Free chapter · Read without an account

𝑬𝒑𝒊𝒔𝒐𝒅𝒆 23

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · AZIZAN BABA




_____________Ana ta sallar Azahar Hajja Fatu ta isa bakin kogi, masu hayar da jama'a su na zaune suna hutawa ta isa wajen, "Assalamu alaikum sannu" amsa mata sukayi, ta ce" haurawa zanyi ƙauyen can dan Allah" ɗaya daga cikinsu ne ya tashi yana zuwa bakin ruwan ya ce "shigo Hajiya mu je" dagewa tayi ta hau kwale-kwalen su ka fara tafiya, hira yake mata dake mai hiran ne.


Hajja Fatu da ba ta shi take ba, Allah-Allah ta ke kawai ta ganta gaban Malam gobe da nisa, ya na ajiyeta ta miƙa masa ɗari biyar.


Ta nemi mai machine ta hau, kamar ko da yaushe a cike gidan yake da mata, Malam gobe da nisa ya na masallaci Hajja Fatu ta isa gidan.



Sallama tayi ta na faɗin "wash! nagaji matuƙa, garin nan ba dai nisa ba wallahi" Sahura matar Malam ta fito daga kitchen ta na ta haɗa gumi ta ce "a'a lale da Hajiya mai kayan gyara ke ce tsakar ranar nan sannu da zuwa" Hajja Fatu ta ce " yauwa matar Malam naga ma layin yau da sauƙi ai" Sahura ta ce " ai ke da daga nesa kike kowa ya san ba kya bin layi, yanzu zai dawo daga masallaci ai sai ki shiga"

Hajja Fatu tayi dariya ta ce " to bayin Allah a dai yi min afuwa" Hajarta ta baje ko zata yi ciniki, wasu suka siya,Malam ya shigo kansa yasha rawani idanunsa ya sha kwalli da zabgegen carbi a hannu da gyaran murya ya shigo gidan, '"uhm,uhm" duk aka nutsu tamkar wani waliyi.



Ya shige ɗakinsa ya zauna akan buzunsa,Sahura ta ce" Hajiya shiga" 

Hajja Fatu ta tashi, ta shige ɗakin Malam, "sannu Malam" ɗago jajayen idanusa yayi ya kalleta yana  ɗaga kai, ƙwaryar da ke gabansa ya gyara,Hajja Fatu ta ce"daman malam aiki dai har yanzu babu wani ci gaba, dan abin har ya fi da, Malam gobe da nisa ya yi zane-zanensa da hannu a cikin ruwan ya jima sannan ya ɗago ya ce " ai al'amarin mijin nata yana da girma, dole sai a hankali zata ga tasirin aikin" Hajja Fatu ta ce" sai ɗansu Babban yanzu ba sa shiri shi da uban, abun dai babu daɗi, ko akwai taimakon da za'ayi wa yaron?"Malam ya ce " ƙwarai za'a samo zuciyar rago da karfatar baya ta ƙafar akuya ja, zamuyi aiki akan sa, Hajja Fatu ta ce" to Malam, sannan ina so ayi min aiki akan shi Maigidan" Malam gobe da nisa ya ce" me kika so ayi masa" cikin jindaɗi ta gyara zamanta ta ce"ina so ya aure ni" da sauri Malam gobe da nisa ya ɗago kansa, ya kalleta sai ya kuma tsafinsa, sannan ya ce" gaskiya Hajiya aikin ki akwai hatsari, in dai kin kiyaye dukkan sharaɗan da zan sa miki, za ki aure shi, kuma za ki mallake shi sai yanda kika yi da shi" Hajja Fatu ta yi murmushin cin nasara ta ce"ko mene ne malam zanyi in dai zan auri Alhaji Aminu dollars" Malam ya ce" ki samo min gashinsa guda biyar mabanbanta, zan baki wani turare bayan angama aikin zaki sha mamakin irin ƙaunar da zai miki" Hajja Fatu, ta ce " to malam wana gashi ne kala biyar mabambanta?" 

Malam Gobe da nisa ya ce " gashin kansa, da na gemunsa, da na hammanta, da na gabansa, da na girarsa ko wanne sili ɗaya" Hajja Fatu ta ce" na shiga uku, ta ina zan samo wannan?" Malam gobe da nisa ya ce "to kuwa da su za'ayi miki aiki" Hajja Fatu ta yi shiru tana tunanin ta ina zata samo wannan abu.


Ni sa wa tayi ta ce" to malam zan kawo duk yanda zanyi, zanyi dan cikar muradina"

Wani garin magani ya bata ya ce a zubawa Abdul-azeez a abinci, sau biyu za'a ba shi, sau biyu kaɗai, ku kiyaye sau biyu kawai zai ci.


Hajja Fatu ta ajiye masa,dubu ashirin a cikin dubu hamsin ɗin da Mami ta bayar.


Godiya tayi masa ta tashi ta fito, Sahura ta ce " to shigo mana Hajiya ga abinci can na sa miki" Hajja Fatu ta ce"a'a nagode Matar Malam,yanzu zan tafi zan dawo cikin satin nan ai" Matar Malam ta kwance bakin zaninta ta ɗauko dubu ɗaya ta ce" dan Allah wannan abun nake so ki ba ni" Hajja Fatu ta yi dariya ta ce" ai yau na tawo miki da hana kishiya" hannuta Sahura ta ja tana faɗin "shigo ciki dan Allah" dole ta bi ta, ta haɗa mata wasu tarkacen ta bata, inda Malam ya ke ajiya ta buɗe ta ɗauko dubu uku ta haɗa da na hannunta ta bawa Hajja Fatu.

Sallama sukayi ta fito ta nufi hanyar barin ƙauyen.


Sai yamma liƙis ta dawo, ko gidansu bata je ba, ta koma gidan Mami, Mami da take ta sa idon ganin ta dawo, ta yi mata waya a hanya yafi sau biyar, Hajja Fatu taƙi amsawa, dan tunanin inda zata samo gashin nan take.Mafita ta samu ta yi murmushi.


Siyama da pretty da Munnir suna karatu tare da lesson teacher ɗin su, suna karatu, Hajja Fatu ta shigo, 


Mami kaɗai ce a parlour'n cikin murna ta tarota ta na faɗin " ya akayi me ya ce?" Hajja Fatu ta ce"yunwa nake ji,tun da na fita ban sa komai a baki na ba" da sauri jiki na rawa Mami ta fara kiran Aina'u mai aiki. 

Da sauri yarinyar ta  tawo tana amsawa "na'am" ta durƙusa ta shiga gaishe da Hajja Fatu.

Ko amsawa batayi ba, Mami ta ce" ke kullum ba za kiyi hankali ba ko, kina ganin baƙi dole sai na ce ki kawo abinci da drinks ko?" da sauri ta ba da haƙuri ta na tashi dan kawo abinci, take ta cika center table ɗin da suke kusa da kujerar.

Sai da Hajja Fatu ta ci tayi nak sannan ta ce" ince dai ba kowa a kusa ko" Mami ta ce " kinga ta shi mu shiga ciki dan Alhaji yana gab da dawowa yanzu" 

A tare suka nufi sama, Hajja Fatu ta wara idanu tana kallon yanda tsarin wajen yake, ina ne zai zama nata ɗakin anan gaba in ta shigo gidan a saman,ɗakin Mami suka shiga.


"Ya akayi kiyi min bayani?",Hajja Fatu ta zuge jaka ta ɗauko maganin Abdul-azeez ta ce "kinga wannan maganin na Abdul ne, a cikin abinci zaki ba shi, za su daidaita da mahaifinsa, sau uku zaki ba shi, zai ƙara jin ƙiyayarsu, amma ba zai nuna ba, sau uku kacal ya ce min, ya ce kar a ƙara kuma kar a rage" Mami ta ce "to shi kuma Alhajin fa me ya ce?" ta ce" uhmm ai aikinsa babbane"

"Na shiga uku me zanyi ya ce?" Mami ta tambaya a ruɗe Hajja Fatu ta ce" wai sai an samo gashin jikinsa guda biyar" ajiyar zuciya Mami tayi tare ta sauke numfashi ta ce" mtsww wannan ne babban aiki, ai dan wannan mai sauƙi ne" Hajja Fatu ta ce " to ai gashin guda biyar aka ce mabambanta" Mami ta ce kamarya, nan Hajja Fatu tayi mata bayani, murmushi Mami tayi ta ce"angama dan wannan ai mai sauƙi ne, yaushe ya ce a koma?" Hajja Fatu ta ce" ko yanzu aka samu za'a iya kai masa ya ce" Mami ta ce "okay ba matsala zanyi ƙoƙari in yanko" Hajja Fatu ta ce "sili ɗai-ɗai za'a kai" Mami ta ce"nagane" turaruka masu kyau da turmin atamfa ta bawa Hajja Fatu ta na tayi mata godiya.


Tare suka sauko driver ta sa ya mayar da Hajja Fatu hat gida.




Tunda abin nan ya faru Abdul bai sake bari sun haɗu da Daddy ba, har washegari.

Ranar ne Daddy zai je Mazoji dan ɗauko su BABA an gyara gida ansa musu komai, ma sha Allah gida yayi kyau sosai, Mami sai yaƙe take, dake weekend ne sunday ce duk yaran su na gida.

Gaba ɗayansu sun rako shi, ana yi masa Allah ya kiyaye hanya, Munnir ne ya tawo da gudu cikin shirinsa ya ce "zan bika" Daddy ya yi mirmushi dan yau yana cikin farin ciki ya ce" to shiga mu je" Mami kamar ta daki Munnir sai harararsa ta ke a ɓoye, ɗauke kansa yayi kamar bai gani.


Abdul azeez ne ya fito ganin babu kowa a parlour'n kuma safiya ce, ko breakfast babu wanda yayi, ɗauki ya hana Daddy zama ya karya, ya ce a Mazoji zai karya.



Abdul ya ce" ina za ku je haka?" Siyama ta ce" yau su AZIZAN BABA za su dawo"

Cikin razani ya ce " wai da gaske?" Daddy ya shiga mota ya na addu'a, jiki a sanyaye Abdul azeez ya ce" Allah ya kiyaye hanya" da kansa ya yi driving suna ɗaga masa hannu.



Tafiyar 2hour suka yi, sha biyu da mintina suka isa garin Mazoji.

Tamkar gidan biki gidansu AZIZA ya yi.


Ana ganin tsayuwar mota a ƙofar gidan, yara suka hau ihun "oyoyo Alhajin BABA ya zo.

AZIZA da aka sha wanka da uwar kwalliya ta cika fuska da ɗige-ɗige da jambaki ta rambaɗa jar hodarta.


A guje ta fito ta na murna, ganin da gaske shi ne, yana fitowa ta faɗa jikinsa cikin tsantsar murna.


"Sannu da zuwa Baban birni" ta faɗa tare da durƙusawa ta gaishe shi.

Munnir ya sauko yana miƙa, AZIZA ta gaishe shi, dan Baba Tabawa ta fara saita ta, akan ladabi, shi ne ta fara dan kar ƴan birni su rainata.


Munnir da ya ga ta gaishe shi, sai ya hau dariya yana ganin yanzu shi ma ya zama babba dan shekararsa sha biyar, AZIZA goma.


Gidan suka shiga duk ƴan'uwa aka baibaye shi, ana yi masa sannu da zuwa, ɗakin BABA ya shiga suka gaisa, shi ma ya shirya tsaf da shi, ya sha shaddarsa mai masifar kyau da tsada, Baba Tabawa da Inna Gaji da suka sa atamfarsu iri ɗaya ta sallah wacce Daddy yayi musu, komai faɗa, idan za su je taro ko unguwa tare to dole a sa iri ɗaya ko da kuwa ba'a magana.


Baba Tabawa ce ta sauke shi da kunu da fanke har da soyayan naman zabin da aka yanke gaba ɗaya.


Gaisawa sukayi, da BABA da Inna Gaji wacce ta ke ƙara gyara jakar littafan BABA wanda zai tafi da su. Kowa yana cikin murna, gaba ɗaya ɗakin BABAn aka cika ƴaƴa da jikoki.


AZIZAN BABA kuwa fita tayi ta na bin gidajen ƙawayenta dan su fito su ga tafiyarsu, su A'i da Haule ma duk sun fito dan rakiya.


Gidan suka shiga su wajen biyar ƙawayen, da gudu ta shiga ɗakin tana faɗin " Baban birni ga ƙawayena" Daddy da ya ke karyawa ya amsa, da fara'a yana tambayar sunayensu duk da ba riƙewa yake ba.


Biscuits ya bayar su siya, sai murna suke.

Su Gwaggo Aliya sai hira suke da Daddy shi ne Babban yaya, yanda ya ke sakewa da su abun yana yi wa BABA daɗi, da Azahar bayan sun yi sallah BABA ya ƙara yin sallama da mutane ,suka nufi rumfar maigari, suka yi sallama, sannan suka koma gida.


Sai da Daddy ya sallami ƙannensa, aka dama fura kowa ya sha, sannan BABA ya tashi yana neman AZIZA su zo su tafi, bayason suyi tafiyar dare.


Ta na ƙofar gida ta ɗauko jakar kayanta tana ta rabarwa, cikin farin ciki, sai da ta gama rabarwa tas, yara suna ta murna, ta ga BABA ya fito yana kwala kiran AZIZA, ganin abinda ta yi, ya sa ya saki baki, cikin fara'a ta ce" yanzu zamu tafi?" BABA ya ce" yanzu kayan naki kika bayar"AZIZA ta ce" du banaso Baban birni ya ce zai siya min wasu ai" dole BABA yayi shiru.



Gaba ɗayansu suka fito, Munnir da AZIZA ne suka fara shiga mota, sai Inna Gaji da Tabawa, Daddy da Munnir ne a gaba.


Ƙofar gidan a cike su Gwaggo Aliya da maƙota ana ta yi musu Allah ya tsare, sai lokacin AZIZA da ƙawayenta suka ji kewa, ƙwallah ce ta cika musu ido, hannu suke ɗaga wa juna, bin motar akayi ɗuuuu.


Su Gwaggo Zainabu da ƴaƴansu da surukai suka gyara gidan tas sannan suka kulle, kowacca ta nufi unguwarsu.

Cikin kewar iyayen nasu..........




Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.