ta yi bayan sun gama gaisawa da Mamy ya juya ya kalli Nur tare da cewa "Ya mai jikin?"
"Da sauki" Nur ta fada alokacin da Mamy ke cewa "Aikuwa ita za'a tambaya mai jiki, tunda sunce kwana take amai, ko dai yau zata koma dakin Auntyn ku ne?" Cikin Sauri Nur tace "A'a gaskiya, idan Kuma hakane saidai mu koma tare." Mamy ce tace "Ai saikuje taren, acan din zaifi, dan wani lokacin kila bazaki tashiba bare ko taimaketa."
Bashir ko tun da Nur tai maganar yabita da kallon mamaki tare da cewa, "Lallai Nur kina yaudaran kanki, wato bazata tafi ta barkiba, yanzun idan mijinta ya dawo fa?" Jimmm Nur ta yi zuwa can ta dago tace "Dama Abba yace su zauna anan"
Wannan karon dariya Bashir yayi adaidai lokacin da Aunty ta shigo, ganin Bashir nata kyalkyata dariya tace "Bashir ya samu mugunta kenan?" Mamy ce tace "Shi da Nur ne, abun da ya faru ta gaya mata itama dariya ta yi tare da cewa ai Nur babu komai cikin kanta sai kuruciya, lokaci kadan-kadan take da hankali, ai ranar da ya dawo ko kwana daya bazai karaba zai dauki matarshi, sai kinga yadda ya fitineni shekaranjiya da daddare, tsakar dare fa wai ya kirata bata dagaba" Bashir da Nur ne suka yi dariya yayin da Nur ta karashe dariyar da cewa "Allah yasa ya dade acan, walllahi gidan yanxun yafi Dadi" Itako Mamy kawar da kanta ta yi tare da cewa Bashir "Ka amso maganin dai ko? Sunce likitan yace Kai zaka taho dashi." Ledan dake gabanshi ya jawo ya mikawa Aunty, yayin da ta shiga dubawa, tana duba maganin ta dago cike da murmushi tace "Ina sakamakon to?, Hannun yasa a aljihu ya ciro takardar ya mikawa Aunty, budewa ta yi tare da cewa "Ma sha Allah, Alhamdulillah, ai ni dama nacewa mijinta cike gareta, yana min musu" Murmushin Bashir yayi tare da kawar da kai, itama Mamy godiya tawa Allah afili kuwa cewa ta yi "Allah ya rabasu lafiya, sannan ta mike ta ta fita adakin. Itako Nur sunkuyar da kanta ta yi fuskarta cike da murmushi, acikin zuciyarta take cewa "Lallai Aunty Bilkisu ta iya wayau, hiranta da kawarta Madina ne ya dawo mata, zuwa can ta yi dariya tare da mikewa, tana kokarin fita Bashir yace "Aunty ki bata maganin ta kaimata, ko wanni akwai yadda za'asha a jiki, laden aunty ta mikawa Nur har ta kusa kofa Aunty ta sake kiran Nur, takardan dake hannunta ta mika mata tare da cewa "Har takardan ma kai mata, yaran zamani kila har toho zata yi ta nuna mishi" dariya Nur ta yi sannan ta fice a dakin ko da Nur ta kaiwa Bilkisu tashi ta yi tasha magungunan sannan ta dauki takardan ta aje gefenta, kafin wani lokacin bacci ya dauketa, Nur ko tana ganin Bilikisu tayi bacci ta dauki wayarta sabo da yawan kallon Number Poul da take jikin katinsa tuni ta haddace number, bayan ta saka Number kasa dannawa ta yi domin wata zuciyar sosai take kwabarta, zuwa can ta tsincikanta da dannawa, saidai ta kasa sawa a kunnenta, muryansa tajiyo duk da cewa wayar na nesa da kunnenta, Jin yadda yake Kiran sunanta yasa ta nufa kunnenta da wayar, ji ta yi yana cewa "Nur bakya jina ne?" Can kasan makoshi tace "Ina ji" Ajiyan zuciya yayi mai karfi sannan yace "Na gode da kika kirani, tun dazon nake dakon kiranki, domin na kasa bacci sam, ni kadai nasan irin radadin da nake ji azuciyata, awannan karon ji tayi kalmar Bata mata dadiba, Wai zuciyarshi na mishi radadi, tsintan kanta ta yi da cewa "Dama zuciyar ce ke ciwo?" Lumshe Ido Poul yayi sannan yace "I ta tafi komai damuna Nur" juyawa ta yi ta kalli Bilkisu Dake bacci sannan tace "To asibitin baka gaya musu bane ai da sun baka magani" Ajiyan zuciya yayi sannan yace "Basu da maganin shi Nur, na riga na gama yankewa kaina hukunci, babu wani magani da zaiyi tasiri ajikina, domin kunar da zuciyata take min kece kadai maganinta, na tabbatar da hakanne bayan ganin ki da na yi dazon, tun daga lokacin naji na samu lafiya, yanzun haka Ina gida tun dazon nake kallon wayar, kiranki kawai nake jira, na gane kece maganin ciwona.
Wannan karon Nur batace komaiba, bayan tsawon lokaci yace "Bakice komaiba?" Can kasan makoshi tace "Ai Gashi nakira." Cike da murmushi yace "Na gode, amman kinsan menene nakosa? Burina inga kinzama tawa, kuma jikina na bani hankalina bazai taba kwanciyaba sainaga na mallakeki, bana yin sekon daya batare da na tunaki ba, Nur kina ganin idan nazo gidanku za'abani auren ki?
Shiru ta yi batace komaiba, domin gabanta faduwa yake sosai, "Nur kinyi shiru bakice komaiba" Tsawon lokaci suka dauka batare da yaji tace kalaba, dan haka ya canza tambayan da cewa, "Nur in tambaye ki?" Can kasa-kasa tace "Umm" Ajiyan zuciya yayi sannan yace "Kina so na?" Shiru yaji tsawon lokaci, zuwa can Kuma yaji kamar tana kuka, dan haka yace "Kuka kike yi?" Wani abu Nur ta hadiye mai zafi awuyanta tare da share hawayen da ya fara zubo mata, Bayan shiru na wasu lokaci yace, "Gobe zanzo wurin Babanki kamar yadda kikace abaya..."
Katseshi Nur ta yi da cewa "Karkazo dan Allah"
Saboda me? Ina ce wancen ranar kece kikace min inje wurin Baban ki?"
"Yanzun nasan bazai yadda, kuma Yaya Bashir yamin gargadi sosai, bazasu yadda ba nasani."
Shiru yayi tsayon lokaci, zuwa can yace "Inda ace ni musumine kina gannin zasu amince su bani ke?"
Eh Nur ta fada a hankali, dan haka yace shikenan, ki kwanta kiyi bacci karki damu kinji?"
Ahankali ta amsa da "To" Jin yana Shirin kashe wayar tai saurin cewa "Karka kira wannan wayar na matan Yaya nane." Murmushi yayi tare da cewa "Bazan kiraba ai, amma dan Allah gobe ma ki kirani" Amsawa tayi sannan ta kashe wayar. Washegari tun da asuba Bilkisu ta fita neman abincin sabanin da da bata iya cin komai. Sannin lalurarta yasa aunty fitowa ta dama mata kunnum tsaniya, nan falon ta zauna tasha tai gyatsa, sannan ta iya yin sallah, da rana iyayen Aunty Bilkisu sukazo gidan duba jikinta, sosai tai murna da zuwan su, lokacin da zasu tafi gaba daya su suka fito rakasu har bakin mota, bayan sun zauna a motar ne kishiyar Maman Bilkisu tacewa Bilikisu "Toh Bilki ki dinga lura da cin abinci, Allah ya raba lafiya" Jimmm, Biliku ta yi kafin tace To kawai sannan tai saurin juyawa cikin gidan kamar zata yi kuka, Mamy, Aunty Saratu da Nur kuwa a tare suka dawo cikin gida, afalo Nur tabar su Mamy ta nufu daki, tana shiga ta samun Bilkisu ta yi zaune a bakin gado, kwalla cike daf da idonta, yayin da takardan da ta kawo mata jiya yake rike a hannunta, tsaye Nur ta yi tana kallonta, ganin kafufuwan Nur yasa Bilkisu dagowa ta kallli Nur a daidai lokacin da hawayen da suka cika idonta suka gangaro zuwa kumatunta, hannu tasa ta share sannan ta mike tsaye tare da cukurkude dakardan tana ya mutsata cikin hannunta, cikin yanayin dake nuna tana cikin tashin hankali...