Free chapter 路 Read without an account

39

by Hauwa A Usman 路 DAMA TA

*DAMATA*






         *Na*




*BATUL ADAM JATTKO*



*Gaisuwa da jinjina* *gareki*

*Biebie Isa*

*DAMATA*

*yana tafiya tareda* *ingan taccen shawaran kune keda Aunty Sis*

*Kaunan kuda karam cinku gareni babba ne*

*Adade anayi sai Gaskiya*


*Mn amir muna tare*



(Editing Mzz daddy)



*39*


*A*unty kirki kina bathroom ne shikenan idan baki fito dawuri ba wllh baya jimawa."


Da gudu yasake saukowa "pappa bari kaga Aunty."

Shiko Nabil bata suyake ba hankalin sa yana kan wayan sa inda suke cht da Sani akan binciken yakeyi shima 


Gudu dr yake sosai har yakara so dan yasan halin surutun su Kharat


Suna zuwa ko gaisawa bai bari sunyi baya nunawa Habiban pic din Fantau yace"tabbas kinyi magana da ita acikin jirgi dan haka nake son kigaya min, 

Abinda kuka tattaun da kuma inda tayi bayan fitan ta agunki kawai nake da daman wanan bayanan please."


Wanan tambayan nasa shiyabawa Habiba daman gane Nabil baisan mesuka firata da itaba kuma baisan inda tayi ba besan suna tare ba cikin dakiya 


 tace "awo wannan kake magana kwarai kuwa nayi mata magana ganin tunda suka shigo da yayanta ya ajiyeta yaje side dinshi sai kuka take ko da akazo tambayan meza akawo bata ko daga kai batayi ba shine naje wajen ta nake mata tambaya meyake faruwa amma ko kuffan bata cemin ba kuma mun rigasu sauka dan haka bansan inda sukayi ba."


Nabil wani k'ara yayi da yazame kasa ya dafe kansa idon sa yayi wani irin kadawa kamar ansa masa barkono matse idon yayi yana son hawaye su fito kozai samu saukin radadinda idon da zuciyar sa yake masa amma idon a soye yake daya daga ido ya kalli dr saida dr yaji gaban sa yafadi 

Cikin wani irin muryar wanda basu sansa da shiba yace "MD da kunsan wacece wanan yariyar awajena daba kubari ta yi wani wajen ba, da baku bari ta bata ba."


  Dr yace"matsayin ta kuma kace kanwar kace, ni narasa ina k'a samo ta bayan ni bansan ta cikin family kuba." Habiba tace niko abban Nol kallon sani nake mata, tamin kamada wata a maiduguri fa na manta inda nasan tane."


  Dr yace"niko ganin ta banyiba." Ajiyar zuciya Nabil ya sauke yace." amma kikace tana kuka ko? 


 Habiba tace "eh kuma sosai."


  To me yasata kuka anya an mata alluran nan kuwa duk da Hadim tace anyi amma meyasa banje na binciki Dr Adegas ba? yace kai gwara da banje ba idan naje nasan sai naga gawar ta dan bazan kyaleta ba idan da anyi allura ina zata san ida take balle tayi kuka da sauri yada go yakalli Habiba yace" kiramin Adegas din."


  Murmushi Muktar yayi yasan za aje kan haka dan haka sai yakira Adegas tun zuwan su lokacin ma Nabil yana Rasha yace idan Nabil yazo duk juyin da zai miki kar kice bakiyi alluran ba kice kinyi.


  Jin haka ma yasa Adegas tabar gari tace sai ya huce ta dawo. 


   Habiba ta dauki wayanta ta dannan dialing ta sai suka gaisa tace" mata Shiddams yana son magana dake ta mekawa Nabil cikin kakkaurar murya ya tambaye ta tabashi amsa cikin tsoro kamar tana gaban sa tace tayi mata, wani irin cilli Nabil yayi da wayan atake yayi filli filla.


"kai kai kai saboda kai me kudin banzane zakamin asarar wayan matata." 


  Habiba tace "ran sane ya baci amma waya isa yacewa d'ana me kudin banza ne bayan da gumin sa yake aiki."


  Nabil ganin baza su taba gane wacece Fandau awajen sa ba shiyasa suke masa wanan abin dan haka ya mike ko yara da suke faman yi masa surutu bai kula su ba ya fice yana hada hanya kamar me jin bacci, ganin Nabil bazai iya tukin ba yasa ya fito da wayan sa ss dinshi ya kira yace yazo yana gidan Dr na Asokoro, Dr ya fito yace bari nayi driver din ka ko, bude mota yayi yashiga baiyi magana ba bayan sun fita a gate Dr ya kalle shi

 yace" ina muka dosane dan gidajen Nabil a ABUJA suna da yawa nan ma kinyi masa magana yayi shide wuse yayi da shidan yaga yafi sauka acan.


  Sunayin parking me gadi ya washe baki yallabai saukan yaushe yau banga labari. ba bansan da zuwan kaba."


 Nabil bai masan yanayi ba sai Dr "yace" baba zuwanne na bazata." Ya bude musu suka shiga da gudu yazo zai budewa Nabil mota kafin ya karaso ma ya fito, yace yallabai barka da zuwa, kansa adafe Nabil ya shiga cikin gidan main parlour ya zube dukda da dan kuransa amma akasa ya zube wanda da dane akwai ma aikatan da ake turowa a cikin gidan gomnati villa sukula da gidan kafin ma ya shigo gidan zai taddasu Dr yace" ni zan koma dan naga kaima ko alluran kin maganan aka maka." Kirane ya shigo wayan sa ya dauka daker dan ya kashe sauran layuka a wayan sai na wanda suke masa bincike akan Fandau kawai yabar inde yaji kira to sune.


  Ya daga wayan "sir mezai hana a yada photon ta asa wasu kudade wllh ayau za aiya samun ta." Da kyar Nabil ya bude baki yace" ka fini sanin hakane, to tafi karfin a bugata ya zama wanda bai isa bama ya kalle ta." 

"Sorry sir Dr saida yatsaya yaji kwakwaf yasa kai ya fice yana dariya wai Shid ya zama haka kuma akan mace lallai ya yarda duk ajin maza su ba komai bane agun mata, Shiddams da manyan babes ke tsoron tun kara yake garari akan wanan yariyar tabbas alhakin tane da na cin zalin aure da sukayi yake dawainiya dasu."


   Fandau sai da Habiba tace "Anty kirki bude tukun ta bude.


"Aunty ya tafi? 

"ya tafi saide fa ya zama kalan tausayi."

Da sauri Fandau tace "meyasame shi? 

_Sai asannan habiba ta tuno ashe Dr ya hanata tacewa Fandau Nabil yana neman ta dan kar ta tausaya masa._ 


 Da sauri ta gyara zancen da cewa

"wai Hadim ce bata da lfy." A nan Fandau ta sake tabbatar wa kanta dasanin Nabil komai ya faru ALLAH ka ciremin son wanda besan da daraja taba na dena wahala akan son maso wani dama bai taba furta yana sona ba ya lallaba ni ne kawai ya mori albarkatun jikina bata san afili take maganan ba saida taji Habiba tana bata baki sai cewa tayi "Fandau kin samu dama da shaidu masu karfi amma kika bari damar ta kufce miki meyasa da yace zai iya baki komai har gidan sa na saudia meyasa baki karba ba da yazama shaida awajen ki." Dr yace" kota karbi gidan bai zame mata shaida ba dan kowa yasan Shiddams da kyauta, ai shaidan ta daya shaidun aurenta magabatan ta tunda ta saki wanan damar ko ai dole, tunda bata samu wanan gatan ba bata da wani dama yanzu ai da agidan su gaban iyayen ya aureta ba zai mata hakaba marar tunani me kwakwalwan kifi, kuka yanzu kika soma ai 

sai asannan Fandau tasan da zuban hawayen da yake bulbula a idonta da ya jika mata gaban riganta. Da gudu ta sauka tayi dakinsu.


*BAYAN KWANA 2* 

Nabil duk wani hanya da zaibi yaga ya sameta cikin *kwanakin nan 2*, amma shiru ba labari idan yace zai yada pic dinta shine zai fi saurin samun ta amma hakan bazai yiwu ba yin hakan tamkar ya dauki wuka ne ya dabawa cikin sa dan asirin sa ne zai tonu, shiyafi son ya same ta yakai wa mama amasayin ya tsinceta ne daga baya sai yace yana sonta tunda dama yayi wa mama alkawarin zai kai mata ita da hannun sa 

gashi Ummi ta matsa masa akan maganan Hadim gashi shima jikin sa ba yajin dadi. Wayan sane yayi ringing yana dubawa Ummi ce ya daga "gamunan muna ABUJA awane gida kake? " wuse" ya bata amsa atakaice 

ba jimawa suka shigo Mala kaninsa wanda suke uba daya ne sai Hanif dan Ummi da ita Ummin.


Mai makon amsa sallaman nasu daga kai yayi kawai ya kalle su ya mike zaune yana matse fuska yanda kirjinsa yake masa ciwo da sauri Ummi ta karasa tana "subahanalla Nabil meya mayar dakai haka? kana ganin kanka kuwa yanda karame idanuwan ka sun sake fitowa meyake faruwa?

Nabil fad'awa jikinta yayi ya saki kuka Mala da Hanif sun tsorata basu taba ganin kukan Nabil ba sai yau kome yake damun sa abin babbane suma durkusawa sukayi agaban su cikin tashin hankali Ummi take tambayan sa.


 "Ummi kuskure nayi wanda bansan hanyan gyaran saba, Ummi zan gaya miki kadan daga ciki ke kadai nakeson gayawa, ke yakama ta kisani kirike min sirrina ki kuma yimin addua."


Kallon su Hanif yayi alaman su fice aiko suka fita. 


"Ummi na tsinci wata yariyar a saudia watanni 7 da suka wuce sai dana a cikin harami, tana gani na ta kira sunana tace min ita yar gidan Zannah Modu ce dan ALLAH na taimaka mata wata mata ce ta yaudare ta da sunan zata kaita tayi aikatau acan tasamu kudin da zata budewa Mamar ta ido shine ta bita saida ta gama tara kudin tukun sai matar ta gudu da kudin yanzu ta rasa yanda zatayi tazo gida, acikin harami take kwana abinci kuma tanayin bara taci shine da ta ganni ta ganeni.

Nima tana fadan haka na gaskanta ta dan kaman ta da Malam, nace zan dawo da ita shine tace idan tazo gida kishiyoyi mamar ta zasuce taje yawon karuwanci ne ta nemi alfarman na aureta inyaso nace nine nace ina sonta alhalin ansamu su rana da Shattema munsan bazamu samu juna ba shine muka gudu mukayi aure da ita, ganin bazan iya barin jinin Malam ya tozarta ba yasa nayar da dawanan Shawaran aka daura mana aure".


  Na yarda an daura mana aure da itane kawai dan darajan iyayen ta shine na ta fida ita London da zuman idan tasamu ciki idan munzo za afi barinmu mu zauna tare shine ni kuma gaskiya na kamu da son yariyar dan burin ko wace, amma kishin Hadim yasa dana bar yariyar na tafi Rasha shine ta kira wata kawar ta likita ta yiwa yariyar alluran zubar da ciki dana wanda zata manta komai nata ta aunota nan Ummi bansan inda zan samota ba Ummi inason yariyar idan bangan taba wllh akwai barazana cikin rayuwa ta." Ya sake fashewa dawani irin kuka.


  Itako Ummi kasa bakin magana tayi sai tafa hannu take da kyar ta samu bakin salati ni Hajara wannan zamani ita Hadim wacce iriyar macece da zata ce baza amata kishiya ba har ta illata yar mutane haka inda ba'a kishiya aduniya da uban ta bai auri uwar ta ba dan wata tatarar karewa ma ita me sunan kishiyar uwar tace, inda ba'a kishiya da ni kaina ba'a aureni na haifeka ta sameka ba nima wata na tarar duk da kai ma kanada naka lefin na boye mata musamman mu da ka gayamana ko da ka tashi daga saudia da kaitsaye gida ka iyoda ita da hakan bai faruba dan meza ka boyeta kace wani saita haifu gashi abinda ya janyo da wane ido zamu kalli Malam da Aisai mutumiyar arziki."

Nade Ummi tayi tayiwa Nabil fada 


_Shiko hamdala yayi ganin koyau Fandau tafito zai mallake ta basai_ _asiri ya tonu_ _ba, yaran su zauna a yaran Hadim din kawai shide_ _yakasan ce da Fatin sa sai yaji wani karfin guiwar nemanta dan yasan Ummi zatayiwa Abban sa bayani yanda zai_ _gane._


Ummi ta sake cewa 

"yanzu kenan tayiwa mutane asaran cikin wata 4."

"Ummi barni da ita na daga mata kafane dalilin cikin da yake jikinta ."


"amma inason ka janye kalman saki da kamata."


" shikenan yanda kikace haka za'ayi Ummina na maida da."


Ummi tace " yawwa sai kuma abuna 2 dole Malam da Aisa susani dan su tayamu adduan nemanta, sai kuma inason kai ma Baban ku yasani daga iya mu kar kowa yasani har sai an sameta kasan halin wanan Innar taku yanzu zata jakula komai." "to Ummi amma Ummi kimin alfarman koyawa Hadim hankali dan kiyaye gaba."


"Wane koyamata hankali zakayi bayan halin da take ciki ma ya isheta jiya wata kawar ta takawota ai bakaga yanda takoma ba ninan da niyar naci maka mutumci nazo sai na tadda lefinta yafi naka, saide ya fatime dole inaga itama tasani dan tananan tana fada baki da kunfa."


Mamar hadim kenan


"shikenan Ummi amma itama kartasan na maryar da Hadim din."


Ummi tace

"Bazata sani ba."



A ranan Ummi ta tasa Nabil a gaba suka koma. Alh Abubakar baban Nabil har marin sa yayi dan lefin shiya daurawa idan bashi yasakewa mace ba har ta isa tayi.


Shiko Malam lefin Fandau yagani dan a ganin sa Nabil taimakon ta yayi ma ai godiya dasa albarka ba irin wanda mama da Malam basuyiwa Nabil ba dan susan saboda su yayi.


Ko wacece wannan matar ta cucesu ta yaudari yarsu ta kaita har saudia. 


Malam ya dukufa addua sosai duk dama yanayi dan yana mutukar son Fandau.


Itako maman Hadim cewa tayi kawai taji tayi lefi amma bai kamata ya dauki Fujjirat ya kaiwa uwar kishiya ba a karbo mata jikar ta, tayi akira mata Nabil kinzuwa yayi sai ita ta taka taje gidan Nabil din amma security suka hanata shiga dan waya suka yiwa Nabil yace kar abarta.


Aiko baki da kunfa tasa Sudais ya juya da ita gidan su Nabil ta samu Ummi ta mata tatas tace takira Nabil din 

Nabil yana shiga ya gaida su "yace Mama ya mai jikin?


"lalle Nabil karena min hankali sai anan kake tabbayana ya mai jiki, aiko mutuwa tayi kaine sila tunda kai kamata duka ba kaga halin da take ciki ba yanzu tun yaushe tazo amma ko ajikin ka bakaje dubata ba."


"Mama inajin baki gama sanin abinda ita Hadim din tayi bane, ai gwara nida na daketa gashinan na bar miki ita kina kallon ta,

Itada ta tashi ba la'anta yar mutane tayi ba? ta kuma batar da ita, amma ina son idan kin koma ki gaya mata Wllh wllh darajan cikin da yake jikinta na kyaleta yanzu amma zata haifu zata ga yanda zanyi da ita, zuwa duba ta kuma karkiyi fatan wannan dan inhar zansa Hadim a idona to zan hallaka ta dan haka rashin zuwana rahama ne."

Kuka mama tasa tana nuna Ummi Hajara kina gani a gabanki dan da kika haifa a cikin ki yake gayamin wanan maganan?


Ummi itama bata ji dadin abinda yayi ba amma tasan halin Nabil idan ransa ya baci zai iyayin fin hakama dan haka tace "tashi katafi kafin ka rufe muda duka."


Cikin kuka Maman Hadim tace ni yaje ya karbo min jikata ya karbota kawai."


Har zai fita Ummi tace "kaje ka karbo Fujjirat."


Juyowa yayi ya kalli mama yace jikar ki ya wuce na jikin yarki idan ta sauka idan macce ta haifa inason asa mata Fatima idan kuma Namiji ne Abba inusa amma fa Fatiman da na fada kar ki dauka sunan kine tunda kema Fatime sunaki." 


Girgiza kai Ummi tayi tace "bance kafita ba." 


Yafice yana cewa danme baza ta barni da masifar da yarta ta jamin ba sai tazo tana min masifa 

Wllh in Hadim batayi furcin ba to wllh Fatima ta baiyana kafin haifuwar ta kai ko ta baiyana inde bata cikin haiyacen ta sai tayi zaman gidan yari baki koyawa yarki yand....... Ummi ce ta katse mishi maganan da jifansa dawani cup na glass sannan ya karasa ficewa "Yaya dan ALLAH kiyi hakuri ke kanki sheda ce akan yanda halin Nabil yake tun yana yaro idan ransa yana bace ba a masa magana bake ba koni idan na matsa wllh abin ba zaiyi kyauba."

"hajara ke sai ya miki ki kyale shi amma banda ni. A zaburi Hjy Fatime ta mike har da gudun ta tafita wajen a daidai inda zai shiga parlour Iya ta same shi ta baya ta fincikoshi "kazo ka gaya min matsayin y'ata awajen ka kuma ko a kotu sai na karbi dukka jikokina."


  A hankali Nabil yasa hannu ya kwace a hannu ta idon sa fes cikin nata sai kace a gaban abokin sa yake yace "matsayin yarki bata dawani matsayi a wajena sai dai idan ragowan sakinta kikeso zan iya bin umarnin ki a masayin ki na uwa a gareni in baki sakinta.


"Sai kuma batun yara kema kince jikoki, jika ko ba d'a bane ki bari me yaran tace a bata da bakin ta" Iya ce ta fito tana "Subahanalla Nabil ya haka" Ummi mari tafara zu bawa Nabil shiko Nabil nade hannunsa yayi a kirjin sa yana jin yanda Ummi take zuba masa marin, kanne sa dukka suka fito sai kuka suke dakyar Iya ta ja Ummi itako Mama zubewa tayi tana rinjin kuka

Nabil ficewa yayi ya fada mota driver yaja motocin security dinshi suka rufa masa baya suka fita cewa yayi airport zasuje dan shi gani yake kamar ABUJA ne zai bashi Fatin sa. 


*GIDAN DR MUKTAR*

"Aunty yanzu jibin zamu tafi kenan? 

"habiba tace insha ALLAH kirki ta Ghana zamu tashi saboda ke Dr ya sara tafiyan ta can dan a wanan kasan bazai ykwu mu tashi dake ba yanzu haka Ghanan ma a mota zamu tafi saboda Shiddams ya tsanata bincike."


"Aunty yanzu haka zankoma banje naga su mama ba."

"Toni Fandau ya zanyi ne nayi nayi dashi yaki, nace idan munje dake kisa nikaf har mufito a kallah de kinga mama zakiji dadi, amma sai cewa yayi ai baki damu da ita ba da baki barta ba, saide idan kezaki gaya masa kiji."


Fandau tace"ni kema kinsan ban isa ba jiya haka yace wa maimu me aiki kar ta karayin komai a gidan nan nice sabowar me aiki ni zanyi."


Dariya Habiba tayi tace"wai dan kikoyi hankali ne yace ko amma da nake tambayar sa yace yana sone kina dan mosa jikin ki kinga cikin ki ya shiga wata 6 dan kisamu sauki wajen nakuda."


Ko da zasu tafi kaduna barin Fandau sukayi da meimu suka tafi.


Shiko Nabil abubuwa ya kacabe masa ga yan kungiya sun matsa masa wata 2 bashi har sauran kun giyoyin sun fara kawo farmaki ana ta yadawa wai Shiddams yabar Chelsea fans dinsa da sauran mutane sun damesa a media ga zaryar hospital yake ma dan ba shida cikakkiyar lafiya kullum ciwon kai dana kirji yake fama dashi, kowane dr idan ya duba shi sai yace yasa wani abu ne a ransa wanda yafi karfin zuciyar sa idan bai cireba to yana barazana ga rayuwar sa aiko yan club din su sunajin haka suka zo tafiya dashi ayi jinyar sa acan yace a'a abu har ya kaishi ga kwanciya sosai.


*HADIM*


Ko makiyinta ya ganta cikin wannan hali zai tausaya mata "Mama yanzu Nabil din bazai zoba bayan ance yana garinnan Ummi yasani a blacklist bana samun sa mama kibari naje London din mana na same sa tunda kince yakoma."

Mama cewa Hadim tayi Nabil ya koma dan ta kwantar mata da hankali amma kullum zancen ta Nabil da kuma a karbo mata Fuj yanzu dai Ummi ta sa ankawo Fuj sai Nabil da take ta ambata wanda acikin asbitin daya ma suke akwance bata sani ba dan ita ma sosai take akwance kullum Dr suna cikin yimata nasiyar ta kwantar da hankalin ta saboda kwata kwata BP dinta baya sauka zai iya janyo matsala idan watannin haifuwan ta yayi idan zamu mata aiki dan....... 

"aiki kuma?

 inji Ummi da mama

Dr Hafeez yace ba na rubuta muku bayanan acikin katin da na baku ba amma kubini office na karamu ku bayani."


Ummi da Maman Hadim zaune gaban Dr Hafeez 

 Yace " yaka mata ku kula da halin da yariyar nan take ciki, yanayin cikin ya kamata a kula da ita sosai tunda ba haifuwa zata iyayi da kanta ba aiki za amata dan mun duba mugani kugunta bazata iya haifuwa ba sai de aciro to alluran da zamu mata idan lokacin yayi ba ayiwa me hawan jini dan zai iya barazana ga rayuwar ta ita kuma BP mai makon ya sauka kullum kara hawa yake....


 Mama kaseshi tayi da cewa aikin banza rashin sanin aikin kune na kasannan yaza ace bazata iya haifuwa ba itada ta haifi yan biyu ma lafiya haifuwa na 3 ace kugunta bazai iya haifuwa ba."

Dr yace" hjy a kugun akwai wani kashi a kugun kowani mutum mace ko namiji to dana maza ta na bata akwai ban banci na maza babu tsagu na mata da tsagu yanda idan mace tazo haifuwa wannan kashin shi zai bude shine zakiji nishi yazowa mace a daidai budewan tsagun na kashin bazai koma yarufe ba harsai d'a ya fado zai rufe, to ita Halima wanan kashin ba tsagu anata dan haka zan iya ja da kowane likita akan bazata iya haifuwa fa."

Mama tsabar haushima kin magana tayi Ummi "tace Dr dena fada duk haifuwan ta da kanta take haifan su Dr Hafeez yace"hjy kina nufin wannan ta taba haifuwa?


Ummi tace "Wanne irin tambaya ne wanan Dr muna cemaka haihuwa na uku zatayi na 2 ma yan 2 ta haifa yariyar da ka gani a gefin ta tana bacce itace yarta ta fari"


Dr Hafeez yace "Hjy ni a bincike na wanan mahaifan bai taba daukan ciki ba sai wannan asali ma shikan sa mahaifan cike yake da matsaloli dayawa da farko yana iy....... 

"dakata inji Ummi dan itama yafara bata haushi itako Mama fuuu ta fice Ummi ma mara mata baya tayi.


Dr yace "niko idan matar na ta haifu da kanta daga ranan zan bar ai kina dan bai min amfani ba."


Sude basu saya bashi amsa ba suka fice.


Suna fita wajen dakin da aka kwantar da Nabil sukace karo da su Jidda sai runjin kuka suke suna ambaton Ya Shid kar kamana haka wllh kaine gatanmu shi kawai suke mai maitawa Ummi ji tayi bata iya daga kafanta dan dama tabar Nabil cikin wani hali yana aman jini dasauri wani Dr yafito yace"wacece Ummi? Da sauri Kamal ya kamo hannun ta yace" gatanan ya farfado ne? ni nasan dama suma yayi ai 

Nabil yana gani Ummi yayi wa Dr alaman ya cire masa roban jawo nufashin da yake hancin sa dan baya iya daga hannun sa Ummi tana karanta duk addu'an da yazo bakin ta takara sa inda take kamo hannun sa tayi dakyar ya bude bakin yace "ba'a ganta ba Ummi an nemeta an rasata bansan hanyan da zanbi na samota ba Hadim ta hallakamin ita naso ALLAH ya barni naga haifuwan Hadim na daukarwa Fatima fansa bakin cikina Ummi tasha cewa nace ina son ta amma ban taba furta mata ba ina ma zan ganta ko a mafarki da nace inason ta inason ta ba a dadi, Ummi zan barmiki wasiya idan ta baiyana kice ina sonta har na rasa raina akanta karki damu da yanda take na rashin hankalin ta kigaya mata nina sani ni da ita zuciyar mu ahade yake Ummi me na yiwa Hadim ta lalata rayuwa ta bayan ni namata duk yanda take so ita fatasa na auri yariyar dan.................   




*Tofa Nabil Allah ya baka lfy amma kar ka tona asiri*馃槶馃槶馃槶


*Ya Hadim zasu kare da Dr Hafeez me tonan silili mai gani har hanji da gaske ne kashin kugunta irin na maza ne wato ba zai iya budewa ba idan tazo haifuwa wane irin matsaloline a mahaifarta* 


*Ya Aisa maman Fandau taji da taji yanda rayuwa ya juya da yarta*



*B JATTKO*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.