Free chapter 路 Read without an account
RAFEEQ Page 3
*RAFEEQ....*
*PAID BOOK....* #400
*HAJJA CE* 馃憟
Da
*ASMY B ALIYU*
*Page 3*...
茒aure da milk 蓷in towel ya fito a 茩ugunsa yana sake sharce ruwan da yake kwance a saman fuskarshi, kai tsaye cloth set nashi ya nufa ya zuge murfin wardrobe 蓷in yana san tantance wa蓷anda zai sanya. Wa蓷anda suka kwanta a cikin zuciyarsa ya 蓷akko domin ya da蓷e beyi irin shigar ba. Gefe bed ya ajiye kafin ya isa wajan mayukansa masu matu茩ar kyau da gyara fata, jikinsa ya shafe dasu sannan ya mi茩e yasa kayan. Shigar riga da wando yayi na farar shadda wacce aka yi masa 蓷inkin zamani masu gajerun hannuwa, ya janyo hularsa zannah bukar ba茩a ya 蓷orata akansa tare da isa wajan madubi yana gyara botir 蓷in gaban rigarsa. Tsayawa kawai ya yi yana zubawa tsari da kuma kamala irin wacce ubangiji Allah ya zuba masa, yasa hannu yanajan dogon karan hancinsa da ya 茩ara 茩awata kyaun fuskarsa sai wani bu蓷e idanuwa yake kamar mai san gano wani abu a cikinsu. Rafeeq Habeeb Gwarzo kenan matashi mai ji da ta茩ama, uwa uba kuma kyawun da Allah subahanahu wa ta'ala ya zuba mishi. Sai dai abinda yake matu茩ar bashi mamaki shine yadda yaga Maimoon Gwaro batayi masa irin soyayyar da yakeji a cikin zuciyarsa, kallansa takeyi tamkar yadda take kallan su Shaheed Gwarzo da suka fito ciki 蓷aya. Juyawa ya yi a hankali ya zaro takalmi yasa ya 蓷auki car key yafito. Kai tsaye wajan tsaleliyar motarsa ya nufa wacce Alhaji Mustapha Gwarzo ya sissiya musu, tashi black marsandi ta Shaheed kuma white sai ta Maimoon red color yayin da Mubarak sai ya dawo za'a bashi tashi. Yana 茩o茩arin shiga yaji zazza茩ar muryarta mai sauke masa duk wani noti dake 蓷aure a jikinsa. Kallonta yake da dukkan nutsuwarsa har ta iso gabansa idanunshi suna zagaye jikinta. Sanye take cikin doguwar riga armless tayi matu茩ar kar蓳ar surar jikinta, kanta da hula kamar net ana hangen tarin gashin dake kanta. "Yaya sai ina kuma?" Ya ri茩e murfin motar yana fa蓷in. "Unguwa." Wajansa taje itama ta ri茩e murfin motar tana le茩a ciki, yadda kusancinsu yazo har yana jin 茩amshin turaren jikinta yana shigar masa cikin kai ne yasa shi fa蓷in. "Kina da sa茩o ne?" Maimoon ta dago tare da kallansa da manyan idanunta farare tas tace. "Naga kasha kwalliya kamar wanda zashi ta蓷i, da alamar Auntyn tawa 拼ar Nigeria ce, ko itace wacce naganku tare?" Cikin ha蓷e rai Rafeeq yake kallanta yana 茩o茩arin shiga cikin motar ya zauna yake fa蓷in. "Idan itace menene?" Maimoon ta samu kanta da ha蓷e rai, cikin yatsina fuska take fa蓷in. "Batai min ba tun lokacin da na ganku tare, haba Yaya duk macen da zaka aura karka bari idanunta su bu蓷e da zuwa irin wajajan nan indai ba matarka bace ta aure. Kawai ni yarinyar batai min tun kallan farko dana ganku." Kallanta ya yi sosai yaga dagaske take maganar, sai da ya murza key a jikin motar yake cewa. "Waye ya za蓳ar miki Abdul-Wahaab?" Tambayar tazo mata a wani irin yanayi, ta turo baki tana wani kifta idanuwa take cewa. "Wahaab daban ne Yaya Rafeeq, ita kuma waccen daga gani bata da kamun kai." Cikin tsuke fuska ya kalleta zai yi masifa sai kuma yaji ya kasa, yasa hannu zai rufe motar Maimoon ta ri茩e tana cewa. "Dan Allah karkaje wajan yarinyar nan baku dace da juna ba sam." Fizgo 茩ofar yai ya kalleta yana cewa. "Kema ai baki dace da wanda zaki aura ba, so kowa yaje yaji da matsalarsa bye sai na dawo." Yaja motarsa da 蓷an karfi har Maimoon tana saurin yin gefe guda ganin kamar zai mangareta. Har sai da ya fice daga cikin gidan sannan ta juya ta koma ciki tana jin takaici indai har wajan wannan yarinyar zashi, bedroom ta wuce ta 蓷auki wayarta tana daddanawa. Rafeeq na fita kai tsaye wani store ya shiga, kayan masarufi yasa aka jidar masa yasa a booth 蓷in motarsa sannan ya nufi gidan marayu dake nan cikin 茩waryar Kano. Daman tun ba yanzu ba Rafeeq yake zuwa kai taimako hakan yasa duk masu gadi da masu kula da gidan suka sanshi, ko baya cikin 茩asar yana turo da ku蓷i ayiwa marayu abinda sukafi bu茩ata. Mutum ne shi da abin hannunshi baya rufe masa ido, yana matu茩ar jin da蓷i a duk lokacin da yayi irin wannan zuwan, yakan ji duk wata damuwa tashi Allah yana yayewa. 苼angaren bebaye masu bu茩ata ta musamman aka fara rakashi, cike da tausayawa ya dinga shafa kawunansu yana sake godewa ubangiji da ya kaishi hannun Alhaji Mustapha Gwarzo, banda haka yasan shima da Allah zai iya kawo gidan nan yayi rayuwa makamanciyar da yaran nan keyi. Sai da aka rakashi ko'ina sannan ya fito ya bada umarnin sauke kayan dake cikin booth tare da yin al茩awarin kawowa yaran da suke under 6years suturar sakawa dan ya lura tayiwa yaran karanci a jikinsu. Yana cikin tuki yaji wayarsa na ringing, janyota yayi daga inda ya ajiye yana dubawa yaga mai kiran nashi, kamar bazai 蓷auka ba sai kuma ya daure yai daga batare da yace komai ba. "Jan aji ma da yazo wajanka sai da ya sara maka, uhmm kana ina ne?" 茒an yatsina fuska yayi kamar tana kallansa yake cewa. "Tuki nakeyi." Yanayin yadda taji yana maganar ne yasa ta gane baya cikin walwala, Zee Leeman ta kuma kashe murya cikin san janyo hankalinsa take cewa. "Ina Ado Bayero mall ko zaka 茩araso?" Kalaman Maimoon ne ya fa蓷o masa inda take nuna masa cewar ba ajinshi bane yawan fita da mace zuwa wajan sha茩atawa wacce ba muharramarsa ba. Sai dai kuma shi mutum ne mai yawan san fita outing, yana so yaga yana zagawa cikin duniya dan ya dinga ganin yadda rayuwa take garawa. Karya kan motar yayi yana cewa. "Ganinan zuwa." Katsewa sukayi yana wani rintsa ido gani yake kamar bayajin shawarar 拼ar uwar tashi, sai dai kuma in har beje wajan Zee Leeman 蓷in ba to babu wani waje da zashi, gida ne kuma ko yaje babu abinda zai yi a can 蓷in. Tunda ta hangoshi takejin wani irin farin ciki yana cika mata zuwa, lokaci 蓷aya kuma ta mi茩e tare da nufowa inda yake. Kallan juna suka tsaya yi Rafeeq ya 蓷age mata girarsa guda 蓷aya alamar "Lafiya?" Handbag suwaga 蓷in dake hannunta ta janyo tare da rungumeta a kirji. "Muje ko?" Ta fa蓷a tana nuna masa hanyar shiga wajan wasanni, shi yayi canji sannan suka biya suka shiga gurin.
Kai tsaye wajan zama suka nema suka zauna, Rafeeq yana kara蓷e idanuwansa a wajan tamkar wani bako. Zee Leeman da takejin wata irin soyayyarsa tana taso mata takai hannunta tare da ri茩o nashi, kallanta yayi sosai kafin ya janye idonsa acikin nata idon yaji tana fa蓷in. "Na茩agu naji kace zaka fara zuwa gidan mu dan su san da matsayinka a family 蓷in, amma kai sai naga kamar baka shirya aure na ba why?" Ya sauke wani irin numfashi yana zare hannunsa daga cikin nata yake cewa. "Zee har yanzu kin kasa gane inda zuciyata ta dosa, please mubar maganar auran nan yanzu." Cikin yanayin damuwa take sake kallansa, tana so ta gane sonta ne bayayi ko kuwa dai shirya yin aure yanzu ne baiyi ba? Gabaki 蓷aya bata gane inda zuciyarsa ta nufa akan ala茩arsu, baya mata wulakanci haka kuma soyayya yake yi mata tamkar yadda saurayi da budurwa keyi. "Kasan ni macce ce Rafeeq, rayuwata kalilance zan so ace duk wannan zaman da mukeyi da kai ya zama mata da miji ne mu. Dan Allah baby ka shirya ka fara zuwa gidan mu su Abba su san da zamanka." Kallanta yake yi cike da tausayawa, yana jin mugun nauyinta akan yace ba itace a cikin wannan zuciyar ba. Maimoon gwarzo ta riga ta gama cika xuciyarsa da soyayyar ta"Kayi shiru baby kodai baka sona ne?" Ya kalleta da mayun idanunsa masu kama da madara farare tas dasu yake cewa. "Tun farkon ha蓷uwar mu dake nace kidena yi min maganar aure saboda bana so kiyi tunanin zan aureki, Zee bana san yaudara a cikin tsari na shi yasa nake ce miki idan har kin samu wani wanda hankalinki ya kwanta dashi toh ki amince masa kiyi auranki. Zuciyata tana cikin wani irin yanayi wanda na rasa ta yadda zan 蓳ullo masa. Kiyi min addu'a kawai Allah ya cika min buri na." Hawaye suka fara zirarowa daga cikin idanunta, yana kallanta ta gefen ido haka kuma yana jin kukan nata har cikin jininsa saboda shi a rayuwarsa baya kaunar yaga ana kuka nan da nan yake jin tashin hankali. "Kana tunanin idanuwana zasu iya ganin wani bayan kai? Rafeeq idan wata ce a cikin zuciyarka ka gaya min hankalina zai fi kwanciya, idan kuma wani hali ne nawa da baka so ka sanar dani sai na gyara, wallahi zan gyara Rafeeq indai akan farin cikinka ne." Wani irin karaya zuciyar Rafeeq tayi lokaci 蓷aya, yanzu ya zaiyi da Zainab idan ya fallasa mata sirrin dake cikin zuciyarsa tabbas zai iya karya zuciyarta. Shi yasa tun farko bai so wannan kusancin nasu da ita ba, bai so tafiyar su ta kawo har nan ba wanda duk laifin Shaheed Gwarzo ne da ya ta cusa masa ita alhalin shi ba itace aransa ba. Haka kuma baya so ya cigaba da 蓳oye mata, dan idan aka cigaba da tafiya a haka zatayi wani tunani na daban akan wanda ke ransa. Damke hannunsa yayi yana kallonta da dukkan idanunsa, wani irin bugawa zuciyar Zeey Leeman keyi a wannan lokacin tana jin bugawar da zuciyarta takeyi har cikin tafin 茩afar ta. A hankalin ya kamo hannunta abinda bai ta蓳ayi ba iya tsawon rayuwarsa wato ri茩e hannun Zeey 蓷in. Runtse idonta tayi zuciyarta na bugawa, fisge hannunta tayi lokaci 蓷aya ta fashe masa da kuka tana girgiza kai take fa蓷in. "Dan Allah karkace banice a cikin ranka ba Rafeeq dan zan iya mutuwa, ka taimakeni karka fa蓷amin hakan dan Allah." Ta fa蓷a tana 茩ara sakin wani kukan da Rafeeq Gwarzo keji har cikin zuciya da ruhinsa. Dukan su abu 蓷aya suke nema sai dai amman kowane nasa ya banbanta da na 蓷an uwansa. Zainab Liman tana sonsa wanda ya lura a shirye take da ta sadaukar da duk farin cikinta saboda shi. Yayin da shi kuma Maimoon Gwarzo ce acikin tashi zuciyar shekaru goma sha takwas a baya, wanda zuciya da gangar jiki basu ta蓳a gajiya da dakon su ba. Banbancinsu shine yana son Maimoon Gwarzo amman batama san yanayi ba saboda rashin nunawa da kuma furtawa. Yasan Zainab na tsananin sonsa da kaunarsa, sai dai shi kuma ba itace a tashi zuciyar ba, dan haka dukan su suna cikin matsala. Hannu yasa yana squeezing sumar kansa, gefe 蓷aya kukan Zainab na hargitsa masa lissafi. "Please Zainab goge hawayenki muyi magana." Ya fa蓷a sounding so very cool a cikin muryarsa. Tissue ta fiddo daga cikin handbag nata tana goge hawayen idonta still wasu na kara fitowa.....
#HAJJA CE 馃憟
#ASMY B ALIYU
#Rafeeq Gwarzo
#Zeey Leeman
#Team tagwaye Novels