Free chapter · Read without an account
...27...
by Sadiya Auwal · SANADIN CACA
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:***
________________________________
*Book 1*
Chp[27]
Basan ya tashi ba saida naji maganarsa tukunna.
"Yaushe kika dawo?"
Cikin magagin bacci yake maganar.
"Uhm ban daɗe ba sosai,sannu ya jikinnaka"
"Da sauƙi kawai zance,miƙomin ruwa nasha,bakina bushewa yakeyi akai akai"
Ruwan na ɗauko na bashi,lokaci guda ya zuqe guda biyu,Wannan wanne irin shan ruwane haka,na faɗa a raina.
"Ga abinci yakamata kaci"
"Mts banajin yunwa, bar abinci nan,ki ƙiramin Tunga kice ya kawomin ajiyata danayi a jeji"
"Ba abinci bane haka,nayine saboda ina tunanin ko jikinka yana buƙata,sannan a halinda kake ciki bai kamata ka zauna da yunwa ba"
Ganin bai sake cemin komai bane yasa na jawo kular dana zo da itan,farfesun hantar na tura masa gabansa,na manta banzo da plate ba..
Matsawa kusada shi nayi ina bashi a baki,daga yanda yake karba ma tabbatar yanayimasa daɗi sosai,dan saida ya kusa cinyeshi tass.
Kofi na ɗakko bayan yagama na zuba masa shayi shima mai zafi.
"Yaushe kika waɗannan abubuwan haka?"
"Lokacin dana koma gidane,saidai kayi haƙuri na fita zuwa kasuwa da kaina,dama inason na faɗamaka saikuma na manta."
"Uhm bakomai nagode da kulawarki,bani maganin can nasake sha naga har dare yafara"
Bayan na miƙomasa yasha ruwa na zuba a buta nima nayi alwala nai sallahr magriba,kaman ɗazu yana kallona har na gama.
Sake zuba wani ruwan nayi nazo inda yake,kallon tambaya yakemin ganin na miƙamasa hannu yabani nasa hannun.
"Kawo hannunka alwala zanyi maka,yakamata ka rama sallolin da ake binka,tunda ka ɗan samu sauƙi"
"Taya kike tunanin zan iya sallah a haka?"
"Indai kana cikin hankalinka to zaka iya yin sallah,domin a kowanne yanayi mutum yake ba'a ɗauke masa sallah,saidai idan baya cikin hankalinsa. Ance idan bazaka iya a tsaye ba ka jingina,in shima bazayyi ba ka zauna,in ya gagara ka kwanta ka kalli gabas,in shima bazayyiyu ba toh zaka iya yi a duk yanda ka tsinci kanka.
To haka ma wajen yin alwala,in jikinka bazai ɗauki ruwa ba saikayi taimama da ƙasa,idan itama bazaka iya da ita ba to saika shafi jikin gini mai tsarki kayi dashi.
Toh a wannan bayanin kaga kai zaka iya yin alwala kuma kayi sallah a zaune"
Bayan gama bayanin bai ce komai ba,amma ya miƙomin hannayensa na fara yimasa alwalar. Cikin nutsuwa nake yimasa alwalar har na gama tsaff.
Rigar dana zo da itah na taimaka masa yasaka,yanda bazata shafi ciwon ba,kafin na juyashi ya kalli gabass,magriba yafarayi wacce ake binsa kafin ya fara da rama sallahr asuba tun sanda aka jimasa ciwo.
Daki daki yake bin sallahr ina zaune ina kallonsa,daga baya daya gaji sai na koma ta baynasa ina tallafamasa. Muna daɗe a haka har akayi sallahr isha ya tsaya da ramakon yayi,ganin yana haki yagaji yasa ya tsaya dayi sai ya huta tukunna.
A bayansa nake ya jingina dani,saiji nayi ya kwanto akan cinyata,kallon fuskata yakeyi,yayinda nima na sunkuya ina kallonnasa,mun daɗe a haka idonmu a sarƙafe dana juna,saida naji hannunsa akan fuskata kafin na dawo zahiri..
Magana yafara a cikin wata murya da banyi tunanin yanada itaba.
"A ɗan zamana dake kin taka wata rawa a rayuwata,ko yaushe cikin juyewa kike da narasa taya zan misaltashi. A lokacin danake son naga kin sake dani saiki ɗankware jikinki,lokacin danazo yimiki barazana kuma saiki dake,idan nayi laushi kuma sai zama jaruma,a yau kaɗai kinyimin abinda ban taba tunani ba,kin zamemin hannun a sanda na rasa nawa,kin zamemin ƙafa da tawa taƙi aiki,kin zauna dani a wannan dokar dajin da babu kowa a ciki saini kaɗai.
Tun farkon da mahaifinki yabani ke a matsayin fansar kuɗina naga rashin dacewarsa nayin hakan,shiyasa na nesanta kaina dake,a tunanina hakan zaisa kiyi rayuwarki yanda kikeso,naƙi shiga rayuwarki saboda nasan nida ke bamu dace ba ko kaɗan,amma sai naga duk wannan koƙarin danake yatafi a banza,ke koyaushe so kike ki cusa rayuwarki cikin tawa.
Wannan ƙasa da kan da kike idan kina gabana,da kuma neman izinina a duk wani lamari na rayuwarki shine yayi babban tasiri wajen karya zuciyata,har tasaka na ajiye komai na ɗauki nauyinki batareda nasani ba. Saboda tunda nake babu wanda yazo da kansa yanemi izinina akan abu,saidai na bashi dakaina in kika ɗauke Tunga.
Sannan tun kina zuwa inda nake ina jin kin takuramin,har yazamo idan banganki ba sai zuciyata tayi ta kewarki. Sumaimah bansan mai kikayimin a rayuwata ba amma dai shigarki kinyi nasarar share wani a fili a ciki kin mamayeshi yazamo naki. Ciwon kan dana tashi a rayuwata bansan lokacin dana faraba,bai taba dainawa ba indai ba shaye shaye nayi ba sai yau,kuma dama yakan tashi ne idan na bijirewa umarnin da zuciyata tabani,saikashi yau kin karanta min wani abu naji ya tafi batareda nasha komai ba"
Tunda yafara magana ban ɗauke idona ba daga kan fuskarsa,shin anya kuwa gojen danasanine yake waɗannan kalaman,meyasa yau ɗaya naga wata nutsuwa a tattare dashi,babu wannan zazzare idon da kuma cije cijen baki..wannan gashin daya maidashi dodo duk babu shi. Kar a ji haushina idan nace yayimin kyau fiyeda mutane dayawa a garinnamu.
Hannuna nasaka akan nasa wanda yake kan fuskata,tareda sakin wani murmushi da bansan ma'anarsa..
"Duk abinda kake faɗan nayi aikata a rayuwarka banice nabaka wannan matsayinba,Allah ne dakansa yabaka a matsayinka na mijina,ni kawai umarnin da aka bani na nayi maka biyayya,kada nayi wani abun batareda saninka ko kuma yardarka ba,sannan na kyautata maka na kasance sassanyar inuwar dazaka zo ka hutas da gajiyarka,na kasance tamkar dare wajen rufe sirrinka,sannan na kulada kai da dukiyarka harma da dani kaina idan baka nan.....domin aljannata tana ƙarƙashin ƙafarka,sai nayi hakanne Allah zai bani izinin shiga"
A yanda nake kallon idanuwansa lokacin danake faɗomasa wadannan Kalaman,naga Abubuwa da dama wanda wasu bazan ce mesuke nufi ba. Kawai naga yashiga mamakin,shin dama ashe yanada irin wannan matsayin a rayuwar wani,kaman nasan mai yakeson faɗa na cigaba da bayanina.
"Tabbas hakane kanada wannan matsayin a rayuwata tsawon lokacinnan,koda wasu zasu gujeka suyi nesa dakai. Ni kaiɗin jigona ne,kuma mahaɗin rayuwata,wanda rayuwata ta riga ta ɗinke da taka tun lokacin da ɗauramin igiyoyin aurenka a kaina,shiyasa duk abinda zakayi wanda bai dace ba zaifi yimana ciwo nida inna sa'banin sauran mutane"
Hawayen daya zubo acikin idona ne ya sauƙa akan kumatunsa,sai sannan ya ƙifta ido,da ya tsaya tamkar wanda ya daskare a cikin ƙanƙara.
"Shin dama har haka na shiga rayuwarki,nayi tunanin dan an ɗaura aure ban kulaki ba bakomai,to idan harda waɗannan haƙƙunan da suke kanki wanda dole saikinyimin kenan nashiga rayuwarki dayawa,na rabaki da rayuwar da kike hankalinki kwance idan babu ni a ciki..kinmin abubuwa da dama,dan haka banaso ki cigaba da zama kina amsa sunan matar mutum kamanni,musamman daya kasance kinada ilimi mai yawa da kuma sanin yakamata,zalunci ne na ajiyeki a cikin rayuwata...zan sake..........".
Kiff bansan lokacin dana rufe masa baki ba ina jijjiga kai.
"Karka fara faɗin wannan kalmar,dan Allah karka furtata a gareni,da lokacin daka aka kawoni gidanka ne ka faɗaminsu zanyi farinciki da jinsu,amma a yanzu dana fahimce ka bana fatan jin wannan kalmar daga gareka,karka faɗesu ka fiddani a cikin rayuwarka"
"To amma meyasa naga......"
"Saboda na hango wata rawa danake son takawa a rayuwar taka,hmmm bazaka sani bane amma kanada wani hali da mata zasu zaga mazaje dayawa basu samu mai irinsa ba,duk da sunaso su samu ɗin. Kai tamkar zinarene a cikin duhun dare,rana bata haskashi na ballantana a gane wanne irin haske yake ɗauke dashi.....koda babu hasken rana ka bani dama nazamo fitilar dazata haska shi,ta yanda kaikanka zaka hango irin hasken da kake ɗauke dashi......dan Allah ka yarda dani,sannan ka bani damar ragamar kulada rayuwarka,kar nesanta ni daga gareka,ta hakanne zamu gano inda matsalar take kuma mu gyara.....ni har cikin zuciyata na amince dakai a matsayin mijina,kuma bana fatan naga ranar da zanyi nadama da ƙiranka da wannan sunan"
Magana nake kawai ina kwararowa abinda yake cikin zuciyata,duk da yanda muryata ke rawa saboda yanda maganganun suka tabani.
"Tunda nake ban taba yin alaƙa da wata mace ba bayan inna sai ke,a da hakan haushi yake bani,amma d kaɗan kaɗan nakejin wani abu na mannani da rayuwarki. Yanzu ma dakikaji na faɗa bawai son raina bane,saidan zanyi hakanne saboda ke,amma tunda kinji kingani ra'ayinkine zaki zauna tareda ni. Nikuma namiki alƙawarin bazan taba guje miki ba,kuma zan kyautata miki na faranta miki daidai yanda zan iya,sannan kaman yanda kika buƙata nabaki jan ragamar dukkan lamurana"
"Naji daɗin maganar ka kuma nagode,nima kuma nayi maka alƙawarin Inshaallah bazakayi danasanin yarda dani ba"
Shuru ne ya ratsa tsakaninmu,saikuma naga ya jare hannunsa daga fuskata yana riƙe kai. A yanda na kula kaman irin abinda yayi jiyane,hakanne yasa na ɗauke hannunsa na mayeshi da nawa.
Addu'o'in danayi jiya na neman sauƙi nafara karanta masa,wanda yawanci sunayen Allah ne da yayi umarnin a ƙirashi dasu,sai fatiha da kuma su QUL guda uku.
Maimaita masa nashigaba dayi bayan naji yayi shuru ma,a haka har nima bansan lokacin da baccin ya ɗaukeni ba anan zaune.
___***___
"Me kikace abbanku ya dawo?"
Hajiya Maryam tafaɗa cikeda damuwa tana kallon fatee.
"Ehh mommy yanzunnan ya shigo gidan,naga ya nufi sashensa bai shigo cikin gidaba"
Tana cikin bayanin hajiya maryam tanufi sashennasa tana tafiyar karairaya kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƙwanƙwasawa tayi,jin shuru ba'a amsaba yasa tasaka kai cikin ɗakin.
A tsaye yake a gaban window yana kallon lambun dayake bayan ɗakinnasa,kana ganinsa kasan faɗawa yayi cikin zurfin tunani.
"Me yasamu wannan babban jarumin naganshi a haka,kaddai kacemin har yanzu baku samu inda barayin sukeba,kuma sun gudu da akwatin baku kamasu ba?"
Tafada kaman mai jin tausayinsa,amma kanaki kasan ta biyu take zancen.
Zan ajiyar zuciya A.M Aliyu yayi tareda cewa.
"Maryam,waishin yaushe zaki girma ki daina wannan abunne kam iyeee,ƴaƴan ki ma bazasuyi abinda kikeyi ba,yanda kikeyi haka kikeso ƴaƴan ki suje gidan mijinsu suyi ne? Ace tsawon sati guda ba nan ina office,duk akan wani abu daya shigemin duhu,amma daga dawowata babu magana mai daɗi sai ta izgili? Shiyasa fah banshiga gida ba bare ki ganni,amma saida kika biyoni kina murnar na faɗi koh ?"
"Uhm dagajin yanda kake magana baku kamasu ba da alama,kenan wannan akwatin dayake ɗauke da bayanai masu hatsari yana hannun 'baya gari"
Juyowa yayi yana kallon hajiyah maryam,wacce take tsaye ta dan goce irin tsayuwar celebrity ɗinnan.
"Shin wai tukunnama taya kikasan cewar kundin a akwati yake,a tunani na dai bamuyi wannan zancen dake ba,kuma ko a kafar yaɗa labarai ba'a faɗa ba,taya kika sani?"
Tsareta yayi da ido tareda yimata kallon tuhuma,wanda hakan yasaka jujjuya ido tareda cewa.
"Ehh dama zaka fara yanzu,dan kasamu ma na kula dakai nazo ina tambayarka shine zaka faramin wannan kallon rashin yardar,tun batan Ahmad kakemin irin wannan kallon na rashin fahimta"
"Ohh dama 'bata yayi ba mutuwa yayi ba?"
Gum tayi da idonta tareda nemo abinda zatace.
"Mutuwa nakeso nace,kaima ai kasan mutuwar yayi tunda har gawarsa an kawo maka. Nida wannan abinda kakemin na ƙin raba sirrinka dani kokuma kana tuhumata ka daureni mana kawai ka huta iyee. Kaje cibiyar bincike kace zaka ɗaure matarka dayafiye maka"
Masifah ta cigaba dayi,ta inda take shiga ba tanan take fita,saida tayi mai isarta ta fice daga ɗakin tareda buga ƙofar.
Runtse ido AM Aliyu yayi tareda ɗora hannunsa a kansa.
Yana jin takun tafiyarta har tayi nisa.
Shin me yayi mata kuma wai itace dayin fushi,shine ya kamata ya ɗau mataki amma duk sanda yayi yunƙurin yin hakan sai yaji ya kasa.
Gabaɗaya gidan mutane uku ne za'a ce daidai,daga Mammah,saleem sai Noor,su kaɗaine zaka gansu da sanyin hali. Amma Sameer kam da fatee kana gani kasan ita suka iyo. Shikuwa Ahmad lokacin dayake nan gwanda kowama dashi,domin ko sashensa a can gefe yake,bayason ana yimasa katsalandan,saidai kaima bazai maka ba.
Sannan yanada basira da sanin mai yake,komai shine yake zuwa a fari kafin sauran ,hakanne yasa kullum hankalin hajiyah maryam yana kansa,in za'ayi masa abu ma ita ke shiga da fita ta hana,shikansa yasan da hakan. Shiyasa ko sashenta baya taba zuwa sai yakama dole.
Kaman yadda AM Aliyu bai yarda da ita ba hakama Gen Ahmad,don daff da mutuwarsa ya buɗe wani file akan ta,tunda ta tafi kuma babu wanda yasake bi ta kan zancen har yau.
Tsohuwar lauyace mai zaman kanta,duk da yanzu bata aiki,amma kuma tasan takan binciken abinda take son sani sannan kuma da yanda zata gujewa mai son bincikarta. Tana da son mulki da son ganin ana mata hidima,don ko shi kansa AM Aliyu dayake shugaban sojoji bai kaita juya sojojin ba,kuma tanada mutanenta a cikinsu,wanda ko mai tace karsu faɗa babu wanda ya isa ya sakasu magana harda shi kansa uban gayyar.
Wannan abubuwan su suka sa kowa hatta ƴaƴan ta suke shakkarta inta juyo ta kansu inka cire Ahmad shikaɗai ne baya tsoronta,kuma shine ciwon idon dayake hanata bacci lokacin dayake raye,yanzu kuwa da baya nan baccinta take sha harda minshari.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
***
VTU ta nan
2347068390570
Shaida kuma ta nan
***
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh
***
Share please